Showing 87001 words to 90000 words out of 200116 words

Chapter 30 - A RUBUCE TAKE (KADDARATA)

abu na farko daya fara jan hankalinta ta gane akwai baqo a wajen,sosai ta zuba mata idanu,sai taji gabanta ya fadi,wanne irin kyau yarinyar nan ke dashi?,ta tambayi kanta da kanta,take taji gaba daya ta muzanta,duk da cewa dama ba wani ado tayin ba,rigar da ita ta kwanta baccin,ganin bata jima da sanyata ba kuma a motar gida zasu fita su dawo yasa batayi wani sha'awar canzawa ba.

Kafin ta dawo daga duniyar tunanin data lula widad ta iso wajen,sunata kakaci ita dasu mimi suna qyalqyala dariya abinsu

"Ina yini momy" ta fada fararen jerarrun haqoranta suna bayyana,sautin siririyar muryarta ta karade kunnenta,ta kuma dawo da ita hayyacinta

"Lafiya.....lafiya lau" ta fadi tana bude bayan motar da sauri

"Ku shiga ku zauna,mimi ku shiga" ta fada tana duban idanun widad,kama hannunsu nawwaran tayi,ta fara saka mimi sannan itama ta shiga tana ci gaba da jansu da wasa.

Wata ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke,har yanxu qirjinta bugawa yakeyi,kyawunta yana damunta,yana kuma son ya zame mata barazana,tafi yarda dari bisa dari kyawunta na daya daga cikin abinda ya fusgi hankalin abbas dinta,ta yaya zata gusar da wannan abu dake shirin zame mata barazana?.

"muje ko" ta tsinci muryarsa dab da ita,sai ta dan bishi da kallo har sai daya kusa shigewa motar,ta taka jiki a mace ta isa gaban motar ta buda daya side din ta shiga.

Wani baqon qamshi ne ya ziyarci hancinsa,ya soma shirin tada motar yana zuqar qamshin,sai daya tada ita sannan ya waiwaya ya kalli hafsat

"Yaushe kika sayi wannan turaren?" Kishi ya kamata,bataso tace ba ita bace ya farga da yarinyar,idan kuma tace itace tayi qarya,duk da haka ta gwammace wa qaryar,sai tadan murmusa

"Eh,cikin bikin nan na siya"

"Yayi dadi sosai" ya sake fada yana dan waiwaya sashen da take,duk da baiji yana busowa daga nan ba,murmushin yaqe ta saki tana basarwa,zuciyarta na bugawa,tana addu'ar komai ya tafi dai dai.

Sun dauki hanyan babban super market din suke siyayya lokaci bayan lokaci,motar shuru,bakajin komai sai muryoyinsu widad mimi da nawwara,a hankali muryarta ke shiga kunnensa,itama ta saje dasu abinta,zuciyarsa cike fal da tunanin ita din fa wai matarsa ce,sai kawai ya gyada kai qaramin murmushi yana qwace masa,saboda shi kansa yasan akwai jagwal,baisan kuma ya zata kasance masa ba.

Murmushin da yaja hankalin hafsa,ta dan juya kadan tana kallonsa,sai shima ya kalleta ya basar yaci gaba da tuqinsa,ita sam irin hirar nan ta debe kewa don kana driving ma bata iyata ba,sai suyi tafiyar awanni amma saidai kowa yaci kansa,imma ya kunna radio imma ya zubawa hanya idanu kwanyarsa ta cika da tunane tunane har su iso inda zasu.

Su suka fara yin gaba zuwa cikin super market din,cewa widad tayi ta tsaya dasu mimi zata dauko mata duk abinda ya dace,bata wani damu ba ta jasu gefe suka zauna,haka tayita zagaye,tana hada duk abinda ranta ya mata a kwandon data dauka,ba wani abun azo a gani take zaba ba,don ba iya zaben tayi ba,majority tare suke shiga da abbas din,shike zabar mata abinda yaga ya dace da ita,takanyi mita a fili da zuci

"Wannan asarar kudine kawai,ni da kudin ka bani da yafi" dubanta kawai yakeyi

"Abinda zaki sakamin din ko kimin amfani dashi na kalla naji dadinne asarar kudi?" Takan basar kawai,itama batasan tana wannan subutar bakin ba a wani lokacin.

