Showing 99001 words to 102000 words out of 200116 words

Chapter 34 - A RUBUCE TAKE (KADDARATA)

tsare hanya"

"Hafsat ce ta kawo miki maganar?" Ya sake dai tambayar hajiyan

"Nace babu komai,Allah ya tsare hanya,ina widad din?" Waiwaya yayi yana kallonta,ita sam hankalinta ma da alama baya wajen,yana farfajiyar gidan inda mai gadin gidan yaketa gyaran flowers,dauke kansa yayi ya maida gabansa

"Tare zamu taho in sha Allah"

"To hakan yayi,sai kun iso"

"Madalla hajiya,Allah ya saka da alkhairi" sukayi sallama kowa ya aje wayar.

Iska ya furzar yana tada motar,idan ya rantse ko kaffara bazaiyi ba hafsat ce takai qararsa wajen hajiyan,don ya sansano hakan daga muryar hajiyan,yasan ta boye masa ne kawai saboda kare martabar hafsa a wajensa,wai me yasa ita din bata jin kunya ko nauyin kaishi qara?,yanzun wannan abun har ya isa takai qararsa gaba?, just one week daya qara baizo ba?,bayan he explains to her?,baisan sai yaushe zata fahimci illar wannan muguwar dabi'ar tata ba,baisan sai yaushe zata gane zubarwa da kanta kima da daraja takeyi a wajen iyayensa ba.

Ya danyi gudu,hakanan banda sallah basu tsaya sunyi komai ba a hanya,don haka awanni biyu da rabi suka kawosu bauchi daga kaduna.

Ba'a jima da idar da sallar la'asar ba suka shiga unguwarsu,ya faka motar a harabar gidansa,kafin ya sake wani abu tuni widad ta balle murfin motar ta fice saboda hangosu mimi da tayi,suma tuni sukayo wajen,saboda sun shaida motar daddyn nasu.

Binta yayi da kallo kawai,har zuwa sanda ta isa garesu suka rungume juna,sannan suka iso bakin motarsa suna dakon fitowarsa.

Tare suka rankaya zuwa ciki,mimi da nawwara kowacce na bada nata zancan,fuskar widad fal fara'a,har suka isa falon hafsat din.

Kallo daya ya yiwa falon yaji bacin rai ya saukar masa,kullum jiya i yau,dukka gyara da qyale qyalen daya zubawa falon daga bikin widad din tafiyarsu kaduna zuwa zuwansu yau gaba daya sun fara dakushewa,sai ka rantse kayan sunyi shekaru bakwai da sakasu,kai koda shekaru bakwai dinne indai ba qazamar mace ta ainihi ba bai kamata suyi wannan dafewar ba,ko ina tarkace ne dake nuni da cewa babu wadatacciyar sharar da falon yakeso,uwa uba turkish carpet dinta ruwan madara ya fara yin qaura daga aihinin kalarsa zuwa brown, qawataccen center table din daya zuba kudade ya siya mata an soma kwanceshi,ba wasu sassa a jikinsa.

"Ina Mommy din?" Widad ta tambayi mimi

"Tana kitchen,wanke wanke take"

"Muje ki rakani" ta kama hannun mimi din suka wuce kitchen din.

Bata a kitchen din,amma qofar backyard na kitchen din a bude yake,sai suka sanya kai can.

Turus widad tayi tana duban iyayen kwanukan dake yashe a wajen tamkar anyi taron biki ko siyasa an watse,kusan dukka wasu kwanuka na kitchen dinta suna wajen,tana tsakiyar su ta hada kumfa a babban baho tana wankewa,tanayi tana maganganun qasa qasa,daurin qirji ne a jikinta na zanin atamfa,sai rigar shirt,kanta dankwalin zanin ne data masa daurin gaban goshi,daga qasa kana iya hango qananun gashinta sun burtso.

"Mommy sannu da aiki" widad ta fada tana murmushi,hafsat ta waiwayo da sauri suka hada ido da widad din,a take taji ta muzanta,bata taba kawowa a yau idan hajiyan ta kirashi zai taho ba,dukka ta dauka sai gobe,don haka yau taci burin qarar da yininta tana gyaran kitchen,tasan shi da falo da toilet sune abu na farko da yaqi jinin ya gansu ba'a kintse ba,yau din kuma alhamis,ta zaci zai taho gobe juma'a ne.

