Showing 9001 words to 12000 words out of 42826 words

Chapter 4 - BANI DA ZABI COMPLETE HAUSA NOVEL

23 Aug 2025

647

fita miskilanci, dan ita idan ta hana kanta abu akoy wa.inda suke tursasata, shi kuwa yaya Alaidine sai dai a hakura dan ko kalonku ba zai yi ba bake ka saka a kokon zuciyarka zai yi abin


A hankali ya ce" kanwata wujdane,


Da gangan ya fadi dan sau goma zai fadi hakan sai ta dago ta watsa masa harara dan ita ta tsani a mayar da ita yarinya, duda ya girme matan ya bata shekara biyu a kala aman sai tana ganin ya raina ta danme ba zai kirayi sunnanta kawai ba


Bata dago da kan ba, sannan bata amsa ba,

Murmushi yake saki na samun nasarar ya hauda ta, zai kara magana Aisha ta shigo da salama


Da fara.a yake mata oyoyo ya ce" lale da mamana,(kamar yanda su Malan ke fada mata), ya ci gaba haba yanzu bakina zai daina tsami kin ga inna na fama da kicin dinta Kanwats kuwa idan ta kulani toh wannan dutsen ya kulani


Aisha dariya ta saki tana karasa shigowa, dukawa ta yi ta ce" ina yini yaya Jamail,

Amsawa yake cike da fara.a , ta juya wajen Wujdane ta shagwabe fuska ta ce" aunty shine kika yi tafiyarki kika barni? Na saba kwana biyu da dawowa da ke har na watsar da abokan tafiyar tawa yau ni kadai na bi hanya ina ta waige


Wujdane ta dan dago, bata da niyar tankawa a yau sanadiyar Jamail dake guri wanda ta radawa natace,

Yana shirin kara tunzurata wayarsa baba ta dauki tsuwa

Da sauri ya zaro ido ya daga

Kafin ya yi magana daga dayan bangaren aka ce" ka zo

Kit aka kashe kiran,

Mikewa yayi yana dan sauri yana salamar su inna da fadin" Inna baban yaya na kirana bara na artaya kar ya daki banza,
Yana fada ne yana kokarin cusa wani abu kasan kwannan ruwan sannan yayi ficewarsa yana dariyar inna na yi masa adu.a har soro


Tuki yake na garari yana adu.ar kar ya kagauta,
Da gudu ya haura ya shige fallon yayan nasa da salama a bakinsa


Zaune yake yana ta faman danna laptop aman wani dan yaro da ba zai fi shekara biyu da ba na ta kokowa da wuyansa da jikinsa, shi kuwa sai dai ya dan kawar da kansa ya ce" boy stop it!

Kamar wanda yake fadin" Boy ka yi kokowar, domin kara makale shi yake


Jamail na shigowa ya san kwannan zancen ya hana shi aiki ne, cikin hikima yake kokarin janye shi a jikin yayan nasa, aman yaron sai ya kuma makale shi yana ihun shi park shi park gashi ranar ranar aiki ce park din ba wani dadi ne da ita ba, du yawanci matan aure ne da yan mata yan school da samarinsu irin masu dan hannu da shunin nan


Kansa ya dafe ya furta " oh goshhh🤦🏻‍♂


Mikewa ya yi tsaye , dan zuwa bedroom dinsa ya dauko abu, a nan tsayinsa da kirar jikinsa ta bayana, Ya salam, wannan bakin mutun ne a africa ko mai? *ALAIDINE* ba fari bane,

Aman ya fi duka yan uwansa haske, irin fatar nan ce ta yan ethiopia, domin sam ba zaka kiraye shi da bakin mutun ba, Alaidine dogo ne zambak , har ya dara Anwar a tsayi,
Ba zaka taba kusanto jikin Alaidine da rama ba sannan ba irin jikin nan ne mai tumbi ko wani loko loko na kiba ba, aa hasalima jikinsa irin na yan dambe ne, hannunsa a wani murde yake dalilin excercise da yake ba dare ba rana du lokacin da yake jinsa a irin yannayin kadaita ko tunanin rayuwa yakan mike ya shige dakinsa na sports ya zagine ya gurzu , yana gamawa lipton kawai zai dan sha ya konta ya huta domin ba kasafai yake fita aiki ba dan irin mutanen da suke zube shagunnansa ,
Alaidine na da idannuwa masu girma sai dai a ko da yaushe cikin ja suke, sannan akoy shi da rashin tsoron saka idannuwansa cikin na mutun koma waye, hakan ke kayar da gaban mutane da dama


Shin menene tarihin rayuwar wannan familly???????????????