Sai data gama zane zabenta sannan suka hadu a wajen biyan kudi,yaga abinda ta diba,takaici ya hanashi cewa komai,ya biya kudin kawai suka fito,baisan yaushe zata koyi siyan abubuwa masu amfani ba,sa'annan kamar ita zata biya kudin,ta saka tsaiwa ta dauki kayan daya dace.

Kai tsaye gidan hajiya ya wuce dasu,tunda hafsat taga titin da yahau tasan can zasuje,sai ta bata rai,amma dai batace komai ba,don batasan bata wasan nata.

Yana tsaiwa a qofar gidan widad tayi zaraf ita dasu mimi suka fice,yadan bisu da kallo kafin ya dawo da dubansa kanta,itama shi take kallo,ranta ya sake baci,sai take ganin kamar widad din yake kalla

"Amma zaka jiramu mu gama ne saimu wuce gida ko?,don inason nadan kwanta,bana jin dadin jikina yau" dubanta yayi kawai,tunda suka fito din batace masa bata jin dadi ba saida sukazo nan,saiya soma zare seat belt dinsa,har ya bude murfin motar sai kuma yace da ita ba tare daya waiwayo ba

"You know what?.....idan zakaso saniya ka sota har qahonta,domin kuwa no matter what ba yadda za'a yi su rabu,mahaifiyata itace duniyata,silar nasarar rayuwata" a birkice ta juyo tana kallonsa,bataso ya fahimci emotion dinta ba,ta buda baki zata jefa masa tambayar rainin wayon ya buda motar ya fice ya barta a ciki.

Katsam hajiya taga shigowarsu,farinciki ya cikata,murmushi ya wadaci fuskarta,tana marabtarsu tana duban widad,tare dason gano wani canji tattare da ita.

Ta sake haske dai ta kuma sake fresh,amma girman da taso taga tadan qara babu shi,alamu dake nuna babu komai kenan daya wanzu tsakaninsu.

Tana tsaka da wannan tunanin yayi sallama da muryarsa mai zurfi ya shigo,idanunsa suka sauka a kanta sanda take zaune gaban hajiyan hankalinta kwance kamar tana gidansu,fuskarta ta wadata da murmushin da zai iya cewa tsahon satin biyun da tayi gidansa bai taba ganinsa ba,ba wani alamun surukuta a tare da ita,yo ina ta gama saninta ma.

"Maraba lale,saiga baqin yamma" hajiya ta fada sanda yake duqawa gabanta daura da widad din yana gaida hajiyan,dai dai sanda hafsa ta sanyo kai cikin falon,sai idanunta suka qara kusancin dake tsakanin widad din da abbas,bugun zuciyarta ya dadu,wani abu ya kama wuyanta,tayi ta maza ta kauda kanta tana zuqar numfashin wahala,sannan ta qaraso falon tana sakin sallama da shaqaqqiyar muryarta.

"Ah,kacemin tare kuka?" Ta fada har cikin ranta tana jin dadin ganinsu gaba daya

"Eh munje sunyi siyayya ne,saboda gobe in sha Allah zamu wuce"

"To yayi kyau,ma sha Allah" hakanan ta duqa itama ta gaidata don ganin idanun abbas din,ba komai a fuska ko zuciyar dattijuwar ta amsa tana tambayar ta yara,bayan lafiya lau data ce bata sake cewa komai ba,taja gefe daya ta zauna ta tsuke bakinta,amma idanunta yana kan komai dake wakana cikin falon.

Yadda taga hajiyan ta maida hankalinta gasu widad din ya qona ran hafsat sosai,ta yita mutsu mutsu cikin kujera cikin bacin rai,tana jin kamar ta tashi ta fice tabar musu falon,sauqinta daya harda yaranta take ja da wasa,don su mimi suna kan cinyarta suna ta harkokinsu,amma ita wannan sam baiyi mata ba,daga qarshe ta buge ta amsa waya ta fice harabar gidan.

