Showing 39001 words to 42000 words out of 42826 words
ya jima rabonsa da shi, mai yiwuwa ya jima bai saka shi a ido ba, aman yaya zai yi? Mutuwar nan dai an yi ta, sannan shi dolensa ne , kuma musulmi ne du abinda zai faru zai yi hakuri ne
Muzkutawa ya yi ya ce" ABA,
A tare suka dago suna kalonsa wanda ya kara kayar masa da zuciya, daurewa ya yi ya ce".......
[3/27, 10:01 AM] ‪+234 803 957 7698‬: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄
*24*
WRINTING BY *SAJIDA*
Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai,
*SAJIDARKU CE*
MARUBUCIYAR:
*YAR MAHAUKACIYA*
*DUK KARYAR KADA*
*DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA*
*NEMAN NA KAINA*
................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH....
Happy happy birthday to you, happy birthday to you, happy birthday to you *YAYA HAYAT* happy birthday to you@ *Allah ya sa wannan shekara ta zamo daya daga cikin shekaru da zasu zo maka da cikar lafiya, su kara maka daraja, su kawo arziki mai anfani, hsppy bufday*
Mom ta yi kiran Lami,
Lami ta fito tana gyara hijabinta dan tunda ta kyala ido ta ga Alaidine a gidan da safen nan ta shiga kimtsa kanta tun kafin ya fita bayanta
Tana zuwa ta raba tana amsawa
Mom ta yi dan murmushi ta ce" ki fitar min da zabi a cikin frij ki saka min su s ruwa yanzu zan fito na hada breakfast , yau na yi rana
Amsawa Lami ta yi ta juya insa Wujdane ta kama hannun Aisha ta mikar da ita dan su bi Lami
Mom ta cel" aa, yar gidan Mom ina zaku tafi ne? Ku fa je ku huta kar ku kwashi gajiya da yawa kun ji?
Wujdane ta dan juyo, ita kam da alama zafa a saka ta yawan magana ne s gidan nan, s hankali ta ce" zamu hada kayan karin ne *Mama*
Mom ta yi murmushi, ta lura aikace aikacen nan sabonsu ne, dan haka sai kawai ta barsu suka tafi kicin, aka bar su Alaidine da su Mom , nsn Aba ya dora daga inda ya tsaya a jawabinsa mai shige da gargadi, sannan ya basu umarnin su tsaya su karya kafin su tafi
Raba aikinsu suka yi, Wujdane kam bata iya wani dogon rarashi ba aman idannuwanta kyam a kan du wani motsi na Aisha,
Aisha ke feraye dankalin turawa ita kuwa Wujdane na gyaran naman da take kokarin dora shi silale
Sosai ta kara wanke naman, duda daman ba wani dati ne da shi ba, ta kawo tukunyarta ta zuzuba shi, ta kawo su kayan yajinta , su gishirinta kadan ta zuzuba sannan ta dan zuba ruwa kadan bayan ta saka albasarta
Lami ce ta kunna mata gaz wanda har sai da ta tsorata yanda wutarsa ke da zafi, ta dora ta rufe tukunyar ta zauna tana daka atarugun da zata hada vinaigrette da shi tana kallon yannayin Aishanta, yanzu da zuciyarta da dadi da tuni ta cika mata kune da labari
A hankali ta matso kusa da ita ta kama mata yankan dankalin turawan,
Kanta a kasa bata wani dago ba ta ce" *kar ki kwalafa da gannin daidai fa a wajen da namiji, sannan ki cire damuwa a ranki insha Allahu Jamail zai so ki kin ji?*
Dago da kanta ta yi tana klon yayar tata, sai ta sakar mata murmushi, sai a lokacin ta farga da irin yanda ta tayar da hankalinta bayan ta san a yanda aka yi auren nan, tausayin Wujdane ne ya ratsa mata zuciya, ita sam bata wani nuna damuwarta ba bayan ta sani sarai itama bata wani jin dadin hakan dake faruwa da ita
