Showing 126001 words to 129000 words out of 200116 words

Chapter 43 - A RUBUCE TAKE (KADDARATA)

mata

"Ina kwana?"
"Kin tashi lafiya?"
"Lafiya lau ya jikin naka?" Idanunsa ya lumshe ya kuma budesu yana sakin murmushi, lallai quruciya na damunta da gaske

"Da sauqi,na warke" kai ta jinjina masa,sai ya sake duban wayar

"Ba kiranki akeyi ba ki daga" fuska ta kwabe sannan ta girgiza kanta,bai sake cewa komai ba ya matsa wajen kujerar da yakan zauna yayi karatu da asuba ya jawota ya zauna,sai widad din ta miqe a hankali ta nade abun sallar nata,ta nufi qofar fita a dakin

"Ina zuwa?" Waiwayowa tayi

"Xanje gaida hajiya" sai ya gyada mata kai kawai.

Daga inda yake zaunen yana hangen hasken da wayar taketa yi,yadda aketa kira ba qaqqautawa ya bashi mamaki,ba tare daya shirya ba ya miqe,ya isa ga wayar ya dauko,sai yaga sunan mommy hafsat,abun ya daure masa kai,ya juya yana duba wayarsa waiko zaiga miscall dinta,may be ta kirashi ne baya kusa bai daga ba,wani abun kuma ya faru,amma sai yaga babu kiranta ko daya,ya daga wayar ya kara a kunnensa tare da yin sallama.

Jin muryarsa ya qarasa fadar mata da gaba,jikinta gaba daya yayi laushi,ta saki abun sallar a qasa,da gaske suna tare,tare suka kwana,kasa motsawa bakinta yayi,ta riga data samu amsar abinda take nema,don haka ta kashe wayar tare da sulalewa a wajen ta saki wani irin kuka mai tsananin zafi da cin rai,shikenan,ta faru ts qare.

Jin alamun an katse ya sashi daga wayar ya kalli screen din wayar,sai yadan tabe baki ya maida wayar ya ajjiye,har ya taka zai bar wajen sai hoton fuskar wayar ya dauki hankalinsa,ya koma ya sake dauka,ya koma saman kujerar ya zauna,ya buda gallery ya soma kallon pictures din a hankali har baisan sanda murmushi ya dinga kubcewa daga fuskarsa ba,kowanne hoto da kalar quruciyar da za'a nuna a jiki.

Hannunsa ya miqa,ya dauki wayarsa ya buda,yayi marking wasu daga ciki ya tura.

Ranar kaf qin yarda tayi ta sake komawa dakinsa,ko hanya qin yarda tayi su hada dashi,tana tsakanin dakin hajiya da kitchen,bayan sun hada breakfast ita da muneera suka shirya komai a falo,tare sukayi break din har hajiyan,sunayi ana taba hira,da suka gama suka sake gyare gidan tare,shi da hajiyan suna dai falo suna hira,a nan sukaci abincin ranar tare da hajiyan,sannan ya koma daki ya shirya ya fice.

A daren ranar yana zaune daga bakin gadon sa,qaramin littafin addu'o'i ne a hannunsa yana karantawa,ya gama komai,kammala addu'arka ne kawai ya rage masa,amma sam baiji motsinta ba,lokaci lokaci yana daga kai ya kalli bakin qofar dakin nasa a haka har ya kammala addu'ar,ya aje littafin gefen bedside ya zuro qafafunsa ya zura bedroom slippers dinsa ya miqe a hankali ya fito daga dakin.

Babu kowa a falon,amma yaga dakinta a bude,yasan suna ciki,yayi gaba zuwa dakin,ya tura qofar bakinsa dauke da sallama.

Dukkansu suka amsa,hajiya na zaune gefan gado,muneera da widad na saman qaramin carpet din dake shimfide qasan dakin,muneeran na maidawa weedad kalbar kanta da santsin kan ya sanya ta ware kamar ba'a taba yinta ba,bataso a taba mata kai tana ta qorafi muneeran na fadin saita yi mata,hajiya na goyuwa da bayan weedad din.

