Showing 12001 words to 15000 words out of 42826 words

Chapter 5 - BANI DA ZABI COMPLETE HAUSA NOVEL

23 Aug 2025

633

wanda ainayin sunnansa shine *ALAIDINE* suka lakaba mai sultan ba dan komai ba sai dan yannayin rayuwarsa ta sadaukai ce ta sarakai, sai Anwar sai kanninsu Jamail,

Haka ya fito da sauri ya nufo wajensu wanda polisawan na ganninsa du suka kame suna sara masa



Aikin da kuka je yi kennan? Wa.innan fa? Su waye su???
Cikin zazakar muryarsa mai sanyi yake jero tambayoyin nan aman fuskarsa a hade take tamau


Baban cikinsu ne ya mike ya shiga fada masa ga yanda abin ya kasance ,


Juyowa yayi yana kallon mutanen da aka ce suna fada harda dambe, wai mata Balki sai tsuru tsuru take da idannu Wujdane kuwa ta sada kanta kasa ba,zaka ce ga kamaninta ba domin hijabinta ua rufe har kafafuwanta


Cike da takaici ya dafe kansa a ransa yana fadin kamar ta Allah da shigar nan take fada a titi, sannan ya tambayi kansa anya wannan aikin ba ajalinsa ya sako kansa a ciki ba??????

Cike da jin haushi ya bada umarnin a saki wa.inda fadan bai shafe su ba a bar su Wujdane kadai har iyayensu su zo,


Yana gama fada ya juya ya dauko wayarda da ky din motarsa rang rover ya fice dan zuwa gidan dan uwansa ya ga ya jikinsa











To fah Wujdane a cel🤦🏻‍♀
[3/27, 9:59 AM] ‪+234 803 957 7698‬: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄





*08*


WRINTING BY *SAJIDA*



Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai,

*SAJIDARKU CE*


MARUBUCIYAR:

*YAR MAHAUKACIYA*

*DUK KARYAR KADA*

*DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA*

*NEMAN NA KAINA*

................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH....







Konci tashi ikon Allah, yau har ya kama sati na hudu da Wujdane ta dage kan hanyar makaranta, ba wai ta daina fita bane aa kunyar Malan ke sakawa ko kadan ta kasa daina zuwa makarantar, sannan kwazo irin na Wujdane ko nace baiwa ba abinda bata fahimta, sosai take gane karatun malansu aman a yi tambayar duniyar nan ba zata daga hannunta ba, haka kuma har yau bata da kawa a ajin bata shiga sabgar kowa


Yau Malan yusuf ya tashi da rashin mutuncin, tunda ya shigo yake kora koda takalminka ba na makarantar bane zai yi waje da kai ne sannan ya baka punishment,

Dalubai du sun nutsu, kowa ya kama kansa ba mai garajen wani yunkurin bale har kilu ta jawo masa bam


Cike da jin haushin Wujdane yanda take yi masa wani kalo da ya fasara a zuciyarsa kallon raini ne ya rubuta wani excercise na math a blackboard,

Kafin ya tayar da wanda zai je ya yi masa excercise din sai da ya tambaya wa zai je kamar yanda ya tsamata va wanda ya daga hannu domin a gaskiya akoy yar wahala


Kanta na kallon kasa kamar yanda ta saba, ba wanda zai ji muryarta sai ma ya rantse shi bai taba ji ba ba shi kadai ba du jama.ar ajin,


Ya jima yana kallon wajen wanda ya saka du daliban shan jinnin jikinsu domin da gani sun san zai zabo mutun ne ya tura


Kamar daga sama ta ji yana fadin" *WUJDANE MALAN LAMINU*

A firgice ta dago da kanta , ta sauke idannuwanta a fuskarsa


Cikin daure fuska ya ce" ki taso ki yi mana excercise din nan sannan kina yi kina kwatanta mana yanda aka yi kika yi hakan, idan ba haka ba zaki fuskanci tsatsauran hukunci na hutun sati guda


A cikin ranta take ayana" ka koreni ma idan kana so, sai wani gefe na zuciyarta ya tunatar da ita Malan fa ba zai ji dadi ba


