Showing 120001 words to 123000 words out of 152888 words

Chapter 41 - Dama Ta

11 Oct 2024

8625

"itama Hadim din tana nan ai.
Inna tace "bazan kore taba dan tana gidan kanwar uwar ta amma nace banda gidan d'ana

shiko Nabil har yanzu ahanyan neman Bilal yake gashi idan yakirashi sai yace muhadu agidan Zannah kawai

*Washe gari agidan Zannah*

Nabil wurjajan yafado gidan Zannah ALLAH ya temaka ba shida bak'i sai wasu almajirai sai malam Dauda da bai gayawa Malam komai ba tun,zuwan sa gaban Malam yaje yazube dan yaje wajen Mama tace bataga Fandau ba tunda tazo kuma tun ajirgi ya gaya mata Fandau tana wajen Bilal
"Malam ansamu Fandau ta fito wllh tana wajen Bilal amma yace sai agaban ka zai bani matata.
"Waye?
Bilal kuma?
inji Malam
"Dan gidan Ahj Maina kange ne.
"abokinka kenan?
"eh Malam gashi kuma nazo da ta shiga ciki Mama tace batanan wllh idan ahannun sa yarikemin ita hartsawon wannan lokaci wllh zamuyi shari a dashi.

"Subhanallah!
meyayi wanan zafin kuma?
Shiko Malam Dauda dayake yasan komai nunawa yayi kamar baya jinsu

"toyanzu ina yake shi Bilal din?
"yace wai idan nawo a kirashi kiran Bilal yayi yace gani agidan Malam din

Shiko Bilal sungama duk wani shiri da zasushi kuma sun samu Baban Nabil sungaya masa komai
yace "suyin daidai yanzu ina Fandau din.
Dr yace suna gidan nan tare muka zo sunshiga ciki,
zamu tafi Gargar tun tuni Nabil yana can.
Yace "au haba.
Ai dasauri Alhajji abukar yayi ciki dan yanason ganin Fandau

Fandau da Habiba sanda suka shiga gidansu Nabil a falon Iya suka tarar da Ummi alokacin suma jajabin abin suke amma dasu kaga su Habiban sai sukayi shiru suka gaisaUmmi tace "ina su Haris Habiba tace "suna Gargar da Inna.
Ummi tace "ah da Hajja Fajji kukazo kenan?
"eh
Iya ce ta zubawa Akkaram ido tace "Hajara ganomin wani d'a ahannun wanan yarinyar kamar d'ana yana karami gayanda yake zillo kamar Shid.
Ummi sai alokacin ta kalli yaron tace eh kuwa amma Habiba dan ta basar da zancen tace "Ummi ina yaran gidanne?
"suna dakin su har kawar kima gaban Fandau yafadi duk da tasan dama yau dole taga Hadim amma taji wani irin dan haka tafara karanto addua
Itama Habiba saida taji wani irin wata kila yau kawancen su da Hadim yazo karshe
Tana cikin wanan tunanan taji Ummi tana cewa Tasleem "rakasu dakin Gana
har zasu fita Ummi tace yarinya kawo dan gidan waye ne? Itade Habiba fita tayi da sauri dan baza aji abakin taba
Fandau ce tajuya ta bawa Ummi Akkam Ummi da Iya suna cewa ikon Allah ga yaro hamar su Maaf suna jarirai Fandau sun kuyar da kai tayi ta fita
Hadim jabe akan katifa tayi wurjanan da sauri Habiba ta karasa inda take
"Mum Fuj kina hutawa fa
Ta karasa ta rungumi Hadim
"lfy naga kinrame ko jikinne? Kafin Hadim ta bata amsa saiga Fandau ta shigo cikin takunta na isa idonta fes abude sallaman da tayi muryarta yadoki kunnen Hadim da sauri ta daga kai aiko sai gashi idon ta cikin na Fandau da sauri ta meke wacece?
wanan mekikazo yimana gidannan yawushe kika warke?
Suma su yasmin sai kallon Fandau suke dan yasmin kam tagane wacece

Hadim a tsorace take nuna Fandau "kece kece?
Habiba tameke tace Ayyya kin santane?
Itade Hadim kallon Fandau take jikinta yana rawa ga dama kafa ba lafiya
Hadim tace wa Habiba "ke kinsanta ne?
Habiba tace "sosai yar gidan zannah cefa Zannah namu na Gargar.

