Showing 6001 words to 9000 words out of 42826 words
rayuwa kai shaida ne, a kauye ma an hana ni zama bale ita a birni? Malan kana gani yaran anguwar nan dan dole suke ce mata MaMa, idan rigimar Wujdane ta fita nesa ba lale ne a yi hakuri da ita ba, ita kuwa ba zata iya mayar da komai ba komai ba ta kawar da kanta har yanzu tamkar wata yarinya karama
Inna ke mitar nan ta dage kan kawai kar ma a soma kai Wujdane Makaranta
Malan ya dago da kansa yana sauraronta, shi kam yana mamakin halayar mata har yanzu, innar yara dai ba wata yarinya karama ba aman cikin ikon Allah du girman mace ana yi ana tarota ne, cikin tausasashiyar murya ya ce" haba innar yara, idan fa hakan na cikin adu.armu na ta nutsu? Ke ganau ce ba jiyau ba Wujdane rabonta da wuni a gida har an manta cikin ikon Allah yau ta farka da muradin komawa makaranta sai a jaraba a gani, ina mai yi miki nuni da a kulun kwanan duniya adu.arki wa Wujdane ita ce abar so ba magana ba, sai mun dawo
Haka ya saka kai Wujdane na biye da shi da Aisha Bayan ta saka nikaf dinta, inna ta yi masu Allah kiyaye ta shiga dan aikacen aikacen cikin gidan cike da zulumin yanda za.a kaya da yarta
A makaranta Malan ya yankawa Malan lamunu kudade wa.inda dole a bayar idan dai ana bukatar Wujdane ta ci gaba da daukan karatu a aji
Bayan dogon nazari ya basu lokaci wanda da yardar Allah zai dawo da wa.innan kudade sannan ya nemi alfarmar ta fara daukan karatu kafin ya cika alkawari da yardar mai duka
Malamin mai mutunci ne, sannan ya san irin kwazon Wujdane, duda yana tsoron dayan halin aman ya yarjewa Malan Aminu ya yiwa Wujdane rakiya har kofar aji sannan ya koma kasuwa dan bubuga abinda ya samu
Du cikin ajin ba mai nikaf, sannan kowa dake zaune sai surutu suke,
Can gefe Wujdane ta samu ta rakube ta sada kanta tana dan juya bironta
Shiru kake ji ajin ya dauka hakan ya saka ta dan dago da kanta,
Malam yusuf ne ya shigo mai koyar masu maths
Rubuce rubuce ya fara a allon makarantar cike da kwarewa yana yi yana kwatanta masu sosai da sosai yanda zasu fahimta
Juyowa yayi yana tambayar ko da wanda bai fahimta ba? Nan ya hango wujdane zaune da nikaf
Cikin yaren turanci ya ce" wannan mai nikaf din fa? Shin bata san dokar makarantar ba cewar ba.a shiga aji da nikaf???
Shiru Wujdane tayi tamkar bata wajen, ko bata san abinda yake nufi ba
Wata yar matashiya mai suna Salima take fada masa cewar bakuwa ce mai yiwuwa bata san abinda yake fadi ba, domin Malan Yusuf akoy rigima sosai bashi da sauki
Cikin bacin rai ya fara fadi yana nufota da hausa cewar" idan har bata iya turanci ba uban me take nema a school din nan kuma ajin nan? Malama ki cire nikaf din idannuwanki mu nan bamu taru a nan dan fuskarki ko wani abin ba,
Cike da kunan rai ta kai hannunta da sauri dan kar ya cire mata ta cire nikaf din kanta a kasa
Tsaki ya ja yana fadin" useless kawai
A hankali Wujdane ta dago da kanta, wani banzan harara ta bala masa wanda ya saka idannuwanta suka yi wuluk da su , ciki ciki take gunaguni wanda Allah kadai ya san mai take fada, ta kada kai ta buda litafinta da niyar rubutu
Sam malan Yusuf bai gani ba, aman daliban da suka juyo kowace kallon mamaki take yi mata, kasa kasa Aisata ta cewa makociyarta" ke kinga wata tamkar ba mutun ba? Ji fa farin fuskarta ko dai wata hoda ce haka ta shafa bayan an hana mak up a makaranta????
