Showing 129001 words to 132000 words out of 152888 words
tas dan ba abinda ta bari na Mama farin ar wani kore yasa Fandau ce tabiyo Malam
Fandau hannun ta narawa ta meka hannun Shattema ya meka mata mesunan ta wanda Bagana take kira da *Isseta* wato yar uwa ayaren shuwaa
Yameka mata Fandau ta rungume yarinya tasake jan yaron mata rungume
Yaran sai kamshi suke kana gani kaga yan gayu
Fandau tace " yanzu Bagana wannan yanan kike ke Allah yabawa Allah Mungode maka da wanan ni ima da kamana.
Bagana tace "YaFandau mugode masa kam godiyar mu ga Allah ba zai taba karewa ba tun randa akacemn wai Fujjirat yarmu ce Maaf da Bilal na mune nake ta godewa Allah yanzu kawai jira muke ayi agama,
Abamu yaran mu,
Akkaam ne awai ban gani ma dan ta gida muka biya Mama tace wai YaShid yafita dashi.
Fandau tace "ka marya yaya yafita dashi?
Kafin Bagana taba ta amsa
Shattema yace ni barin kowajen zama bazan samu ba kenan.
"Fandau tace "lah YaShatteem wllh ina murnan ganin yarana ne zanzo kanka namaka godiya yanda ka mayar min yar uwa babbar yarinya haka
Shateema murmushi yayi yace "Aidama my sweet big girl ce.
Dariya sukayi
Yace" to ya bayan saduwa.?
Tace"kaide bari YaShattee abubuwa sun faru dayawa.
Shateema yace "eh harda na alkairi a ciki ai.
Kafin ta bada amsa sai ga Nabil yafito,
Yana cewa "sister kune Shateema yameke ya meka masa hannun suka gaisa
Bagana tace "kai YaShid ashe kana gidan.
"Eh zance nazo dama Malam yace na shawo kanta ta ta yarda mukoma muyi manage amma tace bata sona.
Bagana da tasan cikin abin da Mama ta gaya mata tace "haba YaShid yazata ce bata sonka amma banji dadi ba"
"A a sister kar ki samu damuwa aini yayan naki ai mai tsadane ayu yake so zan samu mata 4 zai iya.
"Gaskiya kam koni zan samo maka.
"no sister kibari na zabo kinsan bantaba zaba da kaina ba shiyasa na ke samun matsala kinga aure na nafari Bani da lokacin na tsaya nayi nazarin macce saboda lokacin ina tsaka me wuya aharkan wasa Ummi ta zabanin Hadim na 2 ma Hadim ta za bamin shiya so yanzu zan zabi kalan da nake so da kaina.
Bagana da Shateema dariya sukayi
Fandau taci kunu
Bagana tace "yanzu kuma wane kala zaka zabo ne.
Nabil yadan daga kansa alaman tunani yace "kinga nayi yayin fara kajera nayi baka doguwa,
Yanzu kuma fara doguwa nake so amma mejiki sosai.
Bagana tace "yayi za musha biki kenan.
Yace "sosai dan inason naga ammin cud'a yada akeyiwa kowane ango dan ni sabone tunda nake ba ataba min kamun ango ba ita ma Hadim ina London aka kaimin haka ita ma Ummu Akkaam kinga banga lalleba.
Daure faska Fandau ta sakeyi ya kalle ta ta gefen ido yace "yabaki ce komai ba babbar sister.?
Shateema yace "Gaskiya wannan ai cin faska ne akeson yiwa Auntyna.
Bagana tace "a a my neelly itafa tace bata son mu.
Nabil yace "bari na tafi sister za kijine idan na gama nazari dan mata sunanan burjik.
"Yawwa Yayana Allah yabaka sa a.
Ya shafa kan Tajuddin Yafita
Bagana ta juyo tace "Mama tace min guduwa kikayi dan shi yana ganshi anan kuma ina mutanen gidan?
Fandau tace "kanwar sace ta kirashi wannan yar rinin hankalin ce tazo ta faramin ihu dan ita bata san wacece Fandau duk karamin iskancin ta yana tafin hannun na, zan nuna mata ni cikekiyar yar cikin gargar ce ba taka haye nayiwa Barno ba, aini yanzu ba abinda nake jira irin ka ronmu da kita.