Cike da jin haushi ta mike ta nufo shi, ta karba ta dan dakata ta karanta ,

Cike da kwarewa ta dora equation din ta shiga gabatar masu da harshen turanci,


Ba kalacin daliban dake yi mata kallon may be kwakwaluwar ba komai sai majina ba, harta malan Yusuf da ya kawo karan tsana ya dora mata a tunaninsa bata da kwakwaluwar zama a nan hanya ce aka yi mata kansa ya cika da mamaki, ta iya turanci a bakinta, to yaushe ta koya?
Ni kaina na cika da mamakin yaushe ta koya? Larabci dai ba mamaki idan tana yinsa tamkar balaraba har wani khal khal take da harshe sai ga abin mamaki wujdane da turanci sosai a bakinta


Har ta gama ta dawo kujerarta da ido suka rakata har ta zauna, ba mai bakin magana du ta kashe shi


Malan Yusuf ya shiga tafi a hankali, wanda wani irin kunyarta ya rufe shi, a fili ya shiga yi masu kwatance da ita a can kasan zuciyarsa ya shiga yaba mata , yaba kwazonta, nutsuwarta, tsarinta

Haka ya gama ya fice aka bi shi da kayansa har wajen motarsa yar madaidaiciya ya shige ya tafi abinsa



Zaune take a wajen pampo, tana kallon yanda wasu yan mata ke kalkalce kalkalcen kafafuwansu dan tafiya gida, sai dan waigawa take wajen ajin su Aisha aman har zuwa lokacin ba.a sake su ba

Tsaki ta ja ya fi a kirga ta dan waiga ta waigo


Ke wai bakya cire nikaf ne? Ya akayi kulun da nikaf?? Wata yar budurwa kyakyawa ke fadin hakan tana kokarin zama gefen Wujdane


Dago da kanta ta yi ta kali gefen budurwa, dan tura bakinta ta yi ta matsa kadan tana kawar da kanta gefe

Murmushi budurwar ta yi ta ce" ni kuwa ina son na yi kawance da ke, domin na yaba da nutsuwarki plz ki yi hakuri idan na takura maki


Kuma juyowa ta yi tana kallonta, still dai bata yi magana ba,

Ta yi murmushi ta ce"ni sunana Rumaisa, ina gefen pharmacy ne, na jima ina ganinki kin shiga ajin can, kina san zama nurse ne???


Kai wujdane ta dan girgiza ta kuma kallon kofar ajin su Aisha, bata cewa Rumaisa ufan ba


Rumaisa ta buda baki dan ta kuma yin magana Wujdane ta mike ta kakabe hijab dinta ta juya ta nufi kofa dan tafiyarta gida domin yau bama zata jirayi Aishar ba,

Tana tafe tana mitar ta rasa jarabar wasu yan matan



Tana zuwa kofar gidansu ta yi kicibus da Lukman, ya sha yadinsa fari kal ya caje gashin kansa ya saka agogonsa baki da bakin takalminsa, yana saman babur dinsa yana dan kada kafa har zuwa lokacin ya rasa yaron da zai taimaka masa ya shiga yayi masa magana da Wujdane



Kokarin rabawa ta gefensa take ta shige gida ya yi tsalen albarka ya tsaya a gabanta yana zuba mata murmushi


A fili ya ce" Alhamdulilah, yau dai Allah ya yarje min ganinki,


Bata cire nikaf din ba, kanta na kallon gefe tana fadin wannan akoy natace mai kuma ya zo yi gidan nan


Wannan zuwana na biyar ne yan mata, na samu ribar jin sunnanki ma abin ya gagara na rasa ke ce *AISHAR KO WUJDANE MAMA?*


dago da kanta ta yi tana mamakin Wujdane mama, wani dan murmushi ya subuce mata, wato yaran anguwar nan nema suke su lakaba mata sunnan da zai bi ta ko???


