Showing 21001 words to 24000 words out of 42826 words
ranar idi ya fara takata, a fili ya furta" yawa ga dalili dodonsu na gidan
Su dai ba wanda ya fahimci maganarsa, sannan Aisha da Wujdane sun kasa fita a motar, mamaki, tsoro, da komai ya zubun masu, tambaya suke yiwa kansu, wai daman Jamail nan nw gidansu? A irin gidan nan yake rayuwa aman yake zuwa ya zubar da kansa ya dangwali abincin tukunyarsu ya sha labarinsa ba abinda ya dame shi?
Ku fito mana, muryar Jamail yana kallonsu, yaran ma haka suna kallonsu
A hankali ta sako fara kal din kafarta wace bata yi mata kunshi ba, hakama Aisha ta zuro tata da ta sha kunshi masha Allah
Suna fitowa Wujdane ta ja ta yi tsaye da Boy a hannunta taki bin bayansu tana kallon kasa Boy kuwa na ta yi mata magana yana murnar yau ya zo wajen kakaninsa
Daga saman gidan yake tsaye, ya dage labulen kofarsa yana kallon balbalin gidan Alawiya a gefe tana shan jus tana kada ido tanai mai bayani adadin kudin da take bukata dan kaiwa yan gidansu barka da sallah,
A kan idannuwansa suka fito,
Kwarai ya ware idannuwansa yana kallon su, har du suka shige banda yarinya daya da ta tsaya da Boy a hannunta,
Mamaki yake, su waye wa.innan kuma? A ina boy ya sansu boy da kin yarda shine harda yarda da baki haka?
Bai gama tunaninsa ba ya ga Jamail ya dawo ya harde hannunsa daya a kirjinsa yana ta zuba murmushi da alama lalaba ta yake
Gabansa ne ya yanke ya fadi , wani haushin yarinyar ya darsu a zuciyarsa , a fili ya furta" rashin tarbiya ne ko kwadayi ne zai kai budurwa gidan su saurayinta kafin ma a yi masu baiko????????
Alawiya dake zaune ta dago tana kallonsa dan sai ta ji kar ya yo magana, a fili ta furta magana ce????
Kafin ya bata amsa ya juya ya fito dan tabatarwa zarginsa, idan kuwa hakane sai ya sabawa Jamail, daman ba yar gidan mutunci ya je ya dauko ba? Mai yake son mayar da kansa da su kansu ne??????????????????????
Toh fa
[3/27, 9:59 AM] +234 803 957 7698: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄
*14*
WRINTING BY *SAJIDA*
Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai,
*SAJIDARKU CE*
MARUBUCIYAR:
*YAR MAHAUKACIYA*
*DUK KARYAR KADA*
*DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA*
*NEMAN NA KAINA*
................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH....
Wani irin fitowa ta yi da gudu, burinta ta damki yaron nan ta jijiga masa jiki ya gane bashi da wayo ko ta samu sa.ida a cikin zuciyarta
Wani wawan birki ta ja ta tsaya, ta yi saurin sada kanta kasa tana sauke ajiyar zuciya , zuciyarta tamkar ta fashe,
Lukman da ya yi mutuwar tsaye, ya rasa mai zai cewa abokinsa da ya saki baki da hanci yana kallon katuwar budurwa haka na bin yaro da gudu, yaran zamani bata ko jin tsoron ya kaita kasa
Hularsa ya cire Lukman ya shiga fifita zufar da bai san lokacin da ta sabko masa ba,
Dago da kanta ta yi, kallon da abokin Lukman ke jifanta da shi ya tsaye mata a wuya,
Saurin janye rufar nata ta yi ta dago da idonta sosai tana kallonsa irin kallon meye??
Ya salam ya furta yana waiwayen Lukman ya ce" Lukman jibi halaitar Allah
Lukman ya dan kada kai ya ce" eh ita ce Wujdane dina
Dahiru ya dan waigo ya kali Lukman da alamar tambayar wasa kake min?
Lukman ya dan girgiza kai yana kokarin karasawa wajen Wujdane
Dariya ya bushe da ita, ya ce" aman abokina baka da mutunci, kyan ne zai kaika ko mai? Kana gannin yanda yarinyar bata da nutsuwa har zaka wani kwaso ni?
