Showing 27001 words to 30000 words out of 42826 words
aura? Yayi yaya da ita? Shi ai ba mahaukaci bane, da gani a yanda ya gama shagalinsa da ita yanzu zai zo masu da wani bayani, shi dai komai za.ayi ba zai yarda Aba ya canza abinda yayi niya ba, wato ya aurawa Jamail Wujdane haka kawai a bata masu zuri.a? Haka kawai? Ai yau za.a yita ne a wajen nan
Lukman na kebancewa da Aba ya shiga koro masa bayani kamar haka" yau kwana biyu da mahaifina ya dauran aure da yar uwata, bisa sharadin sai an auran ita za.a barni na auri Wujddane, du ban fadawa su Malan ba domin ona son Wujdane bana son abinda zai rabani da ita, tun jiya nake gannin abubuwan da basu dace ba, inda mahaifiyata ta bukaci na jawo kudin sadakin Wujdane din su adana,
Kawai ina zaune nake jiyo magangannunsu suna labarin ai lefe ma da na tara na wujdane aka ce min an kawo ashe ba ita aka kawowa ba gidan su yarinyar da aka aura min suka kai, karshe ma kudin sadakin na Wujdane da na bayar ajiya mahaifiyata ta sayo keken dinki da kayan dinki wai zata shiga koyon dinki da na auro mata yar iska
Hakan ya bakantan rai na ritsasu cike da bacin rai na saki yarinyar saki daya,
Wannan ya tunzura zuciyar mahaifana suka yi rantsuwa da idan dai na zabi auren Wujdane ba ni ba su duniya da kiyama
Hakan ya tayar min da hankali, ya fitini tunanina, ya fitar da ni a nutsuwata, ba inda ban je ba dan a zo a baiwa su mahaifana hakuri aman abin ya ci tura shine tun jiya zuwa yau na zama tamkar mahaukaci yawo kawai nake, ni yanzu ga sadakina na samo a aura min ita kawai mu yi tafiyarmu shikenan
Sauraronsa Aba yake cike da tausayi, sai kawai yake gannin kamar rayuwarsa ke maimaituwa a nan,
Kamo kafadunsa ya yi ya ce" karka yarda, koda wasa karka kuskura ka ki bin abinda suka fada, tunda har kai kadarar taka ta fito a haka, ka rungumeta kawai Lukman, ka sani a duniya babu kuskuren da zaka tafka sama da take maganarsu, Wujdane dai mace ce wada take gaban iyayenta, ysu ba zata kaunaci namiji ya tsameta ya kaita a rayuwar wahala ta gaban abada, shin baka tunanin abinda zaka cewa Allah? Da ace mahaifinka ya aminta ni zan dauki nauyin aura maka Wujdane, aman ina hakinsu dake kanka? Aljanarka tana karkafin digadigensu, basu kore ka ba, zabinka ne bai yi masu ba, ka nutsu ka farka giyar soyaya ke dibanka, babu innuwar da ta kai ta iyayenka lumshi da dadi ko a nan duniya bale a kiyama, lale auren wace ake so yana da dadi aman kuma zaman lafiya da iyayen mu ya fi dadi dadi, Lukman idan ka samu nutsuwa ga numberna ka nemi gidanna mu tatauna, ni ina baka shawara ne wai ba a matsayin dan na girme maka ba aa, sai a matsayin wanda ya san me hakan ke nufi, dan haka idan muka zauna zan baka tarihin rayuwana
Wani irin sanyi jikin lukman ya yi, ya dubi Aba kimar Aba kadai zata haneka karyata lafuzansa hakan ya saka shi fadin" Malan fa? Kenan na bashi kunya? Wujdane fa? A me zata dauke ni na cuce ta ? Elhaj ka san hausa yanzu abinnan sai ya yi ta bin Wujdane har ka ga ta rasa miji a sanadina?
