Showing 147001 words to 150000 words out of 200116 words

Chapter 50 - A RUBUCE TAKE (KADDARATA)

qaramar jaka a kafadarta tana qoqarin yane kanta da kyakkyawan mayafin daya dace da kayan jikinta.

Zuciyarta ce ta tsinke da irin kyan da yarinyar tayi,zuciyartata ta fara rawa,ta kuma fara ayyana mata tsaiwar da yayi widad din yake kallo,saita tsaya cak,ta fara raba kallonta tsakanin fuskokinsu su biyun,gabanta yana luguden faduwa.

Fes yake kallon widad din kansa tsaye ba tare daya nuna kara ko alkunyar wanzuwarta a wajen ba,abinda ya sake dimautata kenan,bakinta har rawa yakeyi sanda jefa musu tambaya kamar wasu 'ya'yan cikinta

"Ina kuma zaku da safen nan.....naga har kun shirya" maganar ta ta tuna masa inda zasu,ya sauke hannayensa dake goye a qirjinsa yana daukar mimi da tafi kusa dashi ya juya zuwa waje yana cewa

"Ki sameni a mota,rana tana yi" da kallo hafsat din ta bishi har ya fice,saita dawo da dubanta ga widad,kamae zatayi kuka saboda wani malolon kishi daya riqe mata wuya

"Izinin wa kika nema da zaki shirya fita unguwa?kin fara rainani fa widad,ki shiga hankalinki" karon farko da taji maganar banbarakwai,tunda dai ita ce mata akayi ta tambayi abbas ne a duk sanda zata fita bawai hafsat ba,to amma tana jin shakkarta ba zata iya tsaiwa mata bayani ba,don batason fada ita sam a rayuwarta.

Hon din motarsa ya hana kowa a cikinsu magana,da wannan yake maka sign idan yana jiranka,duk da haka sai hafsat din ta kalli widad a gaggauce

"Ina zakuje?"

"Gidan hajiya"

"Shine kika saka wadan nan kayan?,bana gaya miki ki dinga killace kanki ba karki bari ya dinga ganin tsiraicinki?" Ta fafa gajiya da soki burutsun hafsat,ita kawai so take taga ta fita a gidan

"Aiba haram bane,tunda miji da mata ne ni dashi" ta amsa mata ba tare da kawo komai a zuciyarta ba,tunda dai tasan da wannan salon anty madeena tayi mata bayani.

Mummunar faduwar gaba ta saukar mata,yaushe yarinyar ta fara fahimtar kalmar MIJI da MATA?,lallai akwai qura,liqi yana shirin balle mata kenan,kasa ce mata komai tayi,saita juya kawai ya fita,widad din ta bita da kallo,akwai abubuwa da yawa.na mommy hafsat din dake bata mamaki,takowa tayi ta kulle sassan nata ta wuce zuwa motar tasa.

Ranar wuni tayi ta kasa zaune ta kasa tsaye,daga qarshe ta dauka waya ta kira anty ummee don ta labarta mata,kiran duniya wayar taqi tafiya,sai taji tana ds buqatar fita taje gidanta zaifi mata sauqi,wannan ya sanya ta yita kiran abbas ta gaya masa zata fita amma bai dauka ba,ashe yabar wayar cikin mota.

Ta kuwa cika tayi fam,zuciya ta dinga raya mata suna can suna holewarsa da yarinyar,lallai biri yayi kama da mutum,ba banza ba yarinyar ke iya kallon qwayar idanuwanta ba ta maida mata magana haka gatsal.

Ji tayi kamar ta rataya mayafi ta fice abinta,to amma tana shakkarsa,tasan ko zai dauki komai banda wannan,bazai lamunta ba,haka tana ji tana gani ta haqura da fitar,taci gaba da kiransa amma saita daina shiga ma daga qarshe.

Basu dawo ba sai dare,suna isowa kuma fa shige sassanta ta kulle abinta,abbas din ya bita da kallo, quruciya har yanzu taba dawainiya da ita ba ruwanta da zancan yau kwananta nw,baya mantawa akwai ranar da a gaban hafsat din ya zolayeta akan a sassansa zata kwana,kamar zata hadiyi zuciya haka hafsat taji amma ta dake tana tuna wasu daga cikin karatuttukan anty ummee,ta dake tana tayashi tsokanartata akan anan zata kwana, qarshe sulalewa tayi ya gudu abinta.