Juyowa Lukman ya yi cike da jin haushin Dahiru, sai dai mai kafin ya yi magana Wujdane ta bude fuskarta da kyau,
Gaba dayansu ta yi masu kallon sama da kasa, yawu ta tatara a bakinta ta yatsina fuska sosai ta karaso kusa da Dahiru kadan ta zabga masa harara wace ya tsorata ainun dan shi ya fara zargin ko aljanna ce, ?
Yawun bakin nan nata ta tofar a fegensa ta wani kada ido ta ja tsaki ,
Kokarin juyawa take sai ta hango Jamail, wanda ya ja ya taka birki yana kallonta da samarinta,
Har cikin ransa yake jin tsanar lukman din nan, wani wawan birki ya ja ya tsaya ya bude glass din motar
A tare suka juya wajensa, wanda hakan ya bashi damar yi masu kallon sama da kasa, ya zabgawa Wujdane harara ya ja motarsa da karfi wanda sai da ya bude su da kura
Da kalo suka bi motar, kowa da abinda yake sakawa a ransa, Wujdane mamaki take wannan sabon salon wulakancin fa?
Kan Uba, ka ga an gwada maka ba sa.ar yinka bace wannan dan haka abokina kawai mu tafi
Juyowa Wujdane ta yi, a yau dai ta godewa Allah, kalolin abinda zai saka ta ciwon kai ta hadu da dama,
Ji take tamkar ta shake wuyan wannan marar ta idon abokin Lukman din, juyawa ta yi ta fada gidansu wanda ta tarar da inna na zaune tana kallon daidai kofar shigowar
Duke yake gaban malan, du ya wani rikice masa yana koro masa bayani
Malan cike da mafificin mamaki da zai iya tsinta a takaitaciyar rayuwarsa a gidan duniya yake kallon Jamail,
Murmushi ya dan saki dan harga Allah sai ya dauka Jamail ya shiga yi masa wasa irin na kakanu
Cike da murmushi Malan ya ce" kai Jamail, ka cika tsokana kai dai,
Dago da kansa ya yi, idannuwansa cike da hawaye ya ce" ba zancen tsokana Malan, ba zancen wasa, dan girman Allah ka karbi bukatata ka cika min burina tun kafin na bar duniya, Malan wannan shine baban burina tun ranar da idannuwana suka sauka a kanta, na sani kana tunanin nayi yarinta ko wani abin? Malan na shiga shekara ta ashirin da biyu, ina da sana.a, a gidan mu ba za.a hana ni ba, ka dubi girman Allah ka yarjewa bukatata
Daidai wannan lokacin kam Malan ya daina murmushin sai tsoron furucin Jamail, cike da nazarinsa ta ce" kana nufin Jamail kana bukatar auren Wujdane? A shekarunka? A wayewar nan ta zamani? Ya za.ai iyayenka su aminta da hakan? Ya kake hasashen faruwar wannan diramar? Lale aure nufi na Allh ne, kuma namiji namiji ne, aman Jamail zamanin ne idan na rinste idona nakan budewa cikin gagawa, domin sam ban hango yin hakan ba, dan Haka ka sakawa ranka nutsuwa ka je ka yi tunani ka ji yarona???