Aba ya yi murmushi ya dafa kafadar Lukman ya ce" *ALLAH ZAI HANA*
Yana gama fadar haka da hanzarinsa ya dawo ya bukaci a nutsu za.a daura aure
Hannunsa ya mikwa Alaidine ya miko masa kudin sadakin Jamail
Aba ya juyo ya raba kudin hannunsa gida biyu wato dubu hamsin hamsin, ya mikawa malan isyaku ya irga ya ce dubu hamsin, ya sake miko dayan ya irga ya ce" wato dubu dari kudin sadakin....
ABA ne ya katse shi da fadin " *AA, DUBU HAMSIN BIYU, WATO KUDIN SADAKIN YARINYA BIYU, YA JUYA WAJEN MALAN YA CE" MALAN INA NEMAWA YARONA........*
π
[3/27, 10:00 AM] βͺ+234 803 957 7698β¬: π¦π¦ *BANI DA ZABI*π¦π¦
*17*
WRINTING BY *SAJIDA*
Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai,
*SAJIDARKU CE*
MARUBUCIYAR:
*YAR MAHAUKACIYA*
*DUK KARYAR KADA*
*DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA*
*NEMAN NA KAINA*
................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH....
Kallo suke yi masa na rashin fahimtar inda zancensa ya nufa,
Zuciyarsa yake dana, tunda ya fara ai sai ya gama, a hankali ya dan matsa hularsa baya wanda ya baiwa sauran gashin gaban goshinsa damar fitowa,
Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon Wujdane a hankali ya furta" dole na kirayi hakan da yaki, yaki ne na zuciyar mutun guda, ina son shiga yakin da na san zan jigata aman kila wa kala zan cima burina,,
Aisha kam daidai wannan lokacin zuciyarta tamkar ta balo ta bar kirjinta, kallonsa take cike da faduwar gaba inda wujdane bata ma san inda maganarsa ta nufa ba
Kai ta dan dafe ta ce" wai yau abinda ka tashi da shi kennan Jamail? Ka bude mana mota mu fita ka ga an fara lekowa daga bango da kofa ana lekomu na san an fara cicira mu ne, ni shi ya sa bana son matse maka guri, yanzu a anguwa za.a dauka wani abin ne har a zo anai maka tambayar rainin hankali,
*Wujdane i love you*
Katsewar mitar Wujdane kennan, wanda yayi daidai da wani irin bugawa da zuciyar Aisha ta yi, haka zuciyar Jamail ta shiga luguden duka ba kakautawa
Shatata Wujdane ta yi tana kallon Jamail, ita bata ma san me kunuwanta suka ji takamaimai ba, hakan ya saka ta sakin wani malalacin murmushi tana kallonsa ta ce" ban ji mai ka fada ba?
Jamail ya sauke ajiyar zuciya ya dan waiga gefen Aisha ko zata taimake shi, aman ina kanta a sade a kasa wanda ba zaka fahimci halin da take ciki ba,
Juyowa ya yi yayi kundubala da tsoron dake dukan zuciyarsa ya ce" cewa na yi ina son ki Wujdane ko laifi ne??
Wujdane ta dan kada idannuwanta irin tambaya da idannun nan, tana kallonsa kafin ta furta" mai kake nufi da maganar nan naka ne?
Jamail ya tsareta da ido, wanda itama cikin idannuwan nasa take kallo, ya ce" shin hausar ce baki fahimta ba Wujdane ko menene???
