Showing 69001 words to 72000 words out of 200116 words

Chapter 24 - A RUBUCE TAKE (KADDARATA)

kawai tasa hannunta a fuska ta fashe da kuka mai cin rai,tana tsananin son abbas tana kuma kishinsa,batasan yadda zata jurewa wannan al'amarin ba,abu mafi dagula mata hankali shine sadakar yalla da akace ya auro,tana sane da yadda suke fidda mace da yaranta daga gidan,ta yaya zata kaucewa wannan?,saita tayi cikin bedrooms dinta gudun kada wani yaji gunjin kukanta,don kukan take da buqatar yi sosai.

Su biyu ne a dakin ita da nujood,sun nutse abinsu saman gadon da yasha shimfida da lafiyayyen zanin gadon da yake tafiyayye tun daga yemen,sai hira suke abinsu suna dariya,babu abinda ya damesu,ita sam bata wani tuna wai amaryace,nan din gidan aurenta ne,zamansu a haka dasu anty madeena yana mata dadi,hankalinta kwance,bata tuna tafiya zasuyi su barta.

Dai dai nan anty deena data gama hada kayanta tsaf ta tura qofar dakin ta shigo,saita saki baki kawai tana kallonsu,gadon da aka gama gyarewa aka sa masa zanin gado mafi tsada suka haye tsakiyarsa abinsu?

"Qaniyarki nujood,sauko" anty deena ta fada tana mata daquwa

"Gadon amaryar zaki kama ku haye?,ke baki mata fada ba ita batayi miki ba?" Nujood din tana dariya ta sauko,sai widad tayi tsam da ranta tana kallon anty deena,itakam batason ana nuna banbamcin nan sam,yanzu meye laifi don sunyi kwanxiyarsu ita da nujood din a nan

"Ke kuma bakiji inna laila na kiranki ba tun daxu mijinki ya shigo kizo ku gaisa?" Kanta ta dauke sannan ta tura baki gaba,ita wannan miji da aketa cewa,ita an takurata fa da zancansa

"Ni banji ba"

"Bakiji ba amma na gaya miki ana kiranki a falo ko?" Nujood ta fada gudun kada tayi laifi

"Ya isa naji,jeki falo nujood" anty deena ta fada tana wucewa ciki,ba musu ta miqe ta fice,ita kuma ta isa babbar wardrobe din widad,ta bude tana duba kayan dake ciki.

Wata lafiyayyar gown ta atamfa ta dauko mata hade da mayafinta ta ajjiye mata,kusan duka kayanta a tsume suke da wani irin turaren kaya na itace mai matuqar qamshi da daukar hankalin duk wanda ya jishi,ta duba inda suka adana mata kayan ado ta fidda mata sarqa dan kunnen da abun hannu masu matuqar kyau,sannan ta dauko mata sabbin undies,saita juyo tana kallonta ganin wata guntuwar pad

"Kin taba yin period ne?" Gaban widad ne ya fadi,saita daburce lokaci guda,saboda bada kowa take magana irin wannan ba idan ba ummunta ba,ganin ta rude sai anty deenan tayi murmushi

"Ni kikejin kunya?,to ai kowa ma yana yi,kin taba yi ne?" Kai ta gyada.mata a hankali,sai anty deena din ta sauke ajiyar zuciya,duk sanda ta daga idanu ta kalli widad din sai taji fargaba da tausayinta,babu tabbacin zata yita zama a haka ba tare da komai ya hadasu ba,tasan halin mazan yanzu sarai wajen rashin haquri,duk da cewa yana da mata,amma sometimes masu matan sunfi fitina,saboda sunsan yadda abun yake

"Sau nawa kikayi?,kuma yaushe ne yinki na qarshe?"