[3/27, 9:58 AM] +234 803 957 7698: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄
*07*
WRINTING BY *SAJIDA*
Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai,
*SAJIDARKU CE*
MARUBUCIYAR:
*YAR MAHAUKACIYA*
*DUK KARYAR KADA*
*DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA*
*NEMAN NA KAINA*
................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH....
Haka kuwa suka yi suka fitar da sauran jama.ar nan suka bar daga Wujdane sai Balki
Mairo na fita ta shiga surfa sauki ta dauki adaidaita ta yi masa kwatance har kofar masalaci baba wanda Malan kan je ya bayar da karatu manya manyan mutane da du talata da yama yakan yi hakan
Tana sauka ta nemi gu ta rabe, ita bata ma san ya zata yi ta samu malan din ba, sannan jama.ar dake kai kawo ba wasu kananan mutane bane bale ta nemi alfarmar a yi mata magana da Malan
Can dai tana zaunen nan wani dan saurayi fari dogo ya zo shigewa ,
Da sauri ta mike ta ce" bawan Allah dan Allah ka ce da malan yarsa na kofa na yi masa magana
Dan dakatawa yayi yana kallonta, a firgice take da alama ba lafiya hakan ya saka ya shiga cikin masalacin cikin nutsuwa ya yiwa Malan dij magana
Cike da mamaki Malan ya fito yana ayana yayansa basu taba zuwa nemansa ba du rintsi, wannan ya tabata ba lafiya ba
Yana fitowa Mairo ta zube jikinta na bari ta kwashe masa komai yanda aka yi ta fada masa ta dodoka rantsuwar cewa ba Wujdane ce ta fara tsokanar ba
Malan baima san mai zai ce da ita ba, cikin sasarfa ya yi mata hani da fadawa Inna, sannan ya juya cikin masalacin dan yi masu salama
Wannan dan saurayin ke kallon yannayin malan, daman akoy shakuwa sosai tsakaninsa da malan, sarai yana mutunta shi domin shi dai bai taba gannin ko jin wani abu marar dadi a tare da malan
Mikewa yayi da sauri ya biyo bayansa gannin yanda yake tafka sauri
Cikin daga murya ya ce" MALAN, MALAN , domin shi har ya fara shesheka bazai iya irin tafiyar nan ta malan ba
Dakatawa Malan ya yi ya juyo, cike da mamaki ya amsa da " na.am *JAMAIL*?
Karasowa Jamail ya yi ya ce" malan sai na ga kamar ba lafiya ba, ka yi hakuri haka kawai ina sonka a raina malan, Allah dai ya sa lafiya?
