Showing 42001 words to 42826 words out of 42826 words

Chapter 15 - BANI DA ZABI COMPLETE HAUSA NOVEL

23 Aug 2025

637

ta saki ta kashe Tv ta kirayi kaf mutanen gidan ta sanar da su cewar an yi rasuwa a yi kokari a samawa gidan nutsuwa na zaman makoki

Sosai ake zaman makoki a gidan Aba, mutane da dama na zuwa yi masa ta.aziya, adu.a kam mamacin na shanta ta sosai da sosai, tun daga kofar gida wajen Aba har cikin gida wajen su Wujdane wa.inda suka bude tsantsar sauka a kulun ta Allah sukan yi sauka wa mamacin nan su yi masa adu.a a wuni zikiri ana hailala da kurhuwalahu ana nemawa mamata rahamar ubangiji ( ya Allah 😭, ina rokonta dan sunayanka tsarkaka, Allah dan girman zatinka Allah, idan wani ya ji labarin mutuwata ko a ina yake, Allah ka bashi ikon bina da adu.a sannan ka bashi ikon furta alkhairi a kaina da ni da dukan bawan da zai amsa da amen da kuluyin musulmi ya ziljalalu wal ikram 😭)

Dalilin zaman nan da ake, sai ya kasance Alaidine kulun yana gida, da shi da Anwar da matar Anwar da yayansa, dama Jamail ba yauba yake kokarin kaurowa gaba dayansa

Alawiya har zuwa wannan ranar bata zo ba, ta tsiro karyar cewa bata da lafiya hakan ya saka ya kyaleta bai takurata ba, idan ya fice a gidan ta mike ta shiga sabgar gabanta hankalinta konce a fili takan furta wani zaman makoki na kin Allah bayan mutanen ba wani sannin zamanku suka yi ba?

Boy na wajen Wujdane, yaron yana matukar sonta domin tana kyautata masa, tana yi masa wanka ta saka masa sutura tsaftatatu, ta bashi abinci a baki ta bashi chocolate t goya shi a batanta du irin girman shi kuwa, ita haka kawai take jinsa a ranta, domin Huzaifa irin yaran nan ne masu shiga rai, cikin jikinsa yake bulbul da shi, ga kyau masha Allah sannan ya maida Wujdane tamkar mahaifiyarsa ko baci ya dauke shi ta shinfide shi yana farkawa sai ihun mama mama yana nemanta, haka yake kiranta da sunna Mama kamar yanda ya ji suna kiran Mom.
Khadija ba yanda bata yi ba dan ta hana shi rabar jikin Wujdane aman matsalar ita bata iya rarashi ba, bata iya jan yaro ba sai dai da yayi abu ta duke masa baki ko hannu shi yasa sam ba wata shakuwa a tsakaninsu

Yau da wuri Alaidine ya dawo gidan dan ya farka da wuri ya tafi wajen sadakar bakwai,

Tunda ya dawo yake lure da taketaken Alawiya, kazar kazar dinta take sam ba wani alamar rashin lafiya a tatare da ita

Da wuri ya konta baci abinsa bayan ya gama nafilfilunsa, sai dai mai yarinyar nan tana yawan fado masa a cikin idannuwansa koda idannuwansa a bude suke, haka ya kwana juyi yana jawa kansa tsaki yana jin haushin kansa, harma ya yiwa kansa tambayar wannan wani irin tashin hankali ne haka? Sai dai ba amsa


Da safe yana fitowa Alawiya ta sha kwaliyarta tana zaune tana shan shayi,

Tsayawa ya yi a kanta ya mika mata hijabi, fuska a tanke ya ce" yau ko mutuwa kike a hanya sai kin je wajen rasuwar kannin mahaifina, dan haka ki mike mu tafi

Ranta a hade ta saka hijabin ta mike ta bi bayansa, idan ranta yayi dubu ya baci da wannan lamarin, dan me yake son takura mata a rayuwa ne?


Haka har suka karaso kowane bai cewa dan uwansa ufan ba

Aba mutum mai mutane, sosai kofar gidan ta cika da mutane , a haka ta ratsa ta shige shi kuwa ya ja ya tsaya Malan Mahaifin su Wujdane sai jero adu.o.i yake suna amsawa har aka gama aka wawatse


Matan cikin gidan ne ke ta fitowa har ya kasance du an fito sai na gida kawai

Mikewa yayi ya shige gidan,

Matar Anwar ce zaune saman tabarma, gefenta Wujdane ce rungume da Huzaifa tana bashi madara a bakinsa sai Aisha dake zaune itama da carbi a hannunta tana ja suna dan taba hira tsakannin matar Anwar da Wujdane

Dan tsai ya yi daga nesa yana kallonta, yanda Boy idan ta kai bakinta ya dan zubun mata a habarta zai lashe abinsa yanai mata daria idan kuwa ta hana shi lashewar sai ya fashe da kuka,
Ajiyar zuciya ya saki a can kasan zuciyarsa ya ce" Alaidine, ka san cewar a duniya ka yiwa kanka hani da soyaya da wata diya mace , ba dan komai ba sai dan gudun ta san sirrinka ta yi maka gori harma ta guje maka, Alaidine yarinyar nan lale mace ce, ta isa mace, aman konciyar hankalinka shine mafi girman bukatarka, so ka kawar da kanka a lamarinta , ko ba wannan fa karka manta ko ita wacece? Fitsarariya ce, yarinyar da kanninka ya so tamkar ransa har suka shaku, yarinyar da ta watsa kanta a banza , so plz ka fitar da tunanin nan, ka watsar da shi ka rufe idannuwanka a kyanta domin kyan dan maciji ne....




Toh fa readers kun ji dalilin Alaidine...........,,,,........ ku kanku kun san irin fitsarar Wujdane, toh aman ai Woujdane ba jahila bace🤔

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login