Showing 3001 words to 6000 words out of 42826 words
kalo irin ka hadu da wani abin da ya mugun birge ka
Bakinta ta murguda ta banka masa harara sai idannuwan suka yi wani wulikwulik da su,
Tsarki ya tabata ga ubangijin da ya halici wannan halita
Muryar wannan bawan Allah ta kuma dakar kunnenta
Juyowa tayi wannan karin da yannayin mamaki shinfide a fuskarta, har zuwa lokacin bata furta masa kalma daya ba, kallonsa kawai take a ranta tana mamakin kowa na gudunta ya akayi shi ya tsaya ko bai ji sunnan da suke kiranta da shi bane? Wato Aljannah???
Sosai ya gyara zamansa ya ce" aljannah da yamacin nan a tsakar gari? Aljannah har ta tsaya ayi haka da ita? Ni koda ke aljannah ce kin yi min
Dago da kanta tayi wannan karin ta shiga kokarin mikewa cike da jin haushinsa a ranta tana fadin" banza bata gari
Idannuwanta ne suka sauka saman Mairo dake kokowa da wasu almajirai na nama, sosai ta cire dan mayafin sai dakuwa suke ta warta su warta
Wani uban tsaki ta ja ta mike ta kama hanyar tafiya ranta a matukar bace tana tsinewa halayar Mairo
Biye yake da ita a saman mashin dinsa irin ash colar din nan, shi fa yarinyar nan sai ta kula shi
Ita kuwa sauri take zabgawa domin bata da kudin mota ko sisi a hannunta kuma ba zata jira Mairo ba domin har magariba ta kawo kai
Ki bari na kaiki, kin ga tun dazu muke tafiyar nan da alama gidan da nisa ko?
Idan tayi magana to tabas titin da take takawa yayi magana, ita fargaba ce ta fara dirar mata jin ana salame sallar magariba,
Ba ita ta karaso anguwarsu ba sai da aka gama isha.i, kafafuwanta du sunyi jajajir haka take baza hijabi
Wannan gayen na biye da ita , shigarsa ba wata muguwar shiga bace, dan saurayi matashi zai kai shekara ashirin da takwas, yaro mai sunna Lukman dan kasuwa ne yana siyar da su atampa da yan daidaikun kayan mak.up a banban layi, sosai yake neman na kansa domin tunda ya tashi ya taso da hakan shi ke ciyar da gidansu
Juyowa tayi ta kale shi daidai kusa da gidansu,
Biye yake da ita tamkar jela, ta ja wani tsaki tayi masa kallon sama da kasa ta nuno shi da yatsa ta ce" Kai malan ka barni haka, lafiya? Sata nayi maka ne ko me? Ya zaka kama bina tun daga anguwar nan har gidanmu? Nayi maka kama da yan iska ne? To ka barni haka karka shafan bakin penti!
Kallonta yake cike da matsannancin abinda ya taso masa na kaunarta, dama haka muryarta yake? Ya salam ya furta kafin yayi wani yunkurin ta fada gidansu
Zama yayi a jikin babur ya jima har ya samu wani yaro yace da shi dan Allah ya shiga gidan nan ya kirawo masa wata budurwa fara mai bakin hijabi yanzu ta shiga
Zaro ido yaron yayi harda kama haba ya ce" wai kana nufin gidan su *WUJDANE MAMA?*
Bai tsaya ya bashi amsa ba ya ci gaba" ai kama tafi kawai domin basa zance da dare, kuma inai maka adu.ar Allah ya sa ba WUJDANE kake nufi ba
Ya sa kai yayi gaba da bakar ledar man ja da ya sayowa mamansa
Ajiyar zuciya ya saki a fili ya furta" zan dawo
Tunda ta shige zaure ta jima a tsaye kafin ta saka kai cikin gidan da adu.a a bakinta sannan tayi salama kasa kasa
Inna ce zaune a balbalin cikin gidan tana zaune saman darduma, kwai ne a gefenta dan ya kara haska mata tsakar gidan domin da abin hadari hadari garin sai yayi duhu
Zuru tayi cike da tsoro tana kallon yannayin tafiyar y.ar tata, yar da tafi kusanci da ita har cikin zuciyarta dalilin kamar da duka yayanta basu yi da ita ba sai ita, ta dauko komai na mahaifinta harda tsagar idannuwansa, yar da kulun ta Allah take jaza mata bacin rai tunani fitina kala daban daban
Tsoro ne ya darsu a zuciyarta harma ta baiwa kanta amsar shikenan da Alama Wujdane ta zubar da mutuncinta domin wani tafiya ne take tana harharde kafafuwa
Cike da sanyin jiki Wujdane ta karaso kusan mahaifiyarta ta tsuguna, murya na rawa ta ce" inna, ina yini? Ya gida?