Kafin Hadim tace wani abu sai ga Fuj tazo awaje tana ganin Fandau tayi kanta tana cewa "Aunty kirki.
Itama Fandau daga ta saba tayi kamar yanda ta saba tace "iyye wannadin Fujn wacece?
Fuj tace "yar gidan Aunty kirki dama sunsa ba haka idan taje tadin ga tambayar ta kenan yar gidan wacece tace yar gidan Aunty kirki
Fandau" tace eh mana rance ma kyuta ba ajiya maganin watarana Fujn Aunty kirki.....
Ai Hadim sandan ma bata tsaya dauka ba taja kafa ta karasa inda suke da jarfi ta fusge Fujjirat ahanun Fandau tana huci tafara magana dama kece Aunty kirki kina nufin kinban race ne kindawo rayuwa ta dan ki tarwa tsamin ne wllh saide ki tarwatse aniyar ki tabiki yar gidan matsafi har alluran bantau ya kasa aiki akanki to wllh aniyar ta biki bade....
"Ameen Ameen Fandau ta katseta haba Aunty yazaki min addua bazaki ban *DAMATA*nace Amin ba ai duk wada aka cewa aniyar ka ta bika baice amin ba tofa aniyar ce batayi kyu ba Ameen.

Shiru Hadim tayi tana huce
Fandau
Tace "Haba aunty kici gaba mana kokin gamane?

Hadim tajuyo kan Habiba tace"Habiba meya hadaki da wannan yarinyar?
Ina kika santa?
da kinsan ko wacece ita acikin rayuwata kuwa nasan da kinsani da zaki gayamin mu hallakata nayarda dake bazaki zauna da itaba to wannan da kike gani annobace da gaiya take rubutu min latter nasan da kinsan ita wacece da maki bari ta kai iyanzu ba danasan bazaki bari ta baiyana ba baiyanar ta kamar tar watsewar rayuwa tane ina.... Maganan ne ya makale mata sanda Tasleem ta shigo da Akkam tana cewa "wai gashi yana kuka.
Fandau tameka hannnu takarbe shi tasashi a nono su Jidda da sun gane wacece Fandau bin yaron sukabi da kallo Gana tace "cikin bai zubeba kenan Yasmin tayi saurin karbar sa tana cewa" haba ai dagani ba tambaya wanan jinin YaShid dukka suka fara murna banda kanwar Hadim Ashuwa
Hadim tace" Innalillashi waninna ilaishirajuna cikin da da idona naga jini ace bai zubeba...
Fandau tace"kina mamaki ne Aunty ai ba abin mamaki a kikon ALLAH kowa yayi iko ba zaiyi irin nasa ba kinyi mamakin ganin abinda kikaso yabaru akaina yafaru akanki ko kin sa azubar min ciki Allah bai yarda ba ke kin haifu yakarba ko gani bakiyi ba sanan anyanke miki maifan balle ki saran samu nan gaba gashi yaran da kike dasu kuma na arone shikuma kayan aro baya rufe katara kinsa asamin alluran bantau gashi ke Allah ya nakasa kafanki.
"Nizaki cewa naka shesheya zata iyo kan Fandau daidai da shigowan Baba da su Ummi Iya tana cewa "haba nifa inaganin yaron nasan namune itako Ummi tarasa mame zatace
Baba yace "kai kai Hadim ta dakata tana huci
"kinyi na farko ba adauki wani mataki ba shine kike yunkuri kai mata duka acikin gidana daga ke har mijin naki ayau zakusan wacece Fandau duk kuzo mutafi dan nasa adauko uwar taki me cewa bata yarda ba anmiki sharri ana shirin kwace mata jikoki tar ta maka mutane akotu to Allah yakaimu Monday ayi akotun ma yafi Duniya ta gama sanin me kuka aikata keda azzalumin mijin naki yanzu haka kafin kotun ma Zannah yana son ganin mu kuma harke duk kutashi mutafi.