???????Tun daga wannan ranar ya zamana fiye da rabin weekend dinta agidan hajiya takeyi,wani lokacin tun a hanya taje cewa ya wuce da ita,sai ya wuce gida bayan ya ajjiyeta,baya musu, saboda hakan shi kansa yana faranta masa rai,saboda yadda take nunawa hajiyan qauna da kulawa,ita kanta hajiyan hakan yana mata dadi,don duk sanda widad din tazo saita gaji da kala kalar girki,saiya zamana shi kansa zaiyiwu wuya baka sameshi a gidan ba,a nan zaici abincin rana har na dare,kai wani binma da safe yake fitowa da jallabiya yazo yaci breakfast ya koma hafsat din na bacci,idan taga bai nema abinci ba saita share taci gaba da sabgarta tana ganin sauqi ta samu.

Abu daya ke qonawa hafsan rai,yadda widad din ke guduwa tana barinta da tulin ayyukanta,tuni ungulu ta koma gidanta na gargajiya,qazanta sai wadda ta qaru,saboda gyaran weekend din data qwallafa rai akansa yanzu ba samuwa yake ba,idan widad ta shigo gidan sai daren da ana ya gobe zasu koma kaduna.

*_MAFARI RAYUWA DA SOYAYYA_*


Tun daga daren jiya daya daukota daga katsina gidan mahaifiyarta,har kawo yanzun da yake shigowa gidan jikinsa gaba daya baya jin dadinsa.

Ya jima a parking space bayan dawowarsa daga aiki,yana zaune cikin mota,shi bai shiga ba shi bai fita a motar ba,daga nan inda yake yana iya jiyo daddadan qamshin turaren wutarta daya zama tambarinta,qamshin da duk sanda zasu bar kaduna zuwa bauchi yake kewarsa,haqurinsa ya fara gazawa,yana dab da hanata weekend gidan hajiyan,tunda ko ba komai idan tana gida,iya qamshinta kawai na saukar masa da nutsuwa.

Cikin tattara qwarin gwiwar sa ya buda murfin motar ya fito,dai dai sanda ake qwala kiran sallar magariba a garin kadunan,sanye yake da uniform dinsa masu matuqar daraja da kuma qara masa kwarjini,yana iya hangen mai gadin gidan amma ya ratse yayi kaman bai ganshi ba,saboda yana jin kamae qafafuwansa ba zasu daukeshi ba.

Da sallam ya shiga parlor din,dai dai sanda take fitowa daga kitchen dauke da wani tray data jera lemon zobo da abarba data koya ta gwada,ya kuma bata ma'ana sosai har fiye da yadda ta zata.

Murmushi ne shimfide saman fuskartata,batasan dalilin da ya sanya kwata kwata batajin dadin gidan ba har sai sanda ya dawo,yayin da abbas din ya zube mata.manyan idanunsa yana kallonta,qafafunsa.na sakeyin laushi kamar bazasu iya daukarsa ba.

Sanye take da wata baqa wul din gown wadda kwata kwata tsahonta iyakarsa qasan gwiwarta,hannunta gajere ne don kana iya hangen hammatarta da kuma tundun qirjinta da cikar da suka fara yasa suke bayyana kansu.

Kanta babu komai sai lallausar sumarta baqa sidik mai laushi data yiwa kalba guda daya tak a kan nata,jelar ta sauka gadon bayanta taba reto,zata tsammaci relaxer ta sakawa kan nata.