Murmushin yake malan din ya saki, shi kansa bai san lokacin da ya furta " police station na hanyar yan Babura zan je
Kara matsowa Jamail ya yi cike da mamakin mai zai kai malan can, wajen aikin yayansa ne, baban office ne yayansa Anwar ke jan wajen , aman ba zai yi masa tambayar mai zai je ya yi ba sai dai ya ce" Lah ai wajen aikin yaya ne, yaya Anwar din nan? Shima yana zuwa nan din ranar lahadi yana daukan karatu
Murmushi malan yayi ya ce " masha Allah Jamail, masha Allah
Dan dakatawa ya yi, shi bai ce wani abin ba , shi kuwa jamail haka kawai ya ga ba zai iya barin malan ya tafi haka ba
Jamail ya ce" Malan mu tafi na kaika mana, da nisa sosai kuma ka ga kafin ka samu abin hawa a anguwar nan an hana motocin haya shigowa sai ka fita sosai wanda a kala zaka yi tafiyar awa ko fi wai danma kana saukin nan, dan haka mu je na kaika dan Allah
Ya karashe yana mai hada hannayensa waje guda
Ajiyar zuciya malan ya saki ya ce" mu je Jamail
Juyawa Jamail din ya yi malan na biye da shi dan zuwa gidansu ya dauko mota
Malan dan dardar yake a bayan Jamail, bama zai iya daga kansa ya karewa ginin katangar kalo ba bale har ya ga tsayinta, da alama daga ciki hawa hawa ne, wani irin zane ne aka yiwa ginnin daga kofa wata fulawa manya manya, kofar shigar kuwa glass ce, irin glass din nan da bata fashewa ko da bindiga sai bomb, sannan kalar blu mai duhu ce ba.a gannin mai ficewa,
Wata yar camera ce a jikin kofar daga sama wada ke haska mai shigowa da mai fita komai da ya shafi kofar gidan,
Ham Malan ke kallon wannan gini kaf anguwar bai ga ginnin da ya kai nan tsaruwa girma shiga ido ba, wai baima shiga ciki ba , kennan nan ne gidan yayan nasu da Jamail ke yawan zuwa yana wuni domin yayan nasu na yawan yin rashin lafiya,
Yatsarsa ya dora kan wani abu, babar yatsarsa , sai da abin yayi zuzu scan sannan ya bada wani pippp sai kofar ta budu
A hankali malan ya daga kafarsa ya saka ya bi bayan Jamail bakinsa cike da adu.o.i yana mai fatan Allah ubangiji ya datar da mu a janatul firdaus, wai wannan gidan duniya ne?
A gaskiya fadin tsaruwar cikin gidan nan bazai yiwu ba, just ka kiyasta iya hangen ka ka saka a ranka ya fi gaban hakan, gaba daya ginnin tsarin fallon ba a kasa yake ba a tsakiya yake, Malan tsoro ne ya rufe shi ya ja ya tsaya yana tunanin wai mai yake haka ne? Ya biyo yaro haka kawai bayan ga Wujdane dinsa can a rufe????
Lalalal broth, yanzu ka dawo mu kuwa yanzu zamu je ai wajen aikin naka, ka ga Malan ne wanda ke bada karatu a masalacin yaya, shine zai je na shigo na dauki mota na kaishi domin da nisa
Matsowa Anwar yayi yana dan dukawa yana mikawa Malan hannun irin girmamawar nan yana gaishe shi cike da mutuntawa
Malan yayi mamakin tarbiyar yaren nan, mafi yawancin yayan masu fada a jin nan sukan dauki talaka tamkar wani abin kyama aman wa.innan yaren sun mutunta shi sosai, yayi murna gannin hakan
Har Anwar ya juya zai fice ya dawo ya ce" Ni malan, lafiya zaka je can office din? Domin na fito idan abin sai an ganni ne kar ku je ku wahala sai na baku lokaci gobe da safe insha allah ko???
Cike da fargaba Malan Aminu ya dago kansa yana duban Anwar, hannayensa ya hade waje guda ya ce" yaro kar dai ka ce min sai kana nan za.a iya sakin mutun? Yarinyata ce ta yi fada aka kaita tana wajen naku abokiyar tafiyar tata ta zo tace min ance sai iyayenta sun zo? Yaro idan sai gobe ai sai dai nima na je kofar wajen aikin mu kwan tare da safen sai mu shiga gidan tare dan ban san ya innarsu zata dauki zancen ba
Malan ya karashe yana dan sada kansa kasa
Gaba daya Anwar ji yayi ba dadi, kansa ya dafe tabas cikin yan matan nan biyu ne, tausayin malan ya darsun masa a zuciyarsa har ya fara tunanin da shi ne da ya zai yi? Da dukan alamu kuma Malan din a ganninsa ba wani abin kirki a hannunsa hasken alkur.ani ke kara cika haibarsa a idannuwa,
Juyawa ya yi ya kali Jamail ya shagwabe fuska tamkar zai saki kuka ya juya falo yana tunanin shi da ya zo ne dan gannin jikin broth dinsa
Please yaya karka bar mace mai rauni dan kawai rigimar fada ta kwana a cel, plz mu tafi yaya, cewar Jamail yana hade hannayensa waje guda
Kai Anwar ya dan girgiza ya ce" Bismillah malan
Ya yi gaba ya budewa Malan gidan gaba shima ya zagaya dan yayi driving, dar Jamail ya shige baya yana sasada kai dan kar a kore shi
Suna karasawa direct office dinsa ya karasa da su Malan , ya yi umarnin a fitar masa da su Wujdane a kawo su office
Har yama ta yi sosai cike da mamaki suka shiga domin fitar da su
Balki ta ci kuka har ta gode Allah, Wujdane kuwa ta ja hijabinta dan sama sama ta kuma rufe daga goshinta, ita damuwarta daya innarta da kuma Malan
Ku fice mu tafi , wani bakin police ya yi musu tsawa
Cike da dan fargaba ta dago da idannuwanta, ta sauke su a bayansa ya juya baya zai fice yana nufin su bi bayansa
Balki ce ta mike jikinta na rawa ta ce" wujdane kar mu bi shi wly ance fada yayan mutane suke yi fa???