Hakan ya saka ta saki ranta ta shiga aikinta da kazar kazar dan su yi su kamala, suna yi suna tambayar Lami irin abubuwan da Mom din ke yi ( iyaye mata, mu kula, kana da shi ko baka da shi idan baka koyawa yaron naka ya wahala ba, idan baka koya masa abubuwan ba, ba lale ne ya je gidan hutu ba, kuma yau ko gidan hutun ya je zai so ace shima yana shiga kicin dinsa yana sarafawa mijinsa kalolin girkin da zasu kara shakuwa a tsakaninsu ba wai kawai mai aiki ya girko ya kawo masa ba, idan yaron naka ya horu da wahalar tun a gida, aikace aikacen ku, wankinsa, du inda zai je ba zai sha wahala ba, sannan kai kanka sai dai a bika da adu.a, Allah ya sa mu dace)
Dankalin nan suka soya, bayan sun yiwa zabin nan suyar sama sama inda suka yi wani taushi, sai vinaigrette, sannan suka hada jus na kwakwa da madara pink suka markade kwakwar suka tace ta tas sannan suka hadeta da madarar nan sai kankara da dan siga da suka hada domin Mom bata hada jus da irin kayan kanshin nan ,
Lami ta jera masu saman katon plat suka kama suka fito
Direct wajen table din suka kai suka ajiye wanda su Mom suka bi su da kallo, a can kassan zuciyar Mom tana jin wani irin farin ciki marar misaltuwa, tana ta faman yi masu adu.a sannan tana so ta dandanna girkin su
Kiransu ta yi ta fada masu cikin sif akoy kaya su kimtsa su sauko a karya
Sama suka hau , wannan karin fakin Wujdane suka fice a tare
Wujdane ta fara yin wanka, kafin take fitowa Aisha ta ciro masu atampa da hijabai, irin hijaban nan masu hannu da tsakiya a hannun sannan da dan tsayinsu domin sun dan zarta gwuiwa, ta dorawa wujdane kalar ruwan anta a saman atamfarta ita kuwa ta dora fari, duka yanda zasu hau atampopin ne
Nan da nan suka shirya abinsu, sai bayan ta dage ta sakawa Wujdane kwali wada idannuwan suka cika da hawaye na kwalin domin ba wani sabawa ta yi da sakawan ba
Sai da ta jima kana take bude idannuwanta ta sauke su a fuskar Aisha
Mirmushi Aisha ta saki tana kallonta, a can kasan zuciyarta kuwa tana taslima ga wannan tsarin Halita na yayarta
Girar Wujdane a tsare take, bata taba asketa ko wani daidaita ta ba, ba baka sidik bace maroon ce sannan ta daidaita tsaf a zagayayiyar fuskarta
Idannuwanta tsarinsu sai dai ace masha Allah, idan ta saka kwali kuwa har wani kyalkyalin kwalin suke su kara haskawa, sai lebenta kuwa ainayinsa pink color ne, ga motsi kadan takan dan laso shi hakan yake sakawa koda yaushe a danyace yake koda bata saka man lebe ko jan baki ba, gashin idannuwanta kuwa gazar gazar haka suke da tsayi da shanyewa, a hankali suke saukowa suna dan magana kasa kasa kasa
Har sun hau table din, Mom tana zuba masu abincin
Khadija ma an tasota daga bacinta, tana zaune kanta daure da dan kwalin shadar dake jikinta, wace ta kwana da ita abinta,
Aba kawai ne da Mom ransu fes, idan ka duba yannayin Alaidine du kamar ya fasa ihu ya bar wajen yake ji, Jamail kuwa du zuciyarsa a karaye na irin yanda Aba ya yi ta yi masu nasiha, Khadija kuwa daman da kyar ta samu bacin, tana jin haushin bayan gata a gidan Aba ya je ya aurowa Alaidine wata matar, ai kuwa ta dauki aniyar sai ta koyawa Wujdane hankali sannan zata jata a jiki ta fada mata sirrin Alaidine din dan idan fada ya hada su itama ta kiraye shi da shegen ko ya saketa ta huta,
A hankali suka zauna, a kujerun da ba kowa wato tsakiya suka saka khadija dake zaune, sai ya kasance Wujdane tafi kusanci da Jamail dake kusan Mom, sai Aisha ta zauna kusa da Alaidine dake kusan Aba, aman kuma suna facing din junna wato kowane na iya kallon dan uwansa sak idan hakan ta kama
Abincin aka fara ci, inda kake jin karar cokula na kara a cikin plat, Khadija kam yayi mata dadi a baki, Alaidine ya ki ya kai bakinsa dan kyankyami sai da suka hada ido da Mom ta yi masa nuni da idannuwanta kan ya ci, hakan ya saka shi cin a tunaninsa ba zai ji yanda yake so ba