Elhaj Kadri ganninka riba, miji a wajen Hajiya Marwa mahaifan ALAIDINE, ANWAR da JAMAIL,

Hajiya Marwa Ya ce a wajen Elhaj Muhamadu itace auta ita da yar uwarta marigayiya Shafa,
Matarsa daya, wace tayi ta hayayafa cikin ikon Allah tayi ta yin yan bibiyu har sau hudu sannan ta yi daya ta kuma samun su Marwa

Daga Marwa haihuwar ta tsaya sannan su uku kadai ne mata Shafa ta koma ya yi sauran biyu kuma Marwar ce auta

Marwa cikin wani irin gata ta tashi, takan fita ta je makotansu gidan Elhaj Abdallah mahaifin Elhaj Kadri,
Elhaj Abdallah ya ninka Elhaj Muhamadu arziki nesa ba kusa ba, sannan mutun ne mai mutunci yana da sadaka da zaka,
Yayansa biyu kawai maza Elhaj Kadri ne baba sai kanninsa Elhaj Abubakar,

Ragamar kulawa da kasuwancin Elhaj Abdallah a hannun yayansa, sosai yake saka su a hanyar koyan aiki su koyi neman na kansu, sai dai saken yayi mugun yawan da su Elhaj Kadri sukan yi wuta a cikin gari ba laifi

Marwa da Elhaj Kadri soyaya suke irin mai karfin nan, wanda da wuri ya nemi a aura masa ita sai dai abin takaici mahaifinta ya nuna ko kusa kawai sai ta gama karatunta na university

Tafiya ta yi tafiya, Elhaj kadri na ci gaba da kula rayuwar Marwa du da irin kashedin da mahaifinsa ya yi masa na cewa idan an hana shi aurenta ya nemo wata mata yawa ne da su a duniya aman fir zuciyarsa da gangar jikin na wajen Marwa wace itama du kwanan duniya takan sha darga da mahaifinta kan kul ta kiyaye duda mahaifiyarta bata da yanda zata yi ne da lamarin nan dan ita sam bata goyi bayan ace budurwa kamar Marwa da yar uwarta sai sun gama karatu ayi masu aure mata ba maza ba, a wannan zamanin

Ya kasance kusancin Marwa da Elhaj Kadri ya kara kusantuwa, takan tardo shi idan bai zo ba yakan bi ta baya ya ganta idan bata zo ba, harma su fice yawonsu idan ta fito makaranta

Elhaj Abdallah mahaifin Elhaj Kadri ya nemawa Kadri auren yar abokinsa wanda suka shiga shagulgulan shirin biki nan da wata biyar

Labari na tarda Marwa ta rikice ta shiga tashin hankali wanda ta kasa boyewa, da farko fushi take da shi mai tsanani daga baya suka shirya har suka shirye shedan ya kara himma aka kauce a lokacin da ba.a shirya ba


Bayan wata biyu rashin lafiya ya tsannanta a wajen Marwa, kulun yan cututuka, wata safiya yar uwarta ta fesa turare da sanyin safiya amai ya ce bismillah

Tun tana yi da karfinta har karfin nata ya kare ta galabaita, cike da tsoro mahaifiyarta ke kallonta mahaifinta ya rike yana maganar a je asibiti zazabi ne
Luuuu mahaifiyarta ta je zata fadi yan uwanta suka rike, cike da tashin hankali ta saki kuka tana innalilahi wa.ina ilahi raj.une, shikenan son zuciya ya kaimu ga halaka, cike ne ai da Marwa, Marwa kin bata kuruciyarki, kin zubar da mutuncinki, kin kawo kanki cikin bakar rayuwa