Wata harara Wujdane ta banka mata ba tsoro ko dar ta bi bayan shi duda a kasan zuciyarta banda adu.ar tsari da take ita kanta a tsoracen take aman bata nunawa ko daya
Bayan ya shiga suka shigo su ma, kanta a kasa bata daga bama bale ta ga mutanen da ke ciki
Anwar ya ce" Malan wacece yar taka????
Malan ya nuno Wujdane ya ce" ga tanan
Da sauri Wujdane ta dago da fuskarta tana jan hijabinta baya, bata taba jin kunyar mahaifinta kamar na yau ba, kwarai da ake cewa yaro ke jawa iyayensa, yanzu ko su Yayanta Abdul fatah basu kawo malan police station ba sai ita? Wani abin bai taba kawo shi ba yau sanadiyar ya haifeta gashi tsamotsamo a tsaye a wajen,
Sada kanta ta yi hawaye na ziraro mata wanda haka kawai ta ji shi na mahaifinta , bata san nawa aka yanka masa kafin ya fitar da ita daga wajen nan, wani haushin Balki ya tirnuke ta ta dago da kanta ta Bankawa Balkin harara na tsana ta ja dan karamin tsaki
Malan ya girgiza kai, ya juya wajen Anwar ya ce" wato yaro, cikin ikon Allah ka haifi da ne baka haifi halayensa ba, ita dai wannan yarinya idan ka ga mahaifiyarta sai ka rantse da ba ita ta haifeta ba , domin fadima akoy hakuri da kawar da kai,
Wujdane tunda ta tashi ta tashi da rigima daidai geargwado, cikin ikon Allah bata da hakuri idan dai ka shiga sabgarta toh zaka tarar, a kulun adu.a muke binta da ita Allah ya sanyaya, yau anyi abin kirki aman sai yamacin ya karashe da haka,
Ja nunfashi ya ce" Alhamdulilah, na san Allah na boye wani lamari a tare da ita, a kulun ina gode masa da ya malaka min ita, sannan ina adu.ar Allah ya shiryar min da ita ya saja mata nutsuwa a duk inda take
Cike da kaunar datakon Malan Anwar ya bada umarnin Balki ta fice ta koma itama gidansu, bayan dogon kashedi da gargadin kar ya kuma gannin kafar wata cikinsu a police station din nan domin ba zasu kwashe lafiya ba,
Haka Balki ta juya har gudu take ta tafi tana godewa Allah da ya takaita tashin hankalin nan
Kallon Wujdane suke gaba dayansu, shi Jamail gaba daya ta gama birge shi, yana son ya ga macen da bata daukan raini, shi kuwa Anwar a wani hali ya shiga, yarinyar ta yi masa fiye da tunanin bawa, kallonta yake a ransa yanai mata adu.ar samun nutsuwa ,
Cike da farin ciki Malan ke yi masu godiya wada ya umarce ta da ta yi wa Anwar da Jamail godiya
Dago da kanta ta yi bayan ta goge fuskarta wanda ya baiwa hannunta damar fitowa , yanda farin fuskarta yake haka na hannunta , faratunanta dogaye ne tsar ,
Idannuwanta ta dago a karo na farko ta sauke su a fuskar Anwar, gashin idannuwanta sun jike da hawaye hakan ya saka suka dan harhade suke kyali tsaf bakinsu ya fito radau, sai zagayen idannuwan ya yi jajajir kamar ya kode domin ba wani kwali a idon,
Murya na rawa ta ce" jazakallah
Bai san lokacin da ya lumshe idannuwansa ba, tamkar sarewa haka muryar ta yi masa rada a kunensa, a hankali ya furta" wa.iyaki
Ky din ya mikawa Jamail dan ya kaisu gida bayan an sha darga da Malan kan abin ya yu yawa, da kyar suka shawo kansa ita kuwa wujdane sai kumbura take tana karawa,
Nan suka bar Anwar zaune ya jinginar da kansa yana ta tunanin to ya aka yi basa kama ko kadan da Malan din,, ?????
