Showing 12001 words to 15000 words out of 63648 words

Chapter 5 - MUTALLAB

Nimcyluv   

08 Nov 2024

3748

gidana a irin wannan lokacin?"

Moh bai ce komai ya zaga ya zauna saman kujera ya jingina ya Wora ?afarsa a saman table Win yana kallon abincin Goje da Darma na tsaye sai muzurai suke yi cikin sauri Alhaji Wada ya Wauki wayarsa zai kira ?an'sanda "Ba wani abu da zai bani tsoro, yadda aka fara dakai dole a ?are da kai Alhaji Wada"

"Waye kai? Me aka fara dani" fuskar Moh a rufe ya saka hannu ya zame abin da ya rufe fuskar da shi "Idan maye ya ci ya manta ai uwa ba zata manta ba, idan kare na yawo zabo na yawo za a haWe ya ranar" ?irjin Alhaji Wada ya buga ya yi baya da sauri ya ce "Kai ne? Me na yi maka"

"Ba labari na zo baka ba, ba fansa na zo Wauka ba na zo ka ganni kasan ina raye ina numfashi ka san cewa na cika Wan babata Ammo Mai dawa nake sarki mai jeji, na gode ?an Amina da ka zama kai ne silar da ya saka na gano wasu abubuwan" Alhaji Wada jikinsa rawa kawai yake ya ce "Don Allah kar ka yi mini komai kar ka taSa yarana basu san abin da ya faru ba" "Idan zan yi mana jira, idan na yi sai ta Saci. Ina je store Win gidan nan?" Da hannu Alhaji Wada ya nuna masa hanya ita kam matar ta kasa motsi saboda tashin hankali bata taSa ganin fuska mai ban tsoro irin wannan ba, yaran sai takurewa waje guda suke yi ko haWa idanu da Moh basa son yi" ganin har lokacin Moh bai tashi ba ya saka Alhaji Wada cewa "kar ka ce zaka mini komai" shi dai Moh kallon Alhaji Wada kawai yake zuciyarsa na tuna masa irin zaluncin da ya yi masa da hannu ya nuna masa yaran cikin kakkausar murya ya ce "Ko dan waWan nan, ba zan so su zama abin da na zama ba" ya juya ya kalli Goje ya yi masa fito da inkiya suka nufi store Wi???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?n kayan abinci kamar hauka haka suka dinga fito da buhun shinkafa katon na taliya da maroni su magi da galan na mai suka jide waje guda.

Yana bada faWi ya mi?e tsaye ya nuna kayan abincin "Ka raba a masallaci ka haWawa mutane da haushin kare guda goma-goma, ka kai har gidanmu" Ya juya zai fita sai ya tsaya ya saka hannu a aljihu ya zaro kunama ?atuwa ba?a ?irin da ita ta Waga ?ari sama ya dam?i hannun Alhaji Wada ba tare da yaran sun gani ba, ya cilla kunamar ciki ya dam?e hannun. AzaSa ta saka Alhaji Wada zubar da hawaye zufa na yanko masa sosai da sosai a hankali cikin ?asa da murya ya ce "Ka kira cinnaku ?an'sanda kenan ka faWa musu an yi maka fashi, idan sun tambayi waye karka yadda ka ce Mai dawa, ka ce SCORPIO" yana kaiwa nan ya kashe kunamar ya soke jikin bango da sauri ya fice kamar wal?iya, su Goje suka mara masa baya.

Fiyya na dur?ushe a gabansa kanta a ?asa ji take dama tana da ?arfin yin kuka a yanzu, ta kasa fahimtar sai yaushe ne komai zai daidaita ya tafi daidai? Tana haWiye abubuwa da dama ba tare da kowa ya sani ba bata bari a san rauninta amma yau ita aka saka gaba akan abin da sam bai kai ya kawo ba? Ita zaiwa haka?.

"Safiyyerh A. Marafa"

Ya kira sunanta a karo na uku sai a lokacin ta Wago kai ta kalli Daddy dake zaune saman kujera hannunsa ri?e da carSi fuska ba wasa ya lura sai ya dage sosai akan Safiyyerh.

"Ya kuka yi da Ashraf me neman auren ki?" A hankali ta ce "Ba komai Daddy"

"Ba komai Daddy, na gaji da jin wannan daga bakin ki Safiyyerh ke kina nuna mini ke mai wayo ce kuma kin girma kin isa ki yi handling dukkan wasu matsalolinki ko? Ke jaruma mai experience akan aikinta Managern FS WORLD INVESTMENT COMPANY? na yarda kina da wayo tunda na kasa sanin damuwarki tsayin shekaru na yarda kina da experience hakan ya sa cikin ?aramin lokaci kika zama Manager but amma.." ya yi shiru yana kallon ta sai kuma ya ce

"Safiyyerh kina bu?atar aure shine cika da ?imar kowacce mace, me kike bu?ata a rayuwa da ba a yi miki ba, wanne gata ban yi miki ba da kika ce kin fasa auren Ashraf?"