Dan Allah ki saurareni, shi mutun daraja gare shi, Dan Allah na yarda da ja min aji ina neman alfarmar na san sunnan kawai a hankali za.a amince da soyayata


Mamaki ne ya cika mata zuciya, a ranar da ya ganta ma bai nuna tsoro ba, shi ne harda maganar soyaya? Haka kawai ta ji ya birge ta ko ba komai ya nuna mata kauna a fili


Dan gefensa ta bi ta ratsa shi ya juyo yana kallonta ya harde hannayensa fuskarsa kalar tausayi


Murmushi ta kuma saki wanda baya gani shi domin da nikaf, kasa kasa ta ce" *WUJDANE MAMA*


Wuf ta shige cikin gidan ita kadai sai murmushi take dokawa ta cire nikaf din


Inna dake bakin murhu tana iza ice ta dago cike da mamaki tana kallonta, murmushi na matukar kawata fuskar yarta, itama sai ji ta yi nata murmushin na fitowa domin fuskar mahaifinta sak ta fito a fuskar yar tata


Karasowa ta yi ta duka har kasa tana gaishe da innar


Cike da kulawa inna ta ce" ina Maman kuwa? ( Aisha )


Bayanta ta juya ta juyo ta ce" a can na barota ni gajiya na yi inna


Inna ta ci gaba da kallonta , sam Wujdane bata iya karya ba idan dai zaka tambayeta toh zata fada ne kai tsaye, ta yi imanin wannan murmushin kuwa da dalilinsa

Kallonta ta yi ta ce" mai ya saka ki nishadi haka,????


Wujdane ta dago da kanta cike da wani abu da take ji kadan kadan na taso mata , ta buda baki zata yi magana kenan sai ga muryar Jamail yna kwala salama


Kanta ta dafe irin na takurar nan ta mike ta yi dakinsu inda inna ke amsawa jamail salamarsa cike da murnar ganninsa, domin Jamail yayi tuwo ya yi tsaki har tsakar gida yake shigowa shi kawai gidansu ne


Tabarma inna ke shinfida masa tana amsa gaisuwarsa,


Dakin su wujdane ta juya ta kwala mata kira tana fadin ki fito ki ba dan uwanki ruwa mana Wujdane!
[3/27, 9:59 AM] ‪+234 803 957 7698‬: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄





*10*


WRINTING BY *SAJIDA*



Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai,

*SAJIDARKU CE*


MARUBUCIYAR:

*YAR MAHAUKACIYA*

*DUK KARYAR KADA*

*DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA*

*NEMAN NA KAINA*

................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH....




Haka ya daukosu ya nufi gidansa da ya gina boyaye wanda ko mahaifiyarsa bata san da shi ba, ya kai su Marwa sannan ya nemo wata tsohuwa ya hada su


Komawa ya yi wa mahaifansa da mahaifan Marwar, aman cikin ikon Allah mahaifansa ko kalo bai ishe su ba, daga karshe mahaifinsa yayi rantsuwar idan ya kuma gannin kafarsa a gidansa toh lale zai tsine masa tunda ya nuna mace ta fi su, cike da tashin hankali ya dauki carte sin banki da mahifinsa ya bara masa wada keda kudadensa a ciki na kasewa ya karbe duka sauran abinda ya bashi kan sharadin in dai ba watsar da Marwa zai yi ba ya je ya bara mata shi


Cike da tashin hankali ya nufi gidan su Marwar, a nan ma dai zancen daya ne, ta yar da dan ta dawo gidan ida bata yarda ba ya yafe ta, mahaifiyarta ce ta biyo bayansa a boye ta bashi yan zannuwa tana kuka ta fada masa dan Allah ya kula da Marwa, karta yada kautar da Allah ya yi mata, ba laifinsa bane, kadara ce sai a karbe ta, insha Allah idan mahaifinta ya huce zata dawo


Haka ya dawo gidan ya zauna da Marwa ya sanar mata komai,
Ta jima tana kuka, ta jima tana astagafari tana rokan Allah ya yafe mata, ta rungumi yaronta inda Elhaj kadri a dakin kofa yake zaune idan ya shiga gidan sai dai dan ya ga lafiyarsu ne ya yiwa yaronsa wasa sannan ya fice,

Haka har ta yaye Alaidine cikin ikon Allah a masalaci ya nemi alfarma wajen liman ya fada masa duka yanda ake ciki

