Showing 93001 words to 96000 words out of 200116 words

Chapter 32 - A RUBUCE TAKE (KADDARATA)

cikin baqaqen boots,yana shirin rufe qofar ya lura da ita,sai ya waiwayo yana dubanta da mamaki kan fuskarsa,da yaji shuru yayi tunanin har yanzu tana daki baccin takeyi,dalili kenan da bai tasheta ba.

Sosai ya sake mata kwarjini,wani tsoronsa ya sake shigarta,sai ta dauke idaninta ganin yadda yake kallonta,tura baki gaba, itafa duk wanda yake kallon mata dan iska ne a wajenta,ta sauke qafafunta qasa sannan tace

"Ina kwana?" Bai amsa ba sai daya rufe qofar dakin,sannan ya tako zuwa wajen yace

"Lafiya lau...." Ya fada yana duban kan dining din,sannan ya sake dubanta

"Kinci abinci ne?" Kai ta girgiza

"Akwai kayan tea a cupboard na kitchen din,zan fita anjima za'a kawo kayan cefane,ba wata damuwa?" Kamar jiya yauma fuskarta kamar ta fashe,yana nufin ita kadai zata wuni a sassan kenan?,wai Allah,ya zatayi,lallai zata mutu da tsoro indai yace zai sake kaiwa dare,ganin batace komai ba sai ya dora

"Akwai mutane cikin gidan nan,zaki iya shiga ku gaisa,ko kuma idan na dawo saiki shiga" ya fidda kudi ya ajiiye mata

"Sai na dawo" ya fada yana nufar qofar,binsa tayi da kallo,kamar ta zura da gudu ta bishi

"Don Allah kada ka sake kaiwa dare irin na jiya" ta fada muryarta tana rawa,waiwayowa yayi yana kallonta,ba tare daya shirya ba murmushi ya subuce masa,shi kam ya jima baiga matsoracin mutum ba irinta

"In sha Allah" yace mata sannan ya fita.

Ta kusa minti talatin a wajen tana jin yadda gidan yayi mata shuru,sai da cikinta ya fara kiran yunwa sannan ta miqe,kana kallonta zakasan a tsorace take,duk da akwao motsi jifa jifa daga harabar gidan,kitchen ta shiga tana neman inda kayan tea din suke,tsahonta bazai kai ba,sai tasa kujera ta taka ta dauko ta dawo dining din ta doma qoqarin hada tea din,gana daya ta rude,saboda ummu ko latifa ke hada mata,koda ta gama hadawa ta dandana sai taji test din baiyi mata ba,ta bare baki kamar zata saki kuka,haka ta runtse idanu tana kurba har ta kusa shanyewa,dai dai lokacin da wayarta ta dauki tsuwwa,ta firgita da ringing din wayar daya soma fita,don a bazata yazo mata,saura kadan cup din hannunta ya subuce,ta ajjiye kofin ta nufi dakin da sauri.

A can qasan gado ta gano wayar,a lokacin ana sake kira karo na uku MOMMY ta gani,shine sunan data sakawa hafsat,ta saki murmushi tana jin dadi,itace ta fara kiranta,cikin zumudi ta daga

"Hello.....ina abban mimi?" Abu na farko da hafsat ta fara fadi kenan,ba tare data damu tayi sallama ba

"Mommy ina kwana?,inasu mimi?" Ta maida mata da tambaya,ba tare data bawa tambayarta ta farko muhimmanci ba,saboda ba wannan bane damuwarta ba

"Lafiya lau....ina abban mimi?"

"Ya fita mommy"

"Jiya a ina kika kwana?"

"A dakina"

"Shi kuma abban nasu fa?"

"Ban sani ba,na rigashi yin bacci" gaban hafsat ya fadi

"Da kika farka kenan a dakinki kika ganshi?" Kai ta girgiza kamar tana gabanta,gabanta kuma yana faduwa cike da fargabar kada ta karanci ya rungumeta,babban abun kunya kenan,tana kuma tsoron kada zancen yaje kunnen mutane a dauka ita din 'yar iska ce

"Daga dakinsa naga ya fito sai ya tafi office"

"Karkimin qarya fa widad?" Kai ta langabe muryarta nayin sanyi

"Allah ki tambayeshi ma" ta furta zuciyarta na addu'ar Allah yasa kada yace ya rungumeta idan ya tashi bata labari.

