Showing 162001 words to 165000 words out of 200116 words

Chapter 55 - A RUBUCE TAKE (KADDARATA)

zanin gadon ya kwantar dasu,ya duba laundry basket dinsu da yake cike taf da kaya da uban bedsheet dinsu masu kyau da tsada,amma sunyi datti kuma bata da lokacin da zata tsaya ta hadasu ta zagaya baya inda washing machine yake ta wanke ba,ko ta bayar wa sale yaron gidan ya wanke su ba

"Allah ya sawwaqe" ya fada a fili,yana raya a ransa gobe zai zauna da kansa ya gyara musu dakin nasu ya fidda kayan ya bayar a wanke musu kafin ya koma,don yaci alwashin ya daina mata gyaran sashe,tunda abun nata sake ci gaba yakeyi.

Kafin ya fito ta hattama wayar,saita sauke qafafunta dake saman center table tana fadin

"Sannu da zuwa"

"Yauwa" ya amsa sama sama yana zama hannun kujera,yayi imanin zaiyi wuya ya zauna cikin kujerar baici karo da danshin ruwa lemo ko fitsari ba

"A kawo maka abinci?" Ta tambayeshi tana danna waya,sai ya girgiza kai sannan yace

"Ajjiye wayar nan zamuyi magana" dan kallonsa tayi sannan ta aje wayar tana kallonsa

"Nace shekararmu nawa yanzu da aure?" Dan jim tayi sannan tace

"Kamar shida cikin ta bakwai"

"Good......me yasa har yanzu kika kasa fahimtar zahirin rayuwa hafsa?,me yasa har yau kika kasa gane kina tafka kusakurai da hankalinki ya kamata ace yakai kai kin kuma gyara" fuska ta bata sosai

"Wanne kuskure kuma nayi?,wai don Allah me yasa bakason zaman lafiya abban mimi?" Da ido ya tsareta,saita kauda nata idon daga kansa,ta sani nashi idanun yafi nata kaifi nesa ba kusa ba,ta hade rai sosai,ya janye idonsa yana miqewa hadi da saka hannunsa a aljihun wandonsa yana kallonta,baisan me yake damun kanta ba,gidadanci ne ko rainin wayo?,komai ka gaya mata ba zata gane ba, batasan maslaha ba batasan fada ba,duka dai dai take daukan kowanne,tunda taqi fuskantar alqibla,bari ya bita da zafi zafi tunda ya fahimci tafi ganewa hakan

"Tunda baki ganewa kuskure ko laifi......fine,gobe banason na tashi na samu wannan tulin qazantar dake sassan nan,idan ma ke tana miki dadin zama ne a cikinta,to karki sake na samu daki da jikin yarana a yadda na sameshi yau" ya qarashe maganar a zafafe,sannan ya juya da dan hanzarinsa ya fice daga sashen.

Kamar idanunta zai fado saboda kallon data bishi dashi,kallon da inda yana tsaye ne a gabanta bata isa tayi masa shi ba,taja dogon tsaki kamar zata tsinke harshenta,ta rasa wanne kalar miji Allah ya hadata dashi,taurin kai kafiya da kuma tsatstsauran ra'ayi,dole ta tattare komai.nata ta wuce daki,gwara ta kwanta da wuri ko ta samu ta tashi da wuri ta gyara iya abinda take ganin zata iya,a goben ma idan widad din bata dawo ba to tabbas zata dauki mota taje ta daukota da kanta ta dawo da ita cikin ruwan sanyi da kwantar da kai,ta yadda babu wanda zai fahimci manufarta.

**********Ranar lahadi,ranar daya zamana saura kwana guda suraj da matarsa suzo,yana gida ranar,don haka duk wasu ayyuka shi ya kama mata sukayi tare,suka gyara kowanne daki yadda zai dace da zaman kowa a cikinsu.

Dakinta ne na qarshe,sun gama komai tare,ta tsaya hannayenta riqe a qugunta tana kallon yadda ya sauya fasalin dakin tana murmushi.

Sanda take kallon dakin shi kuma ita yake kallo,wani short rubber wando ne a jikinta,wanda da kadan ya wuce gwiwarta,sai kuma rigar kayan mai gajeran kayan data fidda shape dinta sosai.

Da wani siririn rubber band kalar kayan jikinta ta daure gashin kanta,hakan ya baiwa doguwar jelarta mai santsi damar reto a bayanta.