Bagana tace "Gaskiya ba tasan ke wacece ba ta sameki araha shiyasa ni har mamakin matan nan nake wai Hadim da ake yaban kirkin ta ako ina yanda take kyata da sadaka ita ce tayi irin wanan abin.
Da ganan Fandau ta kwashe komai ta gaya musu sun jijina sosai
Har Shattema yayi musu salama
Sai ga Amsatu Hadiza suma fa d'awa Fandau sukayi sukayi ta kuka da murna haka yan uwata mata suka cika gidan har manyan sun YaZahra da su YaKaka abin da Fandau bata taba tsammani ba kenan dan bata zaci abin zaizo mata da sauki awajen yayin nata haka ba tazaci zasu mata gorin da fad'an su na manyan ce Sai nanan suka da ita lafiyeyen abinci Fandau tasa me aikin su jummai ta musu sai yamma suka yayi shirin tafiya,
Fandau ta rakosu mamakin ta sai taga YaKaka YaBintu Baana har da motan kuma su suka tuka abin su sai sauran kuma wanda ba azo daukan suba suka kwashisu saura YaMainuna su Nana suma ba jimawa dan gidan Maimuna yazo ya dauke su sai Bagana zasu koma ciki itama Shateema yadan no kai ko parking bai yiba yace tayi sauri ta shiryo yana da wani uzuri
Fandau tace "kai YaShattee da kabari sai dare wllh bamu gama ba.
"yanzu wuni guda amma baku gama ba fira yawuce na awa 2 ai yazama na shirme kai Tajud shigo ina Isseta.?
Bagana tace "tana bacce bari na dauko ta.
tashiga
Fandau kamar tayi kuka dan basu sake sosai sunyi fira ita da yar uwar ta ba sai bayan sun shiga mota Fandau ta kama murfin motan Shateema yace "kar ki damu gobe sai tazo ai.
Fandau tace "Allah zata zo?
yace insha ALLAH.
Tarufe musu motan suka ja
Hadim acikin mota kuka kawai take yanzu wannan yarinyar da na renawa ita takoma haka ashe dama mekyu ce tunowa tayi ita yaushe rabonta da Nabil tunda sukazo ko awaya ta kirashi a fisge yake amsawa tunowa tayi da maganan Fandau nacewa _jiya kinsan inda ya kwana ne_
Wani irin kuka tasa tace wayyooo ALLAH nayi kuskure ni Hadim yiwa kaina kishiya da kaina amma ai Nabil bamuyi da kaizaka min haka ba ai
Jidda tace "Aunty kiyi Hakuri yi addua.
"Jidda narasa ta ina zan fara addua an mezan cewa Allah Jidda kishiya fa ake shirin yimin akuma kwacemin yarana nikam idan suka kwace min yara.
"Aunty kiyin Hakuri kunyi kuskure duk kanku amma kikar bi kaddara ki zauna da ita yafi miki nake gani yara kuma tunda kowa yasan kina son su tsakani da Allah kici gaba da nuna musu so su shaku dake yanda da kansu indan sun tashi baza su nuna miki ban baci ba tsakanin ki da uwar tasu kuma idan an hadaki da yarinyar nan wllh kibita ahankali dan yanda naga idanunta a tsai tsayen nan idan baki sauko ba kowa acikin ku bazaiji da dadi ba tunda kinga yanda YaShid yake sonta duk wannan jinyar da yayi akanta yayi kibi Ahankali kin san komai na Duniya yanda ka dauke shi haka yake zuwa maka.
"Jidda yazan shi yazan iya zama da my star na da wata wane irin rayuwa zamuyin
Zan kunyata agaban kawayena yanzu haka dazu wanan Faridan matar Amjad kinji abinda take fada kuwa wai har da cewa alwalan kifi yakarye yawanci kawayena da nake jida su narasa su kiga yanda muke da Aminan Bilal amma d'azu itama harda yadamin magana balle Habiba kinga yanzu zancen yagama bazuwa cikin kawayena.
