Showing 114001 words to 117000 words out of 152888 words

Chapter 39 - Dama Ta

11 Oct 2024

8608

kunnuwa dan haka akiyaye tabashi danni banyi shima saida izinin maishi kuma yanzu fara DAMATA zuwa yanzu inajin (4months)*
*Bisssalam*

*42*


*A*binyi shine kiyar da muyin adua Allah ya bai yanata dan munemi yafiyar ta."

"Shid kadena min maganan yariyar nan dan ni bana son kodajin sunanta,
Kuma da kake cewa zasu nemi yafiyar ta kamanta batada tunani bata masan memuka mata ba....
"kedakata inde wannan abinda yafaru dake bai zame miki izina ba baza kitabayin nadama ba,
To albishirin ki ni yanzu kowa yasan ni mijin Fatima ne bai yananta kawai nake jira na zauna da kayana duk da bata da tunanin inason ta kuma zan gyara kuskurena yarane de kamar yanda kika fada kin tsira dasu dan bana son asirina yatonu akaran kaina ma,
Kuma kina da hakki na shayarwa da reno da kikayiwa yaran dan anbar miki bawani abubane Allah zai bata wani tunda ita tana da lfy keko baza ki taba iya haifuwa ba."

Har yagama tana jinsa kalaman suna kona mata rai amma bata da karfi da lafiyan da zatayi wani yunkurin dan haka tarabu dashi dan tasan abune da bazai taba yuwuwaba ta zauna da kishiya

Dr Muktar zaune gaman Maman Fandau yagama mata bayani koma tunda ga kan yanda Nabil ya yaudari Fandau da yanda duk abubuwan suka kasance bai boye mata komai ba
Mama wani irin gumine yake raso jikinta na murnan yarta tana cikin koshin lfy da kuma mamakin abinda Nabil yayi yanzu dama maganan da yafada karyane yanzu yan biyun
Nan jikokin tane Fujjirat jikartace
" Mutari hadani da Fandau din a waya mugaisa."

"Dr yace Mama kiyin Hakuri komai yakusa zuwa karshe badan yanayin jikin Hadim bada yanzu angama da komai,
Nide fatana kar kowa yasani har sai yafada da bakin sa dan nasan halinsa."

"bawanda zaiji Insha ALLAH Muktar Allah yamaka albarka ban tabajin labarin da yafaranta min kamar wanan ba ko budewan idona banji haka ba ni Aisa ina da jikoki 4 daga Nabil haryanzu banji son ya saragu araina ba saide makaruwa dan tun farko baisan yata bace da yasani kuma sunriga sunzama taya,
Bazai iya rabuwa da itaba shine yakulla wanan karyar dan yasamu daman zamada ita."

Dr yace"gaskiya kam kodaga yanda yayi jinya adalilinta dakuma yanda yake nemanta yayi nisa sosai akanta."

Hakade suka gama tattaunawa har yafi
Mama cikin al ajabin duniya da mamakin yanda wai suka yaudari Malam Dauda har yadaura musu aure

Bayan sati 4 Hadim tawarke sosai dan harta danfara takawa da sanda take takawa dan de tagamu da kwararen asbiti ne da sosai anyarda da ingancin aikinsu har an sallameta sunzo gida

*Nabil da Fandau* sunyi nisa sosai a chat dinda sukeyi wani lokacima shiyake tabota dan yana jin dadin yanda take tsaramasa kalamai daku ma kwantar masa da hankali akan Fatiman sa dan yazu tagane itace Fatima dan tamasa tambaya cikin dabara kuma yagama ta tayi mugun jin tausayi sa dan ba abinda yaboye mata na karyan da yayi wa Iyayen duk ba gaskiya yafada ba taji dadi
Yanzu ma da kansa ya tabota ganin tana online

_slm bakiye bacci bane dawa kike fira haka kode nasamu kanine_

Tana cikin bawa Akkaram nono taji message ya shigo tasan Nabil ne dan wayan nasane nashi kadai jawoshi tayi ta bude tana murmushi har ta gama karantawa ta maida masa da Ripley
_Ameen kaima ina nema maka yardan Allah yakake ya Fuj da kuma me jiki?_

_Ameen Fuj gata tayi bacci mejiki tana dakin ta ba kinki zuwa dubata ba."_

_Ayyya Abu Fuj naji tsorone kaga matar ka tanada kishi kartamin abinda tayiwa Fatin ka_

_Hhhhhhh baza tamiki ba aike bance ina sonki ba Fatina kodan nace inason tane taji kishinta_