Kusan yaune ranar farko data fara irin wannan shigar saboda aikin da zasuyi,amma iya yau din gaba daya ta hanashi sukuni,duk inda ta motsa idanuwanta suna biye dashi

"Finished uncle" ta fadi tana dubansa tana murmushi,sai ya mayar mata da murmushinta,yanason ya gaya mata ta debi wasu kayan nata da zatayi amfani dasu ta maida dakinsa amma kuma bayason plan dinsa ya rushe,gwara ya barta a hakan,sannu sannu bata hana zuwa.

*W A S H E G A R I*

K'arfe uku na rana su suraj suka iso kaduna,bilkisa matar suraj akwai fara'a kirki da kuma saurin sabo,tun ba yau ba suna hira sosai da widad din ta watsapp,wannan yasa ba wani baqunta can me yawa a tsakaninsu ba.

A nan falo suka zauna bayan abbas ya shiga musu da kayansu ciki,suka koma balcony din sashen suka zauna sukabar su widad din a falo.

Basu rufa mintuna ashirin ba aka kira sallar la'asar,saida dukkansu suka bada farali sannan suka zauna zaman cin abinci,su suna balcony din saman lallausan carfet,ita da bilkisa suna zaune a falon,suna ci suna taba hira.

K'arfe takwas na dare ta shigo dakin da bilkisa ta sauka,rigar bacci ce a jikinta wadda ta sauka har kusa da idon sawunta,saita dora hijabi a kai wanda bai wuce qugunta ba.

Da murmushi bilkisa dake gaban mudubi tana fa shafe shafen turaruka ta waiwayo tana amsa mata,widad ta qaraso tana hayewa saman gadon gami da jan pillow

"Na zaci har kin kwanta" kai ta girgiza

"Ina ni ina bacci mai gidana bai dawo ba" qaramin murmushi widad ta saki tana rayawa a ranta

"Kamar wani qaramin yaro" duk da cewa ita dinma tun dazu take leqawa ta window idan taji motsi taga ko uncle din nata ne,tunda suka fita bayan sun gama cin abinci basu dawo ba.

Duk da sun sha hira sosai da balkisa,ta kuma debe mata kewa amma sai takejin gidan gaba daya wani iri babu dadi

"Nima har na fara jin kamar bacci bacci" ta fada tana maida pillow din saman gadon zata kwanta,sai bilkisa ta juyo da sauri tana dubanta

"Aah.....shi kuma abbansu ahmad din na kaishi ina?"

"Zasu kwana tare da uncle fa" ta fada adan shagwabe

"Aah wlh ban gayyato ki ba,haka kawai kisa nayi baqinjini wajen yallabai yana ganin mutuncina?,daga zuwana na rabashi da amaryarshi"

"Mom Ahmad wallahi kema kin faye tsokana" widad ta fada tana gyara kwanciyarta,bilkisana qoqarin saka wandon sleeping dress dinta tace

"Banda quruciya dake dawainiya dake..... yaci ace kin karanci irin kallon da yake binki dashi duk sanda kika gifta ta gabanshi,ina tsoro nan gaba kada yallabai ya fara tafiya yana kiran sunanki,idan haka ta faru kam hafsat inajin hadiyar zuciya zatayi ta mutu"

"Kai mom Ahmad kai anty bilkisa" widad ta fada tana dariya sosai,don ita dariya ma maganar ta bata

"To ita kuma mommy hafsat me zai sakata mutuwa don kawai uncle na kiran sunana?" Tambayar data sanya bilkisa maida dubanta sosai ga widad,da alama dai har yau batasan wace kishiya ba,batasan kuma kishi ba,uwa uba batasan wace hafsat sani na badini ba,kallon zahiri take mata

"Kishiya irin hafsat ba zasu taba son suga miji irin uncle dinki.yana sonki ba,ba zasu taba so suga kina masa wani abu da zaiji dadi ba"

"Amma mom ahmad,ni bata taba nunamin komai ba" kallonta sosai ta sakeyi

"Ta gama yi miki komai din ai ba tare da kin ankara ba,saboda tasan ba lallai tunaninki ya kawo miki komai ba a kai" Shuru widad tayi tana juya maganar,zancan da suka taba yi da anty madeena ya dawo mata sanda take gaya mata ba gaskiya bane abinda hafsat din ta dinga gaya mata tana tsoratar da ita,to me hakan ke nufi?,wannan shine kishin?,idan kuwa shine yafi kama da HASSADA kawai

"Idan kina tantama daga yau ki sake mata dukkan aikin da kike mata.....ki kula da uncle dinki,don nasan har yanzu idan ta samu dama sakaki aiki takeyi" maganar bilkisa ta saka widad a tunani sosai,kafin tace komai muryoyinsu sun bayyana a falon alamun sun dawo.