Dago da kansa ya yi, zuwa wannan lokacin ya yarjewa tunkarar koma waye dan kar yana kallon ruwa kwado ya yi masa kafa, Wujdane sai ta zama malakinsa sai dai idan baya nunfashi a doron kasa
Farawa da iyawa Jamail bai tunkari kowa da maganar nan ba sai yayansu, wato Alaidine
Gidansa ya tunkara wanda ya tabata a wannan lokacin yana gida dan kuwa yama ta yi sosai
Yana zuwa ya faka sabuwar daleliyar motarsa da Alaidine ya canza masa
Budewa ya yi ya fito cikin nutsuwa yake salama
Shiru ba.a amsa shi ba hakan ya saka shi shiga kai tsaye , Alawiya ya tarar tana zaune kafa daya kan daya, kalo take a tv da manyan kayanta a jikinta wa.inda tafi jin dadin jikinta da su bayan rigimar da suka gama tafkawa da Alaidine, ta kai masa korafin dan me yake kauracewa shinfidarta sai ya nuna mata cewar dalilin azumi ne ta yi hakuri bayan sallah, sai hakan ya kona mata rai ta yi masa tambayar da ya saka shi korarta daga falonsa domin tambayarsa ta yi ko bashi da lafiya ne? Bayan ta fita ya yi kwafa ya konta yana kallon Boy dake bacinsa hankali konce
Dauke kansa ya yi, domin tunda aka kawota gidan nan ba wani amsa gaisuwarsu take ba, idan an gaisheta bata wani amsawa hakan ya saka ya daina ko a gaban waye zai yi mata salama dai
Ficewa ya yi ya shige bangaren yayansa da salama daga bakin kofa
Alaidine da yake konce yana ta lumshe ido ya mike yana amsawa fuskarsa na kalon kofar shigowar,
Jamail ya shiga ya duka har kasa ya gaishe shi
Amsawa Alaidine ya yi, cike da kaunar autan nasu, shi dai a duniya jinninsa ya hadu da Jamail sosai, kai duka yan uwansa nema, kallonsa yake yana jiran jin bayanninsa domin jamail baya zuwa ba da dalili ba har cikin dakinsa
Kansa ya dukar, sai da ya ganshi gaban yayan nasa kwarjinninsa ya tsirka masa, aman ya ya iya idan bai tarbi wannan rigi.ar ba da alama sai ta fi karfinsa
Dago da kansa ya yi gabansa na dukan casa.in casa.in murya na rawa ya ce" yaya , maganar aure ne na zo da.....
Sai ya yi shiru yana kifta idannuwa
Kallonsa Laidine yake, yana jiran jin karin bayani, gannin bai karasa ba ya ce" maganar aure? Wani aure?
Cike da gargadar murya ya ce" nana....nawa!
Kikifta ido Alaidine yake yana kallonsa, can cikin kwakwaluwarsa kuwa kokowa yake da tunaninsa, shin yau mai ke damunsa haka yake haduwa da abubuwan tsayar da zuciya ne???
Baima san mai zai cewa Jamail ba, shi dai abinda ya sani shine akoy shakuwa tsakaninsa da kanninsa ta mamaki, aman babu zancen tsokanar juna ko wasa da juna, suna wasa tsakaninsa da Anwar aman da shi babu wannan tsakaninsu
Ajiyar zuciya ya sauke, gannin yanda Jamail du ya rikice ya takura, a hankali ya ce" Aure zaka yi?
Jamail ya sada kansa kasa, yama rasa mai zai bayar amsa,
Mikewa ya yi a hankali ya ce" yaya ba komai
Niyarsa ya fice a dakin tun kafin ya rasa nutsuwarsa,
Alaidine ya ce" dawo ka zauna
Dawowa jamail ya yi, ya zauna yana kallon kasa,
Alaidine ya ce" bazan hanaka yin aure ba Jamail, tabas na doraka kan kasuwanci bana shayin zaka kasa iya rike gidsnka, ba zanyi shaidar hankalinka ba, sai dai ina da tambaya , mainene makasudin ingiza tunaninka a wannan lokacin da baka cika shekara 22 ba a duniya har mararin yin aure ya darsu a zuciyarka??
Wani banbarakwai ya ji tambayar, sho dai bai san takamaiman amsan ba, baban abinda ya sani shine yana son Wujdane tun ranar da ya dora idannuwansa a saman fuskarta kuma baya bukatar ko da wasa ta kubuce masa, shi ya saka shi kokarin yiwa tufkar hanci
Sun dauki mintuna a haka, shi bai ce ga dalili ba, shi kuma bai sake wata tambayar ba,
Yar gidan waye???
Dago da kansa ya yi jin wata tambayar yayan nasa,
A hankali ya furta" yar gidan Malan liman ce mai bayar da karatu a masalacin gida sunnanta *Wujdane*
Alaidine ya dan daga kansa ya ce" kana iya tafiya, zan waiwayeka insha Allah
Mikewa Jamail ya yi jar kamar ya kife dan sauri ya kama hanyar fita sai sauri yake,
Bayan fitarsa Alaidine ya jinginar da bayansa jikin gadon, a hankali ya furta" ba zan hanaka aure ba, may be halitar du guda ce, kar a je tarihi ya maimaita kansa
Kiraye kirayen sallah ya saka shi mikewa inda ya fito ya nufi masalaci dan ya sha ruwa sannan yana da bukatar gannin wannan malan, domin yan gidansu du sun karbe shi yana son karantarsa.............