Kallonta innar take, sam Wujdane bata tsoron zuciyarta haka take ayannawa a ranta, ace y'a mace ta fice a gidansu tun safe sai yanzu zata dawo abinda ko wani namijin baya kai magariba a waje?
Cike da muryar karaya da takaici inna ta ce" Allah ya shirye ki WUJDANE,
bata ce komai ba kanta a kasa , ta jima a tsugunan nan kafin ta mike ta shige dakinsu
A cikin fashin sallah take hakan ya saka ta lalubo maganinta na ciwon mara ta hadiya, sai a lokacin cikinta ya bada wani kuuuuuu na yunwa alamar ba.a saka masa komai ba a wunnin ranar kwata kwata
Konciya tayi ta takure jikinta tana sauraron muryar Aisha na karanta AL.IMRAN.
Aisha karatu ne take tana tilawa bayan ta gama sallar isha.i, a hankali ta kai dubanta wajen yayarta, a rayuwa tana tausayawa rayuwar yayarta, wannan wace irin rayuwa ce ta daukarwa kanta ne? Yaushe zata farka ta daidaita nutsuwarta? Ita ba wuni a gida ba, ita ba cin abinci ba sai wani lokaci lokaci, haka take galari tamkar tinkiya, bata saka komai a ranta, yayansu ya jibge ta,
Dan hawayen da ya zubo mata ne ta share tana mikewa ta fita
Jim kadan ta dawo dauke da roba ruwan blue yar madaidaiciya
Gefen katifar ta zauna ta ce" tashi Aunty ki ci abinci dan Allah
Shiru tayi mata tamkar ba da ita take ba sai da ta kuma maimaitawa
A hankali Wujdane ta dago da kanta, tana sha.awar rayuwar Aisha aman ita ba zata iya yinta ba, domin kuwa ko cikin gidansu takan jita tamkar ba a inda ya dace ba, kalar idannuwanta idan yayanta na dukanta yakan kirayeta da banza wawa wace bata kama da mutane mai siffar mutan boye,
Hakan na sakawa tayi nesa da kowa
Ki yi hakuri ki mike kinji? Ki yi hakuri dan Allah,
A hankali ta mike ta karbi robar, macaroni ne ce ta sha man ja da yaji,
Zama ta gyara tayi bismillah ta fara ci cikin nutsuwA
Bayan ta gama ta dauki ruwan da Aisha ta zubo mata a kora ta sha , nan ta fara samun nutsuwa na shigarta
Inna ce ta yi salama ta shigo dakin nasu, waje ta samu ta zauna tana kallon su gaba daya
A hankali ta shiga jawabi kamar haka" Wujdane, ki sani a duniya mace yar gida ce, yar a kilace ce, mace yar mutunci ce, kin ga, du isar mace du takamarta idan har ta zubar da mutuncinta na ya mace ta gama, wujdane baki da wani abin tunkaho da ya fi wannan, ki sani saurayi du abinda zai rudeki da shi idan ya gama da samun abinda yake nema ya gama da rayuwarki, ki rufawa kanki asiri wujdane, ki rike tarbiyar mu
Kanta a kasa take gyadawa irin tana daukan abinda ake fadi din nan,
Ajiyar zuciya ta saki ta miko mata rubutun da Malan ya wanke wanda du kwanan duniya ake yi mata dan ta nutsu ,
Hannu ta saka ta yi bismillah ta shanye ta mikowa innar kwannon
Haka inna ta mike ta fice gwuiwarta a sace
Washe gari a daki Wujdane take, du tana ji lokacin da mazan gidan suka fice kowa ya yiwa inna salama ,
Kafafuwanta ne suka dauki ruwa, sun yi luhu luhu da su basa takuwa,
Inna mamaki take har karfe goma sha daya Wujdane bata fito ba? Sai ta shiga adu.ar Allah ya sa ta ji jawabi ne wannan karin
Aisha ce ta dawo daga makaranta karfe daya tana shigowa dakinsu cike da mamaki take kallon Wujdane,
Zama tayi gefenta tana tambayar lafiya kuwa yau take gida???