Huci ta dinga yi tana fidda iska mai zafi daga bakinta,zuciyarta kamar zata fito,bata iya jurewa ire iren wadan nan abubuwan,akan abbas zuciyarta na gaya mata komai zata iya yi.

Ana idar da sallar magariba suka baro gidan,a hanyar komawa ma tamkar kurame,shi ya riga ya saba da irin wannan zaman,uwa uba kuma dama shi din ba mutum bane mai son magana,yayin da hafsat din keta cin daci,gaba daya zuciyarta babu dadi.

Qaramar leda ta dauka ta debi wasu abubuwa d'ai d'aiku ta bawa widad,bata damu ba don ba damuwarta din bane,tasa hannu biyu ta karba tana godiya,shi kuwa baisan me ya faru ba,an masa total dai ya biya kudi,yana tsammanin kowa ya dauki abinda ransa keso.

***********Kuka take sosai tsahon awa guda cur da sukayi suna tafiya bisa hanyar bauchi zuwa kaduna,duk yadda zai mata tayi shuru yayin amma kamar ma bata san yana magana ba,har ransa ya baci ya shareta taci gaba da kukanta.

Tun sanda motar samuel ta daga da latifa kano,su kuma tasu ta dauki hanyar kaduna ta birkice da kuka,bata taba tsammanin latifan tafiyarta daban da tasu ba.

Sai data kusa rufe awa biyu sannan kukan ya fara ja baya,jikinta ya fara saki,sanyin yammaci gajiya da kukan data sha suka saukar mata ds bacci,a hankali ta langabe kanta gefe tana sauke ajiyar zuciya mai nauyin,alamun taci kuka ta godewa Allah.

Dubansa yakai gareta kadan kafin ya dauke kansa yaci gaba da tuqinsa,cikin ransa yana sauke ajiyar zuciya,wannan aure ne ko rigima sabuwa ta sameshi?,ya tambayi kansa.

Karo na biyu ya sake maida dubansa gareta,sai ya rage speed na motarsa ya gangara gefan titi ya tsaidata,ya miqa hannunsa a hankali ya sauke mata kujerar yadda zata ji dadin kwanciyar,ya koma seat dinsa ya zauna dai dai,sannan ya sake kunna motar suka ci gaba da tafiya.

Yammaci lis suka shiga garin kaduna,kofar wani babban gida ya tsaya,ya danna hon,babu jimawa mai gadin ya iso ya bude gate din,fuskarsa cike fal da murmushi,da alama farincikin ganin dawowar abbas dinne,aiko yana sako hancin motar zuwa parking lot na gidan ya biyo bayan motar da sassarfa yana fadin

"Barka da zuwa oga" qaramin murmushi ya saki,yana hangoshi ta madubin,mutum badai barkwanci,ya tsaida motar dai dai sanda ya qaraso gefan window dinsa.

KI KULANI miss xoxo

DAUDAR GORA Billynabdul

RUMBUN K'AYA hafsat rano

IDON NERA Mamuhghee

A RUBUCE TAKE huguma

_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_

_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

0022419171
Maryam sani
Access bank

Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070

*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261

*Al'ummar nijer +227 96 09 67 63


*Thanks for choosing us*=?%?=?%?=?%?=?%?=?%?=?%?

*H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)

Page 45

"Barka da dawowa oga,tun wancan satin muketa zuba idanun dawowar ka,har mai gida yana tambaya" miskilin murmushi ya fita a fuskarsa

"Naso dawowa,to amma ban gama shirye shirye bane,mun sameku lafiya?"

"Lafiya sumul oga,ya hanya?,ashe an samu qaruwa?,to Allah ya sanya alkhairi,yasa abokiyar arziqi ce" bala mai gadi ya fada yana murmushi

"Ameen"ya amsa masa a taqaice,sai ya zagaya da sauri ya soma budewa widad qofa yana fadin

"Madam barka da rana" nauyi ya saukarwa abbas,da alama bala baisan qaramar yarinya bace yake gaidata,duk da ya bude motar bai damu ba yaga ta sake maimaita gaisuwarsa,sakato widad tayi cikin rashin sabo,wai yau ita ake gaisarwa?,ita da take gaida jama'a?