Tare suka fita da bilkisa din,saidai suraj din kawai suka samu yana shirin shigowa ciki,dole widad ta yiwa bilkisa sallama ta wuce nasu dakin.

Ta tura dakin ta shiga,baya ciki amma ga kayanshi nan saman gadon,sai ta qarasa a hankali ta debesu,ta ninkesu sannan ta zubasu a laundry basket,takalman ma tayi musu waje,sai ta koma kan sofa bed ta zauna ta kunna data dinta ta shiga watsapp tana duba saqonni.

Qofar bandakin ya bude ya fito,daure da towel da ya daurashi daga qugunsa,duka duka tsahonsa kuma iya gwiwa,duk wata qirar jikinsa ta bayyana a waje sosai,qaqqarfan jiki daya ginu da excercise.

Bata zaci a haka ya fito ba....wannan yasa ta daga kai,saidai suna hada ido tayi saurin maida idanunta kan wayar tana raba idanu.

Karamin murmushi ya saki,har cikin zuciyarsa yana jin dadin yadda ta kasance,amma a fuska bai nuna ba,yadan basar duk da yadda taketa fusgar hankalinsa,don already ta cire hijabin ta ta ajjiye don tasha iska,yadda ta nannade gashinta yayi masifar jan hankalinsa.

Sannu da zuwa tayi masa tana ta babbasarwa,ya amsa mata yana janta da hira,yayi kaman bai gane ba,ya tsaya gaban madubi yana shiryawa yana satar kallonta ta ciki,cikin dace ya dinga kamata itama tana satar kallonsa,amma duk sanda ya gani din saita bagarar,abin ya dinga bashi dariya sosai,amma ya dinga cinyewa cikin miskilancinsa,har ya gama shirinsa tsaf cikin dakin ya kuma zauna ta zuba masa abinci ya soma ci.

Yana cin yana kallonta da lumsassun idanunsa har ya kammala,cin abincin da da wankan sun ja masa kusan awa biyu,zuwa sannan jikinsa ya gama saki,gaba daya muradinta yakeyi,sai ya miqe,ya zare kayan jikinsa,yabar iya boxer kawai,ya koma saman gadon ya kwanta rub da ciki yana lumshe idanunsa.

Shuru ya ratsa dakin,sai ya bude idonsa a hankali ya zube a kanta,daga yadda take zaune yasan itama kwanciya takesonyi amma tana shakkar rabarsa

"Baby...." Yayi kiranta a tausashe,muryarsa can qasan maqoshinsa,saita daga fararen idanuwanta ta kalleshi, idanunsu suka gauraya waje daya,wani abu taji ya taba zuciyarta sosai

"Am very tired........zo kiyimin tausa please baby" ya fada yana narkewa hadi da yin fuskarsa tausayi,idanunsa suna lumshewa saman fuskarta,yana jin kamar yakai gareta ya fusgota.


*H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*


Page 84


Yadda yayi din sai ya bata tausayi,don haka ta ajjiye wayar tana cewa

"Wai tausa da dadi ne?" Dariya ta taso masa amma a yanayin da yake ciki batayi wani tasiri ba,ya maye gurbin ta da murmushi don ta bashi dariyar sosai can qasan ransa

"Sosaima" ya furta a hankali yana lumshe idanunsa sanda tattausan tafin hannunta ya sauka a tsakiyar bayansa.

Tun tana dari dari har ta sake,ta dage ita bilhaqqi da gaske tausa take masa,yayin da idanunsa suka kasance a rufe,yana jin yadda hannuwanta ke kai komo a bayansa,shi kadai yasan abinda yake ji cikin ruhi da gangar jikinsa.

Kasa daurewa yayi,cikin wani irin zafin nama yayi mata wani irin juyi ya maidata gurbin daya tashi shi kuma ya maye nata gurbin ta hanyar mamayeta gaba daya,hadi da yi mata rumfa da mayalwacin qirjinsa.

Tsoro ya gani a rubuce cikin idanunta,ta soma rarrabasu tana kallon gajiyayyar fuskarsa dake cike da shauqi da mayen so da qaunarta,da kuma burin kasancewa da ita.

A tausashe ya rungumota cikin jikinsa,fatarsu ta hade guri guda,dumin jikin junansu ya gauraye waje daya,ya sanya kansa cikin wuyanta ta soma gaya mata wasu kalamai da suka saukar mata da nutsuwa,suka kuma sakata narkewa a wajen ba tare data sake qwaqwqwaran motsi ba.