_hakane fa aheni akatsa nake to Allah yabarka da Fatin ka_

_Ameen nagode sister kin iya adua da gaske kinkusa aure_

_nade kusa samun mijin amma bance nasamuba_


Yace _ok_

Tace _dadi na dakai kajerce magana bakason magana me tsawo nikuma gashi yau voice naka nake sonji duk da bayau nafara jiba ba_

Bayi mamaki ba datace ba yau tafara jin muryar saba dan yasan ana fira dashi akafafen labaru dariya yayi afili yace maki gama koshin wahala ba

Audio Yayi cikin zakeken muryarshi yace "muryata kawai kike bukata kenan to gashinan ai muryata tanada araha wanda bai kaiki bama yaji akyuta balle keda kike farantamin kike tayani aduan samun *Fatina*."
Yana dariya yake maganan cikin kayatarwa

Ai Fandau jitayi kamar ta shide dan jindadi tana sauraron muryar sa tana wani lumshe ido saida ta saurara yafi so 10
Sannan tarubta masa Ripley

_kasan wani abu?_
_"a a_
_Allah yayiwa muryar ka wani baiwa ko kasan dahaka?_

Yamayar mata kamar haka

_nasani dan naji abakin mafi zakin murya acikin duk kan muryoyin duniya dan Fatima ta dabance muryar ta daban ne kullum sai muryar yamin gizo_

_bayan ita bawan taba gaya baka kenan sa ita_

_nasha ji bazan iya lissa famiki wanda suka ce ba kamar yanda bazan iya irga gashin kainaba amma inason nuna miki nata yafi kwanta min_

_Gaskiya kana fifita wanan Fatin fa zaka sa nadawo yar aunty Hadim fa_

_dako zaki rage girman ki a idona_

_Ummm saina kega kamar kafison Fatin ne wai wakafi so cikin su?_
Yace _Uumm kinsha min wanan tambayar ina baki amsa to dukka inason su dan dukkan su matanane kuma yan uwanane amma ya isa dan bacci nakeji_
Tayi saurin mayar masa

_please amma meyasa nekake nuna rashin damuwa agareni kamata yayi kaji muryana nima kamar yanda naji naka_

Sarai yaga message dinta amma yasauka bai bata amsaba

Dariya tayi tace bawan Allah kenan

Hakan ma saida tayi recording dinta tura masa

"shikenan dama inason nace maka nayi mafarkin kaga *Fannndo*
[2/18, 9:39 PM] ‪+234 816 362 8229‬: *DAMATA*

*NA*

*BATUL ADAM JOTTAKO*


*43*

*Editing AYSHA ALIYU GARKUWA*








*Hadim* duk suna zaune a genaral parlour su Nabil Ummi Maman Hadim,
saiga driver yashigo da Fujjirat dan gidan Dr ta wuni sauk'eta da drv yayi ta arce dagudu tayi wajen Nabil tana cewa.
" Abuu." cikin gwarancita ware hannun sa yayi yace "Oyoyo Mamana."
sannan ya d'an kalli drive yace.
"Kako kyauta dan yanzu nake shirin zuwa d'auko ta."
baturen murmushi yayi yafice

Cikin kulawa da k'auna Nabil ya shafa kan Fuj tare da cewa.
"Wow waya miki wanan gyaran? yayi kyu sosai."
Cikin gwaran cinta tace.
" *Aunty kirki* ."

Maman Hadim tace.
"Kaji harda wani cewa yayi kyu,
wannan bak'ar wani kyu gareta bak'a sai sadaka."
Hadim tace.
"Mama ai Fuj ba bak'a bace."

"Eh mejin tsoronta zaice ba bak'a bace,
wankan tarwad'a ce,
niko bana tsoron ta kinga dole bak'a zance mata."
Hadim tace.
"Kalan chocolate cefa Mama tafi fari kyu yanzu su ake yayi."
Aiko Nabil dad'i har ransa dan Fandau dinsa yatuno kai ya jinjina
Yace.
"sosai Maa sunfi shiga rai da ratsa zuciya."

Hadim sai asannan tagane ta kwafsa daure fuska tayi tace.
"Fuj zonan wai ni Nabil wacece Aunty kirki nanne a gidan Dr?
Kullum taje ta dawo sai tayi tamin zancenta."

ido ya lumshe tare da cewa.
"Bansan taba sunanta kawai nakeji awajen yaran gidan da Fuj."