Haka kawai ta ji ina ai itama makarantar zata shiga , makaranta ce mai hade da islamiya, sosai ake karatun islamiyar komai da larabci, a can ake kusan wuni su duka aka saka aman ita ta ki
A hankali take bin Aishar da kalo har ta gama cire uniform dinta ta kara zama kusanta ta nace kan sannin mai ke damunta
Hijabinta da ta rufe kafarta ta budewa Aishar cikin yannayin gajiya da konciyar ta bata labarin doguwar tafiyar da tayi
Cike da mamaki Aisha ta shiga dakin Malan ta dauko man zafi ta zo ta shashafa mata har bayanta sannan ta fice ta barta ta huta
Kai.kawo kofar gidan su Wujdane ya fi a kirga da tayi tana son shiga tana tsoron yayansu, domin wani lokaci da ta shiga Abdul fata da ya kama kwalo da ita tamkar ya samu jaki, ita tsoronta daya jiya yaya wujdane din ta yi ne?
Mairo mairo.
..
[3/27, 9:57 AM] βͺ+234 803 957 7698β¬: π¦π¦ *BANI DA ZABI*π¦π¦
*03*
WRINTING BY *SAJIDA*
Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai,
*SAJIDARKU CE*
MARUBUCIYAR:
*YAR MAHAUKACIYA*
*DUK KARYAR KADA*
*DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA*
*NEMAN NA KAINA*
................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH....
Tana saka kafarta cikin gidan ji kake wur kwatsam karar cilo langa fada ne ake na kirki ana dambe tsakanin lami da Hajara
Sosai ta shake wuyanta inda yaransu ke tsatsaye suna ta ihu suna ke daki hancin ke dakii bakin ke daki tatasai da kubewa wanda ya fasa ba shi bane
Dan tsayawa tayi ta kare masu kallo ta kada kai tayi wajen zanar su kawar tata
Tana shiga da salama a bakinta
Mairo ( Mariam ce aka mayar da sunnan Mairo )
Dake zaune da daurin kirji tana ta kokarin yin kwaliya ta juyo ta saki baki tanaiwa Wujdane wani kalo
Wujdane ta murguda baki ta ce" kallon fa??
Mairo ta ce" yanzu tsakaninki da Allah danine ( Wujdane) kin san dalilinki aka gayace mu wajen sunnan nan, tunda aka yi haihuwar nan nake tara kudi dan mu samu na mota aman shine har yanzu baki shirya ba???
Wujdane ta yatsina fuska da kalar an dameta ta ce" ke ni nama manta da wani wajen suna, ke yanzu dan su Abu sun ce ana dafa shinkafar gwomnati shine kike wannan rawar kafar? Kinga karfa mu tafi mu jazawa kanmu raini, ni bana son irin shiga cikin yan gayun nan yanzu za.a fara yi maka kallon saman hanci ni kuwa ba dauka ba zanyi
Mairo ta juyo tana kallonta ta cacaba hodar ruwa mai sunna iman a fuskarta irin ta cub din nan mai danko sai wani firirita take da idannuwa tana kokarin jan gira ta ce" kai Danine, kar ki ce dan hinkafar gwomnati ne ni daman can Aradu ina da sha.awar shiga cikin yan gayun ne a dama da ni dan Allah ki je ki shiryo mu daga kar rana tayi sosai a shishige cikin gidan
Kai ta girgiza , tana matukar mamakin irin yanda Mairo bata gani ta kyale ko ta kawar da kai, kwadayi kuwa ba.a magana, waje ta samu ta zauna tana cewa" idan xaki je da ni a haka ki je idan kuwa ba zaki ba ba damuwa sai nayi zamana aman bikin gayar sodi Abua itama mai aikin gidan ta gayace ta muma aka gayace mu bazan tsaya kyalkyale kyalkyale ba irin wa.innan fa daman sai dai kai kayi musu wahalar aman su basu iya yiwa mutun ba, dan haka ke da kika ga zaki iya ki ci gaba
Bata kai ga rufe bakinta ba aka jefo wata rigar mama da har ta sandadare dan dati, wani irin tsami take fitarwa jikinta harda kamar wata kwalkwata ,
Da sauri Wujdane ta mike tana sakin rigar mamar kasa tana kakabe hijabinta
Kanta ta dago cike da bacin rai ta ce" Kan Uba, wannan wace yar kwal uba ce ta jefeni da wannan abin???