Hadim tace" nide ba inda zance
Baba yace "shikenan yizaman ki karki min rashin albarkan da kikayiwa Yayata.
Kusauran kufito mutafi haka zuka tafi akabar Hadim dasu Yasmin


*GIDAN ZANNAH*
Fandau da motan su yayi parking kasa sauka tayi duk sauran mutane sun sauka tadaga kai taga yanda kofan gidan suya ya canza duk da dama zanen sarauta ne amma baikai wanan kyu ba wasu daga cikin almajiran gidan ta gani kamar suna kallon ta sun kunyar da kai tayi kasa Habiba ce takula da Fandau bata fitoba ta zagayo ta bude ta jawo hannun ta
Tace "Aunty ina tsoro.
"tun agida nagaya miki karkiji tsoro tsoro me?
"Aunty haduwar muda Mama Aunty inajin kunyar ta kuma ina tsoron Baba Aunty kisa amedani gida bazan iya shiga ba.
Fisgota habiba tayi ta fito da kita "kinga aiko ke zajija hankalin jama a kanki wanda idan wucewa zakiyi dom dom bazasu ganeki ba kiyi adua kawai haka suka fara takawa har get na biyu wada anan baban parlour Zannah yake nan mutanen suke ta duruwa akofan ma saida ta tsaya tare da kyankyame hannun Habiba janta Habiba tayi ta shiga da ita

*wai wai koni*
*B Jattko saida nayi kamar zan sanbada da gudu ganin taron maza da mata awannan makeken d'akin taron*

Habiba ta ja hannun ta Fandau kanta ararufe har suka samu waje suka zauna wayanda suka zo tare ne kawai suka gane itace amma duk basu ga fuskanta ba
Bayan Malam Dauda ya bude taro da adua
Zannah yayi kyaran muryar yace "to Nabil gaka ga BilAL Maina da kakawomin karan matar ka tana wajen sa.
"eh Malam tana wajen sa
Malam ya Kalli BilAL yace" Bilali ya akayi haka ina kataba jin ana aure kan aure kuzaku fara kaida abokinka?
BilAL cikin nusuwar yafara magana "Gafarta agabana Nabil ya tsara muku yanda ya auri Fandau ba akasannan ba kuma tana da ciki aka zubar da cikin to meye hadita danawa wanda gayanda akayi auren ya bawa Malam labarin auren Fandau na gaskiya wanda Malam Dauda ma yakara da cewa shine maya daura auren.
Zannah yace "to wandan abu da rikitarwa to inaga ba yarinya daya bace wacece tawa Fandau din aciki? Dasauri BilAL yace" tawa itace Fandau dinka dan yanzu haka neman aurenta nazo.
Malam yace "Masha ALLAH to kai Nabil kayi adua ALLAH ya baiya na maka taka Fandau din kaji ba ita bace
Nabil yace "itace Wllh itace.....
Baban sa yadaka masa tsawa yace "kama yarda mutane sha shawu ne irinka bayani da kamana da wanda BilAL yayi ba daya bane zaka kafe akan matar kace.
"Baba itace yazama dole nafadi gaskiya koda duk duniya za su tsinemin ne akan inaji ina gani arabani da matata
Ni newan da BilAL ya bada labari yanzu duk abinda na gaya muku wancen lokacin ba gaskiya bane shiryawa nayi dan na rufe nawa lefin ga Sani shine sheda na kuma shiya karbomin auren awajen Malam Dauda amma kuya femin.
Yana gama fadan haka ya fashi da kuka
Zannah kansa Afirgice yake kallon Nabil dan abin yabashi mamaki yajuya ya kalli Malam Dauda yace"Malam kasheda wanan Sani shiyaje da Fandau aka daura auren?
Malam Dauda yace "shine kuma ni dama Mutari yaga yamin nasani saide munbari ne kawai ya fadi kayansa kuma gashi ya fada.
Zannah yace "yanzu ina ita Fatiman Dr yanuna masa Fandau
Malam yace "ta matso kusa kanta asunkuye tafara ja dabaya dan tsoro Nabil ana nuna ta yameke a razane zaiyi inda take Baban sa yace "koma ka zauna.
Yakoma yana binta dawani irin kalllo yana so yaga fuskanta amma arufe Yana son ya gaskanta Fateeman sace meyasa wanan ranan tazomin da haka naci burin ahuwar mu dake zannuna miki matsayin ki agaban kowa amma Baba yahana.
Malam yace "Habiba matso da ita.
Haka Habiba tameke ta daga Fandau har gaban zannah hanunta yakama yace "tabbas wanan itace tawa Fatiman Fatima Muhammad Nabil shine mijinki?
Gyad'a kai Fandau tayi
shiru Malam yayi duk wanda yasan shi yasan ransa amutu kar mace yake da kuma mamaki da kunyar kunsan shikansa yayi karya wanda zai iya cewa shine karyar sa ta fari aduniya dawane ido zai kalli matansa da yaran sa dayamu su karya yayiwa Fandau Aure da bako yana daga kansa yaci karo da matan sa sunzuba masa ido har yaran sa maza manya rasa mezai ce yayi ya sunkuyar dakai cikin damuwa Baban Nabil ya fukanci haka yameke ya karasa wajen Zannah yazube guiwowunsa cikin tsananin bacin rai yafara magana
"kaicona kaicona Malam karene ni kamaye min gorbin uba asanda narasa nawa uban amma gashi yau nina haifi dan da yasaka b'acin rai wanda banta ba ganin sa acikin fuskanka ba atsawon rayuwata daka ina nema almarman ka zan yankewa Nabil hukunci agaban ka dan Allah kabani DAMATA na hukunta shi kar kace komai lefin sa babbane
Kai Nabil wandan auren naka na zanba cikin aminci kai tsaye bazance haramcecen aure bane amma ba abi yanda shari atace ba baka nemi kauren ta hanun waliyen ta ba bayan tana dashi koni waliyin auren Fandau ne amma ban sheda ba dan haka ba ka can canci zama da itaba tunda bakasan yanda ake neman aure ba shikan sa auren ka nafari kana England na dauki matar na gaimaka shiyasa baka san yanda ake neman aure ba ayanzu nake son karubutawa Fatima ta kardan sakin ta kai ba mijinta bane yarinya me daraja kamar ta ba matar ma karyaci maha inci irinka bane
Wanda hattta iyayen sa basu fi karfin ya musu karya ba yameke yaje ya ciro fefa acikin littafin Malam ya karasa inda Nabil yake ya meka masa tareda biro yace ina son karubutawa Fatima saki.