Wujdane ta dafe kanta da ya dauki sara mata, ta kuma dago da kanta ta ce" yanzu fisabililahi ka rasa wace zaka ce kana so sai ni? Shekara uku kacal fa ka bani a nan gidan duniya, ni kuwa ba bakin uwa ba ba na uba ba zan auri yaro? Ai ni ba zan soma soyaya bama da yaro domin ko lukman hakan ya saka na yi watsi da shi, Look Jamail, ka ga dai ina gannin girman ka, dan haka dan Girman Allah karka soma irin wannan abin ba zai fishemu gaba dayanmu ba, danme zaka yi kokarin kawo min irin wannan wulakancin daidai wannan lokacin? Shin ganni ka yi bani da mai tayawa ko? Jamail idan na yi soyayay da kai ka fadan mai na gane mai? Jamail ni idan ba shekara arba.in da biyar namiji ya yi ba, bana jin zai iya zama da ni a matsayin mata domin sai an samu mutumin da ya fara manlakar hankalin kansa kafin yake gane zama da ni a rayuwa,
Please buden kofa na tafi,
Kallonta yake, cike da mamakinta, yanzu shi take gannin ba zai iya rayuwa da ita ba,? A irin hakurinsa , zai iya ciyar da ita ya yi mata sutura ya biya mata dukan bukatunta na gidan duniya, shin a mai ta dauke shi? Tana nufin ya yi mata kankanta ko me? Aman ai NAMIJI BAYA KADAN , dan me zata fara fasara shi ta haka,
Hannunta ta mika inda ta ga ya dana ya kile motar ta dannan ta bude ta fice abinta ta nufi wajen Mairo da ta tarbota an sha kayan sallah
Kokarin bude motar Aisha take, dan ta fice itama, sai jin muryar Jamail ta yi yana fadin" Aisha ta ina na kasa? Shin menene makusata? Aisha ki taimake ni dan girman Allah ki fada min menene aibuna?
A hankali ta dago da kanta dan bashi amsa, sai dai mai a lokacin da suka yi ido hudu da Aisha wani iri yanda gabansa ya yanke ya fadi har sai da ya katse tunaninsa na sakonni,
A hankali ya bude idannuwansa da ya dan lumshe ya sauke su a fuskarta,
Murmushi Aisha ta sakar masa ta ce" yaya Jamail baka da wani makusa, kawai sai a hankali aunty zata fahimci inda maganarka ta nufa ka ji? Kar ka sakawa kanka damuwa domin Aunty ta jima da irin wannan ra.ayi nata na cewar sai dai ta auri mutun mai shekaru shi ne zai iya rayuwar zaman aure da ita, ka yi hakuri insha Allah zanyi kokarin gannin na karkato maka da hankalinta ka ji?
Cike da sanyin murya ta yi maganarta wanda ya kashe masa jiki, sam bai san dalili ba, a haka yana kallo Aisha ta bude motar ta fito inda ta hango babur din Lukman ya faka yana faman shawo kan Wujdane kan ta yi hakuri ta saurare shi
Ba Wujdane ta dawo gida ba sai da ta saurari Lukman harma suka shirya kan fadan da suka yi , daga nan ma ta bi bayan mairo suka shiga yawonsu a cikin anguwar wace ba ita ta dawo gida ba sai can da dare sosai
Malan ne zaune, a yau km Wujdane ta tabo masa ransa, bayan ya fada masu gaba dayansu su hadu bayan sallar magariba su yi adu.a wace sukan yi du bayan azumi, sannan a ci abinda ya samu, wannan karin harda dan akuya ya sayo da tarin kayan miya wanda sai su kadai ne suka yi adu.ar shekarar sannan suka shiga shirye shiryen yankansu suna ta shagalinsu banda Wujdane dake anguwa yawon fitinar fada
Salama ta yi , wanda sai a lokacin gabanta ya yanke ya mugun faduwa, dalilin hango tarin karan dake ci ya haske tsakar gidan nasu, ga kuma gefe kai da kafafuwa na akuya a aje ga Aisha sai aiki take ita da inna gefe kuwa Hamza ne rike da wayarsa yar nokia yana amsa kira
Kallon da inna ta yi mata ya sage mata gwuiwar nufar su, hakan ya saka ta nufi dakin mahaifinta dan ta bashi hakuri
A hankali ta dakata ta yi salama daga kofa
Kafin Malan ya amsa mata salamarta ta ji dau an fauketa da wani gigitacen mari,
Kafin ta ankara ya shiga balata da kafarsa ransa a matukar bace
Da sauri malan ya fito daga dakinsa ya karaso wajen Abdul fatah dake jibgar Wujdane tamkar an aiko shi su inna kuwa ko su dago kansu sai aisha ce ta mike tsaye jikinta na bari tana kallon yayan nata na dukan yayarta
Malan na karasowa ya ce" aa, aa, Abdul Fatah me haka? Baka da hankali ne? Ka daina kafin na wanka maka mari fa?