"haba Aunty keta kawaye kike su sunfi karfin amusune kishiya ko yanzu yanda yan mata suke daukan wanka su zaga gari ai nake gani mata suragewa kansu kishi yafi,
Kicire batun wani kawaye ki kwaci kanki kine mi yaya ku shirya tunda guntun sonki aran sa kar wannan karamar yarinyar ta miki illa dan naga alamar ta.
"Jidda illa sonawa ai yanzu ne kawai kujira makokina kawai.
Jidda tace "baza ki gane ba Aunty shifa kishi saukine dashi awajen me ta wakali. Ai kwara ke zuwa tazayi ta sameki nifa da zuwa zanyi na tarar kede kiyiwa kanki fadan alkairi kawai.
"shikenan yanzu Jidda za ace na zauna da wata wllh da ba a gidan Nabil bane zan iya zama da wata amma da shi bana jin zan iya.
Jidda juyowa tayi ta Kalli Hadim batayi magana ba dan dama ita bata fiye magana ba gyaran parking tayi ta fita tabar Hadim aciki
Fandau ganin har magari ba akawo ma ta Akkaam ba gashi dama dasa fe ma bata bashi nono ba dan yana bacci ta fito nonota ya ciko yakamata sai ciwo yake mata sosai Mama takira tace akawo shi mama "tace yo ina naga Daudan da tun safe ubansa ya dauke shi wai zai kaiwa FUJJI yafita dashi amma bari nakira shi.
"Mama dan Allah yakawo shi yanzu bai shaba da safe yanzu gashi sai ciwo yake min.
Tana gama waya da Mama ta fata jin hayaniyar su Haris
Suka shigo da gudu Fandau tace "banace kudena shigowa gida da gudu ba kuma nace kuyin sallama. to suka ce tare da komawa kuma suka shigo da sallama ta amsa tare da ware hannun ta suka fara rige rogen Fadawa
bayan ishai suna cikin fira ba sai sukaga Nabil ya shigo da FUJJI da Akkam yana hannun sa sai BilAL da Maaruf suma suna binsu abaya duk kaya irin da kayan yan ball ne amma dogon wandone duk kan su da fulan facing cap dayan ke jane da fari sai yafiyiwa Fujjirat kyu an fito mata gashinta ta fujin fulan da gudu tayi wajen Fandau tana cewa "Aunty kirki Fandau ta dagata tana mata wasan da tasaba yi mata ta na sauke ta ta ciren mata fulan tace "FUJJI na kidena sa irin wanan fulan na mazane kuma kidena sa Wanan rigan shima na yan ball ne."
Ita Fuj bata magane metake nufiba dan hankalin yatafi kan Nol
Nabil Marmushi yayi yace "kika sani ko ita ma zatayi gadon babanta ta zama yar ball ko baki san mata suna ball ba ko anan Nigeria mata sun ciyo mana cup na Duniya balle akace jinin Shiddams ai inde FUJJI tana da ra ayin ball zan mata jagaba duk Duniya asan da zamanta balle yaran nan nawa maza ai dolen su ma su gajeni.
Dr yace "kade tsaya a mazan.
"wllh inta na ra ayi sai tayi."
Fandau tace
" Allah yasauke yarana su zama yan ball.
Nabil yace "ai kin gama ya gama ai asalin sayin da ga ruwa ne tunda uban su yabuga ai ko basu buga ba sunan su yan Ball shiyasa basan sasu makaranta ba saina kowan balls wannan ra ayinane.
"ai bansan dan ball bane na aure ka.
Nabil murmushi yace"Kaddaran haifan y'ay'an ball ya kaiki shiku ma imani da shi yana cikin cika cikan musulumci.
Habiba tace "kai oga daga zuwa sai akama musan yan zance ba ko gaisuwa.
Nabil yace "irin abinda kuka koya mata kenan ai keda mijin naki rashi kunya yanzu idan na matsa mata ma inaga dukana zatayi dan dazu anan parlour na samu ta danne min mata tana dukanta.
