Showing 18001 words to 21000 words out of 63648 words

Chapter 7 - MUTALLAB

Nimcyluv   

08 Nov 2024

3759

haya?i ke fita ta cikin bakinsa ya wani cije gefen baki yana karkatar da kai gefe. Kamar wasa Goje ya ga Moh ya nufe shi da wu?ar shima ya?i matsawa yana ganin kamar wasa ne yana ?o?arin kawai Goje sara su kaga mutane kamar daga sama sun zagaye su. Moh ya?i motsawa sai Goje da ya yi baya ya cake yana zazzaro idanu tare da Waga gora sama. A kallon farko Mai dawa ya gane cinnaku ne ?an'sanda sai ya Wauke kai shi Goje bai faWa da labarin ba saboda shigar fararen kaya suka yi.

"Eng Ali wali ya aiko mu wajan ku kawo muku kaya" sai a lokacin Mangal ya ?arasu yana tale ?afa ya ce "Kaya sun sauka da zafin su kenan yallaSai, amma eh kun razana mu shigowa ba notice sai mu Wauka dire aka yi mana" Wan'sandan ya yi murmushi kawai ya ce "Kuna da kamar Ali wali za ku ji tsoro? Kune matasan da yake ji daku a yanzu musamman wannan da naga ko kallo bamu ishe shi ba" Goje ya juya ya kalli Mai dawa da yake kallon wani sashi daban alamar baya ma jin me suke cewa "Mai dawa sarki me jeji wajanka aka aiko mu domin aikin bana yara bane"

"FaWi"
Moh ya ce yana bada faWi ba tare daya kalli da Wan'sandan ba. Abu ya fito da shi a jaka ya mi?awa Mangal ya amsa ya ce "Ka a dana kada a je a yi ta sha ana Sarna, Eng Ali wali ya ce akwai fita ta musamman kuma ?auyen da za shi basu da kirki dole tafiyar sai daku a ranar zaku cake ku bawa samaniya yazo ta yi hadari" Mangal ya buWa ya ce "Dar hakan ya yi mana, sai Eng Ali wali ko ana su ko ba'a su ya zama dole don uwatar" Police Win ya juya kan Mai dawa a hankali cikin magana mai mu?amin ya ce

"Ka taSa jin mai suna Scorpio?"

"Wa?" Goje ya ce da sauri yana kallon Mai dawa da sai a lokacin ya juyo ya kalli Jafar shima Jafar ya kalle shi da kyau ya ce
"Akwai matsala ne babba, Scorpio yana yi wa Eng Ali wali barazana, yana da babbar hujjar da zai iya kawo masa matsala a mulkinsa kuma babu shakka ko waye Scorpio akwai alamar ya shirya fito na fito da Eng Ali wali, to muna jami'ai ba zamu bari ba tunda a jikin shugabannin da ?an dabarun mu muke samun namu rabon. Ali wali yana bu?atar ka taya shi gano waye wannan Scorpio da sunan shi kawai ake ji ba kamanni"

"Kamarya kenan?"

Mai dawa ya tambaya a ta?aice yana jin ?irjinsa na buWewa sa?o ya fara isa kenan a fili kuma ya sha kunu sosai. Jafar ya dafa kafaWar Mai dawa ya ce "Kamar kai yanzu kowa ya san sunanka Mutallab inkiya Mai dawa saSanin shi da sunan Scorpio kawai muka sani, babu wanda Eng Ali wali ya yarda da shi sai jami'an Dss ka baza jama'arka su tayaka binciko asalin waye Scorpio akwai kyauta mai yawa idan hakan ya tabbata, kuma ya ce ka faWi kome kake so zai baka"

Wani irin kallo Moh ya dinga yi wa Jafar na kan kaga biri, biri ya ganka kifi na ganinka mai jar koma sai kuma ya Waga kai sama yana kallo sama cikin kumburarriyar murya ya ce "Bayan Dss da shi uban gidan naku waye ka ji yana neman SCORPIO?" Jafar ya ce "Me ya sa kake tambaya?"

