Showing 33001 words to 36000 words out of 42826 words

Chapter 12 - BANI DA ZABI COMPLETE HAUSA NOVEL

23 Aug 2025

640

ya farka a mafarkin da yake , aman ina ba hali, zuru ya yi ya zubawa hoton boy ido dake mane da jikin bangon dakin, a yannayinsa kamar wanda yake son fitar da wani abin a jikin hoton , ya dauki lokaci mai tsayi wanda shi bai furta um bare um.um ba



Jamail ne zaune gaban tv yana kallo, duda a yau din nan ya tashi da wata faduwar gaba, aman yana dan jin karfin jikinsa kadan hakan ya saka shi mikewa ya watsa ruwa ya zo ya saka tv gaba yana kalo,


Direba ne ya tsayar da motarsa a harabar gidan Alaidine, Mom ta fito inda Aba ke tsaye yana jiran karasowarta ya fito daga cikin masalaci


Tana fitowa ta karaso fuskarta cike da tambaya,

Aba ya gyara tsayuwarsa, ya shiga shaida mata abinda ke faruwa,

Gim tayi tana sauke ajiyar zuciya, ta san da kwannan zancen Alaidine fir ya ki Jamail ya auri Wujdane dan yana shaida bata da tarbiya, sai gashi abin ya kasance a shi, wato dai Wujdane ta gidansu ce gwara ma su daina jayaya da hakan

Mom ta fara shiga Falon inda ta tarar Da Alawiya na zaune saman kujera tana shan fruits, ta sha kananuwan kayanta domin ana dan zafi zafi a garin, tana kalon series a tv

Mom ta yi salama ya kai sau hudu hakan ya saka ta shiga ,

Ido hudu suka yi da Alawiya dake zaune dangalgal ba wai dan bata ji salamar bane aa, cikin tsarinta kenan idan bata san da zuwanka ba ba wani tarba da zata iya yi maka

Gannin Mom bai saka ta irin zaburan nan ba, na gannin sirikinka a cikin gidanka, saima wani kara kalonta da tayi ta ce" au da Mom ce? Haba ni da naji salamar a raina nake fadin ko waye haka da wannan lokacin bayan lokacin hutu ne???


Mom ta danyi murmushi, ta ce" Alaidine fa? Yana gidan ne?


Alawiya ta dan daga kanta benensa, ta dawo da kan nata ta ce" toh ni dai na ga motarsa kuma na ji kamar budewar bangarensa, aman ban san ko yana nan ba, kin san baya son ana shiga lamarinsa idan har ba shi ne ya jawoka ba


Da mamaki Mom ta gyada kai ta koma ta yiwa Ba iso kawai , wanda yana shigowa Alawiya ta gaisheshi shima ba a wani mutunce ba , ya amsa yana kawar da kansa suka haura sama falon Alaidine


Ratsawa suke domin du dakunan da ya shige kawai a bude ya bar su, suna yi suna salama, har suka karasa dakin da yake zaune

Salama Mom ta yi ta maimaita, hakan ya saka shi dago da kansa yana amsawa fuskarsa na kan fuskar mahaifiyarsa

Kokarin mikewa yake yana fadin" Mom, ke ce??


Karasa shigowa suka yi gaba dayansu, Mom ta zauna daf da shi ta kamo hannunsa na dama da ta ji ya gauraye da zafi,

Aba ma waje ya samu ya zauna, inda gaba daya suka yi shiru ba wanda ya furta ci kanka

A hankali Alaidine ya dago da kansa ya sauke kallonsa kan Mahaifinsa, murya a shake ya ce" aman aba, bayan na sanar maka ga dalilina na kin ta shigo zuri.armu why Aba zaka aura min ita? Ita ce fa abinda Jamail yafi so a duniyarnan bayan ku, Aba ka ga irin yanda yake ba ci ba sha ba wani walwalar kirki dan kawai ta furta masa bata son sa ina da ya ji wannan labarin? Aba kuma bama wanu daban ba sai ni Aba? Ban wani takamaiman santa ba aman na ji bana sonta a cikin gidan kanina ko a abinda ya shafi yan uwana sai gashi Aba ka hada ni da ita? Abana la bani dama na yanke igiyoyin nan da ka daura min Abanna,

Elhaj Kadri bai katse shi ba, sai bayan ya gama, a gankali cikin muryar kontar da hankali ya ce" ni Alaidine danme yasa ka tsani yarinyar nan haka bayan kaima ka furta yanzu cewar bata yi maka komai ba?


