Showing 57001 words to 60000 words out of 200116 words

Chapter 20 - A RUBUCE TAKE (KADDARATA)

Babban falon ummun cike yake da jama'a,saidai da yake yana da yalwa babu laifi ba'ayi cushewar da zaka fuskanci yawan jama'ar dake cikinsa ba.

Duk da fargaba da kuma alhinin rabuwa da widad din tata hakan bai hanata qure ado fiye da duk wani bikin jikarta da za'a yi ba,ta cake cikin wani danyen lace purple color daya haska farar fatarta dake dan bayyana yanayin shekaru da suka soma hawa kanta.

Muhsin ne ya gaya mata ga abbas nan zai shigo,don haka ta kira hauwa'u da batulu(matan baban widad) tace su rage mata jama'ar falon.

Duk da jikinsu a mace yake saboda ganin irin hidimar da akeyi amma wannan aikin kam cikin karsashi suka yishi,saboda suma suna buqatar ganin mijin widad din sosai,cikin lokaci qalilan falon ya sake fili,ya zamana sai manya a cikin dangi suka rage,dai dai lokacin sukayi sallama suka shigo cikin falon su uku.

Kamar yadda a tsarin zubi da halitta gami da kwarjini ya fita daban......hakanan adonsa da shaddar jikinsa ta banbanta data kowa,sai ya fito kamar wani wata a cikin taurari,qanwar ummu da sauran jama'ar dake wajen ke marabtarsu,har suka samu waje qasan carfet suka zauna bisa tsari na tarbiyya,sannan aka soma gaisawa.

"Da gani babu tambaya,wannan na tsakiyar shine surukin namu ko?" Batulu da wani malolon abu ya tsaye mata a wuya ta fada,fuskarta kwance sa murmushin yaqe,kusan kowa a wajen sai da yaji banbarakwai,saboda ba ita ya dace tayi tambayar ba,ko banza ya kamata ace akwai kunya tsakaninsu,saboda a yanzun sune kamar copy na mahaifiyar widad.

Murmushi suraj ya danyi,baisan dangantakar ta da widad ba,ya dauka abokiyar wasa ce,tunda suna irin haka,dalilin da yasa ya maida mata kenan cikin salo na wasa

"Aah,nine fa,kingi batan dabo"

"Allah ya sanya alkhairi,yasa anyi kenan,jikanyar tamu qaramar yarinya ce qwarai,sai anyi haquri da halayen quruciya da za'a yita gani,Allah ya bada zuri'a dayyi ba" qanwa ga ummu tayi hanzari katse doguwar maganar da batulu keson taja,falon sai ya game da addu'ar ameen ameen.

Abbas din na shirin miqewa muhsin yashigo yana fadin ina widad din afito da ita,azo ayi musu hoto

"Ya salam" yafada a ransa,me yasa muhsin zai masa haka,bashi da zabi illa yayi jiraye.

Anty madina da anty deena ne suka fito da ita ta can backyard din gidan,basa so kowa ya tsaidasu bare kwalliyar tata ta baci,suna tafe anty madina na jaddada mata kada ta sake tayi kuka,zata bata fuskarta

"Ke maison kwalliya,kinga yadda kikayi kyau kuwa widad,baki taba kyau irin na yau ba" takanji dadi idan akace kwalliya tayi mata kyau,musamman daya zamana ita din mai son kwalliyarce,to amma kuma bata samunta sai lokaci lokaci,yau din da anty madina ke cewa tayi kyau sai bata ji wannan dadin da takanji ba,ta daiyi qoqarin dakewa,tanason farantawa anty madina rai,saboda kirkinta da yadda take sonta.

Sallamarsu cikin falon ya ja hankalin jama'ar dake falon,badawiyya abokiyar wasa ga widad din,wadda shigowarta kenan falon ta saki guda data ratsa falon gaba daya.

"Ma sha Allah.....ma sha Allah,widad Allah yasa anyi a sa'a,Allah yasa mutu ka raba" bakunan masoyanta dake wajen ya cika da addu'a,yayin da kishi hassada da kuma qyashi ya cika zukatan wadanda ke qin jininta hakanan.