"To kuje ku yi aikin da kan ku" ya faWa yana juyawa cikin sauri Jafar ya ri?o shi ya ce "ka dinga sassautawa zuciyarka da fushi. Bayan Dss akwai jami'ai mafi hatsari da suke neman shi idanu rufe FID Federal investigation department, basu da imani wannan mutanen jami'ai ne da ba zaka taSa tunanin ta ina zasu cimmaka ba, suna iya zuwa a suffar mahaukata ma ko mai neman taimako, su kakkarya mutum ko su kashe shi ko haukata shi ba wani abu bane a wajan su"

"Suka kasa kama Scorpio?" Jafar ya watsa hannu ya ce "Sannu sannu da zarar sun gane kamanmin su, babu mamaki su Sullo ta wata hanyar kafin hakan ta fara ka ruga su kai hari,mun gama magana da kai Mai jeji" ya yi shiru bai ?ara cewa komai ba "Ka yi shiru?"
"Ka bada sha Wayanka, zamu jauwalo ka idan akwai sagi" cewar Goje Jafar ya girgiza kai "Ka bar shi ya yi magana" Moh ya sake kame fuska babu wasa kuma ya?i cewa komai sai ma fito daya ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????fara yi yana kallon bindigar dake hannun Waya Wan'sandan. Bisa dole suka juya suka tafi ba tare daya tanka su ba,daman Goje ya san ba maganar zai yi ba. Goje ya juya ya kalli Mangal da yake zu?ar wiwi a hankali ya ce "Ka raina musu hankali waye Mai dawa waye Scorpio"
"Ni ne, MUTALLAB TAHHB SCORPIO"
Mai dawa ya ce yana zare idanu waje manya gwanin tsoro da razani har sai da Goje ya ja da baya don bai taSa ganin halittar idanu kamar ta Moh ba ?wayar ta juye kamar bata mutane ba kuma sai ?ara ware manyan idanun yake yi.

"Akwai matsala Moh idan suka gano cewa kai ne Scorpio, za su yi maka illa gwara ka Sace kawai daga yankin kafin komai ya sarara" "Gawata za su iya gani su ha?ura da nema na" Ya furzar da iska daga cikin bakinsa kansa ya yi masa nauyi

"Goje an yi sake tunda aka bari na je state cid,ba san komai ba amma a fitar dani. Zan iya ha?ura da komai banda abin da yake damuna a zuciya ni da kai na zan bayyana cewa nine Mutallab Tahhb Scorpio da zarar na cika muradina na abin da na yi niyya"

"Mai dawa"

"Sai godiya"

"Ina tunanin ka ha?ura ka bar wa Allah komai duk zamu baza mu je gare shi ya yi mana eh hisabi" Moh ya taune harshe yana kaWa leSe tare da saka harshe ya kashe wu?ar dake hannunsa "Zafin nake ji a zuciyata zan yi Sarna, zan sha jini"

"Kamar wani maye? Shi Ali wali Win me ka yi masa ne?"

Mai dawa ya ja idanunsa ya lumshe ko yaya idan ya yi shiru sautin kuka biyu yaje ji a kunnen shi, tare da jiyo ?arar wutar dake cinye jikin nata hakan ya saka baya iya runtsawa idan ba wani abu ya afa ba haukwata shi ake son yi. "Na yarda da kai Goje, ka ci amanata askira zan saka maka a ma?oshi" "Ni Wan halak ne. Yanzu ya batun Manager Win? Ka santa ne na ji baka bashi amsa ba" jin ya yi shiru ya saka shi cewa

"Ko dai ka san Managern kamfanin?"

"Karka ka daman"

*****
Fiyya na zaune a saman gadonta tunda ta dawo take kwace tunani ne fal a cikin zuriyarta ga wani irin tsoro da bata taSa jin shi ba, a karo na farko ta ji tana son sanin komai da komai na Kamfanin FS WORLD INVESTMENT COMPANY, da duk mutanen da suka saka hannun jari a ciki data rufe idanunta yatsun hannun take ganin da aka yanka aka zuba cikin leda sosai taga rubutu jikin ledar amma ta manta bata duba ba. Ta juya a hankali tana kallon wayarta kamar mai tunanin wani abu kuma sai ta Wauki wayar tana dannawa numbersa ta kira aka danna line busy. Har zata ajjiye wayar sai ta ji an kira ta zubawa sunan idanun kafin ta ce.