"Sau biyu inayi,yau sati biyu" kai ta jinjina,saita koma gefenta ta zauna,cikin dabara take mata tambaya kan jinin haila da kuma wankan tsarki,cikin ikon Allah komai ta sani,saboda ba baya bace ita din wajen zuwa islamiyya,sannan ummu ta zauna da ita ta mata bayanin komai. Sosai anty deena taji dadin hakan,saita dubeta

"Shiga bandaki ki sake wanka kizo ki shirya zaki je ki gaida mijinki,tunda mukazo baku gaisa ba,ko kun gaisa?" Bata kawo komai a ranta ba ta girgiza kai alamun a'ah,saboda dazun tana bacci ya shigo,sai fitarsa ta gani,yanzun kuma tana nan suna hira da nujood

"Amma anty deena sanda zamu gidan hajiya fa nayi"

"Wannan daban yake,duk sanda kikasan zaki wajensa ko kinyi wanka ki dinga sakewa kinji?,ki dauko kayan kwalliyar nan da aka kawo miki kiyi kwalliyarki ki saka sababbin kaya,maza tashi qanwata ta kaina" murmushi kawai tayi,ta tashin ta shiga bayi ta hada ruwa kamar yadda ta umarceta,tayi wankanta da kyau.

Kusan ita ta shiryata,wani irin tururin qamshi na fita a jikinta

"Muje na rakaki,amma zan dawo,kya taho ke kadai" kai ta gyada mata,bata wani damu ba,kawai tana jin dadin yadda tayi kyau abinta,suka jera da anty deena din tana mata wani karatu cikin hikima widad din na jinta.

Daga dan nesa kadan da part din nasa ta juya,ita kuma widad din ta wuce tana dosar wajen.

A darare,cike da baqunta da kuma tsoro,kasancewar a sannan sha daya kusan na dare ta murda handle din falon,saidai a kulle ta jishi,sai ta saka hannu tadanyi knocking,tana rayawa a ranta indai ba'a bude ba tafiyarta zatayi,to amma me zata cewa anty deena?,tunda tayi mata alqawarin zuwa,kuma bata iya qarya ba bare tace taje ta dawo ne.

Dai dai lokacin da yake zaune qasan carfet,ya bude babbar farar takarda mai girma wadda ke dauke da map na garin kaduna,system dinsa na kunne hakanan akwai wani dan madaidaicin allo dake tsaye a gefe,yayi wasu zane zane da qananun rubuce rubuce da shi kadai yasan ma'anarsu,akwai babban aikin da yake tunkara,wanda yakeson gabatar dashi a sirrance,kamar yadda ya saba,kusan nasarar aikinsa kenan,a duk sanda zai gabatar da aiki na kama masu laifi da sauransu,yakan shirya komai a boye ne,dagashi sai amintattun sa irinsu samuel,sai lokacin gabatarwa yayi sannan.

Idanunsa daya tsurawa takardar yana karantar map din ya daga yana duban qofa,yana tunanin hafsa ce,saboda ta kirashi taji ya dawo ba jimawa,to amma kuma knocking din ba irin nata bane,sai ya miqe a hankali ya juya allon,ya kuma kifa takardar,ya matsar da butar coffee din da yaketa sha a madadin abinci ya nufi qofar.

Tuni fuskarta ta soma narkewa da tsoro,ta sake daga hannu cikin saarewa zatayi bugun qarshe ya buda qofar,iska mai sanyi da taushi dake kadawa a gurin ta yayibo dukka qamshin dake jikinta ta jefo zuwa hancinsa,dai dai sanda ya sauke kallonsa ga baby face dinta,fararen idanuwanta tarwai a haske wajen hadi da hasken falon daya sake haske fuskarta.

Idanu ta zuba masa kamar zata saki kuka,shima idanun ya zuba mata,sai kuma ya janye gefe yana bata hanya,tsaiwa tayi kamar ba zata wuce ba,ta wurga idanunta ta gefensa tana hango cikin falon,tanaskn tava da mutum ko su kadai ne?,hango system dinsa da tayi sai ranta ya bata bashi kadai bane,wannan ya bata sukunin rabawa ta gefansa sosai ta wuce zuwa ciki,tun daga ranar da ummu ke gargadinta da kebewa da duk wani namiji ko kusantar inda suke bata qara bari sun hada inuwa da kowa ba,nan nan kusa kuma data sake tsawatar mata fiye da baya,watanni uku baya sanda ta fara period,ta sake jadda da mata batun.

Wata ajiyar zuciya ce ta subuce masa,yayi tsaye a wajen kamar mai jiran wani,saidai yana shaqar qamshin ne da yayi masa dirar mikiya,hannunsa ya miqa ya maida qofar ya turata,widad dake zaune a darare a qasa tadan fidda ido waje kadan,kai.....ya zai rufesu su biyu?,saita tsirashi da idanu sanda yake takowa zuwa ciki,tana masa kallon tuhuma.