Tray din ta ajjiye,saita fara takowa gabansa tana juyawa gaba da baya

"Uncle kalla ka gani,nayi kyau?,don Allah kwalliyata ba tayi kyau ba?" Ta fada bilhaqqi har cikin ranta tanason yace tayi kyau din,saboda ire iren kaya ne da mamarta mahaifiya ta hada mata su masu yawa da kyan gaske bayan ziyartarta da tayi,tsaraba tayi mata mara iyaka,don bata samu halartar bikinta ba,hasalima sai ana gobe daurin auren widad din ta sani,wannan yasa tayi fushi kwata kwata ta koma gefe,saidai zuwantan yasa tayi mata kyakkyawar tarba,ta kuma hada mata nau'in dukka wani kaya da tasan uwa zata yiwa diyarta,ta hada da nasiha mai kama da hannunka mai sanda

"Kar na sake jin sirrinku ya fito keda mijinki,idan ba haka ba zamu bata dake,kome ya umarceki kiyi kiyishi indai kinaso muci gaba da shiri" a duniya idan akwai abinda ta tsana wani yace sun b'ata,waninma mahaifiyarta da take mata wata irin qauna take jinta har ranta.

Bai ankara ba har ta iso gabansa,juyi daya tak tayi ta fada jikinsa,sai ta riqeshi tana dariya dariya

"Uncle.....ba kace wannan rigar ba zata yimin kyau ba?,shi yasa itama na gwada maka ka gani.....bakace komai ba" ta furta tana tsareshi da ido.

Tuni maqoshinsa ya bushe,ya tattaro yawu ya hadiye yana dan ja da baya

"You look so good baby doll" dan tsalle ta saki a jikinsa tana cewa

"Thank you uncle" cikin dabara yadan ja baya yana zare jikinsa saboda yadda yaji jikinsa ya fara dauka gaba daya,saita sake matsowa ba tare data lura da yanayin da gake ciki ba tana karbar jakar hannunsa

"Sannu da zuwa,na manta" ta fadi tana dariya sannan tayi gaba tana cewa

"Yau wani kalan abinci nayi maka,mommmy ce ta koyamin,tace irin abincinmu ne idan mun dawo nayi maka" duk maganar da takeyi yana tsaye cak yana kallon yadda qugunta yake juyawa ta cikin rigar,kusan rabin bayan rigar an debeshi,farar fata cikin baqar riga......abun ba qaramin qaawa yake bayarwa ba.

Kasa riqe kansa yayi,har jikinsa yake jin bazai iya jurewa ba,saiya ja baya a hankali ya fice daga falon salin alin,sai waiwayowa tayi taga wayam,mamaki ya cikata,tahau kiran sunansa tana leqawa dakinsa,har nata dakin zuwa kitchen bashi anan,saita koma saman kujera ta zauna tana hawaye,me yasa zaiyi mata haka?,ta gama wahalar shirya masa abincin kuma kawai saiya fita bai gaya mata ba?.

Tana qananun hawayenta ta miqe ta shiga daki itama ta daura alwalar sallar magariba ta tada sallar,tana sallar tana goge qwalla.


*H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*

Page 76

Tunda akayi sallar magariba bai motsa ba a masallacin,yaci gaba da zama yana sauraren masu karatu dakeyi tsakanin magariba da isha'i,idanunsa a lumshe amma ita yake hangowa a ciki,yasan dai yau zaisha daaru da qorafi,to amma hakan yafi masa sauqi akan abinda zaije yazo,a yanayin da yake ciki yasan ko hafsat saidai idan zata nuna juriya ne kawai,bawai don qarfinta zai iya dauka ba.

Har aka gama karatun aka yi sallar isha'i ba abinda ya canza,ya kalli agogo tara saura na dare,yasan a yanzun tana shirin kwanciya saboda akwai makaranta gobe,sai ya tashi yayi Shafa'i da wutiri sannan ya baro masallacin,bai koma gidan ba sai daya biya ya siya fruit.

Tana lafe cikin kujera tana qananun hawaye,ga kukan mage daketa zarya yau tsakanin sassansu da ainihin main gidan,ya tura qofar da qaramar sallama maqale a bakinta,ga mamakinsa sai ya hangeta cikin kujerar,yayin da ganinsa ya bata qwarin gwiwar miqewa da gudu tayo wajensa,tana zuwa ta fada jikinsa ta sakar masa kuka

Lips dinsa ya cije,ya dora hannunsa saman sumarta dake tsole masa idanu tun shigowarsa ta dazu yana shafa sumar daga saman kanta har zuwa inda jelar kalbar ta tsaya,bakinsa ya kasa furta komai,sabosa yadda komai ya dawo masa sabo bayab kasancewarta cikin jikinsa.