Kadan ya kalli sashen da suke,ya qaraso ciki,ya samu gefan hajiya ya zauna

"Bakiyi bacci ba hajiya?" Sai tayi murmushi

"Banyi ba,ina dai shiri"

"to yayi kyau,kin hada komai naki waje daya ko?, saboda gobe sha biyu zamu fita"

"Komai a kammale yake"

"Ma sha Allah.....shikenan,dama zuwa nayi nai miki sallama,sai da safe"

"To Allah ya bamu alkhairi ya tashemu lafiya" sai ya juya yana ficewa a dakin,minti biyu hajiyan ta kalli widad

"Maza tashi ki tafi ki kwanta kin baro mijinki,nikam sai da safenku" dif widad tayi,don ita gaba daya ta gama tsarin kwana a nan din,ta dan dubi muneera taga itama ta fara shirin kwanciyar,dole ta miqe,ta dauki siririn gyalen abayarta ta dora saman kanta,ta bude closet dinta ta dauki rigar bacci tayi musu sai da safe ta fita.

A sanyaye ta tura qofar dakin tashiga da sallama,yana zaune daga bakin gado yana amsa waya,haka kawai yaji sanyi har cikin ransa sanda yaga ta shigo din,bandaki ta wuce,ta fidda kayan jikinta tayi wanka,don zuwa yanzu tayi mugun sabo da wankan dare,ta shirya cikin kayan baccin ta fito.

Dim light ne a dakin,yana iya hangen sanda ta fito da kuma hawanta saman gadon,taja duvet ta kwanta ba tare data ce komai ba,qaramin murmushi ya saki,abinda ya faru jiya yana dawo masa,sai ya samu kansa da janyo wayarsa,ya duba wajen music ya lalubo kukan magen jiya ya saka.

Curewa tayi waje daya,tun tana iya ganin zata jure harta kasa,sannu sannu sai gata cikin jikinsa ta cukuikuye shi,ya saki murmushin nasara ya sanya hannunsa ya lullubeta cikin qirjinsa yana sakin murmushi,ita kuna tayi lamo tana sauraren bugun zuciyarsa da nata da kowannensu ke fita da sauri da sauri.



*H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*

Page 65



"Tom.....zamu tafi" abbas ya fada yana duban qwayar idanun widad din,hannunsa zube a aljihun wandon lallausan yadinsa da aka yiwa wani irin dinkin girma.

Daga kai tayi da nufin kallonsa,duk yadda taso ya hadiye abinda takeji a qasan ranta amma ta kasa,dole haka ta saka qwayar idanunta a tasa,dai dai sanda hawayen da take riqewa ya sulmiyo daga idanunta,maganar da zatayi ta riqe mata a maqoshi,sai ta saki kuka sosai,abind aya tilasta mata saka tafukan hannayenta duka biyun ta lullube fuskarta dasu.

Duka idanunsa ya fiddo,ya ciro hannayensa yana matsowa inda take tsaye

"What's happening weedad?" Kai ta girgiza masa,saidai kukan take har yanxu

"Noo....noo,kada muyi haka dake mana uhnnn?" Ya fadi a tausashe,sai ya sake matsawa gabanta,ya saka duka hannuwansa ya zare nata tafukan hannayen daga fuskar tata yana kallonta

"I will be back in sha Allah.....ki daina kukan nan,yana qona ni,zuciyata tana zafi.....ko kinaso nima nayi kukan?" Ya fadi yana jin wani irin rauni da bai taba jin kamarsa ba,kanta ta girgiza amma ta gaza tsaida hawayen

"It's okay,i promise you bazamu dade ba,shikenan?"saita sake jinjina masa kai,haka kawai takeji wani tashin hankali da rashin sukuni a tattare da ita,sai takejin kamar zai tafi ya barta,kamar bazai dawo ba,tana jin kamar an dauke wani muhimmin sashe ne a jikinta,batasan wanne irin feeling bane wannan,tsahon rayuwarta bata taba fuskantar irinsa ba.