[3/27, 9:59 AM] +234 803 957 7698: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄
*16*
WRINTING BY *SAJIDA*
Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai,
*SAJIDARKU CE*
MARUBUCIYAR:
*YAR MAHAUKACIYA*
*DUK KARYAR KADA*
*DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA*
*NEMAN NA KAINA*
................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH....
Salama ta yi ciki ciki, wanda ta samu Aisha zaune da yaran nan na anwar sun zagaye ta sai labari suke bata, itama ta sake da su sosai
A hankali ta karasa kusan Aishar ta zauna, ta sada kanta kasa a lokacin ta yi shiru tana tunani
Dakin kanshi ne yake fitarwa na turaran wuta irin dan maidugurin nan, ya garwaye da sanyin ac sai yake fitar da sanyi mai dadi, Mom kennan ba dai kulawa da tsaftar gidanta ba
A hankali take saukowa, bayan ta gama shan dargu da Alaidine ya tokare daga sama ya harde hannayensa yana kallon ikon Allah Boy yaki ya saki jikin wannan munafukar domin kanta a kasa shi jar yanzu bai ga kalar fuskarta ba hakan ya saka shi amincewa cewa ba mutuniyar kirki bace
Mikewa suka yi gaba dayansu daga saman kujerar bayan mom ta karaso ta yi masu salama
A tare kamar sun hada baki suka koma saman capet din domin Mom ta hau kujerar
Aisha ce ta fara gaishe da mom, wace ke amsawa cike da fara.a malale a fuskarta
A hankali Wujdane ta dago da kanta muryarta can kasa kamar yanda ta saba idannuwanta suna dan kallon Mom ta ce" Barka da sallah mama, Allah ya maimaita mana
Mom ta amsa tana kallon Wujdane, masha Allah take maimaitawa a kasan zuciyarta tana fadin Allah ya raya
Wani irin ja da baya Alaidine ya yi, sanadiyar bugawar da zuciyarsa ta yi, a hankali ya laluba ya fada dakin dake kusa da shi sai dai kash, ashe dakin Khadija ne
Murmushi Khadija dake konce saman bed dinta ta yi tana kallon yannayinsa, a hankali ta taso gannin zai fita ta taho kusa da shi ta dafe kofar fitar tana kallonsa
Idannuwansa ya lumshe, har ya samu ya saisaita nutsuwarsa, kallonsa ya dawo wajen Khadija wada habanta ya yanke ya fadi sanadiyar kwayar idannuwansa da ta ga sun canza launi
Bude min na fita
Ya fada fuskarsa a hade
Gwuiwowinta ta kai kasa, bata bar jikin kofar ba ta fashe da kuka, murya a matukar raunane ta ce" danme ba zaka mayar da ni dakina ba? Na tuba Aban Huzaifa, dukan abinda na yi maka yarinta ce da zuga, yanzun na gane ko kai wanene a cikin rayuwana, ina neman dan girman Allah ka ji kaina ya yafe min, ka mayar da ni dakina
Kallonta yake, a can kasan zuciyarsa yana hangen nadamarta kamar da gaske, dan dukowa ya yi ya rage murya ya ce" kina nufin koda da halin mayar da ke din zaki iya zama da shege?
Khadija ta kara sada kanta ta ce" ka daina tunawa, na yi kuskure, na nemi gafararka, ka manta ka mayar da ni dakina ko na samu sukuni a zuciyata
Alaidine ya mike ya kama kofar ya juyo ya ce" a saki uku ana komen aure kennan? Bayan nan ni bazan iya auren mai uba ba, dan haka ummu Huzaifa ki samu miji ki yi aure kin ji??