Liman din da kansa ya je wajen iyayensu dan gannin ko za.a sasanta, aman suna nan kan bakansu, sai dai shima mahaifiyarsa ta sauko aman tana mugun tsoron mijin nata
Du yada liman ya so ya kwatantawa iyayensu a sasanta basu saurare shi ba, kowane ya hau dokin zuciya duda shima mahaifin Marwar ya dan sauko aman gannin mahaifin Kadri bai sauko ba ya saka shima ya botsare

Liman ya wakilce su bayan salar juma.a aka daura masu aure, inda suka ci gaba da rainon Yarensu mai wani irn hali tun yana yaro,
Alaidine baya son hayaniya, ko dan ya rayu daga shi sai mahaifiyarsa da mahaifinsa ne , Alaidine bashi da tankiya, gumgum da shi baya shiga sabgar kowa ko da wasa

Mahaifinsa ya ci gaba da juya dukiyarsa wanda Allah ya saka mata albarka ta yi ta habaka,
Makarantar biya yake , yana da shekara takwas mahaifiyarsa ta sake haihuwa aka sakawa yaron sunna Anwar

Alaidine girmansa abin al.ajabi ne, bai jawowa iyayensa magana ko sau daya, kwazo gare shi a makaranta wanda hankalinsa ya fi karkata a kasuwanci,

Yana da shekara 18 aka yi masa gori a anguwa, wata mata haka kawai ya zo wucewa ta ce" wannan ai shine shegen gidan cen, sai dagin kai tamkar wani tsarkakake

Wannan magana ta saka su a tashin hankali domin a ranar ya san ko shi wanene , ya yi kuka har ya gode Allah, inda mahaifinsa ya dauke su da mahaifiyarsa da dan kanninsa msi shekara goma da tsohon cikinta suka koma sabon gidansa nesa da anguwar da yan uwansu da kowa suke zaune suna rayuwarsu

Alaidine ya saka wannan magana a ransa, hakan ya saka yake kauracewa mutanne domin yanai masu kallon wa.inda basu da uzuri shima sai ya daina yi masu uzuri

Tun yana da shekara goma sha tara ya nemi jari wajen mahaifinsa

Cike da farin ciki Elhaj Kadri ya bashi ya ja sana.a, wada suke mamakin husa.a ta yanda yake kirkirar abubuwa kala kala

Nan da nan sunnansa ya fito a yaro da kudi, farin jinninsa ya daukaka, lungu da sako maganarsa ce ake ana radin yaro da kudi yaro da kudi
Gashi ya dauko kyau da hutu, nan da nan ya rikide ya kara zama wani hamshaki mai aji

Sosai mata ke wawarsa, abinda ke dagawa mahaifiyarsa hankali kennan, domin har gida wasun ke zuwa nemansa

Du da irin taurin halin Alaidine akiy sadaka, zaka, yana taimakawa marayu, ya gina masalaci tankameme a unguwar da ya gina gidansa wanda yan anguwar kansu ke kiran gidan da ko a turai, domin babu ne kawai babu


Wani lokaci mahaifiyarsa ta saka shi gaba tana ta mita harda kuka kan ya fitar da mace, shi ko budurwar bashi da ita, mahaifinsa dake saukowa daga sama yana sauraron su, shi kansa ya lura da yannayin halitar Alaidine, ya dace ace da mace a kusan sa zuwa wannan lokacin aman shi sam baya ra.ayin yin aure bisa dalilinsa nasa na kansa,


Cike da fushi ya dago da kansa yana kallon mamansa ya ce" Mom, kina tsoron tarihi ya maimaita kansa a kaina ne? Ki yi hakuri da yardar Allah hakan ba zata faru ba


Cikin tsananin bacin rai da tir da halayarsa na fadin gaskiya kwadokwado baya shayi koma wanene ta wanka masa mari ta kara masa, muryarta na rawa ta nuna shi da yatsa ta ce" dan ka ga ana gudun zuciyarka dan kar ranka ya bace ka yi rashin lafiya ba wai tsoronka bane ya saka ko ka fi karfin mu bane, haihuwarka aka yi Alaidine kuma dole ka yi biyaya, idan har baka dauki kadarar rayuwarka ba kai ta gano aman baka isa ka jefe mu da wata kalma ba bayan kadara ce *Bamu da zabi* dole muka dauka, kaima haka zaka dauka