Tas yasa soft handkerchief dinsa ya goge mata hawayen,sannan ya bude tafin hannunta ya saka mata shi,ya maida ya dunqule hannun nata cikin nasa,sai yaja da baya kadan yana gyara zaman rigarsa data cukuikuye yana kallonta,cikin ransa yakejin wani shauqi yana saukar masa,ganin wani yana kewarka.....ya shiga damuwa saboda zaiyi rashinka a kusa dashi......wani irin dadi kima da daraja gareshi a zuciya,wani irin yanayi da bazaice ga lokaci na qarshe daya ganshi tattare da matarsa ba,sai ya buda dukkanin hannayensa yana kallonta da idanunsa masu girma da zuwa yanzu suka rusuna,girmansu ya ragu

"Oya.... give me a hug" jiqaqqun idanunta ta daga ta kalleshi,qaramin miskilin murmushinta ya subuce zuwa saman labbanta,a yau din sai taji bata shakkar yin hakan,ta fara takawa a hankali kamar wadda aka sakawa wani kida na musamman,yayin da idanunsa yaji sun fara narkewa a kallonta,cat walking takeyi,irin tafiyar da sai wance da wance cikin isassun mata,bai taba lura da hakan ba sai yau,ya qaraso gareshi a hankali,ta shige jikinsa kuwa gaba daya,harda qoqarin saka hannuwanta ta zagayo dasu ta bayansa,sai ya tallafa mata,ya durquso ya sakata sosai a jikin nasa,yana jin kamar ya maidata cikinsa.

Sun jima sosai a haka kafin ta fara janye jikinta,ya danyi baya jikinsa a mugun mace yana maida numfashi,kusan minti hudu kafin ya dai daita kansa

"Ayimin rakiya mana" kai ta girgiza tana murmushi,duka idanunsa ya bude a kanta

"Why?"

"Hajiya fa.....so kake ta gane ka rungume ni,sannan tun dazu muka shigo daki ni dakai fa,nidai kunya nakeji" ta qarasa maganar tana turo baki,bai shirya ba bai kuma zata ba dariya ta kubce masa,yasa hannunsa saman bakinsa ya dara kadan sannan ya janye

"Ok, come closer" ya fada yana daga mata hannu,bata musa ba tasake matsowa,ya sukuya a hankali ya bata wani irin hot and deep kisses saman goshi da kuncinta,sannan yaja baya yana cewa

"Na bawa Allah amanarku,ki kula da kanki" ta gyada kai a hankali,sannan ta motsa bakinta

"A dawo lafiya,Allah ya kiyaye yasa ku dawo lafiya" lumshe idanu yayi har ya fice,ji yayi a duniya kamar ba'a taba masa addu'a ba, siririyar muryarta ta dinga masa amsa kuwwa a kunne,har suka isa airport yana wassafa wasu abubuwa da yawa a kanta.

Kafin jirginsu yakai ga tashi yayi kiran hafsat,ko ba komai yana son ya sauke nauyin dake kansa,yanason kuma yayi magana da yaranshi,sai daya kira sau uku,ana hudu yaci sa'a aka daga,saidai muryar yaran ce,ya biye musu sukayi surutu sosai har sai da yaji ya siqe

"Ku bawa mommynku" ya fadawa mimi,shuru na sakanni ya ratsa,sannan yaji mimi tace

"Tace bacci takeyi" idonsa ya rufe sannan ya budesu lokaci guda, irin yadda yakanyi wajen hadiya fushi idan ransa ya baci,baya so tana saka yaransa a ire iren wadan nan abubuwan nasu,yanzu ko ba komai ta koyawa yarinyar qarya

"Alright....idan ta tashi kuce nace ta kula daku,daddynku zaiyi kewarku"

"A dawo lafiya daddy,ka siyo mana jirgi" murmushi ya kufce masa,yana fatan wataran dukkansu ya kaisu umara ko aikin hajjin suma

"In sha Allah mimi na,i love you"

"I love you too daddy" ta amsa masa,dai dai lokacin hafsat da haushi ya cikata tayi fam ta warce wayar,ta jefi yarinyar da harara

"Uwar kinibibin tsiya,i love you too daddy" tayi maganar tana kwata muryar yarinyar

"Koni ban fada ba sai ke,saikibishi ai uwar son uba" taja tsaki tana jefa wayar gefe,harta koma zata kwanta sai kuma taji ta fasa,ta miqe ta fada bandaki ta watsa kwaskwarima,ta fito ta fara shirin fita,su mimi kuwa kaya kawai ta fidda musu tace su debo wasu ta saka musu,gida zasu,idan sun qarasa can a samu wani yayi musu wankan, yaro ba hankali,da murnarta ta shiga dakinsu ta debo musu kayan,uwar ba tare data tsaya wani dubawa ba ta karba ta saka musu,ta hado kansu ta sanyasu a motarta suka fice daga gidan,gidan kamar mazaunin bola,saidai hankalinta a kwance yake,tasan me sanya damuwar saita gyara din baya qasar ma gaba daya,duk sanda ta samu chance ta gyara din,hankalinta yayi gidan,tana son su hadu da anty ummee taji sabbin shawarwari,tana jin kamar tafiyar ta ta fara baudewa.