Amma wani abune yafado masa Aunty kirki ko itace matar Dr kai ba ita bace ita da take kulle adaki tunuwa da wanan yatuno masa Akkaram d'an gidan Dr tunda yaga d'an so d'aya bai k'ara kanin saba,
Dan yaje gidan Habiban tace,
anfita da yaron gayana son doctor yazo su d'auki mataki d'aya amma Dr ya makale a 9ja.!

Ummi ma dariya tayi tace.
"kai Ya Fatime kina kushe min cuwuna fa to ki dubi mace har mace kice sai sadaka,
to kwantar da hankalin ki batayi ta tsohon naku."

Duk aka sa dariya banda Nabil da yake duniyar tunani.

Fuj tasa hannun a aljuhunta tafito dawani paper ta mik'awa Hadim
Tace.
"Aunty kirki sweet."
Karb'a Hadim tayi ta bud'e sweet d'inne ko a ciki an nad'e,
amma takar dar da rubutun cikin yafi daukan hankalin ta dan kullum idan tadawo da sweet d'in aciki amma da acikin pepper kuma duk rubutun irin daya ne tana karantawa amma bata daukan abin da muhin mance sai yau da taga ansa sunanta wai *mum Fujjirat*

Ga aminda aka rubuto kuma ba banbanci da na kullum

```Rance ba kyuta bane..! sadaka yana da ranar fansa..!
Dutse ba abincin gara bane..!
wani baya amsa sunan wani..!
ajiya maganin wataran..! ~Aunty kirki~``` ..!

Hada hausar tayi amma bata fashici komai ba dama kullum hakane zata karanta amma bata fahimta,
amma yau da tasa mum Fuj tasan ita akayiwa massage din kenan gabanta ne taji yafad'i to wacece Aunty kirki?.
Ita dai Fuj karban sweet dinta tayi tana sha.

Itako Hadim sai ta sauk'ata ta dauki sandar ta tana dingisawa ta haura saman,
Wayan Habiban ta kira tana dauka tace.

"Wacece Aunty kirki?."

Habiba tace.

"Ranar ma kinmin wanan tabbayar nace miki bakuwace yar uwar Abban Nol ce.!"

"Kibani ita."

"Ok tana sama bari in kirata,
ai tana da kirki tana son FUJJN ki."

"Ok kiratan."

Habiba ta kashe wayan tukun ta kira Fandau ta mata bayane yadda sukayi sanna takira Hadim tace.
"To gata."
Fandau ta karbi wayan bayan tayi salama tace.
"Mum Fuj ya Fuj ta sauka lafiya?."
Wani irin faduwan gaba Hadim taji danjin muryan wada bata kaunan ji arayuwar ta amma tasan ba ita bace muryane kawai yazo d'aya
da haka tace.
"Eh tazo muna godiya fa da kulawan ki akan 'yarmu,
amma wani abu da kike rubutawa bana ganewa,
shine yau nace baride na tambayeki me fassaran sa??."

"Au wai
RANCE BA KAUTA BA NE..!
SADAKA AKWAI RANAN FANSA..!
DUTSE BA RABON GARA BANE..!."
WANI BAYA AMSA SUNAN WANI..!."
Hadim tace.
"eh."
"Ok kinsan yaran Aro ALLAH yabamu ba dukuba ko,
abin da ba duka aka baka ba kinga rancene ba naka bane nasiha namiki dakuma tunatarwa yara rancene."
"tace hakane fa to nagode dawanan tunatarwar ina fatan wataran zaki kawo mana ziyara ko?."

Wani irin bahagon murmushi mai d'an sauti Fandau tare da cewa.
"ai Aunty zuwa gidan yafi K'arfin ziyara karki damu wataran ana mugun tare."

Hadim tace.
"gaskiya kinci sunanki Aunty kirki kinada kirki,
to bawa Auntyn naki ko."

Fandau tana dariya ta mik'awa Habiba wayan
Habiba tace.

"to ya k'afar?

"Alhamdulilah da sauk'i."

daga nan suka dan taba hira dan ita Hadim bata kawo akanta wani Fandau tana kusa ba kawai tana son jinne me Aunty kirki take nufine kawai.

Nabil ne zaune a d'an wani runfa na shan iska acikin gidanshi kiran Maman Fandau yashigo woyar sacikin murmushi ya d'auka Yace.
"Allah ya taimaki HAJIYA Mama."
Tace.
"Ameen tareda d'ana ba."

"Mama ya gida?

"kowa lafiya amma sai rashin Fandau bawani labari ne?."

Abin yabawa Nabil mamaki dan shi bata tab'a tuntub'ar sa akan Fatima ba koda shine yamata zancen haka take cewa yayi hakuri insha ALLAH za aganta yadena damun kansa,