Alaidine ya sauke ajiyar zuciya ya ce" Aba yarinyar nan munafuka ce, bata da nutsuwa, Aba ta wulakantar da kanta, sannan ai Allah ma yayi mana nuni da mu zabawa yayanmu iyaye na gari Aba


Aba yayi murmushi jin ta inda Alaidine ke son bilo masa, ya ce" ka san menene Alaidine, yarinyar nan ita ce ta biyu da na je da kaina nema maka aurenta har na dauro maka cikin ikon Allah, mahaifiyar Huzaifa ka saketa dan kawai ta jefe ka da kalmomi bayan kai namiji ne, kayi karatu mai zurfi kana cikin kara yi , a musulunci an fada mana cewa mace ana yi ana tankwasota ce, a nasarance an gwada hakan, aman cikin ikon Allah sai ka zamo wani mai auri saki wanda matan da ka aura ni ban taba kawowa raina cewar wai zaka yi hakan ba, to ka ga dai Wujdane amanata ce, ni kuwa zan gargadeka da babar murya, walahi Alaidine karya kake ka mayar da Wujdane karamar bazawara, idan na kawo maka ita gidanka karshen ki ka gutsutsura namanta, aman fa na hane ka, na haramta maka sakinta Alaidine, idan ka kyautata zamanka da ita ka so kanka da nutsuwarka idan ka muzanta kuma ka san hukuncinka

Mom ce ta dago da kanta gannin Aba maimakun ya lalaba Alaidine din aa, sai fada yake surfawa, yannayin tausayi ta yi da fuskarta ta ce" Aban Alaidine....

Hannu Aba ya daga mata ya dawo da hankalinsa wajenta, ya ce" na gaji da zubawa yaron nan ido yana auri sakin nan, yau da ace yana da kane mata aka yi masu haka yaya zai ji? Baya tunanin haihuwar mace a nan gaba? Ke kar na kaiki nesa Momynsu baya dora abin a kanki yayi tunanin idan hakan ya same ki yaya zai ji?

Da sauri ya dago da kansa , daman idannuwansa sun gama rinewa, shi ya tsani ana jan magana guda, aman shine Abansa zai saka momynsa? Shi du duniya ai ba wanda ya kai momynsa zama mutumin kirki, sannan ira kadai ce macen da ya sani ba munafuka ba,

Mikewa Elhaj Kadri ya yi ya fice, wanda bai tsaya ko.ina ba sai bangaren da Jamail yake, zuciyarsa cike da tausayin yayan nasa, aman idan bai fitowa Alaidine ta bayan gida ba ya aika ya saki Wujdane a yau yau din nan domin bata ce masa komai,


A hankali Mom ke kontar masa da hankali, wanda yana sauraronta a kasan zuciyarsa yana ayana yanda zai koyawa yatinyar nan hankali, Mom ta ce" idan ma kana zarginta koda idannuwanka sun nuna maka da ba mai zama dam bace, ka yi hakuri ka rungumeta sanadiyarka sai ka ga ta shiryu son, yau da ace mahaifinka yayi watsi da ni, da yanzu bansan inda kake ba, mai yiwuwa a watsar da mu gaba dayan mu a raraba mu,
Ta karashe zancen tana kallon kasa tana gannin tamkar yanzu ne abin ke sake faruwa da ita

Tausayin mahaifiyarsa ne ya tsarga masa zuciya, a hankali ya dora kansa saman cinyarta ya ce" Mom, ke kadara ce, karki hada kanki da wannan banzar