A daren ranar daya sauka ya sake kiran hafsat din don ya gaya mata sun sauka lafiya,amma harta qaraci ringing dinta bata daga ba,har a lokacin ma tana gida bata koma ba,mamarta ta sake cewa da ita

"Shareshi,wani abunma duk laifinki ne,ace mijinka baya shakkarka me akayi kenan" .

Yasan dai ba yadda za'a yi ya mata irin wanna kiran tace bata gani ba,kuma koda a daxun baccin take da gaske ai yaci ace tayi kiransa bayan ta farka,ransa yakai qololuwar baci,yaji kuma a ransa bazai sake kiranta ba indai shine,sai ya maida akalar kiran nasa ga widad.

Dukkaninsu wata irin sakewa sukayi shida ita,sunyi hira mai tsaho,duk abinda tayi a yau din sai data zayyane masa shi kuma yana kwance saman gadon hotel din da suka sauka yana biye mata,a nan take bashi labarin taga tallan wajen wani koyar da girki a kaduna tanaso

"Iyeee .... dole wai so take ta fini iya girki...... alright,zansa Samuel ya yiwa rose magana" da murnarta sosai ta shiga masa godiya,har yaga godiyar kamar tayi yawa,ita kuwa a wajenta normal ne,kamar yadda aka horeta kenan a gida.

Kwana daya da zancan kuwa saiga rose tazo har gida samuel ya kawota,haduwar farko jininsu ya hadu da rose din,saboda tana da matuqar kirki da kuma ban dariya,wannan ya sanya saurin sabo a tsakaninsu duk da rashin saurin sabon da widad ke dashi,shiryawa sukayi ita da muneera da aka bar mata suka wuce wajen sukayi register da komai da komai sannan suka dawo gida,tun daga ranar rose ce ke zuwa ta kaita ta kuma dawo da ita gida,cikin lokaci qalilan sukayi sabo,itama tana son widad saboda kirkinta,don idan sun dawo din sai ta tsare rose ta zauna taci abinci,harma suyi hira da ita,sau tari ma idan ta gwada abinda ta koya saita ajema rose din,komai tabgwada din kuwa sai yayi kyau exactly kamar yadda ta koyo,abun yayita bawa rose mamaki da sha'awa,wata irin gifted ce weedad din.

Ganin yadda widad din keda sha'awa girke girke,sai rose din ta ware wasu ranaku take koya mata irin girkin nasu qabilar,idan sukayi wasu daga ciki takance

"Oga yanaso wannan" tsaf widad ta dauke wadanda tace yafiso din,ta dinga practicing nasu da kyau,har suka zauna mata,ita a karan kanta dadi takeji,tana jin dadin yadda a yanzun ta fara iya kalolin girke girke da dama, yadda ta maida hankali a kitchen yanzun bata maida haka kan karatunta ba,gefe guda ta matsawa anty deena, kullum saita qara mata bayani akan abincin ainihin qasarsu,duk da wannan dama tana ganin ummu tana yinsu sosai,saidai bata taba cewa zatayi da kanta ba.

Cikin wata daya ta koya abubuwa da yawa ta fannin girki,ansha barna,don kullum da abinda za'a girka,saidai ta samu experience sosai.

Tun saura kwana uku su dawo take ta practicing abinda zata dafa musu shida hajiya,sunyi hira da anty deena da anty madeena sosai,sun kuma bata shawarwari cikin hikima,ana ya jibi zasu dawo muneera ta taimaka mata suka gyare gidan tas,sukayi goge goge sosai,washegari kuma rose tace mata

"Madam ko za'a kaiki saloon?" Fadin da rose din tayi sai ya zama kamar tuni a wajenta,tace ta kaita.