Sake juya idanunta tayi akan fuskar widad karo na uku kafin ta samu sukunin amsa sannun tata data yi mata,idan idanunta ba gizo yayi mata ba yarinyar qara haske da kuma qiba tayi,ga wani dan banzan qamshin turare da taketa bulawa hancinta,wani abu mai qarfi ya taso ya kama zuciyarta, muryarta ta sarqe,har sai da hakan ya bayyana cikin sautinta,ta jefa mata tambayar muryarta a cushe

"Dake da waye?,da yammar nan?"

"Ni da daddynsu mimi" tayi maganar tana kallon qofar da zata sadaka da kitchen din,saboda tuni hancinta ya shaida mata wanzuwarsa a wajen,sassanyan qamshinsa daya fara yo gaba.

Idanun widad na kansa haka na hafsat,yayin da nasa idanun ke kan hafsat din da tarin kwanukan wanke wankenta,wanda ko ba'a gaya masa ba yasan halin nata tayi,wato tayi girki ta jiqa kwanon,gobe ta bare sabo ko wankakke ta sake wani girkin a ciki.

Tuni idanusa suka cika taf da bacin rai,banda wanda ya shaqa daga falo,da kuma dattin daya hanga akan sumar yaransa,ga qurajen zafi da suka fesowa nawwara,tabbacin ba'a kunna musu gen kamar yadda ya bar sallahy,bayan ya aje kudin komai da komai.

"Sannu da zuwa" ta fada tana miqewa hadi da sauke zaninta data yaye cinyoyinta

"Yauwa" ya fada yana komawa da baya,cikin sa'a ko rashin sa'a,sai ya taka sauran rubabben abincin data kwakwkwafe a kwandon shara,Allah yasa boots ne a qafarsa,yaja da baya ya murje qafar tasa ya fice daga wajen.

Cikin shan jinin jikinta ta soma takawa zata bishi,har tayi taku uku saita waiwayo tana duban widad,zuciyarta na cika da kishin kwalliya da sutturar jikinta

"Zauna ki kamamin wanke wanken nan ina zuwa"

"To" ta amsa mata,babu gardama,ta soma ratsawa ta cikin kwanukan tana tattare hannun rigarta,ta zauna kujerar data tashi,ta fara jan kwanukan tana wank su,mimi na mata hira.

Har ta doshi hanyar sassansa saita tsaya,ta kalli jikinta da kyau,ita kanta ta shaida tsami takeyi,sai tayi ribas,ta koma da baya zuwa bedroom dinta,ta kunna heater a gurguje ta saba sabulu ta dauraye da ruwa,ta tsaya gaban mudubin ta ta balbala turare sannan ta zura wata doguwar rigar baqar atamfa,ta dora daurin dankwalinta sannan ta fito.

Har zata wuce ta tuna tabar mimi a can,saita koma ta tsaya daga qofar kitchen din tana qwala mata kira,yarinyar ta taso,ta kama hannunta suka bar wajen,tana jefawa widad harara a fakaice

"Saikin gane Allah daya ne wallahi yarinya,muje zuwa wai mahaukaci yahau kura".

A falo ta samu nawwara,tasha chocolate har ta godewa Allah,ta aje mimi a nan ta wuce kai tsaye bedroom dinsa.

Yana tsaye gaban mudubi yana maida maballin wata jallabiyya mai azabar kyau,hade take da wandonta da aka yima aikin zare daga qasa, lallausan qamshinsa daya karade dakin ta zuqa,tana son turarensa matuqa,saidai ko ya bata bata iya jurewa shafawa kullum da kullum

Sarai ya hangeta ta cikin madubi sanda take shigowa,amma bai fasa abinda yakeyi ba,hakanan bai waiwayo ba,jikinta ya qara sanyi,ta tako a hankali kanta a qasa,tayi mazauni a kujerar bayansa

"Sannu da zuwa ya hanya?" Ta sake fadi

"Lafiya" ya amsa mata a taqaice,ya dauki comb yana sake taje kansa,sannan ya daura agogo ya dauki daddumaersa a qagauce

"Zanje sallah na dawo,ki gyaramin sashe na" daga wanann ya juya ya fice a dakin,yana jin yadda shegen turarenta daya tsana yake cika dakin,baisan ita din wace irin mace bace,duk abind yake so tofa sunyi hannun riga,kamar ma tana jira yace ga abinda yakeso ta qalubalanceshi,duk wani abu da zaiyi mata don gyara da kyautata rayuwarta yayi amma ita kamar bata maraba da hakan.