Sun jima a haka,yanata karbar feelings yana mazewa har zuwa sanda ta lafa da kukan

"To mene na kukan?" Cusa kanta tayi a qirjinsa,itama qamshinsa yana qayatar da ita,sai data tura baki gaba kamar yana kallonta sannan tace

"Ba kaine ba,na dade inata shan wahala,nayi maka girki kuma daga shigowa saina nemeka na rasa"

Murmushi ne ya subuce masa,ya hadiyi yawu da qyar sannan yace

"That's all?" Kai ta gyada masa a hankali

"To ya isa,yanzu bari nayi wanka nazo naci abincin,ai bance bazanci ba ko?" Hakan daya fada yayi mata dadi,ta rakashi dakin ta hada masa ruwan wankan da kanta,amma sanda taga ya fara balle botiran rigarsa saita miqe zata gudu.

Hannu daya yasa ya dawo da ita gabansa,ya futa tsaho sosai,saiya sake janyota zuwa jikinsa suka hade waje daya,ya bata saman qafafunsa ya taka,hakan ya qara mata tsaho,yana riqe da ita da hannu daya,daya hannun kuma yana cire maballan.

Saura hudun na qasa,saiya saki,ya kamo hannunta a tausashe ya dora akan qirjinsa

"Qarasamin" ya fada yana saka daya hannun nasa ya zagaye bayanta dasu,hakan ya bata damar tsaiwa sosai,saidai dukka hannayenta biyu rawa suke,fatanta kawai ta cika umarnin mommmy data gaya mata duk abinda yace yanaso daga yau ta tabbatar tayi.

Fuskarta yaci gaba da qarewa kallo sanda taje cire masan,tun daga cikakkiyar girar idonta,qaramin lallausan kabbanta,tana da wani irin kyau me sanyi da tsayawa ????































!
"
#
$
%
&
'
(
)
*
+
,
-
.
/
0
1
2
3
4
5
6
7
8
9
:
;
<
=
>
?
@
A
B
C
D
E
F
G
H
I
J
K
L
M
N
O
P
Q
R
S
T
U
V
W
X
Y
Z
[
\
]
^
_
`
a
b
c
d
e
f
g
h
i
j
k
l
m
n
o
p
q
r
s
t
u
v
w
x
y
z
{
|
}
~

?
a rai,duk da har yau yaga alamar batasan wannan baiwar da take da ita ba.

Duk second daya da zasu qara a haka sake qayatar dashi tsaiwar take,rawar da hannunta keyi yasa ta dauki lokaci kafin ta gama,duk da cewa saman qafafunsa take a tsaye,amma hakan baisa yaji gajiya ba ko kadan

"N.....na gama"ta fada muryarta tana dan rawa,saiya sukunya gishinta yayi kissing dinta,zuciyarsa nata tunzurashi ya zarme amma yana mata waigi,two step back yayi yana sauketa sannan yace

"Thank you" ya furta hade da wani siririn murmushi ya wuce ta saman labbansa,saiya fara zare rigar,ta juya da hanzari ta fita a dakin, murmushi ta qara saki yana girgixa kai,ya dauki towel da widad din ta yiwa waje na musaman ya rataya ya shiga wanka,wannan ya bata damar guduwa daga dakin.

Komai ta shirya masa a table mat,sai data tabbatar komai yayi sannan ta wuce daki ta debo books dinta na makaranta da aka basu assignment ta dawo dasu parlor din,don dama kusan ko yaushe tare sukeyin assignment,saita koma koma ta zauna saman kujera tana jiran fitowarsa,wayarta na hannunta tana chart.

Ba jimawa sassanyan qamshinsa ya soma isowa parlor din,ta daga kai a hankali tana dubansa,yayi kyau cikin wasu light blue din kaya,fuskarsa tayi fayau kamar wanda yayi aikin wahala,saidai yayi fresh ya kuma yi kyau.

Tana murmushi ta miqe tana cewa

"Kazo kaci uncle please" tayi maganar tana karyar da kai gefe,sai ya sakar mata murmushi,komai nata burgeshi yakeyi,duk da tana komai ne ita bilhaqqi da gaske,ya tako a hankali har yanzu jikinsa babu qwari ya zauna.