Waje ne mai kyau da zaka yiwa kallo daya kasan sun iya aikinsu,cikin yarensu sukayi magana da rose bayan sun gama gaisawa,mutum biyu aka gamawa sannan aka kama kanta.

Sosai matar tayi mamakin yanayin kan widad din,da kanta matar mai suna ada tace bata buqatar relaxer.

Wani irin gyaran kai akayi mata,wanda ita kanta widad din sai data tsaya ta kalla kanta da kyau a madubi bayan sun koma gida,muneera tace

"Wallahi matar nan ta iya gyara matar uncle,inama idan bikina ya taso nan zanzo tayimin"

"Kizo wallahi,saina rakaki" ta fada tana sake kallon kanta dadi yana cikata.

Isowar yammaci sukayi a washegari,kafin isowar tasu komai ya kammala kamar wata babbar mace,cikin atamfa ta shirya dinkin riga da skert,saidai ta gaza daura dankwalin sai yafashi tayi saman kanta,tana maqale jikin window din falonta har zuwa sanda motar data daukosu ta sako kai harabar gidan.

Bin motar tayi da kallo,tana zuciyarta na bugawa da sauri da sauri,farincikin da batasan dalilinsa ba takeji yana ratsa zuciyarta,taci gaba da kallon motar har ta shige parking lot

"Sun iso,bakiji shigowar motarsu ba?,kizo muje mu taraso" muneera dake sanya hijab dinta ta fada tana kallon widad, waiwayo tayi tana duban muneera,sai takejin kamar qafafunta ba zasu iya kaita wajen ba,ta girgiza kai

"Kije yanzu ai zasu shigo" kai ta kada tana dariya

"Oh,wai kunyar hajiya kenan kikeyi,to nidai nayi nan" ta fadi tana yin gaba da sauri,ta bude qofaf ta fice.

Sanda ya shigo ta dauka zata iya dakewa,sai tsintar kanta tayi a gabansa,shima yayi tsammanin zai iya jurewa amma sai ya kasa, hannuwansa gaba daya ya bude mata,batayi wata wata ba ta fada ciki,ya maida ya rufeta gam a cki yana sauke wata wawiyar ajiyar zuciya,yayin da ita kuma ta fashe da kuka sosai cike da wani tune na shagwaba,sai ya gaza jurewa tsaiwar,ya sulale ya zauna a wajen,hakan ya bata damar zama sosai a jikinsa.


*H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks: Huguma*

Page 66



Sun dauki mintuna a haka sannan ta daga kanta suka hada idanu,shima ita yake kallo,haka kawai taji wata kunya ta kamata,saboda kallon da yake matan ya mata nauyi sosai a gangar jikinta da zuciya,hakanan bata saba ganin kalar kallon ba a tattare dashi,saita cusa kanta a qirjinsa tana shaqar wani bala'e'en qamshi da fatarsa ke fiddawa

"Eheenn.....baby na ta fara sanin kunya ne?" Tambayar data sakata ji kamar zata nutse,sai kuma ta janye jikinta da sauri tana fadi cikin fidda idanu waje

"Hajiya!" Dukkansu bin falon sukayi da kallo,ba hajiya babu burbushinta,sai suka kalli juna a tare,kafin yayi komai ta rigashi miqewa tana narke ido

"Hajiya fa uncle" amsar da shima bai santa ba,yasan dai yana gaba tana biye dashi,komawa tayi ko ciki ta shige.

Tare sukayi hanyar dakinta,suna zuwa widad din ta lafe daga bakin qofa,shi ya tura ya leqa,saiya samu hajiyan zaune cikin dakin daga qasan carfet ta miqe qafafunta

"Oh,hajiya kina ciki kenan" ya fada cikin jin kunya da nauyi yana shafa kansa,mazewa tayi kamar ba abinda ya faru

"Wallahi,kasan ko yaya tafiya take ba'a rasa jiki da gajiya,kaima ya kamata ka shiga ciki ka huta hakanan,sai Allah ya kaimu anjima"

"To hajiya a huta lafiya" ya fadi cikin jin nauyi,sai data murmusa sannan ta amsa mishi,ya maida qofar ya rufe sannan ya juyo suka hada ido da widad din.

Qwalla ce

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login