, tana shafa sumar kansa tace" kowa ma kadarar ce ke afku masa kafin daga bisani idan yaci gaba to wannan kuma yana neman izgili, sannan yau kowa da ka ganni yana son ya zama dan mutunci, yana son ya rayu a cikin mutunci, karka yi gagawar yanke hukunci dine,, ka bi mahaifinka a hankali ka ga dai yanda ya dauki zafi da kai, dan haka ka faranta masa kar ku fito rana fa,

Shi dai sauraronta yake, sannan abinda ya sani ne bai isa ya rabu da yarinyar yanzu yanzu ba, a hankali idan hankalin mahaifinsa ya konta zai nemi ya raba auren nan, shi fa ba zai iya zama da yarinyar da kanninsa ke so tamkar hauka ba, shi yama zai iya wannan cin amanar, ga yarinyar fitsarariya ai idan ta samu hakan birgeta ma zai yi


Sosai Jamail ke kuka rungume a jikin mahaifinsa, wanda ya gama jin abinda ya faru, harma Aisha na zaune a matsayin matarsa Wujdane kuwa matsayin matar yayansa, ya sani ne shikenan Wujdane ta kubuce masa, domin da wani ne aka aura mata shi sai yayi jiranta, aman sai ya fado kan yayansa kuma a yanda abansa ya fada yayan nasa ya tsaneta tamkar ransa, ya san wanene Alaidine, idan ya tsani abu ya fiya zurfafawa a lamarin hakan ya saka shi jin tsoro matuka a kasan zuciyarsa, koma wa zai auri Wujdane dinsa baya so ta wahala, duda Alaidine ya kasance wanda ya raine shi, ya bashi tarbiya, ya kaunace shi, ya bashi dukan bukatu na nan gidan duniya, mutumin da ya sha salwantar da farin cikinsa wa su, ya san ba wani rabo kuma tsakaninsa da Wujdane, ya hakura da Wujdane, aman zai roki alfarmar kar a wulakanta masa da wujdane, hakan ne ya saka shi fashewa da kuka ya rungume mahaifinsa,

Sosai yayi kukansa har ya gode Allah, kafin yake tsagaitawa yana share hawayensa, a hankali ya ce" Abana, Allah ya sa hakan shi yafi zama alkhairi, Allah ya saka maku da alkhairi ya kara lafiya, Allah ya biya duniya da kiyama

Wani irin abu ne ya saukowa Aban wanda ya matukar kashe masa jiki, Jamail, jamail, ba dai hakuri ba, jamail ba dai daukan girma ba, haka Aba yayi ta lalaba shi, ya samu ya dan ware kafin yake iza keyarsa ya kimtsa suka fice tare masalaci


Bayan salar magariba, sosai ake ta rabon abincu na sadaka da godiyar allah, Aba ne ya zubawa Alaidine ido gannin bashida niyar tayar da motoci a je daukan amaren bayan gidan cike yake da jama.a, wanda alaidine din na can yana fama da Alawiya wace sai a lokacin ta ji mijinta yayi aure ta tare shi da koke koken sam bata san zancen ba, yayi zuru yana kallonta........
[3/27, 10:00 AM] ‪+234 803 957 7698‬: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄





*22*


WRINTING BY *SAJIDA*



Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai,

*SAJIDARKU CE*


MARUBUCIYAR:

*YAR MAHAUKACIYA*

*DUK KARYAR KADA*

*DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA*

*NEMAN NA KAINA*

................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH....



Idan Alaidine ya tanka mata toh tabas bangon dakin nan ma ya tanka mata, kawai kallonta yake yana mamakin yaushe ta ga damarsa har haka? Dan yayi aure sai me? Ita da ya je aurenta yayi mata alkawarin ba zai kara wata bane? Ko an gaya mata auren soyaya ne da zai ji tsoron fada mata? Jan tsaki yayi ya lura idan ya biye mata zata ga damarsa ne hakan ya saka shi mikewa ya lulobo lambar wani yaronsa samir

Samir ya daga cikin mutuntatawa yake gaisar da Alaidine

Alaidine ya ce" kana ji? Wajen da muka je da safe aka daura auren nan ka samu mutane ku dauki motoci a je a dauko amaren, gidan Aba can zaku je a hada ku da mutane, sannan idan kun dauko gidan Aban zaku kai su ka ji?