"Ashraf..."
Kiran ta Waga ta kara a kunne ta yi shiru ta cikin wayar ya sauke numfashi da ?yar muryarsa a hankali.

"Na ji tsoro Fiyya" ta Wan tura bakinta gaba kamar yana kallonta muryarta mai daWi ta ce "He said he was scared" ya ?ara fidda numfashi kamar tana gabansa "Maama kina wahalar dani da kika zaSi aikin nan na kusa mutuwa, na ji ba zan iya barin ki ba kuma ke ce dai wacce nake so Fiyyar nan tawa"
"Ba na ce ka daina ce mini Maama, why not Fiyya kawai?" Kamar mai raWa a hankali Ashraf ya ce "I am sorry bestie me"
Dum! Haka ta ji kan ta ya yi masifar sarawa da sauri ta dafe kan nata tana jin kamar wani abu na janta a gigice cikin faWa ta ce "Karka sake kira na da wannan sunan" ta cikin wayar ya ce "Ba zan sake ba amma lafiya kike? Yanzu kike mini magana cikin soyayya Fiyya me ya sa sometimes kike abu kamar bake ba? Are You okay?"

"Kai na ke ciwo"

Tana cewa haka ta kashe kiran ta cillar da wayar nata zuwa gefe guda. Da sauri ta mi?e babu ko hula a kan gashinta yana tashi sama tana dafe da kanta bata ganin ko gabanta duhu ne a cikin idanunta haka ta dinga sauka akan matattakalar benen. Karo ta yi da mutum cikin sauri ta kama hannunsa tana Worawa a kanta "Yaya J kai na zai cire wani abu nake ji, ciwo yake mini kamar ana jana" gabaWaya ta rikice ta ?an?ame shi har zufa ke tsattsafo mata.
Kama hannunta ya yi ya jata saman kujera ta?i sakin shi ya zauna a hankali tare da zaunar da ita ta yi saurin Wora kanta a cinyarsa ya ri?e mata kan yana murza goshinta nata very careful kar ta ji zafi. Sun jima kana ta shiga sauke ajjiyar zuciya numfashinta na sauka ya Wan le?a fuskantarta yaga bacci take ya saka hannu ya juyo da fuskarsa yana zuba mata idanu ya ri?e hannunta har lokacin bai ce komai ba.

"Aliyu"

Da sauri ya saki hannun nata yana zame ta ya mi?e tsaye Ummi ta kalli Fiyya ta kalle shi ta ce "Ita kuma lafiya take bacci a nan? Yaushe ta shigo gidan ai lokacin tashi bai ba?" Captain dai ya yi shiru ta juya ta kalle shi sosai ta ce

"Lafiya take?"

"Ban sani ba"

"To ya naga kana haWe rai duka zaka kawo mini me kai komai naka babu walwala Aliyu ka dubi girman Allah ka dinga murmushi shifa yin murmushi sunna ne ta ma'aiki" ya shafa kan shi yana zuba hannu a aljihu cikin gaskiyarsa ya ce "Ban iya ba wallahi Ummi ki koyan"

"Shi murmushin? Allah ya rufa asiri to wannan matarka ta shiga uku" yana dai tsaye bai ce komai ba. "Maama?"

"Ummi"

"Maama ta shi yammaci za ki yi ?unci ko ciwon kai idan kikai bacci" ta buWe fararen idanunta suka haWa idanu ta sha kunu sosai tana tura baki ya zabga mata uwar harara ta yi baya zata koma baccin.
"Kee" ya kira sunanta ta buWe idanu "Tashi kafin na yi balle da wannan silar ?afafuwan" mi?ewa tsaye ta yi ta murguWa masa baki bata ce komai ba shi kuma ya yi kamar zai juya ya dam?o hannunta ta ?walla ihu daidai nan Daddy ya shigo parlon cikin sauri ya sake ta.