Girgiza kai Nabil ya shiga shi
"yace wllh da wanan hannun nawa bazan iya rubutu saki ga Fati ba.
"idan baka saketa amasayi na nawaliyin ta ba zaka saketa matsayayina nani ne uban ka bisa umarni idan baka sake taba kadena amsa sunan d'ana kuma ta take anan zan tsine maka.
"Baba kaji tausayina wllh mutuwa zanyi idan nasake rasata.
"ai idan da zaka mutun da yafi komai sauki da anrage iri dan gaba bansan irin yaudaran da za kuyiwa a wani wajen ba kuje kusake wannan zanban nakuba musamman yanzu ta matar taka take juya.
Nabil zaka saketa ko kazabi tsinuwa
Ni *Habubakar Ibrahim damasak* nat.......
"zan saketa kar ka tsine min Baba.
"to zaketa
Yakarba yabara rubutu duk awani karkace saboda hannun sada dayake mugun rawa

Afirgice Fandau ta bude fuskan ta ta fara magana cikin kuka da firgice

"Baba kar kasa yasakeni kar kamayarni karamar bazawara wllh inason mijina
Nabil da dakawa yayi yatsaya kalonta cikin kuka
Tsawa Baba yadaka masa yace kazabi...

Rubutun yafara amma fa wahaye duk yajika fefan sai yankewa yake yaru buta
_ni Muhammad Nabil nasaki matata Fatima Muhammad bisa umarni mahaifina amma batanin komai ba ALLAH kayafemin_

Yajefar da biron yakifa kansa a kujera
Baba ya dauka ya karanta afili
kowa tsaida yaji ba dadi
*dama haka saki yake yana da korjine wanda ko makiyin ka akayiwa sai kaji badadi*

itako Fandau jirine yafara ibanta Habiba tayi saurin zaunar da ita

Baban Nabil yace "kwantar da hankalin ki Fatima ki godewa ALLAH agobe ba yau ba zan daura miki aure tunda ba wani idda akanki dan da ciki kika fita tunda kika haifu baku haduba bakida wani iddan sa
Kai BilAL kanason Fatima?
BilAL yace "Eh Baba badan kar ayi aure marar tushe ba da anan zan aura maka ita amma kaje gobe kaso da waliyan ka.
"nagode Baba.

