Showing 30001 words to 33000 words out of 42826 words
abin ya baka mamaki
Kawayen su Aisha sun yi gefensu daban sun dora tukunya a zuwan na yan matan amarya ne
Kamar daga sama wajen yama sosai kake jin murya sama sama na tashi, ana zubar da tijara kala daban daban, muryar ta mutun biyu ce hakan ya saka inna a hankali ta sauke su Wujdane daga jikinta ita a tunaninta baci ma suka yi sai dai ta ga Wujdane ta bita da ido, a ranta tana mamakin taurin rai irin na Wujdane har yanzu ta ki ta yi kuka sai dai zuru zazabi kuwa ya rufeta ruf
Inna na fitowa ta ga wata datijiwa ce da jan hijabinta, sai wata budurwa ita kuwa da bakin hijab, cikin shigarsu ta mutunci shigarsu ba wani tsiraici ko rashin mutunci a cikinta, sannan masha Allah a wanke kal da su
Budurwar ce ta yiwa inna kallo daga sama har kasa ta ja wani uban tsaki ta juya wajen datijuwar ta ce" gogo ai inajin wannan itace uwar yar iskar domin a yanda aka kwatantata ance kama da aljannu ne da su
Juyowa Gogon nata ta yi ta ce" ohoooooo aho itace, to yayi daman ke muka zo ganni, ke yanzu in ba rashin hankali ba, yar taki ta gama yawon anguwa anguwa gida gida, ance watarana bama a gida take kwana ba idan tayi daren yawonta, shine kuka yiwa yarona asiri kuka shanye mana shi har ya kasance baya ji baya ganni sai ita ko? To ta Allah ba taku ba domin Sabra aka aura masa kuma itace matar Lukmanu har gaban abada, mutanen banza mayu, idan ba son zuciya ba baku haifa min dan ba baku rainar min ba aman da anga yana da dan abin hannunsa hikenan an like mas har ana tarda hi wajen aikinsa dan a kara damke hi? Ai idan takamarka sauko wani a kan hanya ya kwana
Inna kam yau ta ga rana gannin idonta, a yau ta ga jarabawa kala daban daban, a hankali ta matso tana kokarin gannin ta kontar da wannan tarzomar, ta shiga lalaba su Mahaifiyar Lukman Sabra matar da aka aura masa aman sai tirjewa suke suna kara zubar da rashin mutunci suna zage zage , ba inna kadai ba harda Malan sai sun kama sunnansa su zuba rashin mutunci
Du taron jama.ar nan dake wajen bikin kawai an taru kowace na dauka da idannuwanta , da kunnuwanta dan ta ji dadin bayar da labari, ba wace ta yi yunkurin shiga, ba abinda ya kawosu kennan ba, shigarwa wani fada? Aa, inna baiwar Allah zuciyarta ta karaya haka hawaye ke silalo mata wani na korar wani tana sharewa tana kokarin basu hakuri kan su tafi
Wujdane ce firgigit ta mike zaune, ta sauke idannuwanta saman Aisha dake zaune jikinta na bari, tana son fita tana tsoron maganar anguwar nan nasu, mai za.a ce da su idan ta fita? Dama an yi masu sunna yau yau din nan idan ta fita ai sai a kara a sama
A hankali Wujdane ta yunkura ta mike, hijabin dake jikinta ta cire inda gashin kanta ya yi lambar a gadon bayanta da dan ribom dinta, doguwar riga ce aka yi mata ta atampa wace ta yi mata das a jikinta ta fitar da wani kyau nata, idannuwanta ba kwali aman kamar ta saka, lips dinta kuwa ainahi ma pink kolor ne ga cicije su da ta wuni yi sai suka kara yin ja suna sheki abinsu, idannuwanta sun rufe da wannan tijara da take tsintowa,
Yelemun kuwa tana daga labulen dakin ta ga du yan anguwar sai kus kus suke suna dariya kasakasa, yan matan amaryar kansu sun cakulu da su , innarta na faman ta tsayar da rogimar aman wa.innan mata biyu tamkar zugasu take
Yaye labulen dakin ta yi gaba dayansa ta fito ta karaso gaban mutanen su duka ta ja ta tsaya,
Idannuwanta ta dago ta yarfawa Sabra dake magana wace tsitttt sai da ta katse maganar nata kafin take ci gaba daga inda ta tsaya tana kara matsawa kusa da mahaifiyar Lukman
Ai gogo kin ganta, irin jan fatan nan karuwan kasashen waje an gama shaye shay............