Dago da kanta ta yi, muryarta cike da rauni ta ce" dan kawai baka son mayar da ni zaka ce ka yi min saki uku bayan biyu ka yi min? Shin kai ba musulmi bane da ba zaka manta rayuwar da muka yi ka mayar da ni ka ga a yada zan zauna? A yanzu da na gama sannin manyan sirikanka na rayuwa nake amana da su nake jin haushin yarintar da na zuba har ka sake ni,
Zuwa wannan lokacin ta kusa samun galaba a kansa, juyo da kansa ya yi, q hankali ya furta" da ba dan rantsuwar da na gindaya ba da na waiwayeki, ba maganar rike ki ne ba aa, maganar a lokacin raina a bace na yi muguwar rantsuwa harda haramta ki a rayuwana, Khadija ke ce ta farko da na rayu da ita a matsayin mace sannan ke kika bani kyautar da har yanzu nake jina cikeken mutun, ba zan yarda ki wulakanta ba, ni da kaina zan nema maki yafiyar su abanki, sannan daga millon goma abinda ya yi sama bukatarki zan biya maki, ki samu miji malamuncinki ki yi aure kin ji?
Tana kallonsa tana ji tana ganni ya fice a dakin hakan ya saka ta zubewa a nan ta saki kukan nadama( magana zanar bunu ce)
Yana saukowa ya tarar da Mom ita kadai zaune,
Karasowa ya yi a hankali ya zauna bayan ya yi mata sannu da gida
Amsawa ta yi cike da kulawa, tana murmushi ta ce" idan baka zo ba nakan shiga wani yannayi na rashin ganninka a kusa da mu, idan ka zo kana zo mana da tsare tsare masu wuyar gani, yanzu son dan Allah kawai sai ka kora yara daki suna shagalinsu? Ai sallah ce sai ka barsu su dan huta kadan ko?
Kallonta ya yi, bai ce komai ba ya dan kawar da kansa a kasan zuciyarsa yana ayana ai bazai yiwu dan sallahce su kunna kida a cikin gida haka ba dan basu da tarbiya
Ta san ba zai tanka ba, domin ya ki jinnin sha.annin kida da abubuwan da suka shafi jakan, kawar da kanta ta yi itama ta ci gaba da kallon tvn
Mom ina Jamail ne?
Dago da kanta ta yi tana kallonsa, ita bata ga abin takurawa kai a lamarin Jamail, ita kwarai yaran sun shiga ranta ba yanda bata yi ba dan su karbi abin barka da sallah fir suka ki har rigai rigai suke wajen fita, sun nuna idan suka je gida da shi innarsu ba zata saurara masu ba, yaran sun shiga ranta daman fil azal take sha.awar tara yara tumba mace ba, aman cikin ikon Allah ukun ne su ne rayuwarta
Murmushi ta yi ta ce" ai ya tafi ya mayar da su Wujdane
Dago da kansa ya yi da alamar bacin rai bayane karara a fiskarsa ya ce" yanzu fisabililahi Mom sai kace wasu jininsa na jiki? Ya zai fito yawo da yara haka cikin gari, nawa yake Jamail din da zai fitino da wannan rayuwar, meye abin sha.awa a bibiyar yara haka? Mom kuma har ki yarda da hakan dan Allah? Ai wannan da gani basu da tarbiya idan ba haka ba ta ya zasu shiga motar namiji haka ba wani yayansu ba ba wani muharaminsu ba su bi shi zikau zikau su shiga gari da shi? Yanzu fisabililahi haka ake rayuwa? Kuma sai ya dauki boy yana cakula shi a shirmensa ko?
Sannu mai da, maganar Mom ra katseshi wace ta zubawa sarautar Allah ido yana bambamin balaki dan kawai Jamail ya kawo yaran da a kulun ta Allah idan dai zaka zauna da shi maganar gidansu ce tarbiyar gidansu, mahaifinsu mahaifiyarsu, komai, yarinyar da yake muradin aure a rayuwa, yarinyar da a yanzu ita kanta zata yiwa iyalanta sha.awar ajiyeta a matsayin mata, bai ko zauna da mutun ba bai san halinsu ba aman ya dage yana zuba masifa a kan hakan
Hade fuska ya yi tam, ransa ya gama baci, gannin zaman nasu da mahaifiyarsa ba zai