Ajiyar zuciya ta sauke,hankalinta yana kwanciya

"Shikenan,ina fata baki manta komai ba?"

"Eh momy"

"Da kyau,ki kula da kyau kinji ko?,ki kula"

"To mommy.....mommy amma ki bani mimi ko...." Bata tsaya jinta ba ta gintse wayar,iya abinda takeson ji kenan,sauran koma meye ba damuwarta bane,ta aje wayar gefan gadonta tana furzar da iska

"Shegiyar yarinya,kike cewa wani wai na tambayeshi,abbas din zan yiwa wannan tambayar?,ko ke ban isa na miki makamanciyarta a gabanki ba" sai kuma murmushi ya subuce mata

"Anty ummee kinyi a rayuwa" ta fada a fili,ta duqa tasa qaramin muqulli ta bude drawer din jikin gadonta da take bawa kulawa ta musamman,kudade ne a ajiiye a ciki,ta fiddosu ta fara rigasu tana hade kansu waje guda,ranta na mata fari sol,yau sai taji gidan ya mata dadi,musamman idan ta kalli sassan widad din ra ganshi a rufe,sai taji kamar ta tafi kenan.

Tana cikin maida kudin kira ya sake shigowa mata,ganin sunan mai kiran saita hade ranta,taja tsaki ta dauke kai,anty shafa ce yayarta,tasan kiranta baya rasa nasaba da zancan kudi,kullum zancanta na ta kawo wani abunne,ita kuwa kudinta bana tabawa bane,don haka ta maida wayar silent ta miqe tana kallon agogo.

Sha biyu saura na rana,ko brush batayi ba bare ayi zancan breakfast shara ko gyaran gida,tana son abbas tana son ta kasance ko yaushe dashi,to amma idan suna tare irin wannan sakewar ce bata samu,shi yasa ba kasafai take damuwa da nisantar juna a tsakaninsu ba.

Tunawa tayi tabar yara a falo,har tayi hanyar toilet saita sauya akalarta zuwa falon,tana addu'ar Allah yasa basuyi mata barna ba.

Tun daga nesa ta hangi mimi tayi dafa'an a tsakar falon,ta fasa kwalin cornflakes ta cika madara kwano ta dama da ruwa tana ta durawa nawwara,tsawa ta kwaza mata,sannan ta fidda danu tana duban kwanon

"Innalillahi" ta fada da qarfi,sannan ta nufi mimi da sauri, batayi wata wata ba ta gabza mata mari,gaba daya yarinyar ta jawo mata asara,kudin da ya bayar a siya wadan nan kayayyakin ta lankafesu,ta fitar da tsohuwar madarar daya taba siyawa yaran tasu tashan tea,ta ajjiye a dining tace suyi amfani da ita kafin ya dawo,yanzu ta daga madarar dukanta ta zazzage musu.

"Uban wa yace ki taba?" Ta fada tana kama kunnen yarinyar,cikin kuka tace

"Mommy,nawwara ce takejin yunwa" sai lokacin ta tuna bata basu komai ba ashe,ta saki kunnen nata tana huci

"Ba sai kizo ki gayamin ba,kin tashi kin cuci mutane kin musu barna,matsa ki bani waje" haka ta sanya tsintsiya da ta gyara gurin,tana yi tana mita,yaran na rabe a gefe,mimi na hawayen murde mata kunnen da tayi.

*Arewabooks: Huguma*

KI KULANI miss xoxo

DAUDAR GORA Billynabdul

RUMBUN K'AYA hafsat rano

IDON NERA Mamuhghee

A RUBUCE TAKE huguma

_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_

_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

0022419171
Maryam sani
Access bank

Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070

*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261

*Al'ummar nijer +227 96 09 67 63


*Thanks for choosing us*=?%?=?%?=?%?=?%?=?%?=?%?

*H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)

Page 48

Tana cikin wannan mitar aka buga qofar falon

"Waye na?" Ta fada cikin fada fada,ranta fal quncin mimin ta karya mata budget

"Nine,sale ne"

"Shigo" ta fada kanta tsaye bayan taja tsaki,duk da tasan abbas baison haka,don baya bari a shigo masa har inda iyalinsa suke kai tsaye.

Da sallama yaron ya shigo yana sunkui da kai,don bai saba shigowar ba,ga hafsat din da daurin qirji,sauqinta akwai t-shirt a jikinta,a samanta taja zanin ta daura

"Ina kwana hajiya"

"Lafiya lau ya akayi?"