......tsittttty kake ji maganarta ta katse, da sauri du aka kalo Wujdane wace ta dauketa da mari, du sai mamakin daman haka wujdane ta keru suke,
Gaba dayanku kowace ta tatara ku fice a gidan mu, walahi talahi yanzu yanzu ko na gwada maku na fi ku rashin mutunci yan kwal uba kai, Wujdane ce ta fada idannuwanta kyar a kan daga iyayen har yayan,
Gannin sun tsaya suna shewa ana tafawa ana kallonta irin an raina maka hankalin nan ya saka ta juya da gudu wajen murhu da ake dori,
Wujdane bata damu da zafin tukunyar da suka kuma dorawa ba ta ruwan zafin ta dora hannunta ta tunkude tukunyar, marfinta ta dauko ta shiga kwasar garwashin da yayi jajajir yana ci da itace ai kuwa tace da wa Allah ya hadata idan ba su ba
Nan da nan sai ihu da kururuwa ya tashi na jama.a haka suke fitowa a guje ita kuwa kamar sabuwar kamu tana nufosu tana dana masu ashar ranta a matukar bace tana fadin .......?
[3/27, 10:00 AM] +234 803 957 7698: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄
*23*
WRINTING BY *SAJIDA*
Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai,
*SAJIDARKU CE*
MARUBUCIYAR:
*YAR MAHAUKACIYA*
*DUK KARYAR KADA*
*DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA*
*NEMAN NA KAINA*
................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH....
Haka suka raba dare ba wada ta samu rintsawa a cikin su ,
Kamar yanda suka saba gidan inna tun karfe shida suka fito falo, nan fa suka nemi kayan aiki wanda Lami mai taya Mom shara da wanke wanke ta gama sallah tana jan carbi ta basu kayan aikin tana mamaki a ranta, amaren ne zankada zankada haka da su zasu yi aiki? Gum dai ta yi da dan bakinta gulma na cinta
Fitowa suka yi daga kicin din domin tare suka shiga ta fitar masu da kayan aikin harda na goge goge bayan shara
Falon Mom ba dai girma ba, hakan ya saka su rabuwa suka kamo gefe gefe suna shararsu
Aisha ta cire hijabinta ta ajiye nan kasan capet din inda Wujdane kuwa ta daure shi a tsatsonta dan su yi aikinsu cikin nutsuwa
Cikin kankannin lokaci suka hade sharar waje guda kafin suke raba abin gugar suka kamo tun daga lungunnan wanda rabonsa da hakan tun sallah
Daga masalaci suka sauko, kiran gagawar da Aba ya yi masu, Alaidine ne da Jamail sai Aba
Aba ke gaba, Alaidine na biye da shi a baya sai Jamail, kowanne da carbinsa yana dan ja
Zuciyar Alaidine cike take da tambayoyin kar dai a je Aba kiransu ne yayi su tafi da matan da ya kakaba masu? Aba kiran menene wannan ya yi masu haka? Lafiya tun karfe biyar ya umarcesu da yake abin hawa ne da su, gashi yanzu asuba na yi zaka ga musulmai na ta fitowa domin zuwa masalaci, dan haka yana bukatar du gabatar da sallah a masalacin anguwarsa dan yana son yin magana da su, abinda dai ya fi basu tsoro gaba dayansu shine aba ya kasa hakura har safiya ta yi ?