Tana serving dinsa tana zuba masa surutu, yana daurewa ne kawai yana biye mata, saboda yadda gaba daya qamshinsa ke tafiya da hankalinsa,uwa uba rigar ta mugun fidda surar qirjinta da suka fara cika suna bin girma da jikinta ya fara yi,ta gama zuba komai ta tura masa tana cewa

"Aci a bani mark" kai ya jinjina ya fara diban abincin yana ci,shuru yayi yana jinjina dadin taste dinsa,baisan sunan abincin ba saboda bana hausa fulani bane,amma tako ina ya tafi dashi.

Itakuwa tana zaune gabansa ta tsira masa ido tana jiran jin abinda zai fada,kusan minti biyar shuru,saita fara bubbuga qafafunta

"Uncle..... uncle.....baiyi dadi bane?" Idanunsa ya zube mata ya lumshesu kadan sannan ya jinjina mata kai

"what a wonderful taste!.....na kasa magana ne don kada nayi shirme,I have never eaten food that tastes like this" dadi sosai ya cikata,dariyar farinciki ta kubce mata,saita matso tana dauko pillow zata saka masa a baya tana cewa

"Bari na fara da saka maka waigi kada ka fadi" hakan da tayi ya bawa tudun qirjinta damar gogar jikinsa,nan take ya qware da abincin da yake qoqarin hadiyewa yahau tari.

Da sauri ta tsiyaya ruwa ta bashi tana masa sannu,duk fuskarta ta nuna damuwa qwarai,idanunta sukayi narai narai da hawaye,tayi tsai tana kallonsa gami da jero masa sannu har tarin ya lafa

"Sannu uncle,ko na qaro maka ruwan?" A tausashe ya dubeta,wani kimarta da mahaukaciyar soyayyarta tana ratsashi,he never thought that she would care about him so much duba da qananun shekarunta da kuma yadda wadda ta girme mata ta ninka shekarunta ma ba haka take masa ba.

He wonders how she shows concern for him,ko yaya yayi dare ko ya gaggara cin abinci duka sai tabi ta damu kanta,bare taga alamun bashi da lafiya,saita zauna ta dasa masa kuka har sai yayi da gaske wajen qarfafa jikinsa da nuna mata ya warke,ko iya wannan kulawar ya samu alhamdulillah,ko iya haka ya fuskanci manufar hajiya akan yarinyar.....ko haka aka tsaya ya samu tarin abubuwa da yawa daya rasa daga wacce suka debi shekaru tare,ko a iya wannan ya samu abubuwan da ada baisan namiji yana samu daga wajen matarsa ba,saidai yana buqatar qari.....zuwa lokacin ya fara gano muhimmancinta me girma cikin rayuwarsa,yana son ya maidata tashi.....halak malak......yanason su sake zama.abu daya,yana son dandana mata soyayya mai zaqin da dandanonta bazai iya fita daga halshenta ba,yanason ta zama tasa ta har abada.

Sai data tabbatar ya nutsu sannan ta debe kayan abincin,ta kuma gyara wajen tas yana daga zaune cikin mutuwar jiki yana kallonta,daya daga cikin abinda yake burgeshi da ita,bata yarda tabar waje a hargitse ba.

Dab dashi ta zauna har cinyarta tana gogar tasa,cikin jikinsa ta aike masa da wani saqo me nauyi ba tare data san tayi ba,a kwanakin nan da sabo ke sake shiga tsakaninsu haka take masa,ko meye zatayi tana maqale da jikinsa kamar mage,ya fuskanci ta saba ne tun a gida,tana da son jiki,kuma hakanan dama takewa ummu.

Saman cinyarsa ta dora littafin da hannunta duka,sannan a shagwabe tace

"Uncle..... assignment fa" jikinsa gaba daya ya dauki rawa,yasa hannu cikin zafin nama ya janye hannayen nata duka biyu daga jikinsa,tsoro yadan shigeta ganin yadda ya sauya lokaci daya, muryarta a narke kamar zata saki kuka tace

"Uncle bazaka yimin ba?"kai ya girgiza muryarsa na dan rawa

"No"

"Amma shine ka ture ni?" Ta sake fada hawaye

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login