Sai dai ga mamakinsa wani taushi, kanshin kayan kanshin nan da dan gishirigishirin ya saka shi lumshe ido, a boye ya saki ajiyar zuciya ya dan gyara yana fakaitan idannuwan mutane yana dan tsakura
Sosai jamail Jamail yake cin abincinsa dan ya san girkinsu daman, a hankali ya dago da idannuwansa cikin sa.a kuwa suka sarke da na Aisha wace ta dago dan zuba ruwa
Sun yi kallon cikin ido na wajen sacond biyar kafin ya sakar mata murmushi mai kayatarwa wanda ya sakata jin kunya ta yi saurin mayar da kanta wajen abincinta ta kasa dauko ruwan sannan ta kasa ci gaba da cin abincin
Kamar hadin baki suka miko hannayensu dan daukan baban flask din jus din , ita ta san jus ne a ciki, shi kuwa a zuwan ruwa yayi masa, hannunsa ne ya doru saman nata,wani irin dago da kai yayi jin hannu tamkar na jariri, caraf suka hade idannuwansu,
Idonta ta rintse jin hannun namiji a saman hannunta, ta yi gagawar budewa, shi kuwa shagalta ce yayi da kallon idannuwanta, yanzu kuma sai suka bashi sha.awa mainakun haushi, aman abinka da miskili sai ya watsa mata hararar da ya saba
Bakinta ta yatsina ta dan karkace shi ta murguda masa shi kana ta janye hannunta tama fasa daukan jus din,
Mamaki taru ka kashe Alaidine mana, tambaya yake yiwa kansa" wai dam fitsarariya ce har haka? Daga hararanta sai ta murguda min baki??
Tashin Aba ne ya katse masa tunaninsa, inda Mom ta mike ta mara masa baya suka haura gefensa
Kokarin mikewa yake, wanda kafin yayi wani yunkurin har Khadija ta gifta shi ta shige kicin
Gannin du ana tashi ya saka su harhada kayan da aka ci abincin, sai Wujdane ta fara tafiya dan kaiwa kicin
Hadewa suka yi da Khadija ta fito a kicin din, Khadija ta yi mata kallon kaskantaciya, sannan ta dan saki buda a hankali ta rage muryarta ta ce" farin ya kaishi wannan karon kennan, zaki gane baki da wayo idan ya shige ki tamkar gonar talaka sannan ya rataba maki saki uku, ni din nan dai ni ce a yi a gama ina kallonku, domin nice kadai na iya daukan cikinsa na haifa masa Boy, du wata ta bayana karya ce ko yar gidan wanene balarana na ji a labari cewar ba.a tara aka tayar da kai ba
Tana gama fada ta fice bagazan bagazan ta tafiyarta dakinta
Zuru Wujdanw ta yi tana antayowa kanta tambayoyi, wannan ita ce matar tasa ko mai? To aman ya akayi bata ga wata shakuwa ta matar da har suka samu yaro da shi ba tsakaninsu? Ko tana matarsa danme zata fafada mata magangannu haka mararsa dadi? Ko an gaya mata son mijin nata ake ne? Daman sakin nawa yayi tun yanzu da bani da kamarsa a masoyana
Kwafa ta yi ta shige kicin din tana ayanna bafa zata dauki iskancin matarsa ba, du a tunaninta Khadijan matar Alaidine din ce
Tana dawowa ta tarar sai Jamail kadai , Aisha tana kicin din bata fito ba,
A hankali ta karaso wajensa tana murmushi ta ja ta tsaya ta ce" yayana, ina neman alfarma
Dago da kansa ya yi ya sakar mata murmushin shima, ya ce" Au, yau kuma? An amince na girman ne ko mai? Oh aunty wujdane manya
Kawar da kanta ta yo tana dan turo bakinta ta ce" dan Girman allah kar ka wakanta min Aisha, Jamail Aisha yarinya ce, bata da wani tunani in ba na kuka ba, kuma karka manta itama sai da ta jo hukuncin da aka zartar a kanta, karka wulakanta min ita na roke ka
Sai da ta gama, Jamail ya ce" na san Aishana yarinya ce, duda da farko ba ita na so ba aman ina mai tabatar maki zan kula da dukan lamuranta, karki wani damu kin ji?