Suna shigowa gidan ya kara umartarsu da su je , wato su biyo bayansa ciki
Aba ya fara sako kafarsa falon da salama a bakinsa, domin koda ba kowa ya dace du musulmi zai shigo waje ya yi salama, balatana ya san Momyn yara da kuma sabko dan ta yi masa break, aman me, sai yan mata biyu yake ganni suna ta faman gugan capet
Da sauri Aisha ta janyo hijabinta a saman kujera ta zurmuka wanda hakan bai bata damar mikewa ba,
Wujdane dake zaune dangalgal saman nata ta saka hannunta tana ja , tana ja , gannin ba zai fito fa ya saka ta mikewa tsaye a hankali kanta a kasa , gashin kanta da aka yiwa parking har gaban goshinta ya zubo sosai daga gaban rigarta har ya fice tsayin wajen mamarta,
Zani ne a jikinta wanda ta tumurmure shi da hijabin, kokarin koncewa take harda zannin dan dimaucewa da gannin maza har uku wanda Jamail ne kadai ta sheda a cikinsu , domin ko Aba ita bata taba haduwa da shi ba
Kamar wanda aka dasa yake kallonta, gannin abinda take shirin yi ya saka shi sada kansa kasa sosai tamkar yana gaban hukuma kuma ya aikata laifi, tsaki yake ja can kasan zuciyarsa na wannan bata da hankali zata kuncewa mutane wani bakin zani, domin saman doguwar rigarta ne ta dora zannin Lami mai dati dan kar abayarta ta yi dati Aba kuwa tuni ya haye sama dan kiran Mom, Jamail kuwa juyar da bayansa ya yi tun lokacin da Aisha zata saka nata hijabin yana irga bugun zuciyarsa,
Lalalalala, na shige su yau nayi baci har haka , kai gajiya da bashin baci basa barin bawa sai sun bi shi, ohohoh ni yasu jikarsu har yayan nawa suka tafka aikin nan? Dan na san Lami dai ba guga take har can ba,
Tana yi tana karasowa domin sai a lokacin ta gama azkhar, danma jiki da sabo shi ya ta tashin domin an gaji iya gajiya
A tare suka kai kasa Aisha da Wujdane suna gaishe da Mom da Aba wanda a lokacin sun fahimci shine Mahaifin su Jamail
Amsawa yake cike da kulawa, yaran sun shiga ransa domin da gannin dan yannayin da suka nuna suna da tarbiya ya samu mai gaishe shi haka a tsugunen nan har kasa abinda baya samu wajen sauran sirikansa
Mom kuwa kamo su ta yi tana mikar da su tana amsawa , ta nufi kujera da su ta zaunar da su , babar kujerar dake facing din su Aban
Tana juyawa suka silale kasa saman capet din suka zauna irin zaman makaranta
A rayuwa idan Alaidine zai gaisar da mahaifiyarsa sai ya duka har kasa, wannan haka ya taso tun yana yaro bayan ya gama gaisar da ita a tsugune sannan yake zuwa ya rungumeta a jikinsa yayi dan lamo, baya taba daina hakan ko daya a rayuwarsa
Yauma hakan ne ya yi , daga karshe ya rumgumeta a jikinsa yayi shiru yana sauke ajiyar zuciya, uwa uwa uwa, ita ce mace kwaya daya da ya san idan ya rungumeta ba zancen cutarwa da zai biyo baya ko ta danna mai wani mugun abin ko idan rigimarsu ta hada su ta kiraye shi da *Shege*
Haka Jamail ma ya gaisar da kowa, kanna ya dan juyo wajen su Aisha da Wujdane, muryarsa a dan sake ya ce" aa, yau su Aunty Wujdane anyi kwannan gidanmu?