Gaban ummu suka so kaita,amma saita musu nuni dasu ajjiyeta gaban abbas din ba tare da tayi magana ba,sun fahimta,saboda haka suka nufi gaban abbas din da ita,ganin haka yasa tun kafin su qaraso suraj da muhammad da suka masa rakiyar suka janye baya,suka basu fili sosai.

A hankali suka tsugunnar da ita a gaban nasa,rabin fuskarta yana rufe,saidai hakan bai hana kayan adon dake jikinta bayyana ba,suka ja da baya,sai falon ya dauki hayaniyar abokan wasa da suketa yiwa juna tsiya tsakaninsu da uncle muhsin,abinda ya dan janye idanun mutane kenan daga kan abbas da widad din.

Tana zama awajen wani irin qamshi ya soma fita daga jikinta,sassanyan qamshi mai fusgar hankali da kwantar da zuciya,irin qamshin dake saurin sakawa zuciya karaya da wani irin sassanyan yanayi,ya daga idanunsa a hankali,fararen hannayenta da suka jan lalle irin na asalin yamalawa su ya fara gani,a hankali yaci gaba da kallonsu kafin ya daga kai zuwa ga fuskarta,dai dai sanda itama ta daga kanta zuwa gareshi don ta gaidashi kamar yadda anty madina ta gaya mata,fuskarta ta fito tarwai da wani irin haske data qara

"Ina yini" ta furta,bugun zuciyarta na bayyana har saman harshenta,ya kuma biyo ta sautin gaisuwarta ya sanya lafazinta fita a rarrabe,amma hakan sai ya qarawa sautinta mai cike da quruciya kyau,sai ya dan lumshe idanunsa kadan yana amsawa

"Lafiya qalau" yana ganin fuskarta a yau ta sake zama ta manya fiye da ranar da ya ganta a gidan muhsin,a yau din ta dan sake zama babba kadan ba kamar ranar ba

"Sir.....me hoton ya gama dauka,saura na tsaye da wanda za'ayi muku da hajiya ummu saboda tarihi ko?"

Sam baima san zaman da tayi wai hoto akeyi ba,muhsin ya cuceshi,yanzun idan baiyi wasa ba kafin la'asar hoton ya riga rana fadawa cikin kafofin internet,ko a haka baisan yadda akayi labarin bikinsa ya karade duniya ba,ko ina ka duba tsakanin whatsapp twitter facebook da instagram zancan da akeyi kenan

"Dagota mana please,yanzu yanzu aka gama baka amanarta fa suna kallonka" suraj ya rada masa,no more option sai bata hannunsa da yayi

"Taso" ya fada yana kallonta,labbansa daya furta taso din take kalla,tsoro da mamaki fal idanunta,dama shima dan iska ne?,abinda take fada kenan a ranta,a gabansu ummun yake bata hannunsa?,bashi da kunya ashe shima?.

Bata gama wannan tunanin ba taji ya kama lallausan tafin hannunta,ba shiri ta miqe ta kuma zame hannunta da sauri hawaye suka fara taruwa a idanunta,lallai saita gayawa ummu abinda yayi mata,so yake ta mutu?,bayan ummu ta hanata tsaiwa kusa da kowa ma?.

_to masu karatu,gafa amarya widad mai cike da tarin wauta quruciya gata kuma goyon kaka,ba'a fara wasan bama,muje zuwa dai_=??=??=?O?
KI KULANI miss xoxo

DAUDAR GORA Billynabdul

RUMBUN K'AYA hafsat rano

IDON NERA Mamuhghee

A RUBUCE TAKE huguma

_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_

_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

0022419171
Maryam sani
Access bank

Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070

*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261

*Al'ummar nijer +227 96 09 67 63


*Thanks for choosing us*=?%?=?%?=?%?=?%?=?%?=?%?


*H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks: Huguma*

Page 30

Anty deena ta ankara da yadda taketa narai narai da idanu,kadan take jira ta fara sakin ruwan hawayen nata,murya qasa qasa ta yadda ba wanda zaijisu tace

"Haba mana widad,so kike ummu ta gani hankalinta ya tashi?" Kai ta girgiza tana kallon idanun anty deena da golden eyes dinta

"Okay,maza hadiye,hadiye kinji qanwata" kai ta sake gyadawa,sannan aka fara daukan hoto.