Cikin salo da kuma qwarewa ya fara aike mata da wasu saqonni da dukkan jikin da jini ke gudana a cikinsa zaiyi wuya ya tsallake musu,saqonnin da suka dinga bin dukka wata jijiya dake aike da tunani da kuma tantance abu suna tsinketa,suka dinga dilmiyar da ita zuwa wani bigire na daban,bigiren da dukka wani tsoro nata ya gushe yayi nasa waje.

Saida komai ya kankama sannan ta fara gani kuskuren data tafka,tuni aikin gama ya gama,ya sake tabbatar wa zuciyarsa da gangar jikinsa cewa ita din mallakinsa ce halak malak.

Kamar wancan karon,wannan karon ma yanayi ya shiga sosai,ya riqeta sosai cikin jikinsa yana sauraren siririn kukan da take fitarwa,wanda kusan fiye da rabinsa shagwaba tafi yawa a ciki,yasan yau dinma dole zata jigata ta kuma ji jiki,don shi kansa yasan halinsa ta wannan fannin,amma kuma bazai kai karonsu na farko ba,baiji komai ba ya biye mata ya dinga lallashin abarsa,yana kuma dauke kowanne hawaye nata da harshensa.

Jinta yake takai masa ko ina,koma meye zai iya yi mata,haka ya lalace wajen rarrashinta.

Har sukayi sallar asuba suka idar taqi duban fuskarsa,ta gaidashi kanta a qasa,ya saki murmushi,ya matso kusa da ita ya zauna sosai har gwiwoyinsu suna haduwa,yasa hannu a hankali ya janye hijabinta baya,kyakkyawar fuskarta ta bayyana,ya sanya hannu ya kamo tafin hannunta ya saka cikin nasa yana ci gaba da kallonta

"Fushi ake dani baby?" Ya tambayeta yana narkewa kamar shima zai sakar mata kukan,kamar jira takeyi ita saita rigashi,ta sakar masa nata kukan qasa qasa

"Ba kaine ba......shine ka yimin wayo,saboda kaga ka girmeni" tayi maganar tana mele baki,kaman zaiyi dariya amma sai ya danne

"Am sorry,nima fa ba'a son raina ba,bansan nayi ba sai daga baya"

"Kuma fa gidan nan kasan akwai baqi,yanzu idan mom ahmad ta gane me zance mata?" Dariya sosai ta sake kamashi kamar yayi me,amma ya tabbatar idan yayita yanzu zai jama kansa jagwal

"Waye yace miki ana ganewa?, ba'a fa ganewa kayi,kuma ma....." Sai yayi qas sosai da muryarsa,ya sake matsowa da fuskar sa dab da ita kamar zai shige cikin hijabin

".....kowa yanayi,itama nasan sunyi jiya......." Bata barshi ya qarasa ba ta cure waje daya cikin hijabinta

"....don Allah uncle" a wannan lokacin kasa boye dariyarsa yayi,ya dora fuskarsa saman qafafunta yayi dariyarsa sosai yana jin nishadi yana wanzuwa a rayuwarsa.

**********Sati guda daya rak amma dai dai yake da wasu shekaru a wajensa,sati guda daya daya canza rayuwarsa da tunaninsa,tayi wani mugun tsayawa cikin rayuwarsa,ta kuma barma zuciyarsa wani babban tambari da yakejin har duniya ta nade bazai taba goguwa ba.

Jinta yake sosai a ransa,wani irin ji da yake ratsa zuciya matuqar ratsawa,tattali qauna da soyayya yake nuna mata irin wadda idanuwa basu saba gani ba,wasu abubuwan shi da kansa baisan yana yinsu ba,ta mantar dashi dukka wata damuwa tasa da matsalar da yakejin yana ciki.

Duk da bata gama sakewa dashi gaba daya ba,amma zai iya cewa ya samu fiye da rabin abinda yakeso,ya sani cewa da zarar ta sake sanin darajarsa ta kuma sake hankali da wayo,zai shiga sahun mazan da sukayi sa'ar matana aure a duniya,wani irin qauna da kimar hajiyarsa ke sake kwaranya a zuciyarsa,uwa uwa ce......uwa daban take,ashe irin wannan take ta kwadayin samar masa shi yasa ta dage cikin qanqanin lokaci sai data shigo da widad din cikin rayuwarsa?.