Habiba tace" ayya wllh nima banji dadin abinba saide wllh nide ban koya mata rashin kunya ba Allah yaki yayen gaba.
Nabil yace "Ameen yawuce ai dama ita my one ai dan ni takeyi yanzu kuma ni Fandau tace bata sona na hakura yanzu saide ayi zumunci kawai. Dr baisa bakiba dan shi Nabil baya kulashi har yanzu
Habiba tace "au haka akayi.
Nabil yace "ai baki ma sani ba ai dake da mijin ki ku kuka hada komai kuma kuke zugata ina ga kuna tunanin ban sani bane to nasani kuma ku kuka hadata da BilAL din ma tona bar masa yanzu Mama tace nakawo Akkam ne yasha mukoma da baza ku gan muba.
Dr yace "ashe muna da amfani tunda har za aneme mu dan mu shayar.
Nabil daure fuska yayi dan yanzu gaba yake da Dr
Itako Fandau tashi tayi ta shige d'aki dan taji haushi magana Nabil naya hakura da ita
Fujjirat ta bita Nabil maya bisu har su Nol suka bi bayan su suka shiga
Dr yace "ban ce kashiga har d'aki ba.
Ko juyowa banyi ba yashige ciki
Fandau tana shiga tazauna abakin gadon tana tunani yanzu shikenan da gaske Nabil ya hakura da ita karfa garin jan jaji ta rasa damar ta har suka zo kusa da ita bataji ba dan bata rufe kofan ba balle taji k'aran budewa
Acinyar ya daura mata Akkam yasa hannun sa cikin riganta kawai sai jin hannun tayi a kan boobs dinta wani irin yar taji ajikin ta da saurin ta ture hannun sa tace "me haka?
"ido yakanne mata me kikaga abincin mu za abamu.
"kuma abincin da kai kake bashi.
"Ai dan ba abani dama bane da zan bashi.
Tace "yanzu dama kasamu kena.
"Eh mana da ban gankiba yanzu ko nagan ki.
su Nol wasa su kawai suka kama
Shiko Akkam tunda yajishi cinyar uwar sa ya fara laluman nono ita kuma ta kasa fitawa ta bashi shiko Nabil wani mugun sha awar tane yake d'awai niya dashi yakasa tashi da ga dur gusan dakyar ya bude baki muryar sa can k'asa yace "ki bashi zamu tafi.
Tace"wai kana nufin da Akkam zaka tafi.?
Yace"Eh
"tace yaron da yake shan nono zaka dauke shi agaban uwar sa ko da yake ba yanzu kuka fara wanan zalincin ba kuka kwace jaririn daya fado atake ma balle d'an wata 6.
Yace "ai naga yana shan madara sosai badan Mama bama da bazan kawoshi ba
Fandau ya kike son nayi narasa ki kince ba kya sona sai nabar miki yarona wanda nasan kiyar yar uban su zai iya shafar su,
Koba haka ba kiji tausayina mana ki bari indin ga ganin yarana akusa konaji saukin wasu abubuwa shikenan kullum hankali na arabe su Maaruf suna wajen Inna kullum sai naje na duba su ga FUJJI awajen Hadim suna gida ita ma sainaje sannan ga Akkam yana wajen ki kuma bakya son gani na Ni kuma bazan iya hakura da ganin d'ana ba shiyasa nake son na had'asu waje daya dan su hada kansu nima na samu nusuwa ko yakika ga.
Sai taji wani mugun tausayin sa dan yana maganan ne cikin kalan tausayi
Tace"ni nace maka bana son ganin ka.?
"Dazu mekika ce dana ce inason ki cewa kikayi bazaki karbi tayina ba tunda ban baki son lokacin da kike nema ba Fandau idan idona da gangan jikina bai sa kingane ina son kiba wllh fada abaki bazai fa shimtar dake ba amma
tunda bakya sona bazan iya tur sasa kiba dan ke mace ce dama d'aya tak kike dashi gwara na barki ki auri wanda kike so nikuma namiji ne inada dama wajen na auran mata har hudu iya adalcin da zanmiki da nuna miki so da sanyi yanuna son Gaskiya nake miki bawai sha awa da kike zargina akai ba to na goya miki baya ki auri wanda kikeso dan bazan bari ki cutu .