Gaba daya ji yayi ya qosa ayi a gama,murya can qasa yace da muhsin

"Please muhsin,am tired wallahi" murmushi yayi,sau tari yana bashi dariya,bai taba ganin dan police wanda bai jure hayaniya ba irinsa

"Okay" ya fada yana dagawa widad hannu,a hankali ta qaraso wajen tana kauda idanunta daga kallon abbas,haka kawai idan ta kalleshi sai taji gabanta ya fadi

"Maza kusa ayi muku ku biyu" wani irin tsoro ya kamata,gabanta ya tsananta faduwa,sai ta narke cike da tsoro tana kallon uncle muhsin,wanda shi sam baima san me takeyi ba

"Matsa widad lokaci na qure musu" anty deena ta fada,kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki ta fara takawa zuwa kusa dashi,nesa kadan dashi ta tsaya,saida mai hoton yayita magana da taimakawar gargadin da anty deena ke mata da idanu ta sake matsawa aka dauka

"Enough please" ya sake fada

"Dama ai an gama" suraj ya amsa wannan karon yana dariya,sallama sukayi dasu ummu,akwai yiwuwar su kwana a kano,duk da babu tabbas, uncle muhsin keson hakan,saboda akwai walima daya shirya musu.

Tun daga wannan lokacin gaba daya ta sake zama sukuku,ita gaba daya komai ya kwance mata,hakanan banbarakwai take kallon komai,daga qarshe dai a daki ta qule ta qarasa yininta,duk kuwa da sabgar da ake cikin gidan.

Da daddare kuwa bata yarda ta kwana da kowa ba sai a bayan ummu,kowa tsiyar ai dole su rabu yake mata,wannan ya sanya zuciyarta karyewa ta kuma soma kuka sosai,da qyar ummu ta rarrasheta.

********Washegari tun da safe anty madina ta aiko kiranta,tana sanye da dogon hijab da ummu ta fidda mata,ganin cewa a yanzun wani nauyi ya hau kanta,kuma gidan akwai 'ya'yan baffaninta maza,ga kuma baqi maza still 'yan biki da basu kai ga tafiya ba.

A kitchen ta taddata tana ta hidimar hada abincin safe,sai ta waiwayo tana kallonta

"A'ah,ya haka?,bakiyi wanka ba dama?" Baki ta turo gaba a shagwabe tace

"Anty madina duka duka yaushe garin ya waye?,kuma Allah an fara sanyi fa" rai anty madina ta bata sosai

"A'ah,daga yau sai yau,kada na sake gani,idan akace mace tana da aure da wuri take wanka ta gyara jikinta kinji ko?,ta fidda kayanta tayi kwalliya sosai" kai ta gyada a sanyaye,ita dai komai sai ace aure aure,duk an takurata da kalmar nan.

"Shiga dakina a hankali kada ki tada min abba,akwai turarenki da kika bari jiya saman mirror,ki dauka ki feshe jikinki sosai,sai kizo zan aikeki" amsawa tayi da to,don ita badai qauna da turare ba,ta wuce dakin anty madinan.

Ba jimawa sai gata ta dawo,tana ta zanga qamshi kuwa,ta nuna mata wani baske tace

"Dauki maza kikai sitting room din kawunnanki" ba tare data kawo komai a ranta ba ta amsa da to,ta dauki kwandon tayi ficewarta,tana tafe tana tsayawa magana da mutanen dake mata magana a hanya,cikin sauran baqi na gidan,har ta isa qofar setting room din.

Jim tayi tana duban baqin half cover din dake qofar setting room din,wanda keta sheqi

"Waye ma to a ciki?" Ta tambayi kanta,bata sani ba don haka ta tabe baki,cikin wannan d'arin d'arin nata da rashin sabo da maza ta saka kai ciki tare da yin sallama.

A lokacin kansa yana duqe a qasa,yanata trying number hafsat ce,wadda tunda ya taho basuyi waya ba,duk kiran da zaiyi sai ace masa is switched off.