Murmushi ta saki, wanda har sai da hakoranta suka bayana, Aisha da ta lafe ta rabe tana sauke ajiyar zuciya domin komai a kunnanta ya fito, sai Alaidine dake sama ya tsura masu ido, shi dai bai san mai suke cewa ba, aman a yannayinsu sai kawai yake hango tsantsar nishadi a tatare da su, gabansa ne ya fadi ya shiga tambayar kansa, ko dai yarinyar nan ta bata masa kani shi ya sa ya haukace shi yana sonta, Aba ya tashi ya aura masa kanwarta kar dai su dora daga inda suka tsaya ( ku ji fa😳😳)
Ficewa yayi a gidan ba tare da ya yiwa kowa magana ba ya nufi gidansa
Zaune Alawiya take, ta sha ado da doguwar rigarta ta atampa, Alawiya fa ba baya ba wajen kyau, sannan fara ce tas itama, gashi dai ne bata da shi, shima dan ta wakanta shi ya kakarye yama dadage, bata samu yin girki ba ta tashi da fitinar ina ya je, dan du a tunaninta bama a gidan ya kwana ba
Tana sakar zucinta sai gashi ya shigo , ransa a kololuwar bace, Alawiya kuwa ta mike ta tarbe shi da sabon salon iskanncinta
Kallonta ya tsaya yi tana furta masa kiri kiri cewar" daman auren da ya kara ita ta san dan sex ne, aman ko kunya baya ji ya tafi gidansu ya dane mace sannan ya dawo mata gida ya wanke dauda? Domin ba alamar ya wanke daudar da ya kwaso a jimin wata karuwar,........
Dago da idannuwansa da suka yo jajajir yayi, ya sauke su a kan Alawiya dake masifa ita an taba ta,
Nufota ya shiga yi tana ja da baya, domin idan akoy abinda bata marari a rayuwarta shine kasancewa da shi, dan kuwa a lokacin da ta nace baya kulata da ya kula tan ya kusan halakata, harma ta yi dana sani ta ci kuka, tun daga lokacin take tsoron kasancewa da shi, bata ma mararin hakan ko kadan
Murya a marairaice ta ce" karka taba ni plz, baka fa yi tsark............
.....kafin take karasa maganarta ya cafkota, muryarsa da ta soma gushewa da kyar ya furta mata" idan na hada da naki da nata kin ga sai na yi mai dalili............
...
...
Nan ya.......
🌚
[3/27, 10:01 AM] ‪+234 803 957 7698‬: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄
*27*
WRINTING BY *SAJIDA*
Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai,
*SAJIDARKU CE*
MARUBUCIYAR:
*YAR MAHAUKACIYA*
*DUK KARYAR KADA*
*DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA*
*NEMAN NA KAINA*
................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH....