Da kallo ta bishi,kafin ya gama ficewa,tabi qofar da harara tana jan tsaki

"Mutum sai shegen izza da tsari,daga dawowarsa gaba daya ya batamin duk wani lissafi ba,banda ya taho da waccar yarinyar yaushe na gama wanke wanken,na gyara nawa sashen,na gyara nasa?,sannan daga qarshe yacemin abinci yake jira na dafa masa kamar wata jaka,Allah yau saidai kowa yaci takeaway" ta fada tana sake jan tsaki,ta miqe tana kade zanin gadon da tun kafin ya tafi yake shinfide akai ba'a daga ba,kuma ko yanzun bata da niyyar dagawar.

*Arewabooks: Huguma*

KI KULANI miss xoxo

DAUDAR GORA Billynabdul

RUMBUN K'AYA hafsat rano

IDON NERA Mamuhghee

A RUBUCE TAKE huguma

_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_

_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

0022419171
Maryam sani
Access bank

Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070

*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261

*Al'ummar nijer +227 96 09 67 63


*Thanks for choosing us*=?%?=?%?=?%?=?%?=?%?=?%?


*H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)

Page 51


Tun tana wanke wanken na marmari har ta soma ji gaba daya hannayenta sun fara mata zafi,sannu a hankali gajiya gaba daya ta saukar mata,hannunta yayi jazur saboda wankin kwanukan da kuma zafin detergent,tunda tunda uwarta ta haifeta bata taba wanke wanke mai yawan haka ba,da qyar ta samu ta kammala,ta gyara daurin dankwalinta daya sabule ta baro wajen.

Babu kowa a falon,bama alamar suna nan,hakan yasa ta wuce zuwa sashenta kai tsaye,bayan ta ciro key din da ya bata a qaramar purse dinta.

Idanu a narke ta shiga sashen nata,sai zuciyarta ta karaya,taga kamar zataga latifa,ta tuna wayon data yi mata ranar da zasu bar bauchi,komai yana nan a killace yadda latifa ta barshi,ba wani datti sai 'yan qananun qura dake shiga wajen sanadin babu giftawar kowa,ta zube saman kujera tana share qananun qwalla,itakam tana jin kamar tsanarta akayi,kowa yana gida banda ita?,hakanan ta gaji da zaman,ba motsin kowa cikin gidan,ba alamun kuma zata samu wani abun da zata ci,ta miqe cike da shegen tsoron nan nata cikin sanda ta isa kitchen,ta duba store dinta ta fidda indomie,cikin tsoro da fargabar kada ta cabe irin ta rannan ta kunna wuta ta dora.

A kitchen din ta zauna harta dahu,ta juye a plate,tasa fork ta debo ta dandana,sai murmushi ya subuce mata,tayi dadi fiye da yadda ta zata,har abun ya burgeta ita kanta,ta dauki plate din da hanzarin tayo hanyar falo,tana fitowa sai tayi turus da plate din a hannunta,ta manta ba'a kaduna suke ba,ta yaya zata wuce momy hafsat dake gargadinta koda yaushe ta tafi dakinsa?,saita koma ta zauna jiki a salube,ta sanya cokalin ta fara diban taliyar tana ci,ko TV ta kasa kunnawa saboda tsoro,sai taji kamar ana tafiya daga bayanta.

Duk da ba'a nutse take ba amma hakan bai hanata jin dadin taliyar ba da gaske,tana ci idanuwanta suna mata nauyi,don haka kafin ma ta kammala bacci ya kwasheta a wajen,ko hannu bata samu wankewa ba.