Ta fannin widad din ta sake zama wata tabararriya ta gaske,shagwabarta take zubawa yadda taga dama,biye mata yakeyi,ta koma tamkar su mimi,ko tari tayi sai ya tambayi ba'asi,duk wani koke koke da take masa a duk sanda ya samu yadda yakeso sam basa damunsa,yasa hannu ya karbe ya kuma shnaye dukka rigimarta,hasalima shagwabarta na daya daga cikin abubuwan dake saurin kunnoshi da rura wutar soyayyarta a zuciyarsa,wannan ya sake haifar da shaquwa tsakaninsu shi da ita,duk da har a lokacin yana tantamar tasan kalmar so?,abu na qarshe da yakeson ya gina gini mai ingancin da bazai rushe ba cikin zuciya dama rayuwarta gaba daya.

A qarshen watan ya gama yanke shawarar meye mafi girman tukuci da zai bawa rayuwarta?,yana tsaka da wannan tunanin saiga kyautar kujerar hajji har guda biyu daga wajen tsohon governor ya bashi kyauta,yayi masifar jin dadin aiki da abbas din,kuma har yau yana yaba masa,wannan yasa time to time yake tabo abbas din,inda tason ran Excellency dinne da tuni abbas din ya koma aiki qarqashinsa,saidai shi bashi da wannan interest din,dole ya haqura ya qyaleshi,amma lokaci lokaci yana taboshi akan wasu harkokin tsaro da suka shafeshi,kamar yanzun da zaiyi tafiyar,yaji ba wanda ya dace ya tafi dashi da yafi abbas din.

A lokacin babu wanda yaga ya dace da wannan tafiyar sai widad din,don haka ya karba daya yasa sunanta a daya ba tare da tasan ma da kujerar ba,aka soma processing na tafiyar,wadda zasu yita ne in group cikin tawagar his Excellency din.

Cikin sati na gaba suka shirya zuwa bauchi,tun bayan zuwan da sukayi suraj da matarsa sukazo musu basu sake zuwa bauchi ba sai a yanzu.

*********Karon farko data zauna ta hadawa abbas din kayan tafiya bauchin,a lokacin ya fita office,baisan ma ta hada din ba,sai daya dawo daga aiki,ya buda akwatin,ya jima tsugunne yana kallon luggage din, murmushi yana kubce masa,yadda ta shirya masa komai kamar shi da kansa ya shirya kayan nasa,ya girgiza kai ya miqe yana jin qaunarta tana sake ninkuwa cikin ransa,tasan buqatarsa,tasan choices dinsa tun yanzu.

Kai tsayr toilet ya shiga ya gama wanka ya fito,yana tsaye gaban mirror yana tsane ruwan wankan dake jikinsa,wanda ke fidda qamshin daddadan turaren wankan daya cakuda dana shower gel dinsa,fuskarsa yake kalla,cikin kwanakin har wani canzawa yaga yayi,kuzarinsa ya qaru,kamar yadda yaga yadan sake cikowa,fatarsa kuma ta qara haske kamar mai amfani da wani mai na daban.

Ana taba qofar ya maida idanunsa ga bakin qofar,ya kasa ya tsare yana jiran shigowarta.

Da sallama ta shigo cikin siririyar muryartan nan,sanye take da wata fara sol don smoked gown,kanta babu dankwali sai farin ribbon data matse sassalkan gashinta,fuskarta fes yau babu digon komai saina man lebe da ya sanya siraran lips dinta suketa qyalli,ba shiri ya saki comb din ya waiwayo harde da hannayensa a qirji yana qare mata kallo.

Shigar yau ta fidda asalin tushenta wato larabawa,kamar diyoyin larabawan da suka samu kyakkyawan kulawa,rigar ta karbeta,haka gyaran data yiwa gashinta wanda gaba daya wani abune da bilkisa ta koya mata kafin su tafi

"Bakison kiga uncle din yafi ji dake akan kowa?,to haka zaki dinga yi,ma sha Allah,inda nice da wannan jikin naki da wannan gashin.....ai da tuni na kori hafsat" ta fada tana qyalqyala dariya,don dama sam babu jituwa tsakaninta da hafsat din,duk da amintakar dake tsakanin mazajensu, bilkisa bata daukar raini ko wulaqanci,hakanan dama tun usul ita bata jituwa da marowacin mutum,wadan nan siffofi kuwa dasu hafsat tafi shuhura,wannan dalilin yasa matan abokansa da suke manyan mutane masu manyan muqamai iri daban daban a gwamnati suka janye jiki daga matarsa da gidansa,don babu wadda kejin dadin mu'amala da ita,idan sunzo gidan sai dole,kamar haihuwa da sauransu.

Dukka hannayensa ya bude mata,yana mata alamar ta taho,saita tsaya daga bakin qofar ta noqe kafada

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login