Yana shirin zama suka hada idanu,farare sol din idanuwanta suka hadu da nasa manyan idanun,sai yadan lumshe nasa kadan,ya janyo computer dinsa gabansa yana cewa

"Bakiyi bacci ba?" Kai ta gyada a maimakon ta amsa masa,sannan tace

"Ina wuni?"

"Kin yini lafiya?" Ya amsa mata yana daddanna system din ba tare da ya sake dubanta ba

"Lafiya lau,dama anty deena ce tace nazo na gaisheka,wai bamu hadu ba dazu" yadda tayi maganar cike da quruciya da kuma sakalci shigen na yaran fari ya tilasta masa daga kai ya kalleta,suka sake hada idanu a karo na uku,qaramin murmushi ne ya subuce masa,kallonsa take kanta tsaye kamar mai masa kallon tuhuma,ya karanci me take nufi a cikin zancanta,amma yana sa yaqinin ita din bata fahimci komai ba,ta taho abinta ne gaba gadi

"Anty deena ta kyauta,kinga ta fiki kirki,sai ita tayi tunanin kizo ki gaida mijinki" ya bata amsa yana sake maida hankalinsa ga system din nasa

"Uhmmm" ta fada cikin rashin sabo da kuma baqunta.

Coffee din gabansa ya tura mata yana sake kallonta,saita girgiza kai alamun a'ah,saboda ummu ta hanata karbar abun hannun maza,yana nan kuma daram a kanta bata manta ba,bai sake cewa komai ba sai kawai ya miqa hannunsa,ya jawo allonsa yaci gaba da aikinsa,abun da ya dauki hankalin widad kenan,ta dinga binsa da kallo

"Dama malamin makaranta ne?,amma kuma nujood tace mata har bindiga ce dashi,to amma wa yake koyawa karatu bayan shi kadai ne a dakin?,inama zai dinga koya mata,tayi missing makaranta da karatu sosai,tanason karatu" ire iren wadan nan tunanukan ta dinga yi,har sai da taga aikinsa yakeyi sosai cike da qawa zuci,ta dan fara motsawa,so take ta koma,amma kuma tasan ba zata iya fita ita kadai ba,saidai ya rakata,amma kuma ta kasa buda baki ta gaya masa.

Marker din hannunsa ya ajjiye yana fesar da iska daga bakinsa,yayi taku biyu baya a hankali,sannan ya duqa dab da ita,idanu suka sake hadawa,sai ya kauda kai ya soma zuge jakar dake aje a gefanta,wasu tsofaffin takardu ne da yasa samuel ya kawo masa su zai duba wani abu a jiki,yasoma zarosu,sai tsanya tayi tsalle ta biyosu har guda biyu,daya ta fada gefe dayar kuma kai tsaye ta fada jikin widad.

Gigitaccen ihu data saki ya sanyashi watsar da takardun hannun nasa,kafin ya ankara tayo kansa tana tsalle gami da kiran wayyo Allah,wayyo ummu,taso rudashi amma ya tattara hankalinsa waje guda,saidai duk yadda yakeson dawo da ita nutsuwarta widad batasan yana yi ba,mayafi tuni ta cillar dashi,dankwali ma ya zame,lafiyayyen baqin gashinta dake fitar da qamshi ya tarwatse.

Suciyarsa tayi wani mugun bugawa sanda ta shige jikinsa tana,sassalkan gashinta ya wanzu a fuskarsa,ihu take da zazzaqar muryarta dake cike da tsoro tana fadin ya cire mata

"Calm down,ki nutsu,tsanyace fa kawai" ya fada muryarsa na dan rawa kadan,saidai ko daya bata jishi ba,tsoro ya cika kwanyarta a lokacin.

*AREWABOOKS:HUGUMA*

KI KULANI miss xoxo

DAUDAR GORA Billynabdul

RUMBUN K'AYA hafsat rano

IDON NERA Mamuhghee

A RUBUCE TAKE huguma

_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_

_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

0022419171
Maryam sani
Access bank

Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070

*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261

*Al'ummar nijer +227 96 09 67 63


*Thanks for choosing us*=?%?=?%?=?%?=?%?=?%?=?%?