Daga yanayin da ya samu gidan yasan cewa babu wani abinci da zaya samu,don haka koda aka idar da sallar magariba bai shigo gidan ba sai da akayi isha'i,daga nan kuma ya dauki motarsa ya wuce yayi musu takeaway,bai bi ta halin hafsat din ba,don ko kaffara bazaiyi ba yasan ba wanda ya qoshi a gidan ciki harda yaranta,don haka ya hado dasu.

Afalo ya sameta ta kammala mopping,tana ta fada dasu nawwara,fadan da bashi da dalili,yasan dai duka bazai wuce akan aikin sharar daya sanyata ba,yaran suka masa oyoyo ya daukesu yayi hugging dinsu,sanna ya ajjiyesu hade da ledar hannunsa yana cewa

"Bari naje na dawo muyi dinner ko?" Suka daga kai cikin zumudi da jin dadi.

"Ina kuma zaka je?" Ta tambayeshi cikin d'ar d'ar ganin ya kama hanyar fita da leda daya,waiwayowa yayi ya dubeta,bai bata amsa ba yaci gaba da takawa

"Kawo nakai mata ka zauna kai kaci naka abincin" ta furta tana matsowa,saidai kafin ta iso ma ya fice abinsa,baisan me yake damun kanta ba,ita idan tayi laifi ma bata yarda tayi bare ta kamo hanyar gyarawa.

Sau hudu yana knocking yaji shuru,sai kawai yayi amfani da spare key dinsa ya bude ya shiga.

Sassanyan qamshin turarukan da latifa ta tsuma sassan dashi har yanxu yana nan,kamar ma a yanxun ake turara wajen,turaruka masu tsada da kama jiki na asalin shuwa.

A yashe ya hangeta saman carfet ta cure waje daya,ya taka a hankali zuwa cikin falon,ya dauki remote ya sanyin ac din,ya ajiye remote din ya maida dubansa gareta,ko pillow babu a kanta,ya ajjiye ledar a hankali a gabanta,sannan ya durqusa yana tunanin yadda zai gyara mata kwanciya.

Pillow din ya miqa hannu ya dauko,sannan ya zauna sosai,ya sanya hannuwansa duka biyu ya dagota,sumar kanta data baje ta watsu saman baby face dinta,sosai pink lips dinta suka dauki hankalinsa,bai taba kallonsu da kyau irin yau ba,wani irin sexy lips masu daukan hankali,girarta da suka kusa hadewa da juna ta sake qawata fuskarta da kyau.

Ji yayi sunyi mugun kusanci da juna,kamar wanda aka sawa electric shock ya saketa da sauri,ta farka a firgice sanadin sakinta da yayi,jinta kusa da mutum kuma ya sake sakawa ta tsorata da gaske,saboda tasan dai already kafin ta kwanta ta rufe qofarta.

Ihu ta sanya sosai a tsorace,yasa hannunsa da sauri ya rufe mata bakinta yana cewa

"Ke....meye haka,it's me" jin muryarsa ya sake kad'a mata cikinta,ta tattara qarfinta tana tureshi,dai dai lokacin da hafsa wadda ta saka zama ta biyo bayansa ta turo qofar falon da sauri ta shigo.

Da yadda za'a fadi yadda taji a lokacin ya wuce haka,gaba daya ji tayi wani tashin hankali ya rufto mata,widad din a jikin abbas dinta?,sam batasan gabansu take nufa ba,har sai data isa,gaba daya zuciya ta gama gaya mata ta fincikota daga jikinsa ta rufeta da mugun duka ne,saidai tana isa din abbas din yana buda hannayensa widad din ta fice tana sakin dan qaramin kuka,gaba daya a tsorace take, jikinta sai rawa yakeyi tana kallon fuskar hafsat wadda ta ritsata da idanu,hantar cikinta ta gama kadawa kamar wadda aka kamata da kwarto,yanxun me zata cewa mummy?,duk yadda take kiyayewa da yin takatsantsan yau ta kamata a jikin wani.