Mom ta yi murmushi ta ce" aa, gidanku fa? Kai ai ba yauba muka mika ka wajen yayanka, yau shima zai mika ka wajen matarka ai yanzu kuma yanzu zaka san an yaye ka da gaske,
Dan sinne kansa ya yi, wanda jin ance yayansa ya saka Wujdane dan dago da idannuwanta wajen mom inda take tunannin nan yake yayan nasa, sai kuwa suka hada ido, domin so yake shi sai ya tantance ta ya ga abinda ke kayar masa da gaba a wajenta
Wani mugun kallo, irin kallon kaskancin nan ne ya wurga mata, wanda a take a lokacin gabanta ya yanke ya bada bam, ya gama bata mata rai, bata wani dauki lokaci ba ta zabga masa wani uban harara ta kawar da kanta, ta mayar wajen Aisha da ta lalubo hannunta ta rike jikinta na dan bari, tsoro ne ya darsun mata a kasan zuciya na yanda Jamail bai ko kali inda take ba, baiyi mata wata magana ba
Mamaki kamar ya kashe shi, a kasan ransa yake tambayar kansa wai da ni take hararan nan? Ni ta harara? Aman lale yarinyar nan bata da kunya, shine zata wani juyan ido ita ga tsaurara ko? Zata gane bata da kunya ne
Aba ya gyara zamansa ya ce" asalamu alaikum warahamatulahi wa barakatuhu
A tare suka amsa salamarsa wanda hakan ya saka su bada tunaninsu wa shi,
Ya ci gaba" kamar yanda a jiya na yi maku bayannin yanda hulunci Allah subahannu wa.ala ya yi aiki a kan maganar auren da na dauro muku a jiya, shine zan dora da bayanaina a gaban mahaifiyar ku,
Alaidine, kai ne baba, sannan a rayuwa ka yi aure aure, a yanzu haka kana zaune ne da macen aure a gidanka , dan haka aure da zaman aure ba sabon abu bane a wajen ka, sai dai sharadin a nan shi ne, wannan aure da na je na nema maka ni mahaifinka, ba talar yarinyar aka yi min ba, ba sadakarta aka bani ba, aure aka nema nata aka bani cikin ikon Allah bisa hanyar da musulunci ya hukunta mana, Alaidine a jiya na fada yau zan maimaita, ban lamunce maka sakin yarinyar nan ba, kamar yanda ba zan tauyeka kara wani auren ba, Alaidine ka ji tsoron Allah , ka kare mutuncin kanka da na iyalinka, ka nemi lahirarka ka manta da du wani shirme
*Wujdane* Aba ya yi kiran sunnan Wujdane wada ta dago da kanta a hankali tana amsawa a hankali, can kasan ranta tana fadin" shi dinma auren ne da shi kennan,
ABA ya ce" wannan shi ne mijinki da aka daura maku aure jiya, shi dai aure ibada ne, wato hakuri hakuri da kawar da kai, da kaskantar da kai, ta haka zaka cima burinka cikin ruwan sanyi kin ji? Ki yi hakuri, ki karbi aurenki, ba yanzu zaku tare a gidanku ba, domin na fada masa tsarin gidansa ba na ajiyar mace biyu bane, ko ya kara wani ginnin a ciki ko da gidajensa ya saka a gyara guda ku tare kamar yanda aka shiga gyaran na su Jamail
Sai kai Jamail , ina so ka sani du dan adam Allah yakan jabartarsa ta hanya daban daban, idan ya yi hakuri ya jure zai ci ribar jarabawar cikin ruwan sanyi
Komi kake ciki ka mika lamarinka ga rabil izati, ka rungumi aurenka , kar ka wulakanta yar mutane, sannan yanzu ka fara shiga rayuwar auren ka yi kokarin shinfidata da kyawawan dabi.u dan kuwa abinda ka sabawa kanka da matarka zaka ga da kowace ma hakan ne, aman idan da fahimta da dadin rai zaka ga aurenka shine babar kyautar da Allah yayi maka ta saka nutsuwa farin ciki a rayuwarka domin aure ga wanda fa ya bi koyarwar ma.aiki ni.ima ne, nutsuwa ne, farin ciki ne, dan haka ina mai shawartarka domin idan kaima na ji wata baraka ba zata yi mana kyau ba daga kai har ni
*Aisha* nana Aisha, ki yi koyi da halayen mai sunnanki kin ji? Ki kasance mai hakuri mai biyaya kin ji? Karki raina mijinki ko abinda ya kawo maki, ki tausasa lafuzanki ki kyautata halayenki zaki ga da kyau a rayuwarki kin ji?