"Eh dama me yiwa engine service ne yazo,za'a bada kudin a siya kayan aikin,sai mechanic din da zai dauki motar oga ya kaita garage za'a mata service itama" tsuke fuska tayi,don tasan kudaden daya wara ya bata saboda a duba motar da engine din suna da yawa

"Bakaniken ya dauki motar,amma shi me yiwa engine service kace ya barshi kawai,sai mai gidan ya dawo"

"To....amma engine din yana bada matsala fa,jiya ma....."

"Abinda nace kayi zakayi ko raayinka zanbi?"

"Sorry madam" ya fada yana juyawa yabar falon,cikin ransa yana Ala wadai da dabi'arta,sarai yasan an bata kudaden,fitar dasu ne ba zata iya ba.

Tsaki taja tana duban yaran

"Ku wuce muje na dafa muku abinci" jin xancan abinci sai mimi ta ware,sukabi bayanta zuwa kitchen din,saidai tana ganin ta buda kwalin indomie yarinyar ta bata rai,ta gaji da ita,don jiya da daddare ma ita ta dafa musu

"Indomie mommy?,bana ci nidai" cikin takaici ta kalla yarinyar,ubansu ya batasu da kala kalar abinci,ita kuwa ba zata iya dorama kanta wannan wahalar ba

"Ba zakici ba ubanme zakici?"

"Irin abincin gidan hajiya"

"Meye abincin gidan hajiyan?"

"Tuwo ko dambu"

"Nabi tuwon da gudu,zakici ubanki wallahi,idan bakici ki zauna haka,yunwar cikinki" saita bare kwalin ta dauko guda biyu ta zuba a tukunyar.

Kusan dai a gantale suka tsakuri taliyar,bata tsaya ta mata ma dahuwar arziqi ba bare darajar hakan ya sanya suci da yawa,daga qarshe ma.idan ta debo ta baiwa nawwara sai ta tankwabe hannunta,da yake ita din tafi mimi fada,sai ta tattarasu ta barsu ta shiga sabgarta,dole da yunwa ta ishesu suka dawo suka ci a haka bayan tayi sanyi.

????????? Hirar da suka sha da ummu da abbanta na kusan awa biyu ya sanya tajita tadan sake,sai kuma dan motsin da take jiyowa lokaci lokaci cikin gidan ya sanya bata matsu da yawa ba,ta dan saki jiki ta soma kade dakin da gyarashi kamar yadda latifa ta koya mata,sannu a hankali sai gashi ta gyara dakin fes,sadai fa tadan dauki lokaci,ta shiga toilet ta wanke fes,ta kama qugu tana dariyar farinciki na ganin yadda ta gyara dakin kamar ba ita ba,ta kama baki tana murna

"Ashe dai na iya,amma ummu ke hanani,bari na kira umma latifa na bata labari" ta koma gefan gadon tana kaffa kaffa kada ta bata zanin gadon data d'ameshi da kyau,ta fara duba number latifa wadda basu jima da gama waya da ita ba itama,Latifa na daga wayar ta fara bata labari

"Iyeee shalelen ummu,girma yazo,haka akeso,kiyita tsafta kamar ummunki,saura girki" dariya tayi tana sake bata labarin wahalar data sha,latifa na biye mata,ummu ja gefansu tana murmushi,duk da rabin hankalinta nakan shalelen tata.

Wunin ranar bata wani ji yunwa ba,koda taji yunwa dinma tea ta hada tasha ta kwanta abinta.

Kafin magariba tayi wanka,ta shafe jikinta da turarukan da latifa ta hado mata a kayanta,kusan sai data shafa kowanne turare,har ya soma yawa ya fara hawa ka,kowanne mai sanyi da dadin qamshi ne,amma yawan da yayi yasa ya jirkita,amma ita ko a jikinta,wata dubai abaya ta saka,ta dawo falo ta maqale jikin window tana leqen harabar gidan,gabanta yana dan faduwa kadan kadan,saboda ganin magariba ta gabato babu shi ba alamarsa.

Ana qwala kiran sallar magariba motarsa tana shigowa cikin gidan,samuel ne ya kawoshi,shi ya koma shi kuma ya shigo ciki.