"Da kyau Soja gwara ka nuna ?arfinka akan Wiyata, yanzu zaka tattara ka koma inda ka fito"

Captain ya juya ya bar parlon gabaWaya yarinyar haushi take bashi har zuciyarsa. Daddy ya kalli Fiyya ya ce "Maama, yaushe za ki girma ina ganin wawtar wanda ya Wauki mu?a min Manager ya ba ki wallahi"

"Daddy kune kuke raina ni wallahi, na girma am matured enough" ya girgiza kai kawai kasancewar t.v. na kunne aka fara karato ta?aitattun labarai. Sunan Scorpio aka fara ambata matsayin wanda jami'an tsaro na hukumar FID Federal investigation department suke nema idanu rufe. Dake t.v a hankali ta juya ta kalli mai karanto labaran matashin Wan jarida dake aiki a gidan t.v na VOA juyawa ta yi ta ce "Daddy Wan bani aron wayarka"

"Ki yi me da ita?"

"Wayata zan kira, ina son fita ne wajan Kinal" ya mi?a mata wayar ta Wan jim tana Waga hannunta tare da copy na wasu numbersa sai kuma ta mi?a masa bayan ta yi deleting tana murmushi "La la la na tuna inda na sata"

Ya kalli t.v ya kalleta ya kuma kalli wayarsa, ya dai amsa a ransa yana mai jin tsoro da mamakin kaifin tunanin Maama. Ummi kuma ta ce "Ayi ta neman mutum kamar kiyashi shi kuma ya rasa sunan da zai sawa kan shi sai kunama?" Daddy bai yi magana ba Ummi da abin ke ta cinta ta kalli Fiyya dake shirin haurawa sama ta ce "Maama ta shi me ya yi ne?"

"Ummi ina zan sani, idan kika Wauke yadda ake juya biyar ta zama goma ba abin da Fiyya ta sani" tana cewa haka ta haura cikin sauri tana nanata numbersa dake kanta cikin sauri ta yi wanka ta shirya cikin abaya ta yi rolling tare da fesa turare sauri-sauri take a haka ta sakko hannunta ri?e da waya ko jaka bata Wauka ba. Daddy ya dube ta ya kalli lokaci "Wai zuwa wajan Kinal baya tashi sai yamma? Ita Kinal Win nan ta dinga zuwa mana zai fi"

"Daddy ba jimawa zan yi ba, na jima ban je ba mun gaisa ba"

"Maama bani da nutsuwa haka kawai idan kika fita gari ya hargitse bani number Kinal Win nan na kira ta" kafin ta yi magana J ya yi saurin ?wace wayar Fiyya ya ce "Bari na kira maka ita Daddy" babu sunan Kinal a jerin wanda ta yi waya dasu yau cikin sauri ta amsa ta ce "Number Kinal a kashe yaje fa J wai ni yarinya ce na san yadda zan kare kai na no body can come and hit me" Ta kalli Daddy da Ummi ta juya ta kalli J ta ce "To tsoran na mene ni Safiyya A Marafa?"

"Allah Ya tsare Maama jeki" amsawa ta yi da amin ta raWawa J kunne "J akwai gulma yau bari na je na dawo" tana fita harabar gidan mota ta shiga ta yi mata key cikin nutsuwa dake driving har ta fita ganin ta hau kan titi ta dubi bayan motarta ta cikin gilas wata ajjiyar ta sauke mau nauyi ta rufe idanunta ta buWe sai kuma ta Wauke hanyar ta nufi wani titin daban a zuciyarta addu'a take yi sosai.

*****
Eng Ali wali na zaune a parlo cikin wani gidansa da yake ganawa da ?an siyasa masu mara masa baya a kujerar shi. Ya dubi CSP chief Superintendent of Police ya ce "Ina son ku Wauke idanunku akan yarana, ko me kuke bu?ata zan baku idan Sarna sukai zan ji da komai" Csp ya ce "Hon yaushe za mu cigaba da zuba idanu ?an dabarka suna yin yadda su kaga dama a garin nan musamman a unguwar Birget gashi lamarin na shirin haddasa faWa tsakanin ?an cikin gari da su ?an Birget, mu jami'ai ne mun san gaskiya muke take ta"