A hankali ya daga kansa yana motsa labbansa tare da amsa mata sallamar,idanuwansa suka fada a kanta sanda take takowa kamar mai takatsantsan kada ta taka kwalba,baby face dinta dake tsakiyar blue black din hijab dinta ta fito fes,qananun gashinta masu santsi dake kwance gaban goshinta sun sake qawata fuskar,dan qaramin bakinta me red lips ta dan tsukeshi waje guda,fuskarta sam babu fara'a,sai ya lumshe idanuwansa kana ya maidasu qasa ga hannunsa inda wayarsa ke riqe,shidai baisan me hajiya ta hango ba data zabi ya auri qaramar yarinya har haka,kyau?....ko kuwa me hajiyan ta kalla?,shi kansa bai sani ba.

Tazarar wasu inches ta bayar a tsakaninsu ta ajjiye kwandon,tana daga tsugunne ta gaidashi da siririyar muryarta

"Ina kwana?"

"Kin tashi lafiya?" Ya amsa mata yana sake daga kanshi gareta a karo na biyu,bata amsa masa ba sai miqewa da tayi tsaye ta soma shirin ficewa a setting room din,saboda gaba daya a tsorace take,already ummu tayi mata horon tsoron maza sosai da shan inuwa daya dasu,a yanzun kuma bata gama sanin muhimmancin abbas din ba

Da kallo yabi bayanta,dariya ta taso masa can qasan ransa,ta yaya cikakkiyar budurwa mai shekaru da wayo ta aikata haka?,sai ya gyara zamansa kadan yana lalubo sunanta

"Widad" ya furta a tausashe,tsayawa tayi cak gabanta yana faduwa,dama yasan sunanta wai?,ta tambayi kanta

"Zo mana" ya sake fadi,abinda yasa ta waiwayo kenan,suna hada idanu duk wani kuzarinta yayi nasa waje,sai ta narke fuska

"Ummu zata yimin fada idan na dade" kai ya girgiza yana lumshe idanunsa kamar yadda yake a al'adarsa

"Ba zaki dade din ba,yanzun nan zaki tafi" kallonsa takeyi,sai ya jinjina mata kai alamun tabbatarwa,don haka ta dawo a hankali,ta samu nesa dashi ta zauna.

Tattara dukka hankalinsa yayi ya zuba mata idanu,yanzun ta ina zai fara mata bayani ma?da wanne harshe zai mata magana ta fahimci abinda yake cewa quruciya duk ta baibayeta?,a qa'ida babbar budurwa ce yanzun zaune a gabansa,sai yafi sanin yadda zai dinga handling abubuwa har su saba da juna.

Motsawa tayi kadan tana hade rai saboda yadda yake kallon nata ya sake takurata,ya fahimci haka sai ya aje wayar hannunsa,a bisa tilas ya arawa fuskarsa murmushi sannan ya fara magana

"Ummu ta gaya miki an daura miki aure ko?" Kai ta gyada tana kallonsa

"Good,daga yanzu na zama yayanki,na zama kuma abbanki,zamu tafi dake can zan kaiki gidana,zamu tafi tare,kema gidanki ne duka,zakiyi duk abinda kikeso a ciki,kina so?" Idanunta masu tsananin haske da ratsin gold color ta fara rarrabawa a tsakanin nasa idanun,sai ya kafeta da idanu sosai yana kallon yadda suke juyawa,yadda ta mele baki ta kuma tabe fuska hadi da lumshe idanunta,eye brows dinta masu tsayi suka hade waje guda sannan ta sake bude idanun warrrr a kansa yasa tsigar jikinsa ta zuba

"Bazan dade ba zaka dawo dani wajen ummu?" Ajiyar zuciya mai nauyi ya sake yana dan murmushi kadan

"In sha Allah,nima daga yau na zama yayanki ko?"

"Uncle dina dai ko?,naji nujood na cewa sunanka uncle abb...." Kasa qarasa sunan nashi tayi,tana jin kada tayi abinda bata kyauta ba,murmushi ya subuce masa ba tare da ya shirya ba,har fararen haqoransa suna bayyana,ya fuskanci nauyin kiran sunan nasa take

"Uhnnnn,uncle abbas" sai ta gyada kanta tana hade hannayenta waje guda,yakai duba ga hannun nata,tsararren jan lallen nan nata yana nan tas saman hannunta,ya zuba masa idanu kamar mai karnatar taswirar zane,lallai akwai hikima mai yawa ga masu yin lalle,har da suke iya tsara zane haka ya bada wani kala da nau'i mai kyau.