"sannu da zuwa" ta furta tana jan dankwalinta daya zame saboda santsinsa daya hadu da sulbin gashinta,ta miqe tsoron nan nata yana bayyana,tanason karbar masa ledar daya shigo da ita kamar yadda ta saba duk sanda taga kaya hannun babba,amma tana shakka matsawa inda yake,a haka har ya qaraso ya ajjiye,ya zauna yana tube takalman qafarsa

"Lafiya kika wuni?" Kai ta gyada masa,sai yadan lumshe idanu yana gyada kai,qamshin jikinta gaba daya ya cika falon,kamar anyi barin turare

"Samomin ruwa nasha" hanyar kitchen din ta kalla,baiyi duhu sosai ba,don haka da sauri tayi hanyar,a nufinta tayi sauri ta dawo kada wajen yafi haka duhu.

Binta yayi da kallo,ko yaushe ya kalletan sai ya dinga jin mamaki na shigarsa,wai matarsa ce wannan,ta dawo da ruwan ta russuna ta miqa masa kamar yadda ta saba yi tun a gida.

Hannu yasa zai karba,yadda tayin yana burgeshi,duk da abub mamaki bane,duba da gidan data fito,muhsin kadai ya ishi a shaidesu,don ko cikin abokansu daban yake,wani abune da zai iya cewa baisan lokaci na qarshe da hafsat tayi masa ba wai don zata bashi abu.

Sakin ruwan tayi da sauri sanda hannunsa ya sauka akan nata,jikinta ya dauki rawa,taja da baya tana yarfe hannu jikinta yana rawa,hawaye na shirin tarar mata a ido,shi bai kula bama,don ya duqa zai dauke ruwan bayan ya furta

"Subhanallah" sanda ya dago harta samu waje ta rakube,ya bita da kallo yana mamakin yadda take matuqar tsoron tarayya dashi,kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa,ya bude gorar ruwan ya fara sha,sannan ya miqe yana cewa

"Zanje sallah,idan na dawo zaki shiga ciki ku gaisa da mutanen gidan,ga abinci nan a leda ki dauki naki" kai ta gyada masa gabanta na faduwa,bata samu nutsuwa ba har sai da yayi alwalar ya fice,ta bishi da kallo tana hararar hanya qwalla na gangaro mata,yanzu idan ummu ko mommy suka ga wannan abun da yakeyi fa?.

A falo ya tsaya jiranta,ta fito yafe da mayafin abayar bayan ta cire hijabin da tayi sallar dashi

"Koma ki samo babban mayafi,akwai mutane a waje" yayi maganar sanda yake dage labulen falon yana sake duba farfajiyar gidan,jikinta ta kalla,itadai bataga wani aibu a haka ba,amma sai batace komai ba ta koma ta lalubo mayafi cikin kayanta ta fito,suka jera zuwa cikin gidan.

Babban gini ne,don yadan fi nasu girma da kayan alatu,sanda ta shiga ta samu matar gidan a falo,ta karbeta da fara'a,saidai tunda ta gaidata ta rasa me zata cemata.

"Ban gane fuskar taki ba,ko kanwar amaryar abbas ce?" Qas tayi da kanta tana jin nauyi yana kamata,saita girgiza kai alamun a'ah

"Ko amaryar ce da kanta?" Saita daga kai alamun eh,matar ta maida kanta sosai tana kallon widad din sosai,abbas data sani,abbas dake da.babbar mace kamar hafsat yaje ya auro wannan qwailar?,lallai Allah mai iko,sau tari mazan da suka fiya izza da kuma jin kansu daga qarshe haka suke qarewa,har gwara wannan din,kyakkyawa ce data amsa sunanta,komai nata mai ban sha'awa da daukan hankali,nan gaba kadan idan ta ida zama cikakkiyar mace lallai ba shakka sai an kalleta an qara,dole hankalin hafsat din ya tashi,amma a fili sai tace da ita

"Ma sha Allah,Allah ya bada zama lafiya kinji amarya" bata iya amsa mata ba,sai shuru data sakeyi kawai kanta a qasa,gaba daya bata jinta a sake,tun asali dama ita din bamai saurin sabo bace,tana da wuyar sakewa da baqin fuska,don haka bata wani jima ba ta miqe tace zata tafi

"To ina zuwa" ta fadi tana miqewa ta shige ciki,ranta da zuciyarta fal mamaki,ba jimawa ta fito da wasu kayan barci set uku ta bata,hannu biyu widad ta saka ta karba sannan ta fito.