*H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)

Page 36


Yadda ta shige masan tamkar zata koma cikinsa,gaba daya ta kasa gane me yake fada,sai kawai ya buda hannayensa,ya kuma rungumeta sosai a jikinsa,yayi mata riqon tsauri ta yadda ba zataci gaba da tsalle ba.

A hankali ta fara samun nutsuwa,kukanta ya fara ja baya,sai a sannan kuma ta tuna ajikin wani take,tayi wani irin zillo ta zame daga jikinsa,cikin tashin hankali hadi da wani sabon tsoron,tunda take tsahon rayuwarta ko yatsarta ba wanda ya taba riqewa,amma yau gata a jikin wani?,ta shiga uku?,yanzu shikenan ta zama 'yar iska?,idan ta samu ciki ta mutu fa?,bata kyautawa ummu ba,sai sabbin hawaye suka barke mata,jikinta har rawa yakeyi

"Tafiya zanyi" ta fada bakinta yana rawa,kafeta yayi da idanu yanason gane me ya tsoratata kuma dai?,kafin ya gama wannan tunanin aka fara knocking qofar,ya maida kallonsa ga qofar,kafin ya bada izini an murda handle din an shigo.

Hafsat ce dauke da jug da cup,da farki idanunta naga abbas,sai kuma sabon qamshin da taji ya baibaye falon yaja hankalinta,a hankali idanunwanta suka sauka kan widad dake tsaye tana tsuma,jikinta yana rawa,kanta babu dankwali bare mayafi,dukka suna watse a qasa,ga hawaye shabe shabe kan fuskarta,gabanta yayi wani mummunan faduwa,abubuwa biyu suka bugeta lokaci daya.

Zallar madarar kyau data gani kwance saman fuskar widad din,duk da shekarunta qananu,da kuma tunanin daya darsu a ranta a take a lokacin,abbas ya nemi tarayya da widad din,tunanin daya kusa sanyata zubar da kayan hannunta,jikinta duka ya dauki rawa.

A nutse ya amsa mata sallamar,ya dauke kansa ya maida ga widad data fara yin gaba zata fice,har yanzu tana hawaye

"Dakata" ya fada cikin salo na umarni,cak ta tsaya amma har yanzu jikinta rawa yake,tasan tata ta qare,tana shiga su anty deena zasu gane wani ya tabata.

Inda ta yasar da dankwali da mayafin ya qarasa,ya dauko mata ya tsaya gabanta ya miqa mata yana kallonta,sannan yace da ita

"Daura" jikinta na rawa ta karba din,amma ta gaza daura dankwalin,sai mayafin ta yafa kawai

"Muje na rakaki" ya fada sannan ya waiwaya ga hafsat wadda ta yiwa kanta mazaunin dole don kada ta fadi

"Ina zuwa" yace da ita suka fice shida widad din.

Kuka sosai ta fashe dashi kamar qaramar yarinya,da gaske abbas neman tarayya da yarinyar yayi?,har zuciyar abbas ta fara qawata masa ita?,duk qoqari da jajircewar da taketa yi kenan tana neman tashi a banza?,ya akayi tayi saken da har yarinyar tasan tazo sashensa?,ba shakka sanyata akayi,tunda 'yan uwanta suna nan,tabbas ba zata ba haka ta sake faruwa ba,sai ta miqe tana barin flask din kawai ta fito ba tare data bi ta kansa ba,idanuwanta har basa gani sosai saboda tashin hankalin da takejin kanta a ciki,a daddafe ta dinga laluba hanya har takai kanta sassanta.

A gaba ya sanyata yana biye da ita har suka isa sasssan nata,ita ta fara knocking,tayi tayi shuru ba alamun za'a bude,sai yace ta matsa shima ya shiga tayata,amma shuru kakeji,saiya waiwayo yana dubanta

"I think duka sunyi bacci fa" kai ta langabe tana kallonsa,idanunta na fidda ruwan hawaye

"To a ina zan kwana kenan?,don Allah ka tashesu mana" ido yadan zuba mata na wasu sakanni kafin ya kawar da kansa,quruciyarta ta gaske ce

"Ki koma ki kwana a can,da safe saina rakoki,lokacin sun tashi ko?" Ya fada cikin sigar lallami,saboda yadda yakejin kansa yayi week,bacci ma dai a taqaice yaji yana saukar masa.