Amsawa take kanta a kasa, wanda har wani hawaye yake zubo mata a kumatunta,
Mom ta ce" Allah ya saka da alkhairi Aban yara, Allah ya biya mun gode mun gode
Aba yana amsa mata yana yi mata dan murmushi
Kiran Lami Mom ta yi
[3/27, 10:00 AM] +234 803 957 7698: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄
*21*
WRINTING BY *SAJIDA*
Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai,
*SAJIDARKU CE*
MARUBUCIYAR:
*YAR MAHAUKACIYA*
*DUK KARYAR KADA*
*DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA*
*NEMAN NA KAINA*
................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH....
Kallonta kawai inna take, inda Aisha ta fito da gudu ta ja ta tsaya itama domin du sai wani tsoro ya darsun masu kar a je ta haukace
Ba wujdane ta tsagaita korar mutane ba sai da kowa ya fice a gidan ta bi bayansu ta jawo dan kayuran gidan nasu ta rufo ta saki dan yololon labulen dake kara rufe gidan ta juyo da marfin tukunyar nan a hannunta da garwashin nan a ciki, ya dauki zafi iya zafi ko da kalo zaka gane
Tana shigowa tsakar gidan da sauri Aisha ta matsota da niyar karbe marfin sai dai ina, yayi zafin da ba zata iya kama shi da hannunta ba,
Da sauri inna ta karaso ta karbe ta juya tana ajiyewa ta juyo sai suka hade da Wujdane ashe biye take da ita zungwai zungwai,
Inna na juyowa Wujdane ta fada jikinta ta rukunkumeta, ta ja wani numfashi mai nauyi,
Innna ta rufe idannunta, da sauri ta ciro Wujdane a jikinta ta dagota, murya a raunane ta ce" Wujdane ki yi kuka kin ji? Idan kana jin ciwo irin haka kuka kake yi sai ka ji sasaucin zuciyarka, ki dan zubar da hawaye koda kadan ne sai ki ji kin saku Danine,
Kyafta ido kawai take, can ta dafe kanta ta ce" inna kaina ciwo, sannan ta dafe kirjinta ta ce" inna nan dina ma ciwo, inna ina jin ciwo sosai
Inna ta rungumota jikinta sosai, a hankali ta ce" kin san Wujdane, muna sonki fa, kar ki yi tunanin iyayenki basa sonki, da farko halayenki muka guda, daga baya muke jin tsoran yanayinki, aman karki dauki wannan abin da ya faru a yau ki kakabawa zuciyarki kin ji? Ki dauki hakuri ki sakawa ruhinki ki yi imanin cewa kadarar ki ce, Allah ya rubuto haka zata faru ne da ke Wujdane, ba wai dan mun tsane ki ba, kar ki ji haushin mahaifinki, ni na tabata idan ya dawo zai zo mana da dadadan albishir domin Wujdane kin ga tun ina yarinya nima, yake kula da ni, mutun ne mai son mutanensa yana fita hakinmu, ki yi hakuri kin ji?
Sai a wannan lokacin zuciyar Wujdane ta karaya, wata zufa ta karyo mata, bugun zuciyarta ya karu, ai kuwa sai ga hawaye wasu na korar wasu, ta buda baki da niyar yin magana sai kecewa ta yi da kuka, wanda hakan ya yiwa mahaifiyarta dadi, ko ba komai zata samu sasaucin zuciyarta
,Alaidine,
Tamkar mahaukaci haka ya shigo gidansa, yana tsayar da motar ya bude ya bar wayoyinsa da komai harda su passport dinsa da yake da niyar yin tafia a ranar,
Falonsa ya ratsa ya fice sama ya nufi dakinsa na can kurya ya shige ya rufo yayi ruf da ciki
Tunani yake so yayi, so yake ya tsayar da tunaninsa, so yake ya gane a wani yannayi yake ciki so yake