Samir ya amsa masa yana mai fadin " yanzu kuwa oga, daman nace wai mutanen nan da suka dauki labarun daurin auren nan, suna jiran saka hannunka dan su gabatar a gidan tv

Cikin karaji ya ce" kar su soma, du wanda ya yarda ya yadani a wannan abin sai na yi shara.a da shi, , kittt ya katse kiran yana huci


Shiru Alawiya ta yi tana kallonsa, a hankali ta fice dan amsa kiran wayar mamarta


Toh fa amare kam sun fito a amare domin inna baiwar Allah zaginewa ta yi ta shirya yayanta, da wasu abayoyi bakake wa.inda ta ciro a cikin akwatunnan nan, akwatuna dai na Aisha ne wa.inda aka yi mata na lefe daga wajen Jamail, abayoyin an mugun kawata su da duwatsu farare tun daga wuya har kasan dinkin sannan a hannuwa da bayan rigar, haka mayafansu gaba daya duwatsu ne masu kyalin gaske

Turare ta fefesa masu, ba wani mak.up a fuskarsu su duka sannan ba fuskar wace take fara.a

Ana haka su Malan suka shigo da su Hamza du da alamar gajiya a tatare da su

Tabarmar leda katuwa inna ta shinfida a tsakar gidan wace du suka zazauna, wajen ya dauki shiru

Ajiyar zuciya malan ya sauke sannan ya umarcesu da su yi adu.o.i inda Hamza ke ja suna amsawa gaba dayansu

Bayan an gama Malan ya dago da kansa yana kallon su Wujdane da Aisha, ajiyar zuciya ya kuma saukewa kafin yake gyara zamansa ya ce" kunga sha.anin Allah ko? Wujdane da Aisha a wannan lamari ni bani da ta cewa sai dai kawai kamar yanda Allah ya juya abin nan haka Allah ya sa alkhairi ne aka yi, wato duniya bawa ke haukansa sai ka ga mutun na tsara idan nayi kaza sai na yi kaza da rayuwana, du a cikin hakan yana tsarawa Allah na zartar da yanda ya zana tun ran gini ne,
Shi aure sunna ce, aure nada daraja madaukakiya, miji kalmar da kowa ya sani ne aman ba kowa yake daukanta a hakan ba, Allah yace da ina umartar wani ya yiwa wani sujada tabas da na umarci mata ta yiwa mijinta sujada, bauta na kaiku ku yi, ku bautu aikin gidan mijin ku domin ibada ne, ku fita a hakinsa da na iyayensa da na jama.arsa,

Wujdane Aisha, ku sani neman aljanarku zaku tafi, daman ba wani kawaye kuka cika ba, bana so ku fara a yanzun, kar in ji kar in gani kuna fitar da sirin gidanku, koda wani abin ya hada ku da mazahenku ku gagauta fadawa Allah shi zai sanyaya maku lamarinku, kar ku soma kwaso matsalarku tsakaninku da mazajenku kuna fada fada mana, shi dai hakurin nan da ake jadada maku fa sai kun yi shi dole,
Haka Malan yayi ta yi masu nasiha, yana kara nuna masu girma da darajar mazajensu a gare su, yana kara tsoratar da su da su kara kiyayewa, yana kara nusar da su kan su yi biyaya

A haka har motoci suka zo, zo ka ga mamaki Samir sai da ya cika anguwa da motocin daukan amaren, Aba ya kara karfafa abin da mata sosai na rakiya, haka suna ji suna gani suna kuka tamkar ransu zai fita aka raba su da iyayensu wanda inna kukanta na biyu ne, da rabuwa da su da kuma kukan bata da shakikin dan uwa ko aminiyar da ta yiwa yayanta mata rakiya gidan miji, sai su sai masu daukar su haka malan ya lalabata ta shiga daki ta hade kai da gwuiwa tana rizgar kuka, tana mai yi masu adu.ar Allah ya sa wannan aure da aka yi masu gaba dayansu ya kasance farin ciki wa kowanensu sannan silar tsirar su duniya da kiyama, ita dai ta sani Aisha akoy hakuri, wace ta fi daga mata hankali Wujdane ce, ko ya zasu kaya??????