"Amm....."

"Ba'a musu da babba right?" Ya fadi cikin sigar tambaya yana ritsata da kallonsa,karon farko taji idanunsa sun dan mata nauyi,saita sadda kanta qasa,ya sake sakata a gaba kamar dazu suka koma,jikinta duk a mace, hankalinta a tashe,anty deena ce ta jawo mata,ta yaya zata kwana daki daya dashi?.

Yayi mamaki sanda ya dawo yaga babu hafsat din ba dalilinta,sai ya tsugunna ya tattara komai waje daya ya adana,har a sannan widad na zaune a takure a waje daya,ac din dakin ya kashe gaba daya,ya rage fitilun falon,saiya kalleta

"Muje ciki ki kwanta" fuska ta tattare waje daya,tanason cewa a'ah amma kuma batason yaga kamar ummu bata koya mata cewa ba'a yiwa babba musu ba,tunda gashi dazu ya fada,haka ta miqe tana biye dashi har cikin bedroom din nasa.

Da ido take kallon komai,bedroom din nada wani irin weather mai saukar da nutsuwa,sassanyan qamshinsa ya kama dakin sosai,komai fari ne qal,kuma komai yana kan tsari a killace,saita haye kan sofa bed ta dunqule,shi kuma ya wuce bandaki.

A ciki ya shirya cikin wasu silk pyjama sky blue,yayi brush ya feshe jiki da bakinsa da turarukansu

"Zaki canza kaya ne?" Ya fada yana dan duban gefanta,cikinta ne ya bada qululu saboda tsoro,yana nufin ta cire kayan jikinta ta sauya wasu?,a dakinsa?,saita damqe jikinta waje guda kamar wadda ya taho zai rabata da suturarta,ta jijjiga kai da qarfi

"A'ah,wadan nan nakeso na jikina" dariya taso qwace masa amma ya danne,a yadda take acting yasan lallai batasan meye cikakken ma'anar aure ba,to amma me yasa take tsoro haka,sai ya rabu da ita,ya jawo wayarsa da nufin kiran hafsat din yayi mata sai da safe,duk da baisan me ya fiddata daga dakin ba,ya tsammaci zatace zata kwana kamar jiya.

Sau uku yana kiranta tana katse kiran,abun yadan daure masa kai,amma saiya tattara ya watsar,dare yayi,hutu yake buqata

"Ki koma gado ki kwanta" ya sake fadi,kamar dazun dai a firgice tace masa a'ah,sai da yayi da gaske sannan ta kuma taga ya yibi filo da bargo yana shirin bar mata dakin sannan taji ranta ya sake.

K'ofar tabi da kallo sanda ya fita,sai kuma ta fara baza idanu,dan banzan tsoron nan nata ya dawo,ji tayi kamar ta bishi,amma ba zata iya ba,curewa tayi waje daya ta lulluba har kanta,saita saki kuka,anty deena ce.....duk ita tace sai tazo,gashi nan sun rufe mata qofa,bayan sunsan ta fita,kewar ummu ta taso mata,ta dinga hawaye ita daya cikin filo,har bacci barawo ya saceta.

A hankali ya bude qofar dakin,duk da akwai qarancin haske amma yana iya hangenta a cure waje daya,sai ya kada kansa ya wuce bandaki.

Alwala ya daura ya dawo dakin,ya feshe jikinsa da turare ya sauya jallabiyyar jikinsa,ya taka a hankali zuwa gefan gadon,hannu yasa ya bubbuga saman filon a tausashe,ta motsa kadan kamar zata tashi,sai kuma ta sake qudundunewa,cikin muryar barci tace

"Don Allah ummu,ba'a idar ba,yanzu aka tayar" shuru ya danyi yana nazarinta,ta kwabe fuska gaba daya tana tura baki gaba a shagwabe,har kuma a hankali ta saki bakin nata,da alama ta koma bacci sosai.

Kai ya girgiza kawai,bai hango komai ba banda zallar quruciya a tattare da ita,shikam baisan ya al'amuran zasuci gaba da tafiya ba,bai hango sauqi ba,sai nauyi daya

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login