Wani kwalo mahaifinta yayi ta yi da ita har ana rikeshi, yar uwarta na gunzar kuka

Sai da ya gama dukanta ya jawota a kasa har cikin gidan Elhaj Abdallah,

Yana zuwa suna karyawa a falo ya hankadota
Jiki na tsuma ya nunota da yatsa ya ce" tunda kika zabi rayuwar iskanci har kika dauki cikin yaron da ake shirin aurarwa sai ki zauna idan kin haife ki bar masa abin ki nemo mijin zan aura maki, aman daga yau na haramta maki saka kafa cikin gidana idan kuwa kika sakan sai dai a kwashi gawarki


Yana gama fada ya fice ya bar Marwa nan yashe

Haka take rayuwa a takure cikin gidan su Elhaj Kadri, du yanda yake so dan gannin ta samu sa.ida abin ya gagara, mahaifiyarsa ta kasa ta tsare ko abin ci ne sai dai a boye ya miko mata, har ta kai watan haihuwa

Elhaj Kadri zuwa wannan lokacin ya gama yanke hukuncin yanda zai yi a washe gari, sai dai a cikin dare nakuda ta kama ta ,

Sun yi tunanin zata haife a nan abin ya ci tura har ta fara fita a hayacinta

Cikin tashin hankali Elhaj Kadri ya nufeta ya kinkimeta
Mahaifinsa cikin bacin rai ya nunosa da yatsa ya ce" kar ka kuskura, idan har ka yarda ka fita da yarinyar nan na yafe ka,

Jikinsa a mace yake kokarin basu hakuri da nuna masa halin da take ciki aman fir suka kiya

Har kasa ya duka yana basu hakuri ya fice a motarsa da takardunsa na banki ya nufi asibiti da Marwa
Cikin ikon Allah aka bata taimakon gagawa ta haifi sambalelen danta namiji, a nan Mahaifinsa yayi masa kiran sallah yayi masa huduba da sunnan *ALAIDINE*




Ci gaban labarin a next page i.a
[3/27, 9:59 AM] ‪+234 803 957 7698‬: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄





*06*


WRINTING BY *SAJIDA*



Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai,

*SAJIDARKU CE*


MARUBUCIYAR:

*YAR MAHAUKACIYA*

*DUK KARYAR KADA*

*DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA*

*NEMAN NA KAINA*

................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH....




Haka Wujdane ta jure ta kawar da kanta ga daliban nan ta dauki rubuce rubucen nan har aka dana karaurawar fitowa a karya

Wujdane bata yi gigin fita tarin daliban nan ba domin tayi imanin idan ta fitan sai wani ya nemi shiga sabgarta ita kuwa ba zata lamunta ba,

Cikinta sai kugi yake yi mata wani kuuuuuuuuu na yunwa domin ko abincin dare jiya bata ci ba, a hankali ta dora hannunta saman rigarta tana dan kokarin danar da yunwar


Tana nan zaune sai ga Aisha da wata kawarta fauziya, sun shigo da leda a hannunta

Zama tayi tana fadin " Aunty kinga na sayo maki abin kari ko zai yi maki??
Tana fada ne tana bude abincin a ledar tana nuna mata

Kasa kasa take hararar Fauziyar nan domin ta wani raja.a gaba daya a kallonta,
Kai ta juya gefe ta ja dan tsaki bata taba ledar ba bata ce komai ba

Aisha ta dan saki murmushi tana kallon Fauziya ta ce" am ni freind leko mana ajin su ely ki gani idan ta gama rubuta exercise ki karbo mana plz


Juyawa Fauziya tayi tana dan mamakin yayar kawarta

Tana fita Wujdane ta juyo ta bude ledar ta dan fara ci da bismillah

Haka Aishar ma ta saka hannunta fankasu ne da yaji suna ci ba wani hira suke ba sannan Wujdane tana dan kakawar da kanta

A hankali Wujdane ta ce" kinsan jiyan nan yara suka yi ta yi min ihun aljannah, shin halitata ta muzanta har haka ne ? Mai yasa mutan3 basa kallon kansu sai dai su damu da tawa halitar har su zo sunai min tsokana? Wannan abin na damun rayuwana
Ta karashe tana sada idannuwanta alamar she is sad