Fandau tace
"ashe son nawa baiyi nisa ba tunda gashi zaka iya hakura dani.
"baki ji ance hakuri yaza ma dole ba ai hakuri yana magani komai Fandau kin min komai arayuwa, ko yaran nan nasa agaba ina gani nasan jinin kine ajikin ki suka fito zai iya ragemin zafin dan haka dole kema nabaki abinda kike so ai awai wata yarinyar da ta dade tana bin bayana yar kono ce zan iya auranta na had'a ta da Hadim inaga su. Ishe ni rayuwa.
Shiru Fandau tayi kwai kode da gaske yake inko haka ne yazanyi
Afili kuma tace "ni kuma meye matsayi na awajen ka.?
"ai ke ta musamman ce matsayin ki awajena yazuce duk ida kike tunani ko cewa kikayi na hakura da Hindu ta kano zan hakura.
Tace "ni bawan nan ba matsayin aurena.?
Nun farawa yayi yana jinjinawa iya takun sa na bugan cikinta yace "bayan sakin da namiki bisa umarni na maida ki agaban Malam shi ya sani najen na nemi yardan ki danaje na tadda kina waya da wancen dan iskan to kinga har yanzu kina matsayin matata saide idan kince na sallame ki zan iya bin umarnin ki dan ni ba abin da nakeso irin nabi zabin ki nasa ki cikin farin ciki kamar yanda kika sani alokacin da muke tare wanda nasan yanzu ma koda bama tare idan naga yaran ki zaki ciga ba dasani.
"waida gaske auren zakayi auren huce haushi kenan.?
Yace "Eh hakane dan Gaskiya da na taba mata 2 nagani bazan iya zama da daya ba."
Ajiyan zuciya ta sauke ta sa Akkam a nono amma sai saiga Nabil yazu bawa wajen ido har Akkam ya tsaki nono tana dubawa yayi bacci zata kwantar dashi saiko ya dauke shi ya meke tare da jan hannun sauran yaran har yajuya tace "da gaske tafiya min da shi zakayi.
"Eh wannan damar kine har yanzu kina da sauran dama ta zama da yaran ki kiyi nazari kafin gobe damar ta kucce miki dan rabuwa da yara ba kara min asara bane kiyin nazari yana gama fadan haka yaza hannun yaran sa suka fita a parlour ko yatarar da su Dr suna kallon ya zuce su ko Habiba da take cewa agaida gida bai kalla ba
Fandau ta sha kuka
Amma tana gayawa Dr da Habiba suka ce plan ne ta zuba basa ido fada suka mata sosai akan ita tabari yagane tana sonsa dan yariga yagano tane kawai
!
Fandau kasa bacci tayi dan kuka ta shayi
*WASHE GARI*
Habiba bata je ko ina baBagana tazo gidan kamar yanda shateema ya mata alkawari suna cikin fira Fandau tace " yawwa ni Bagana jiya ina son na tambayeki bayan tafiyar su YaMainuna sai Shateema yaza kuka tafi abin yabani mamaki wai Yabintu da YaZahra Yakaka naga har da motan su duk dama nasan maza zajen su masu kudine amma harda mota haka.
Dariya bagana tayi tace "yo ai na gasa yazame musu yanzu Yazaina tace itama sai ta tsiya yanzu haka rabin kudin ta yana wayen Shateema ita ma Aisha ta hurawa mijinta wuta ina ga ma yatsiya mata bata koya bane yasa batazo da shiba,
Kawai dan sungan ni da mota kowa gasa yatashi....
Katse ta Fandau tayi da cewa kema kinada mota.?
Bagana tace "ai nina fara yi sun zata Shateema ne ya tsiyamin.
"waya tsiya miki?
Bagana "tace wata rana Shateema ya kaini gida da yamma yace aiki yamasa yawa na hau napep na koma nace to shine dana gashi wayan tacewa Mama zanje na hau napep shine Shiddams yana wajen ya dinga tsoka nana da wai kamar ni big girl acikin napep shine