sai gashi yau da kanta take tambaya,
karfa taga gazawarsa shiko ba irin neman da bai yiwa yariyar nanba cikin rawan murya da kamar zai yi kuka yace.
"Wllh Mama ana cikin bincike fa,
amma har yanzu bawani labari,
mama idan bansamu Fandau ba rayuwa bazata zo dai-dai ba yanzu nakoma bakin aikin na amma nakasa shiga filli ko sau d'aya Mama,
amma nasa ayi istahara man agani nide na sha sawa anamin anacewa tana hannun mekyu da kaina ma nayi amma danagan ta a mafarki sai tajuyamin baya."

Cikin kuka yakarasa maganan

Mama taji tausayinsa duk da tasan karyar da yayi.
"Haba mesunan malam kazama namiji mana ka kuma sake kokarin nemanta dan tunkafin kagaya mana matar kace kamin alkawarin kawota da hannun ka."

Yace.
"nayi Mama amma gashinan nakasa cikawa Mama duk tunanina yakare akanta narasa yazanyi har wajen 'yan duba saida na Ayyana zuwa sai kuma naji tsoron,
*Hukuncin Allah."*
book din Aysha Ali Garkuwa kenan mai fitowa

Mama tace. "Subahanallahi kul kai da kasa addu'a kana da Allah meyakai ka sakin reshe ka kama ganye."

haka takoma lallashinsa saida yadan sauk'o
Tace.
"ina Fuj?."
Yace.
"Sunfita dasu jidda da su Gana."
"kasuwa sukaje?."

"eh harda Iya da Inna ZAINABU suna da yawa sunzo
Duba Hadim ne."

"kai dana sani da nabisu nazo ai dubata nima."

"Ba damuwa Mama akwai yan zuwan jibi zansa Grema yakarbo passport dinki ayi visa dake."
"nagode d'ana."
A haka
Sukayi sallama

Yau har su Maman Fandau sun sauka Hadim ta tarbi Maman cikin fara adan ita arayuwan bata da matsala dakowa sai kishiya bata sonjin wanan kalman ko ga watane ba itaba.

Shiko Nabil sai yau yabud'e sakon Fatima menaci kamar yanda yasaka mata
Yana dariya ya bude a
Audo saida ya gama karan ta sakonnin ta duk na korafine akan kwana 2 yashare ta sai ida tace.
_amma banso mukayi irin wanan rabuwan ba dan na d'aukeda amatsayin d'an uwa dalilin haka na nemi muga juna kafin nabar kasan amma kayi burus dani inason inmaka albishi da maganan da nagaya maka na nakusa samun masoyi ya tabbata dan nasamu *mijin raina* shaharare kamarka wanda da maka dama ni burina na auri wanda ya shahara a ball dan tun ina yariyar inke da wanan raayin burina yaci ka nasamu mijin raina kaima ina maka fadan samun Fandau dinka_

_nasan kasan mesonnawa dan makusan cinka ne_
_*BILAL MAINA KANGE BG* nayi murna da zama matar abokin kaga muna tare *FATIMA MUHAMMAD GARGAR*_
*Bissalam*.

Sai pic din Bilal da yagama budewa ya baiyana afili yafurto nima ban soki ba me BilAL zaiyin dake ta haka kika bullo kuma yariya dariya yayi sosai yace amma da nake pic din kika turo da yafi dan naga yanda kike amma fa sunan Gargar yabugeshi dama yar meduguri ce kuma gargar anguwan Zannah ne.

kunan audio nata yayi saime jin muryar da arayuwansa bazai taba banta meshiba ya fara dukan dodon kunnen sa
kamar agabansa take maganan.
*SHIKENAN DAMA INASON NACE MAKA NAYI MAFARKIN KAGA _FANNNDO CE_*.

Meyasa tun ranan bansaya naji ba nace ina bacci ashe me irin muryan Fateena ce dan tundaga ranan bai wani sake bude message nata ba
saiya sake dubawa *FATIMA MUHAMMAD GARGAR*
full name nata ya akayi sunan ma yazo dayan da Fatima sa gaban sane yaji yasake faduwa yace to wacece yasan de ba Fandau bace dan Fandau batada lafiya kuma me zai kawota London! amma daya duba Last seen
Wajen 1week kenan rabonta da online yariyar da kullum sai yaganta on ya kunna
Voice yaji so ba adadi muyar natane de ba wai gizon ne ba kawai sai ya yanke hukuncin yayi call nata har yayi dialing amma aka ce masa anrufe layin gaba daya cikin haushi yasake shiga cikin sakon nin nata yaci karo ko da sokon da take cewa.