Rai ta hada sosai ganin yana ta kallon hannun nata, saita zare hannuwan nata zuwa cikin hijabin tana sake qudundunewa waje guda,ya dauke kansa yana maidawa ga dan qaramin leda yar mitsitsiya daya shigo da ita,sai ya dauka ya tura mata

"Wannan waya ce,ki cewa ummu a kunna miki,akwai komai a ciki,zan dinga kiranki,sauran kuma kudi ne,duk abinda kikeson siya ko kike son amfani dashi ki dauka a ciki,kada ki sake tambayar kowa yayi miki wani abu" murna farinciki da kuma mamakin bata waya da akayi ya lullubeta,to amma kuma tana tsoron kaiwa umnu kayan tace wani ne ya bata,duk yadda take zumudin wayar saita noqe

"Wallahi ummu zata dakeni,zatace waye ya bani" murmushin dole ya sake subuce masa

"Kice uncle abbas ne,idan ma bata yarda ba kice a kirani,bazata miki fada ba" sai ta matso kadan,ta dauki ledar tana cewa

"An gode,Allah ya saka da alheri" girma yaji addu'ar tayi masa,sai ya bita sa kallo kawai harta fice,ya maido dubansa cikin falon yana sauke gauron numfashi,tsahon zamansa da hafsa bata taba fadin haka ba,duk girman kyauta idan yayi mata

'An gode' shine iya abinda ta iya fade kenan,bata buqatar cin komai,so yake kawai yaga sun dauki hanyar bauchi,to amma babu dadi su kawo suga baici komai ba,gashi ya baro baqi a masauki,don haka ya fidda qaramin flask din tea dake cikin kayan,ya hada tea.

A gaggauce yake sipping,yana tsaka da kurba uncle muhsin yayi sallama

"Aah ya haka bakaci komai ba?" Ya fada bayan sun gama gaisawa yaga abbas na ajjiye cup din

"Sauri nake ne,ya kamata mu dauki hanya da wuri,saboda kamar gobe nakeson komawa kaduna,akwai gyare gyare da za'a yi acan,a office ma kuma ina da ayyuka da ban gama settling nasu ba bare na dora da nawa,ban taba aiki a kaduna ba sai wannan karon,kaga ina buqatar maida hankali na sauke nauyin al'umma dake kaina" kai muhsin ya jinjina

"Gaskiya ne,to shikenan,muje kayi sallama dasu saimu fita tare,zaka saukeni a al-hamsad tower zan shiga wani shago akwai abinda nakeson dubawa,zuwa azahar an kammala walima in sha Allah saiku wuce kafin la'asar"

Sai data gama nuqu nuqu da fargabar nunawa ummu kayan daya bata,da taga ba zata iya ba saita wuce sassan anty madina,ta sameta ta fito a wanka,don haka ta zauna cikinsu walid dake falo suna kallo harta gama shiryawa ta fito ta sameta

"Widad,har ya tafi baqon?" Kai ta gyada tana miqa mata ledar

"Wannan ya bani,sai da nace bazan karba ba ummu zatamin fada,yace wai ba zata min komai ba" dariya ta subucewa anty madina

"Taso nan" tace da ita bayan ta karba ledar,suka matsa gefe can inda yaran ba zasu jiyosu ba,zama tayi ta zaunar da ita a gefanta

"Shi wannan ai ba baqo bane yanzu,mijinki ne kin gane?,kamar ni da abban walid,kamar ummu da alhaji,kin gane?" Tadai jita,amma bata gane mai take nufi ba,ita kallon abban walid da anty madina takeyi a mazaunin yayanta ne,ummu kuma alhaji babanta ne

"Bari muga me miji ya baiwa matarsa kyautar farko?" Ta fada tana dariya,ta zazzage ledar,kwalin kyakkyawar waya qirar samsung ta fado hade da sabbin kudi a miqe fil dasu

"Lalalala,ah lallai wannan diya tamu da goshi take,tun yanzu?" Dariya ta kubcewa widad,haka kawia taji kunya ta kamata,saita sanya tafin hannunta ta rufe fuskarta anty madina na tayata dariyar

"Zankadi,bude idonki

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login