Tana gama fada ta haura sama da gudu mijinta ya tare ta yayi ta rarashinta


Bayan wannan da kwanaki mahaifinsa ya shaida masa an bashi auren yar gidan amininsa wanda ya san komai kuma ya yi amana da hada auren

Bayan sati biyu aka daura masa aure da khadija

Shi kansa bai san haka yake da muradin mace ba sai a kan Khadija, khadija ta kawo masa mutuncinta sannan tana gannin girmansa

Wai dai wani mugun abin , mahaifiyarta ta ji labarin ko wanene alaidine, nan fa ta kama hure mata kune har Khadija ta fara fito da halayen da bai santa da su ba

Daman ba aikin fari take ba bale na baki, domin da ma.aikata birjik a gidan masu kula da komai, sai ya kasance shi Khadija ta fara kauracewa a shinfida,
Da ta lura da ciki ya shigeta sai tashin hankali na kulun kala daban, tayi ta kuka idan ya tambayi ba.asi sai ta furta" ni dai an cuce ni an lalata min rayuwa


Abu tamkar wasa cikinta ya girma ta haife ta samu yaro namiji aka saka masa" *Huzaifa* suke kiransa da boy

Tunda ta haihu sai sabon kulafuci, ita ce wannan ita ce wancen, Alaidine bai taba kai kashenta ko kararta ba, kudi kuwa tamkar wuta haka take kashe su, shi kansa baya kashe kudin da take kashewa, boy kuwa tamkar ba ita ce ta haife shi ba, ta banzatar da shi bata damu da shi ba

Wata safiyar Asabar, Mahaifinta ya zo nemansa har gida dan ya kasa samunsa a waya kan harkar business, ya tarar da Khadija sai sababi take Alaidine kuwa yana sama yana hangenta ya harde hannu a kirjinsa yana tir da halayenta a kasan zuciyarsa harma yana mamakin kansa da yake iya kawar da kai yanai mata uzuri

Cike da masifa ta wsnkawa Huzaifa mari , wanda ya ji tamkar ta watsa masa wuta a fuska, cikin azama yake saukowa inda mahaifinta ya labe yana kallon ikon Allah


Yana saukowa ya dauki yaronsa idannuwansa har sun canza launi, ya nunota da yatsa ya ce" rashin mituncin naki har ya kai ki tsalake banzatar da aurenki da kike ki dawo dukan min yaro? Why Khadija? Mai yasa bakya gannin irin yanda nake kokarin gannin na fita a hakin ki na kula da amanar mahaifina? Idan bakya iya rayuwa ne da ni ai gwara ki fada da ki cutar da yarona, idan ni ne ki je ki yi bani da damuwa aman harda dan da kika haifa khadija?

Cike da bacin rai ta ce" eh man, dan me ba zan dake shi ba? Shi dan *Shege* ?


Tamkar an dauke wuta haka abin nan ya dirar masa, wanda ya yi sanadiyar kara nutsawarsa a rayuwar duhu,
Hannu ya daga ya wanka mata lafiyayen marin da ta kai kasa bakinta ya fashe take gefen kuncinta ya sundume

Hannunsa na rawa ya nunata ya ce" *na sake ki saki biyu* idan kin samu miji zaki iya aure domin baki da idata


A lokacin mahaifinta ya bayana a fallon yanda ya mayar da ita tamkar ganga, yayi alkawari ba dai a gidansa ba

Cike da tashin hankali ta nufi gidan su Alaidine din ta fadawa mahaifiyarsa da kanta komai,

Duda ta ji haushi hakan, aman sai ta ga idan ta kiri khadija ta yi butulci , domin itama da aka kore ta mijinta ya rungumeta, hakan ya saka ta bata daki take zaune tamkar gidansu

A haka aka yiwa Anwar aure da matarsa Bahija, yarinya mai daraja mai daraja mutane,

Tun daga wannan lokacin sai Alaidine ya dawo sabo, yakan zubawa mace kudi domin ya gama fasara su a kudinsa suke so, ya aura idan kun jima ku yi wata biyu ya salame ki domin yakan gwada mace cikin

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login