"Ana magana" abbas ya fada yana cire belt seat dinsa,maimakon ta amsa saita maida masa gaisuwar,saboda rashin ganin dacewar ta amsa din,amsawa yayi ya kuma bisu da addu'ar zama lafiya da zuri'a ta gari,ita dai tana jinsa ba tare data amsa ba.

Muqulli abbas ya miqa masa sannan yace

"A shigo min da kayan qofar parlor bala"

"An gama oga" ya fadi yana karba da hannu biyu

"Muje" ya sake fadi yana duban inda widad taja ta tsaya,tana kuma bin gidan da kallon baqunta.

Wata siririyar hanya suka bi,sai gasu qifar wata qaramar baranda mai kyau dake dauke da wata qofa mai dam fadi,yasa key ya bude qofar ya shige,ta bishi a baya,kamar za'a ce kettt ta zura da gudu.

Madaidaicin falo ne amma ya qawatu matuqa,akwai qofofi guda uku a cikinsa na bedrooms guda biyu,daya qofar kuma ta kitchen ce sai dining area,sai qaramar qofar da zata fiddaka bayan gidan.

Qarasawa yayi gaban daya daga cikin dakunan ya buda daya

"Ki shiga nan kiyi wanka ki huta" bata iya amsa masa ba,sai gaba datayi zuwa qofar dakin tana raba idanu,turqashi,yau fa ake yinta,a wanann dakin zata zauna ta rayu ita kadai?,abinda yake nufi kenan?,ga gidan ta fahimci babu wadatar hasken rana,duk da cewa yammaci ne amma alamu sun nuna hakan,kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki ta sanya kanta cikin dakin,dab da zata shige yace

"Ki rubuta duk abinda kikeso,zan aiko a karba sai a kawo miki" sai a sannan ta samu daga masa kai,qwalla tana cika mata idanu,har yayi gaba ya dakata,ya juyo a nutse ya sanya idanunsa cikin nata

"Me ya faru?"ya tambayeta yana kallonta,cikin jajircewa tayi qoqarin maida qwallar data cika mata idanu

"Tsoro nakeji"ta amsa masa kai tsaye

"Tsoron me?"ya tambayeta cikin mamaki, maimakon ta amsa masa saita maida dubanta ga dakin da ko qwan wutarsa ba'a kunna ba,saboda haka ya danyi duhu,gyara tsaiwarsa yayi,tana jin tsoro,to amma kuma baisan me zaiyi mata ba,hakan yana nufin saidai suyi sharing daki ita dashi?,kai ya girgiza kadan
"NO" ya amsawa kansa,sai yanzu ya tuna da dan banzan tsoron da take dashi,ya manta the first time he saw her...ihun kyankyaso taketa yi,harda cire dankwali,takawa yayi ya matsa zuwa inda take tsaye,ganin ya nufota ta tuno da wani abu,tayi hanzarin jaa da baya a tsorace,har abun yaja hankalinsa,yadan dubeta kadan sannan ya dauke kansa,wannan bayan tsoron su kyankyaso hala harda tsoron mutane ma tanayi?.

Qwan wutar dakin ya kunna,haske ua gaurayeshi,abinda ya rage mata tsoron dakin kenan,ya fita a dakin ya bata waje yana cewa

"Sai anzo an share dakin,akwai qura" saboda sanda hafsata ta tashi tafiyarta a birkice ta barshi,shi kuma takaici yasa ko takan dakin bai sake bi ba tunda ta fita daga ciki.

Sai data tabbatar yabar wajen sanann ta saka kai cikin dakin,ta tsaya tana duban komai,a hautsine yake,ji take yi ba zata iya zama ba,don kafin tafiyar latifa ta koya mata yadda ake gyaran bedroom xuwa falo,kuma babu laifi hannunta yadan fada,ta janyo jakarta zuwa tsakiyar dakin tayi mata waje.

Zama tayi tana qarewa dakin kallo,idanunta fal hawaye,ta rasa qwarin gwiwar gyaran dakinma gaba daya,tana jin kamar an dauketa daga duniyar ta an kawota wata duniya ta daban.