Tana fadi tana nuna rigar mamar
Mairo ta mike ta dauki rigar mamar ta leka ta jikin zanar ta jefa masu tana fadin" banzaye fitinanu, wai fa Adamu ne zai kara aure kuma na budurwa shine ya basu naira dubu dadaya harda dari bibiyu abinda bai taba yi masu a matsayin kishin laifi dan ya kawo amaryarsa, toh shine Hajara ta ajiye nata kudin ta tafi dauko markade kafin ta dawo ta tarar ba dari biyun shine wannan fadan tace ai Lami ce tunda su kasai suka san da kudin sannan da ta fita ba kowa a gidan sai su din, tun safe suke wannan ragabzar mijin ya fice abinsa yayi tafiyarsa, umanmu kuwa ta hane mu da shiga domin tunda adamu ya taba nuna yana son nan nawa suka sha masifa da umanmu sai bama shiga sabgarsu
Wujdane ta tabe baki cike da kyankyannin Adamun kansa, bata cewa Mairon komai ba
Mairo ta saba da halayar kawarta hakan ya saka itama taci gaba da shiryawa tana tayi mata labarai dan karta daina tafiyar
Tunda bus ta ajiye su suke tafe har anguwar sunnan,
Anguwa ce irin ta daidaikun masu hannu da shuni, irin anguwar nan ce dake cakude da masu abin da talakawan
Ja tayi ta tsaya sanadiyar hango gugun samari a kofar gidan
Mairo da ta shan jan baki ta juyo tana kallonta daman ta san a rina wai an saci zanin mahaukaciya domin du dabararka da Wujdane bata bi ta tsakiyar maza koda a idi ne zata rakube ne, aman da mata ne koda sun cika anguwar nan sai ta bi kuma ka tsakwaleta ku daku
Waje ta samu ta zauna gindin wata bishiya tana fadin" sai kin fito
Mairo bata tsaya magiya ba domin ta san kare kukanka ne ba zata bita ba hakan ya saka ta juya kawai ta tafi cikin sake salon tafiya wai ita yan mataπ€
Zaune take tana kallob kasa,tunani take tana fatan su koma kafin yama Yaya Abdul fatah bai dawo ba dan yana da haushinta ( ita bata ma damu da daga fita gaisawa da saurayi ta fice mai gaba daya ba)
Yan mata ne su biyu, sanye da ankin gidan sunnan da wani saurayi a gefensu suna tafe suna labari suna dara na darawa na jin haushi su ji
Wace ke gefe ta juyo da biyar dinta a hannu ta ce" bara na bayar da sadakar biyar nin nan zaifi gyara ni da na je na jefar idan ya so khalifan ya zo nema sai na amsan masa a wajen mama
Saurayin ne yayi dariya ya ce" ke da aka baki ajiya zaki yi kyauta da shi? Bakya gudun rigima ko???
Gaba tayi ta Nufo wajen wujdane itama tana dariyar ta miko tana fadin malama karbi sadaka
Ta maimaita ya kai sau biyar Wujdane na kallon kasa bata dago da kanta ba sannan gaba daya ta nanade kafafuwanta da hannunta a cikin hijabinta baki,
Jin mai maganar taki ta bar wajen ne ya sakata dago da kanta cike da bacin rai ta sauke idannuwanta a fuskar yarinyar
Ihu ta saki ta saki naira biyar din tana fadin" Aljanna wayo aljanna wayo na shiga uku Aljanna
Mutannen dake gefe da wannan saurayin suka yo wajenta suna tambayar a ina aljannar ne,?????