Mugun kallon data watsawa widad din ya sanyata cikin sauri da kuma rawar murya tace

"Wallahi mummy ina cikin bacci,bansan ya shigo ba...." A nutse abbas dake tsaye ya waiwaya ya kalli hafsat din,da sauri ta dauke rikitaccen kallon da takewa widad ta maida ga abbas din cikin rudewa,yarinyar tana son balle mata liqin da tayi,sukayi kallon kallo na sakanni,kallon data hangi ayoyin tambaya masu yawa a idanun abbas din,ta hadiye wani yawu mai tauri,cikin qasa da second goma dabara ta fado mata,ta maida dubanta ga widad din

"Ni Matsalata dake shegen tsoro,kinsan dai gidan nan babu wanda zai shigo,dagamu sai mu,ki dinga addu'a idan zaki kwanta kinji" tayi maganar cikin karyar da harshe,saita matsa tana zaunar da widad din sosai,amma qasan zuciyarta a mugun matse yake,kada fa ya zamana abbas ya fara latse d'iyar mutane,ta miqe sosai ta tsaya tana dubansa

"Abban mimi.....ka dinga haquri,kaga dole ayi mata uzuri,akwai quruciya sosai a tare da ita" lumshe idanunsa yayi bisa fuskar hafsan,shi baima gane abinda take fada ba,gaba daya bugun zuciyarsa ne yake neman sauyawa,saiya maida dubansa ga hafsat din dake matsar qwalla

"Ga dinner dinki nan,ki taso ki rufe qofar" ya furta yana juyawa cikin mutuwar jiki,sai hafsat ta biyo bayansa tana cewa

"Kisa key ki rufe qofan falon kinji,saiki rufe ta bedroom din ma,sai da safe"

"To Mommy" ta fada,cikin ranta tana jin tazarar son da hafsat din ke mata abbas din bai kama koda kwatarsa ba,haka tasa muqulli ta rufe qofar sannan ta dawo falon,tsoro ne fal ranta da zuciyarta,tana jin kamar ta bisu,amma kuma haushinsa takeji,don me zai dinga taba mata jikinta,a gurguje ta tattare komai ta wuce bedroom dinta,shima sai data saka key ta rufe da kyau sannan ta canza kayanta zuwa na barci ta haye gado,yau ko.wankan ma bata tsaya yi ba.

Ta jima tana juyi ciie da tsoro, duqunqune cikin duvet,wannan gidan yafi na kaduna girma,hakanan gidan kaduna dakunan kusan a kusa da juna suke,tana jin kusancin abbas dake dakinsa a jikinta,sabanin wannan da kowa bangarensa daban,cusa kanta ta sakeyi cikin duvet din,hancinta na zuqo mata qamshin turarensa,wanda ya kama rigar jikinta radam,sai taja tsaki,haushi na cika mata zuciya

"Dan iska" ta fada tana murguda baki.

**********washegari bata bude qofarta ba har sai dasu mimi sukazo suna buga mata,taji dadin ganinsu,suka dinga wasansu a falonta,ita kuma ta shiga kitchen ta dafa musu jallop din taliya.

Da dan gyare gyare cikin girkin,to amma da yake ba wani cimar kirki yaran suke ba sai abincin ya musu dadi sosai,suka zauna sukaci kaman ba gobe,itama cikinsu ta zauna,sunaci suna surutu tana tayasu,sai da suka qoshi sannan mimi tace

"Mummy ce ta aikomu,tace kiyi mana wanka,bacci suke wai basu tashi ba" bata ji komai ba,don zamanta da yaran ita dadi yake mata,sannan ita kallon hafsat din take kamar anty deena,don haka ta kunna heater,ta tara ruwa mai dumi sosai,tayi musu wanka kuwa fes,ta shafa musu manta sannan ta dubesu

"Ku karbo kaya wajen mommy din a saka muku" da gudu suka fella suka fita,saidai basu jima ba sai gasu sun dawo da kayansu a jikinsu

"Mommy tace kizo" jikinta ta kalla,da da hali wanka zatayi kafin ta fita din,don gaba daya bata jin dadin jikin nata,saboda bata samu yin wanka jiya ba,amma kafin ta gama tunanin maganar mimi ta katse mata

"Yanzu yanzu wai tace" mayafin doguwar rigarta ta zura tabi bayansu suka fice.

Sallamar widad din ta sanyata ninke kudin da take irgawa ta daga bayan pillow dinta

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login