A inda ta barshi ta sameshi,ya sake mata jagora suka koma ciki,tana ta kallon gate,ji take kaman ta fita ta miqe qafarta,suna shiga falon ta miqa masa kayan kamar yadda takewa ummu a gida idan an mata kyautar abu

"Gashi" ta fada tana ajjiye masa kusa dashi,dai dai lokacin da ledar ta zame,matan dake jikin takardar sanye da irin kayan baccin dake cikin ledar suka fito.

Kusan tare suka dauke idanunsu shi da ita,taja baya da sauri qafafunta na sarqewa zata wuce ciki

"Zonan" yayi kiranta yana karantarta,da baya da baya ta dawo,ita a lallai ba zata iya kallonsa ba,har abun yaso bashi dariya,ya dake da yanayin dakiyarsa da kuma miskilancinsa

"Dauke abinki ki tafi dasu"

"Banaso" ta fada kai tsaye tana maqale kafada,a mamakance yake kallonta

"Bake ta bawa ba?"

"Ni ta bawa,amma banaso,bana saka irinsu" dariyar da yaketa riqewa ta subuce masa,amma saita fita ta sigar murmushi

"Zauna" yace da ita yanata kokawa da dariyar tasa,ta baya ta zauna har yanzu taqi yarda su hada ido dashi.

"kinsan amfanin wadan nan kayan?" Fuska ta qara daurewa,tana sake tabbatarwa basu hada ido ba,kai ta girgixa masa ba tare da tayi magana ba

"Oya....open your mouth,ban jiki ba"

"Ban sani ba,kayan 'yan iska ne fa" tayi maganar tana narke fuska,kamar zata saki kuka.

Wannan karon duk yadda yaso boye dariyarsa sai data fidda sauti,yayi qoqarin daidaita kansa,da gaske ta jahilci aure,da alama aiki je jajur a gabansa a kanta,bai tsawwala sai ya samu komai daga gareta ba,amma aqalla ta gama sanin meye auren kansa,don da alama batasan meye shi ba.

"Kwashesu ki tafi" ya bata umarni a taqaice,ta baya ta zuro hannunta ta jawo ledar zuwa gabanta,sannan ta miqe da sauri sauri tayi dakinta.

Tana shiga ta jefa ledar saman sofa bed tana zumbura baki kamar zata fashe,ledar ta qarasa yayewa kayan suka fito sosai,bata gama kula da hotunan jiki bama sai yanzu,ta qarasa tana daga kayan saita jefar zuciyarta a a cushe

"Lallai matar nan ma 'yar iska ce ashe itama,don me zata bata wadan nan kayan?" Hadasu tayi ta cukuikuye ta jefa cikin sif,ta koma saman gado ta lafe a cikin bargo abinta,idanunta ta rufe,tana fata bacci ya dauketa tun tana iya jin motsinsa,basai waje yayi shuru ba.

?????????Washegari ma haka ya fita,bai tsaya yin breakfast ba,yauma ita dinma kamar jiya,bayan ta gama 'yan gyare gyarenta da zata iya,saita dawo bakin window din falon ta zauna,lokaci lokaci tana yaye labulen tana leqa farfajiyar gidan,abinda ya tayata zama kenan,duk da yace mata tana iya shiga cikin gidan ta zauna a can,kota debe kewa,amma kasancewarta mara saurin sabo taji gwara tayi zamanta a nan har zuwa sanda ya dawo gida.

To tsahon kwanaki biyar kusan haka rayuwar ta dinga gara musu,da safe idan zaya fita aiki zai sameta ne a falo,sabida yafi dakinta haske,zatayi masa a dawo lafiya bayan ta gaidashi,ya ajiye mata kudi ya kuma tambayeta bata da matsala,sannan ya mata sallama,takan bishi da idanu tana jin kamar ta bishi,wani lokacin yana ankare da ita,wani zubin hankalinsa yayi gaba,zata gyara dakinta data fara sabawa dashi,ta gyara falo ta goge shi tasa,duk da cewa tana daukan lokaci kafin ta gama,amma yana kintsuwa,kyan sharar nata da gyaran nata yake gani,saboda tafi hafsat nesa ba kusa ba, at least ita bata barin qura ko datti,sabanin hafsat din da ko ina a birkice yake,duk da suna da komai a store,to amma bata taba dora girki ba,yana sawa a kawo mata abinci,idan ya dawo tana cikin falon,amma wata qurya ta daban,a can zata zauna ba um ba um um,tana kallonsa kawai,duk da tana buqatar hira da

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login