_To YASHIDDAS yaune tashinmu fa dan ma nasan zakaje bikin mudan yazame maka dole_
Afili yace.
" Towai ko da gaskene?." da sauri yagirgiza kai yace.
" Sam bade BilAL dinaba bayanda za'ayi ya shirya aure batareda ya gayamin ba."
amma shi yanzu duk bawanan ba yafison yaji muryar wanan wanda take masa gizo da Fandau

Yana cikin haka wayansa ya fara ringing yana dubawa BilAL ne ya dauka yana cewa. "Kamar ko kasan kaine araina dan yanzu nake shirin
kiranka."
BilAL yace.
"Sai kuma gani ba toya akayi?."
Dariya Nabil yayi yace.
"kimanin 3 months kenan muna chat da wata yarinya har tace galabata mukayi dan sabo da ita to dan tamin tayin kanta nace a a, yanzu kuma naci karo da sakonta wai dama shaharata a wasan ball take so yanzu tasamu wani shima shaharare ne burin ta yacika kawai saigashi ta toromin pic dinka dan ita wawuyace."

Dariya BilAL yayi yace. "Me abin wawanta kan aciki ai wanda Fatima tayiwa tayin kanta yaki amsa shine wawa domin *DAMACE* babba sosai tazo masa yasake yarinya yar sarauta yar babban gida bata inda bata kai macce ba,
burin kowane namiji na karbeta nikam dan gudun kar *DAMATA* ta kubcemin,
yanzu haka ma ina airport din London zan tafi neman auren ta ahe dasai dai kaji na angwace."

"Wai dama da gaskene ?to wacece ita tacemin sunanta Fatima Muhammad garga,
kai kuma gashi kacemin Yar sarauta ce yar wane gidane kaina yadaure? ."

BilAL yace,
"yes da gaskene naji tausayin tane dan tafadan min tarihinta kakaf kusan irin abin da Hadim tayiwa matarka,
aka mata saide ita ba aci nasaran sa mata alluran ba,
kuma ita nata zalincin ma yayi yawa wai fa auren sukayi dan ta haifu su dauka sumata sakin wulakanci kuma har ta haifun yanzu haka yaranta ukku suna wajen su amma tafita da cikin nabiyu amma acewar ta wai nima nasan mijin nata masai dai dan tanason cusa masa haushi bazata gayamin ba sai bayan munyi aure,
Da auren gaggawa naso muyi da ita saboda nina daukawa kaina lefin nina yaudareta na aureta gudun kar abata wani wada Iyayen suka zaba mata nikuma inason ta shine muka gugu na aureta,
dan tacemin
kishiyoyin Mamar ta zasu mata gorin taje karuwanci amma dayake ta na tsorace da abin da wancen mugun ya mata shine tace ita sai anje gaban iyayen tukun ."


Cikin firgice Nabil da yaji kamar ya dankare awajen kode Fateen sace
Dasauri da rawan baki yace.
"tagaya ma ya zaman ta kewansu ta kasance? tagayama ya yanayin yaran nata yake mata ko maza?

"Eh tagayamin da farko macce ta haifa na 2 kuma twins duk maza
Yana yin zaman su kuma labarin da tsawo idan kanason ji ka sameni a airport din dan bayanzu zamu tashiba."
ai Nabil baima gama sauraron BilAL ba yakashe wayan jikin sa yagama bashi Fateema sace kawai da sauri yashiga gidan.

amma me yatarar ana wani danjan da Inna ZAINABU idan maku manta ba a koi photon Fandau adakinta na itada Bagana da Mama kuma na taba cemuku Fandau da takeson koyan rubutu tarishin rayuwan ta take rubutawa to pic din yana cikin wannan life story nata ta turashi kasan bed sai yau yasmin ta fito dashi tana gama karantawa ta cikin kuka tace.
" Wllh awannan karon idan ba ayarda dani ba zanfasa kowa yaji." kunsan Yasmin lawyer ce mekare hakkin dan ADAM dan haka tana da mugum tausayi gakuma ta jima tana tara bayanan dan bata yarda da yanayin Hadim ba su Jidda ko dasu aka karanta Inna ZAINABU da Maman Fandau duk suna dakin sai da akayiwa

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login