Bata tashi ba sai da aka kira magarib,ta miqe tana kame jikinta waje daya,saboda dakin ya mata datti,kasancewar bata taso ta saba zama cikin dauda haka ba,koda yaushe zaka samu sassan ummu qal qal,ko tsinke bata bari ya sauka,shi yasa basa shiri da jikokinta,don da zarar kazo ka zauna ta fuskanci kai dan bata guri ne yanzu zata koraka,widad dince kawai keyin yadda takeso a sassan ba tare data hanata ko tace mata komai ba.

Toilet din ta shiga tayi alwala,tazo ta shimfida dankwalinta ba tare date nema abun sallah ba ta tada sallah,ko da ta idar tana zaune a wajen,har zuwa sanda aka turo qofar dakin,ta waiwayo a tsorace,saita zuba masa ido sanda yake shigowar,tsoro na kamata,a yanzun ya canza shiga,shirt da trouser ne a jikinsa da suka dace da jikinsa,suka fidda qirar jikinsa dake tafe da tsaho da murjewad jikin kadan,don ba zaka kirata qiba ba.

Ido ta lumshe,tana jin dadin qamshin turarensa har qololuwar ranta

"Kinyi sallah ne?" Kai ta gyada masa ba tare data iya kallonsa ba,sai ya dauke idanunsa daga kanta ya kalli agogon hannunsa

"Zan dan fita....." Tun kafin yakai qarshe ta daga manyan idanunta ta watsa a kansa,haka kawai yaji nashi idanun suna lanqwashewa zuwa lumshewa,kafin ya budesu ya azasu a kanta,har zuwa sannan manyan fararen idanunta suna kanshi,ta yaya zai fita ya barta a wannan gidan ita kadai?,duk da bata da tabbacin ita daya ce cikin gidan gaba daya,amma itakam ko dakin ummu bata yarda ta zauna ita kadai,inaga gidan gaba daya

"Bazan dade ba zan dawo,za'a knocking za'a kawo abinci,saiki bude ki karba,idan kuma wani abu ya taso ki kirani a waya" wani mugun tsoro ne ya shigeta sanda ya juya yana ficewa,kuka sosai yazo mata,ta cure waje guda tana cusa kanta tsakanin qafafunta

"Wayyo ummu"ta fada muryarta can qasa wadda ke cike da kuka,sun kawota inda bata da kowa,kamar basa sonta,itakam meye tayi musu?,sai taci gaba da rera kukanta a hankali,har zuwa sanda taji kiran sallar isha'i ta miqe ta bada farali,ta sake komawa yadda take.

Tana jin anata knocking kamar yadda yace amma ko yunwa zata kasheta bata jin zata iya miqewa zuwa falon har ta bude,tana jinsu har suka gama bugunsu suka tafi,saita sake sakin kuka tana takurewa waje daya.

Lokaci lokaci tana duban agogo tare da fadin

"Allah kasa ya kusa dawowa" saita sake maida kanta tana sharar hawaye,har kusan awanni uku babu shi babu dalilinsa.

A karo na barkatai ta sake daga kanta don kallon agogo,saidai hasken farfajiyar gidan ya hasko mata mage dake tsaye jikin window din dakin nata tana kada jela,wani mugun tsoro da razani ya shigeta,take jikinta gaba daya ya fara rawa,hawayen idanunta suka ninku,ta fara karanta ayatul kursiyyu a rarrabe saboda yadda bakinta yake rawa,a duniya babu abinda ta tsana take mugun tsoro irin magen,don saboda ita kowa na gidan ya haqura da ita,sabod koda ka kawota sai ummu ta sanyaka ka maidata inda ka daukota.

A hankali magen ta soma kankarar glass din jikin window din kamar me neman hanya tana kuka mieeeuuuu mieeeuu,ba abinda yaxo kwanyar widad illa ga magen har ta shigo ta fada mata a ciki,take ta saki wata qara hade da kuka.

Sautin muryarta yakai kunnuwansa sanda yake tsaye yana knocking qofar falon,kusan sau biyar kenan amma baiji motsinta ba,har ya fara tunanin ko tayi barci ne?,sai kuma saqon muryarta

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login