Cike da fargaba Alaidine ya ce" Aba, ka fi ni sannin duniya mun zota ne na dan lokaci kalilan, dukan mai rai sai yayi kaura zuwa kiyama, ba ran da ba zai yi wafati ba, hakuri shi ne Allah yayi mana nuni da mu yi, domin dole ne bamu da yanda zamu yi
Kallonsa kawai Aba yake, bai iya furta masa komai ba, kallo na tsoro, kallo na tsoron jin abinda zai fito a bakinsa
Mom kam jikinta ya gama rikicewa da rawa, tsoron fal ranta ji take tamkar ta kwato magana a bakin Alaidine aman ya tsaya sai kwana kwana yake, cike da kosawa ta ce" kai Alaidine,.lafiya? Mai yake faruwa ne? Wani ne ya rasu? Ka fadawa mutane ka tsaya kana ta jan maganar bayan ka ga halin da Abanka ke ciki?
Ta karasa maganar tanai masa tsawa tsawa
Ajiyar zuciya ya sauke ya ce" Aba, rasuwa ne aka yi, kaninka ne ya rasu yanzun ma daga makabarta nake
Zurbat suka mike daga Mom har Aba suna kalon Alaidine wanda ya sada kansa kasa yana dan damanma bai je anguwar ba
Ajiyar zuciya kawai aba ya saki ya zauna yarab a kasa ya kurawa kasa ido
Mom nan da nan ta fara sharar kwallah, ta kasa cewa komai banda innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, tana gannin kannin mijin nata a idannuwanta,
Aba ya jima bai yi wani motsin kirki ba , har sai da abin ya fara basu tsoro , a hankali ya ce" Alaidine yaushe ya rasu ne?
Alaidine ya sauke kansa kasa ya ce" Aba yanzu na tarar za.a yi sutura aka yi da ni sai bayan an gama ne na fahimci shi ne
Mom ta dago da idannuwanta da suka yi jajajir ta ce" kai kuwa wa ya nuna maka gidan? Ya aka yi har kake zuwa? A ina ka san gidan?
Ajiyar zuciya ya saki yana kallon mahaifinsa ya ce" Mom ai ina lekawa wani lokacin, nakan je na tsaya gefe guda dan gannin halin da suke ciki, to yauma na je ne na ga ana fitar da gawar
Kanta ta mayar wajen Aba, a hankali ta sanyaya muryarta ta ce" Aba ka yi hakuri, ka yi masa adu.a sannan mu tafi mu yi masu gaisuwa Aba, dukan mai rai mamaci ne karka rike a ranka domin karka manta muma jiran tamu muke
Aba ya sauke ajiyar zuciya yana kallonta, can ya ce" tabas *MARWA* na yi imanin wanda ya amshe shi ya fi ni son sa, abinda ya tsaye min a rai shi ne rashin lafiya ya yi? Ya adinninsa ya canza wasu halayan? Ya wajen yiwa iyayenmu biyaya ya daina taurin ran nan nasa? Shin yana tuna ni nima kamar yanda nake tuna shi duda bamu wani mugun shakuwa ba a lokacin har na bar gidan? Ina cike da zulumin mutuwar kanina ne, ina adu.a ne a kasan zuciyata kan Allah ya datar da shi, Allah ya karbi bakuncinsa, sannan inna koka ranar tawa mutuwar harma ina adu.ar Allah ubangiji ya sa ranar mutuwarmu ita ce ranar farin cikin mu, ranar shiga kabarin mu itace ranar hutun mu,
A tare suke amsawa da amen ya rabeel Alamen
Nisawa ya kuma yi ya ce" ba zamu tafi gidan ba Momyn yara, domin karki manta Abana yayi furucin idan har ya kuma ganin kafata kalata koma mai kama da ni sai ya tsine min Albarka sannan sai ya kwana sallah kan Allah ya yi mana hisabi idan har ba sakin ki na yi ba na dawo gare su a lokacin da kike cikin halin rayuwa sanadiyana, daga baya da na koma ya rantse cewar ya kare da ni ya cire ni a yayansa,
Kawai zamu yi zaman mutuwar dan uwana a nan, mu yi masa adu.ar uku da na sati mu bi shi da adu.a sannan mu yi kokarin gyara namu zuwan, Allah ya sanyaya
Yana gama fada ya ciciba ya mike ya haye sama da niyar shiga dakinsa
Ajiyar zuciya Mom