Du irin yanda Wujdane ta kai ga taba ran mahaifinta abu na farko ne da ya fi tsana a taba lafiyarta
Cike da bacin rai Abdul Fatah ya nuno Wujdane da yatsarsa ransa a bace ya ce" Aba, shin yaushe yarinyar nan zata yi hankali ta samu nutsuwar zuciyarta ne? A yau wajen samari ana labari har ta kai an daina jin nauyin nawa a gabana ake cakalkalarsu ita da wancen jakar kawar tata, shin a mai kika dauki rayuwarki na ya mace ke wujdane,,? Ko maza a wannan lokacin suna kofar gidajensu aman ku yanzu kuka fito daga gidan mai alaro wai kun daki amaryarsa? Shin Aba yaushe zaka bari yarinyar nan a koya mata hankali?
Sai fada yake yana huci inda Wujdane ke zaune dangagar a kasa tayi zaman yan bori, kuri da idannuwanta sai kallon yan gidan nasu take, ta jibgu dan jibguwa aman ba ko digon kwallah a idannuwanta sai cicije lebe take
A hankali.Malan ya ce" duka ba shi ne magani ba, daga hannu da kake a kanta yana iya jawo maka raininta a lokacin da kake bukatar ta girmamaka, ni kaina a yau Wujdane ta taban zuciyata, bani da wani uzuri da zan yi mata a gabannan sai maganata ta karshe shine ta fitar da mijin aurenta nan da sati biyu kacal, idan ba haka ba ni zan yi mata miji,
Malan na gama fadar haka ya shige dakinsa ya zauna yana hangen Wujdane wanda yake kokowa da zuciyarsa kan kar ya fito ya lalasheta,
Itama kifar dakin nasa ta tsurawa ido, zuciyarta na halbawa, irin halbawar nan mai sauri sauri, da sauri ta juyo da idannuwanta ga innarsu, aman inna bata kallonta daga karshe ma innar daki ta shige, yayi sauran daga ita sai yayunta da kanwarta wanda cikinsu idan ka cire Abdul fatah kowane ji yake kamar ya rugo ya rungumeta ko zata daina jin zafin dukan da aka yi mata, Hamza kuwa cike yake da jin haushin dukan da abdul fatah ya yi mata duda ya hana shi daga hannu samanta aman shine zai yi ta kwalo da ita a haka din nan baya gannin yanda jikin wujdane yake tamkar na jariri zai kama dukanta haka
Wujdane ji tayi wani abu na bun fuskarta, a hankali ta kai hannunta daidai gurbin idannuwan nata ta lalubo
Da sauri ta kai idannuwanta tana kalo, eh da gaske hawaye ne, hawaye ne take , hawaye ne a fuskarya, ai bata san lokacin da ta mike tsaye ba ta.......
Readers, i.k so sorry, hidindimu ne suka yi min yawa, insha allah da na samu sasauci page zasu ninniku sannan a kan lokaci, daga sajidarku
[3/27, 10:00 AM] βͺ+234 803 957 7698β¬: π¦π¦ *BANI DA ZABI*π¦π¦
*20*
WRINTING BY *SAJIDA*
Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai,
*SAJIDARKU CE*
MARUBUCIYAR:
*YAR MAHAUKACIYA*
*DUK KARYAR KADA*
*DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA*
*NEMAN NA KAINA*
................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH....