"Ku cigaba da takewar su wannan yaran suna da wa'adi dana samu na ci zaSe ko inuwata babu mai gani a cikin su. Don haka ku rufe idanunku a toshe kunnuwa, zuwa gaba har matsayi zan saka a ?ara maka mu yi ?an dabaru" CSP ya jinjina kai Eng Ali wali ya Wakko kuWi mai yawa ya mi?a masa yana cewa "Idan kun kama masu dilar ?wayoyi da kayan maye na san ana mi?a su hannun NDLEA ko? Ka tabbatar ?wayoyin na zuwa wajan Jafar shi kuma zai bawa yarana, kar ka sake sunana ya fito daman ai ?a?an asara ne ko an kama su ba za su taSa furta ni suke yi wa aiki ba, lastly magana akan Scorpio Win nan yana neman bani ciwon kai bana son ya zama damuwata, idan F.i.d suka riga ku kama shi akwai matsala"

"Karka damu hon mun zuba yaran mu ta ko'ina"

Eng Ali wali ya ce "Lallai Scorpio ya zo hannu kafin zaSe"

Cikin sauri Fiyya ta fito daga cikin motarta tana shiga cikin wajan data zo a reception ta tsaya na wasu mintina tana zaune ta fito tana murmushi ta ce "Ikon Allah kamar tare kuke?" Fiyya ta buWe idanunta sosai ta ce

"Wa?"

"Captain yayanki"

Gabanta ya faWi ta kasa cewa komai Kinal ta zauna ta ce "Wallahi zuwan shi biyu fa, nima dai na yi mamaki amma ya ce aiki yake dubawa shi ne ya le?o mu gaisa har ma na tambaye shi ke sai bai bani amsa. Amarya ya kike ya sabgogi"

"Good. Yanzu lokacin ku ne Kinal siyasa ta matso ana ta fama da habaice-habaice"

"Kamarya habaici?"

Fiyya ta cire gilas Win idanunta ta ce "babu abin da mawa?a suka iya sai habaici wallahi ku zagi wanda kuke so kuma ku yabi wanda ku kaga dama" Kinal ta yi murmushi ta ce "A'a ni ba ruwana idan an kira ni dai wa?a ina yi amma ai ni ta soyayya nake yi tunda a nan na fi kauri, ina nan ina shirya miki ke da Ashraf" Fiyya ta sauke numfashi ta ce

"Ina cikin matsala Kinal ban so faWawa kowa ba wallahi"

"Subuhanallahi matsala wacce kuma? A kamfanin ko gida ko wani wajan?"

"Kema kin san a gida ba wanda zai mini komai sai mai ba?in halin nan, tunda ya dawo ya uzzura mini ko parlo bana fitowa mutum sai ba?ar zuciya Wan wahala kawai aikin kawai" Kinal dai ta zuba mata idanu kafin ta ce "Mene damuwar?"

"Kwana biyu da suka shige ana bibiyata kullum idan na fita, harta nan wajan da na zo sai da aka biyo ni, ni ba damuwata kai na ina tsoron su Daddy su sani kin san abu idan ya same ni tashin hankali suke shiga. Kinal ban san su waye ba me kuma suke bu?ata saboda bani da issues akan kowa wallahi na ji kawai ina son sanin wanda ke following nawa duk inda na je gwara mu yi fito na fito da shi, da na ce ko na yi hayar ?an daba nima suna take mini baya?" Kinal ta buWe idanunta sosai ta ce "Daman na fara zargin kina da taSin hankali Fiyya, ke yanzu ina kika san inda ?an daba suke bare ki je? Bakya tsoro ko shakka ai matsalarki police ne wannan ina ganin a gayawa Captain kawai" tsaki Fiyya ta yi tana mi?ewa tsaye "gwara duk abin da zai same ni ya zaman da dai na faWawa Captain ni ina da abin yi" "?an daban za ki yi haya yanzu kenan?"

"E" sai kuma ta koma ta zauna cikin nutsuwa ta kalli Kinal ta ce "Akwai abubuwan da bana ganewa kwana biyu kamfaninmu ina son na yi bincike

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login