Jin tunanin yarinyar zai dame shi ya saka ya mike ya fita ya harhada takardu ya fara dubawa yana kara zagaye police station din
Tafe suke malan na kara yi mata nasiha, cike da kula , Jamail kansa yayi tsam yana sauraro yana mamakin du abin nan da ta aikata malan yanai mata nasiha, uhum da wani uban ne ba mai hana shi dakata
Har suka karaso gidan wanda yara yu suka biyo motar suna ihun jirgi a anguwarsu domin irin motar nan ce mai tsayin nan,
Motar na tsayawa Wujdane ta bude ta fito a bayan ai kamar an watsa su suka fara guduwa ta ko.ina suna ihun walahi *MaMa* da malan ne a motar, du suka warwatse dan mai dukan yaro ce va zata saurara masa ba
Yauma bata tsaya cin abincin daren da su ba, ta fada dakin ta shiga baci
Malan bai fada ma inna ba, sannan bai fadawa kowa maganar ba bayan a titi da Mairo ta dan barbada cewar Wujdane na rufe sai ta yi wata , ganninta ta dawo ya saka ake zuwa har gidan su mairon anai mata ihun makaryaciya ta ji kunya
Da safe kofa ka san fitarta bayan ta shaidawa Aisha cewar ta tafi makaranta dan ta samu ta gama rubuce abubuwan da ya kamata bata da a litafinta
Sai da Malan ya fito take shaida masa ai ta fice makaranta da ya tambaya
Dan jim ya yi sannan ya fice har inna na tambayar lafiyar malan kuwa du wani sukuku take ganinsa???????????????????????
Konci tashi yau wajen sati...........
[3/27, 9:59 AM] +234 803 957 7698: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄
*09*
WRINTING BY *SAJIDA*
Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai,
*SAJIDARKU CE*
MARUBUCIYAR:
*YAR MAHAUKACIYA*
*DUK KARYAR KADA*
*DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA*
*NEMAN NA KAINA*
................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH....
Wujdane dake konce mamaki fal cikin ranta, mamakin yanda aka yi su malan suka sake da wannan bawan Allah, har wani dan uwanta inna ke cewa, a ina ya zama dan uwan nata????
Cike da jin haushi ta fito jin inna na kuma kiran sunnanta, wannan karin ba nikaf din aman da hijab dinta har kasa
Silbar wajen Malan da a ciki ake zuba masa ruwa idan ya zo domin ya fi kowanne haske ta dauko , ta bude randar cikin dakin inna tsaftataciya da kulun sai ta wanke ta ta juya wani ruwa sanyi karai da kanshi ta zuba masa ta kawo ta ajiye masa
Can gefe ta zauna ta turo baki ta hade fuska ta sada kanta kasa,
Kallonta Jamail yake can kasan zuciyarsa dariya tamkar ta kashe shi, shi kam ba zata bashi wuya ba domin yana zaune da wanda ya