Afirgice Nabil yajiyo atsawace yace "
Wllh wllh duk wanda ya aurin matata yafara irga kansa cikin wanda zasu yi gado da makara aranan ga Fatima naga uban daya isa ya daura auren ta ina raye. Yasake kifa kansa yafara rusa kuka kamar yaru ba necewa shine Shiddams mutumin yafi SHEHU da gomna acikin garin meduguri adon mutane
Baban bai ceko maiba azagin da Nabil yayi dan yasan halin d'an nasa idan ransa yabaki zai iya bude baki yazageshi ma

Malam yayi Gyaran murya zai cewani abu Baba ya tashi yakara sa inda yake cikin kunne sa yarada masa wani abuda duk bacin randa Malam yake ciki saida yamurmusa
Daganan Malam yarufe da adua ya sallama kowa Akkam yanawajen Ummi har zasu fita

Malam Dauda yace" ina mesunsn nawa ita ko Fandau kuka take sosai Habiba tayi bangaren Mama da ita su BaGaji ansamu abin fada sai kira suke duniya abin tsoro abin magana irin wanan agidan Malam mama de shigewa tayi bata kulasu ba Hadim kam dama batazo ba
Baban Nabil shima bangaren Mama yashiga Fandau yaja gefe sunjima sannan yafito yatafi Fandau ta rungume Mama sai kuka suke har dare matan gidan suna shiga suna fita har zance yafara yaduwa gari itako Fandau burinta taga Bagana dayaran ta kawai

Shiko Nabil kinfita yayi agidan yasa Zannah agaba yana kuka har 10 dare shima Malam dannewa kawai yake amma jiyake kamar yayi kukan dan bai san hanyar da zaiyin ya gyara kuskure karyar da yayi ba dan bai zaci abin zai zoda hakaba amma ya danne nasa yake lellashin Nabil amma ina kamar kara masa suke sai zaje zaje yake ganin idan ya matsa shidin ma Nabil gaya masa magana zayi yasa Malam yafita wajen Abokin sa akaramin parlour sunfita sun barshi
Sai wajen 11 Malam yashigo ganin baiga tafiyan Nabil ba yace "Nabil yau kenan agidannan za ka kwanan?

"Eh wllh namai da matata sakin umarni nayi kuma na mayar zanga wanda ya isa yazo yafitamin da mata tunda na mayar ta Malam ka tekamin kar na rasata.

" a a Nabil wanan rigimane tsakanin kada mahaifin ka kana gani yahanani magana yace nabashi DAMAR sa amatsayin sana ma mahaifinka kaga dolo nabashi damar ko yanzu haka ma maganan daurin aure yake agobe karfe 8 nasafe Nabil tayi yayi yafada jikin Malam yanawani irin fitar da nunfashi saida Malam ya tsorata yace kaga tashi tashi kashiga ciki kasame ta idan tace kai tafiso akan BilAL sai insan yanda zanyi injuya abin bana son kasake danuwa irinna wancen lokacin kasha wahala kaji.
Nabil yace" tana ina?

"Tana wajen uwarta.
Nabil yameke da sauri zaifita.

Malam yace "ina zuwa kuma?
"Malam wajenta.
Dariya yabawa Malam yace"amma saida safe ko?
Aiko waigen Malam baiyi ba yafice

Mama kam yau ba bacci ita da Fandau fira kawai ake ayi kuka ayi dariya tayi mutukar mamakin yanda Nabil yake kula da Mama suna cikin haka sukaji anata dukan kofan falo da karfi kamar za aballe duk suka sorata itada Fandau saida ta zo kofan Mama tace "waye?
Yace "Mama kibude nine.
Mama tace "lafiya Nabil yace" kibude.
Mama takalli Fandau alaman ta shiga ciki tunkafin ta karasa fudewa ya fado ciki yayi falon yazube agaman mama yana kuka yana mata magiya yagaya mata yanda sukayi da malam
Mama tace"tunda yabaka dama ka shiga tana ciki.
Da sauri yayi hanyar dakin da akace Fandau take
Amma me yana shiga yatsaya jin wani irin dariya Fandau takeyi awaya

Haba my BilAL kasan fa aurenmu na gaggawa ne
Amma nide nafison koda bayan daurin aurene ayi dan events wanda zai nuna munyi auren SO dakuma yanci
Nima na dandani irin abin da yan gatan amare sukeji
dariya ta sake fashewa dashi
tace kamar ya gobe iyanzu muna manne kana nufin daga an daura aure zaka rabani da
Mamata kenan nima zanso ace gobe iyanzu muna manne.........
Wani irin mari taji yasauka afuskan ta

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login