Aba ya ce" Malan Laminu ina nemawa dana *Alaidine* auren yar wajenka *Wujdane*
A tare suka dago da Malan da Alaidine, wani irn faduwa da gabansa ya yi har sai da ya dafe kirjinsa, ya dago da dara daran idannuwansa daga wayarsa da yake duba ball da aka yi BarΓ§a da Reel, a wani haukace ya juyo wajen abansa wanda ya yi masa kallo daya ya dauke kansa ya mayar wajen Malan Laminu wato Malan, da malan ishak
Kamar da wasa Alaidine na zaune dangalgal a gabansa da kudin aljihunsa mahaifinsa ya daura masa aure da yarinyar da a ranar da ya ganta tsanarta ta darsu a ruhinsa, a yanda ya fahimci rayuwarta bata da kamun kai har tana furtawa namiji ya yi mata kadan kennan ta san mazan ne, yarinyar da shi bama zai nuna kamaninta ba, yarinyar da kanninsa Jamail ke so kamar ya mutu, yarinyar da yayi yanda yayi dan karta shigo zuri.arsu a matsayinta na wada sam bai yarda da lamarinta ba, yarinyar da a duniya idan da akoy abinda zai nuna da kyama toh tabas itace domin kawai haka ta darsa masa rayuwarsa a zuciyarsa sai gashi
An daura auren *Elhaj ALAIDINE abdul kadri, DA WUJDANE Laminu bisa sadaki naira dubu hamsin lakadan* , da *JAMAIL ABDUL KADRI DA NANA AISHATU LAMINU A BISA SADAKI NAIRA HAMSIN LAKADAN*,
Nan fa ya ci gaba da yadawa ya zo kan soron gidan Malan ya rangada wannan labari
Aisha ta zabura ta mike tsaye jikinta na wani irin bari, kallonta ta maido wajen innarsu da itama ta yi zuru cike da mamakin sunnan Alaidine da aka kira da sunnan mijin Wujdane, tambayar kanta take shin waye Alaidine kuma? Ko dai malan sadakar Wujdane ya bayar?
Wujdane ce ta fado jikin inna, ta kankameta sosai domin wani irin sanyi sanyi ne yake ziyartarta, da wata irin faduwar gaba, kanta yayi mata wani irin nauyi, haka ma zuciyarta, bakinta yayi wani daci ta rasa gane kanta, a hankali ta dago da idannuwanta da kwayar cikinsu ke ta wulgawa tamkar zasu fado, zufa na keto mata ta zube idannuwanta cikin na mahaifiyar wace itama sak irin idon Wujdane din ne , murya a shake ta ce" innata, Lukman dina bai zo ba ko innata? Innata wanene *Alaidine* kuma????????
A hankali Aishama ta fado samansu itama ta saki kuka, kuka na abinda ya riske ta, farin ciki take da bakin ciki, idan ta tuna Jamail ba ita ce a zuciyarsa ba, ta tuna halin da yayarta ke ciki sai ta ji komai ya fice mata, idan kuwa ta hango ita Aisha itace matar Jamail muradin ranta sai kawai wani dadi ya rufeta, hakan ya hadun mata ya bata wani irin nauyi a zuciyarta itama ta fashe da kuka
Inna sauraron magangannu take, yanda ake kaikaikai ku leko ku ga wanda aka daura aurensa da Wujdane, iye lale Allah na sonta, kaikaikai aman shima bai sani ba mahaifinsa ne, toh dama auren harda na Aisha? Toh sunnan mahaifinsu daya ko dai yayan mijin Aishar ne, aman ba.a ga mijin Aishar ba, iye angon Wujdane din ya tafi a mota a guje kamar baya son auren,
Rungume yayanta ta yi a jikinta ta saki labulen dakin ji take tamkar ta fita ta cewa jama.ar tsakar gidan su tafi ya isa hakanan ta gode, sai dai abin haushi yanzu ne ma wasu ke kara zuwa dan gulma
A kofar gida kuwa wasa sabon kallo, shagali kawai ake, sosai da sosai, daga nan aka kwasa dan zuwa masalaci wajen sauka, zo ka ga malan da Aba fuskokinsu fayau shagalinsu kawai suke suna amsar barkar da aminnan arziki ke yi masu
Dugunzuma suka yi inda Malan bai samu damar shigowa dan ya karawa inna bayani, harda su Abdul Fatah du suka yi masalaci kowane na mamakin wannan iko na Allah ( haka ne, wani baya auren matar wani, wani baya haihuwar dan wani tun ran gini tun ran zane )
Wuni aka yi gidan inna ana ta dafe dafe na abubuwan da ya sawaka, makota sun bude ciki sun yi nak, domin a gidajensu ba samun hakanan zasu yi ba, kowa mamakin ana dafa shinkafa da makaroni a sabgar gidan Malan sai kace wani atajiri harda nama da isasun kayan miya, idan ka ga yanda jama.a ke wawa sai