Aisha cike da tausayi da kaunar yayar tata, ta kale ta, ta ce" aunty, ba halitarki ce ta muzanta ba, aa , Allah ne ya yi ki cikin bayi masu baiwa, aunty karki manta abinda aba ke fada mana idan yana sufanta mana kamanin ma.aiki, idannuwansa tamkar na mage, Aunty baki da wata halita karkataciya, haka Allah ya yo ki wanda du mai kallonki sai ya razana da tsarin halitarki, ki kawar da kanki bi.izinnillah komai zai huce


Kallonta Wujdane take, a duniya Aisha ta zamanto mutun ta uku a masu tausaya mata sannan kaunar da take nuna mata sosai da sosai ce, Allah ne ya hada ko a cikin yan uwanta ta tabata aisha mai rungumarta ce,
Bata kuma furta wani abin ba har aka dawo inda Aisha ta fice dan zuwa ajinsu

Sosai Inna ta yi mamakin Wujdane dinta ce aka je makaranta aka dawo ba.a yi fada ba,

Yanzu haka fura take kirbawa a turminsu, furar da idan malan ya dan yi samu yakan sayo inna kuwa tayi abinta a gida ba ta mashin ba,

Kirbawa take tun karfinta hannunta du yayi jajajir , Aisha na gefe tana gyara shinkafar hausa mai cike da tsakuwa innar kuwa na bakin murhu tana iza wuta

Wulgawar Mairo ta gani ta kofar gidansu wAda ta wulgar ya fi a kirga hakan ya saka dam ta silale ta fice innar bata ma ankara da ita ba


Tana fitowa Mairo na tsaye tayi saurin riko hannunta tana fadin" Kan uba, wai Danine da gaske kenan ana ta zunden kin koma makaranta na karyata kinga kuwa, aman yanzu in ba rigimarki ba mai zaki yi da makarantar nan? Yayan talaka dai ba wani yanci ne da su ba a nahiyar nan , sai ka gama karatun ka dawo aikin hannu dan baka da dogon hannu, shi ne zaki wani koma yau anguwa an wuni ana camama banda ke???



Wujdane ta yatsina fuska suna tafe ne Mairo ke zubar nan, sai ga balki fitsara yar gidan indo

Balki daman na hakon Wujdane tun wani lokaci da ake bata labarin irin masifar Wujdane tayi tsanlan albarka ta yi alkawarin ita kuwa sai ta cima Wujdane din,


Tsayuwa tayi kikam a gabansu bakin baban titin da za.a tsalaka age kantin yan gayu dan su sayo mayafin da ake yayi a layin nasu naira dari hudu wada Mairo ta samo dari shida zasu je su gwada ko za.a siyar masu ita da Wujdane

Da sauri Mairo ta ja ta tsaya jikinta ya soma bari, hangowar su Yinusa saurayinta sun aza zaman yama da suke yi da abokanansa, sannan ta san halin Balki sarai ba dai masifa ba domin Balki idan ta rike ka ta gala maka cizo har cire fata take dan balaki kuma idan ta makaleka sai an yi da gaske za.a raba ku

Cikin fuskar tsoro Mairo ta ce" kinga dai Balki bamu tana higa sabgarki ba, dan haka ki yi hakuri dan Allah kar ki higa tamu har a zo anai mana taro

Balki ta zaro ido ta ce" ke yar kundun uba, ke har kin isa na tare ki ki yi min iyaka da ke? Yau zan gwadawa yan matan layinku karyar rashin kunya ne da ku daga ke har zabayar nan


Girgiza kai Wujdane ta yi ta juya dan bin bayan Mairo dake janta dan karta biyewa Balkin

Balki na gannin hakan ta kamo hijabin Wujdane daga baya ta janyota cike da izgili da neman fitina sai kara fifitar da idannu take tana kada girji ita ga mai balaki