Wujdane da 5ake nunawa suke kallo, wani irin fari tamkar bata da jini a cikin jikinta, sai idannuwanta kalar maciji, wannan saurayin dake tare da su ya shiga janyeta yana fadi tun karfinsa" Inahu sulaimana wa.inahu bismilahi rahamani rahim
Shi kansa ya tsorata da yannayin halitarta, abinka da farin mutun ya saka bakin hijabi,
Du kama guduwa suka yi suka bar wani saurayi shi daya dake kallon Wujdane wada ta cika da takaici
A hankali ya duko ya ce""""""""":""""""""":::"""""""
[3/27, 9:58 AM] βͺ+234 803 957 7698β¬: π¦π¦ *BANI DA ZABI*π¦π¦
*05*
WRINTING BY *SAJIDA*
Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai,
*SAJIDARKU CE*
MARUBUCIYAR:
*YAR MAHAUKACIYA*
*DUK KARYAR KADA*
*DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA*
*NEMAN NA KAINA*
................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH....
A wunin ranar nan Wujdane ko kofar gida bata leka ba, tana ta bacin gajiya daman tana fashin sallah
Can da malan ya zo ya tarar da fara.a a fuskar Inna da ya tambayi dalili ya gano ta fara samun kan yar tata ne, cikin murna ya dube ta ya ce" innar Wujdane, koda kinyi kokarin boye soyayarta a zuciyarki a idannuwana bata boyuwa, Allah ya inganta
Kanta ta sada tana murmushi bata ce komai ba, haka ya mike ya leka dakinsu ya tarar har sun yi baci su dukansu kan Aisha na saman cikin Wujdane ya yi masu adu.a ya rufo dakin
Yau ta kama talata, tun karfe bakwai Wujdane ke zaune kofar dakin mahaifinta, kanta a kasa tana dan kallon yanda tsuntsaye ke saukowa su ci geron da innarsu ke zubawa du asuba ta Allah a tsakar gidan hakan ke janyo tsuntsaye kala kala su yi ta ci suna dan waken su
Yau ba bakin hijabin bane a jikinta, kayan makaranta ne irin na Aisha, blue din dogon wando sakake da hijab fari har kasa da riga blue a ciki, gefenta nikaf dinta ne da ya sha wanki kaf jikinta kalkal bata da dati ko kadan,
Malan Laminu ne ya fito da shigarsa na jalabiya fara da rawaninsa dan madaidaici kamar yanda ya saba
Da mamaki yake kallon Wujdane, idan dai ba idannuwansa sun samu matsala bane kayan makaranta ne ta saka, toh aman mai ya canza mata ra.ayinta ne? Ita dake maganar makaranta sai dai a aljannah idan tana cikin bayin da zasu shiga, dalili kuwa shine, a makarantar ya kasance wasu malaman na wawar neman soyayarta, wasun lalata da ita, wasun su tsangwami rayuwarta , haka dalibai idan dai ta fice sai an tsokane ta da zagin mai idannun kurukuru ya na mage, mai farin zabaya da sauransu
Amsa gaisuwarta yake yanda ta kara dukawa har kanta, Wujdane ba dai ba ladabi da biyaya bata da raina mutun koda a waje ne sai idan ka tabota nan fa zaka gane bata da wayo
Tsaye suke da innarsu malan na kallon yanda take zaune bata furta masa muradinta ba, aman shi ba sai ta fada ba tsakanin da da mahaifi fuskarta kadai zai kalla ya gane yarenta
Malan, ni kam ba katsalandan nake son yi ba, aman ka fi kowa sannin halayar Wujdane, nafi kowa murnar ta je makaranta ko dan yawon nan da ta saka a gaba, aman Malan kar ka manta zuwanta na karshe fa, ta yiwa yaya da kanwarta dukan tsiya ta tare hanya sai da aka kirawo ka, malan yara ba zasu daina tsokanarta ba, haka nima nayi