A haka har aka iso tankamemen gidan Elhaj Kadri, layi aka yi inda motar amaryar farar motar Alaidine, wace ya saka aka kawo masa ita a cikin satin nan , yana son ya fara gwadata da fita da ita idan ta karbu yayi odarta

Tunda aka tsaya ba.a kashe fitilolin motocin ba, sai kyali suke suna yi suna mutuwa suna kunnuwa, hayanaya ce ke ta tashi sosai mutane sai fitowa suke ana tsatsaye

Mom ce ta fito, da abayarta fara mai duwatsu, a hankali ta karaso har wajen motar ta saka hannunta ta bude marfin motar

Hannun ta mika tana murmushi ta ce" Marhababikum yayana, ku fito da kafar dama da bisimillah

A hankali suka fito kowace kanta a kasa, tun bama Aisha ba jinta take tamkar iska ta dauketa, Wujdane kuwa tana yi tana dan daga kanta, bata wani jin wani abin da ya fi na rabuwa da su inna,

Mom ta shiga tsakiyarsu ta riko hannayensu, ji take yau ba wanda ya kaita murna, saima da Aba ya dora cewar a gidan zasu tare har ya ga hankalinsu ya daidaita, ji take yau ta samu yaya matan da take nema, jinsu take har can kasan zuciyarta

A haka suka shiige ana ta rangada buda,

Wani zaman aka kuma dorawa sai can aka watse kowane da murna aka sada amaren da dakunansu wanda tare suka raka kowace ta ga mazaunin yar uwarta kafin suke amincewa da baci a sabon guri

Alwallah Aisha ta dauro tana bin dakin da kallo, ita tsoro ma take wai nan ace dakin da zata rayu ne? Allah kenan mai rahama mai ji kai, yanzu ita tana cikin daular nan da nepa da sanyi da kayan dadin nan haka su innarta kuwa suna can cikin duhu da yololuwar katifa , ko mai suka ci? Gagawar astagafari ta shiga yi duba da a cikin duhun itama ke rayuwarta, a haka da hasken salati basu wani damu ba, a hankali ta zauna ta shiga adu.o.i tana rokon Allah ya sakata a zuciyar mijinta, ya bata ikon kyautata masa,


Bangaren Wujdane kuwa daman fashin sallah take, haka al.ada lan zo mata sau biyu a wata, wanka ta yi ta dawo ta rakube jikin bed din ta kasa hawa, carbinta take ta ja a hankali ta daga kanta sama sai ga wani siririn hawaye ya surnano mata, a fili ta furta" Lukman ka ga abinda ka jaza min ko? Mai yasa ka san ba aurena zaka yi ba takura ka shiga rayuwana? Gashi an hada ni aure da namijin da ban san kamaninsa bama bale halayarsa Lukman, dan me ka koya min jin dadin kalamanka? Ka koyan sauraronka? Ka fada min akoy namijin da zai iya jurar halayanna harma ya koya min shakuwa da shi? Ka yi min alkawarin idan mun yi aure kulun zaka kaini wajen innata , a yanzu ka jaza min wannan ka fadan wa zai kaini? Kanwata da muke baci katifa daya a yau an raba mu sannan an barmu da kadaici rayuwar yan gayu ka fada min wa zai dora kansa saman cinyana yanai min labari? Wa zau dake ni idan nayi laifi yau an raba ni da yaya abdul fatah? Wa zai yi hawaye a boye idan na yi laifi an raba ni da yaya Hamzana? Wa zai yi min nasiha kan halayana da ni kaina ban san ina aikatawa ba sai idan inna na jaje ya lalashe ni yayi min nasiha ya nunan cewa ni baiwa ce, kyauta ce daga Allah yau an rabani da

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login