Wani irin juyowa Wujdane ta yi da hannunta bata sauke yataunta ko ina ba sai fuskar Balki, ta kara wanka mata wani marin tamkar yarta,
Ai kuwa suka kacame kowa na dukan dan uwansa nan a cuci mazan Balki ya fado kasa tarin tsumakwarai harda pant baki kurin
Ai kuwa yara suka dau ihu da soya

Balki na gannin hakannan ta shiga kokarin sai ta cirewa Wujdane hijab dinta wada a ranar bata da dan kwali a ciki hijab din ne kawai ta dora saman kitsonta na doka da inna ta yi mata

Jama.a ne ke kokarin sai sun raba fadan nan wanda abin ya gagara har sun kai kasa sosai Wujdane ta shake wuyan Balki ta hanata katabus

Ihu ake karta kasheta , sai manya suka fara tsoron saka hannunsu aje tayi kisan kai ,

A bakin titin akoy polisawa da suke aiki a ranar, su suka zo suka runtuma jama.a da wanda ya ji da wanda bai ji ba du suka kame wanda harda su Wujdane a bayan mota kuri suka nufi police station


Zaune yake da wayar office din ya sada kansa kasa ya dafe habarsa, amsa waya yake cike da tashin hankali,

Anwar kenan, saurayi ne matashi, baban ma.aikacin polisai mai ji da kansa da jini a jika, magana yake da mahaifiyarsa tana fada masa jikin Sultan ya tashi, gashinan dai da kyar an samu malan ya yi masa adu.ar nan ya samu baci aman zuciyarsa bata sauka ba


Ajiyar zuciya Anwar ya sauke ya ce" Mom, wannan zuciya ta yaya na rasa kanta, ace mutun a gidan duniya ko gardama ya yi da wani shikenan sai ya sansandare dan idan mutumen ba na ya daka bane sai abin ya zama matsala idan kuwa na ya daka ne sai yayi kamar ya kashe mutun? Yanzu ita Mardiyar ta tafin ne??

Ba.a dai jin abinda mahaifiyar tasa ta fada , sai shi ne ya sauke ajiyar zuciya ya ce" sunar ma.aiki ne, wanda du musulmi zai so ace ya zama cikenken mutun, Mom yayana uku a duniya, yaya ya nace kan idan dai ba macen da zata shirya da boy ba zai taba zama da mace ba? Mom rayuwar nan sai a hankali daman yanzu duniya da ta zama haka da wuya ka samu macen da zata soka domin Allah har ta so yaronka, auri sakin yaya ya yi yawa da har ina murnar wannan an jima da ita har an kai wata uku ashe sakin na nan zuwa? Idan ba yaya ba dole ya kawar da kansa da wasu abubuwan ya ci gaba da kulawa da dukiyarsa, kin sani ne Mom ni aikina na nan ma ya iya da shi bale har na iya da tarin dumbin dukiyar nan ta yaya? Aman ba komai zuwa yama zan shigo dan Allah ki yi masa abinci da kanki Mom zai ci sannan masu aikin nan du su koma bangarensu kar ya farka ya sauke a kansu



Yana tsaka da maganar ta computersa yake kallon yanda ake tuntunkuda mutane a cel, harda mata da yara, kansa ya dafe yana fadin" Ya Allah, mai kuma suka yi wa..innan ? Ni da na aike su su duban hanya shine zasu fara kame?


Mikewa ya yi sai a sannan na ga tsayinsa, dogon namiji ne zambal, bashi da rama ko kusa, kakarfa ne mai aji, idan ba fada maka yayi ba ba zaka taba kawowa ranka cewar yana da aure harda yara uku, aikin police na cikin tsarin mafarkin rayuwarsa ne wanda a dole ya takurawa yayansa har ya amince masa ya je ya fito police din yake bautawa kasarsa,
Ba zai fi shekara 29 ba, domin mahaifinsu *Elhaj Kadri ganinka sa.a* baya barin yaro ya kai wani lokacin kafin ya yi masa aure, yakan cewa abinda ake muradi za.a samu, a kasan zuciyarsa yana yin hakan dan gujewa yayansa fadawa halaka wato tarihi ya maimaita kansa a tsautsayin da ya fada masu shi da matarsa uwar gidansa kafin su yi aure,
Du duniya yayansa uku Sultan

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login