"Daddy ya ce na zaSi aiki ko aure"

"Sai kika zaSi me?"

"Aiki" Daddy ya dinga kallon ?ar tasa shi ya rasa gane wani mataki zai Wauka a kanta.

"Ba za ki yi auren ba kenan, ba?in cikin jikoki kike mimi Maama? Sai na faWi na mutu za ki yi auren me ya sa kika kasance stubborn ne, ko don kinga ina biye miki?" Fashewa ta yi da kuka sosai ita kanta bata san kukan ya ?wace ba, kalmar mutuwar da Daddy ya faWa ya firgitar da ita sosai idan Daddy ya mutu ta shiga uku.

"Daddy gasu Yaya J, su Marafa, su Captain Daddy me ya sa sai ni za a yi aure ne? Ni ce ?arama fa nawa nake gabaWaya ko aure za ka mini ka ?ara mini lokaci Ashraf zafin zuciya ne dashi baya fahimta ta a kodayaushe"

"Maama kuma taurin kai, ji da kai while zafin zuciya, Safiyyerh dole za ki yi aure" runtse idanunta sosai kenan duk abin da take ya tashi a banza? Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un me ya sa Ashraf zai yi mata haka me ya sa zai haWata da mahaifinta? Ta kasa cigaba da kukan abu ya tsaya mata a wuya sosai. Har Daddy ya je bakin ?ofar shiga sashinsa ya tsaya ba tare daya juya ba ya ce

"Cikin satin nan zan Waura miki aure da Ashraf in sha Allah"

Dum! Haka ta ji zuciyarta ta buga da ?arfi har tsakiyar kanta kuma ta ji hakan, ta runtse idanunta sosai take ?o?arin jan numfashi ta kasa ta yi saurin ri?e wuyanta da take jin kamar an soka mata abu a ciki saboda zafin da yake. Cikin sauri J ya ?arasu parlon daman ya shigo da nufin yiwa Daddy sai da safe ya nufeta yana ri?o hannunta ya ce "Manager lafiya? Mene?" Kafin ta bashi amsa Marafa shima ya shigo ya nufe ta, haka Dr Hash gabaWaya suka zagaye ta suna tambayarta lafiya kasancewar suna mugun son ?anwar tasu kamar rai. Hannun J ta ri?e gam tana nishi hawaye na zubu mata sosai ta kasa magana hakan ya saka Dr Hash mi?ewa ya Wakko ruwa mai sanyi ya yiwa J alamar ya Wago ta, a hankali ya dinga bata ruwan tana sha ya zame rubar ruwan.

"Junaid kwantar da ita saman kujera ko ka kai ta Waki"

"Bari ta ?ara jin dama dama a dai ?aro gudun acn ta fi sha?ar iska da kyau" cikin sauri Marafa ya nufi wajan ?aro a.c a hankali suka ji an ce

"Kar ka ?aro" ya juya ya kalli Captain dake zaune kan kujera abin shi yana dannawa, yana zaune Daddy ya kira Fiyya duk maganganun da sukai yana zaune har halin data shiga. "Captain daman kana ciki kana kallo Maama ba lafiya?"

"Ni na Wora mata?"

"Amma baka ce mata sannu ba, she's our little sis our favourite" kallon da Captain ya yi wa Marafa ya saka dole ya yi shiru dukkan su ba wanda ya iya cewa Captain komai domin sun san hali basa shiri da Fiyya bai shiga sabgarta ba, duk abin da ya shafe ta babu ruwansa da shi. Ko magana bai fiya yi ba ana ganinsa kowa ke nutsuwa domin shine babba a cikin su Fiyya kuma Auta. Fiyya ta yi lamo jikin J tana sauke numfashi Dr Hash na ri?e da hannunta jin jikinta ya fara Waukan zafi sosai. Da ?yar ta lallaSa J na ri?e da ita suka haura sama duka sauran mazan suka bi bayansu banda Captain da yake harkar gabansa.

Wajejen 2:30 Daddy ya sauke numfashi yana kallon yadda take sauke numfashi a hankali ko a baccin bata da walwala ya juya ya kalli Captain dake tsaye hannunsa zube cikin aljihu "Aliyu me na ragi Maama da shi a duniya dana kasa fahimtar meke damunta? Ita Waya ce mace ?ata laifi ne don na so ta yi aure?"

Captain dai ya yi shiru idanunsa a saman fuskar Fiyya Daddy ya mi?a hannu ya taSa goshinta ya ji har lokacin da zafi daman ya fi ?arfin awa guda zaune a wajan, yana cikin Captain ya buWe ?ofa ya shigo da tunanin babu kowa cikin ganin Daddy ya saka dole ya tsaya. "Maama ki yi mini alfama ki yi auren nan, shi ne abin da za ki yi ki faranta rai na" ya gyara mata hannunta daya lan?washe kana ya mi?e tsaye zai fita

"Aliyu mu je"

"After you daddy"

Daddy ya jinjina kai ya fita yana janyo ?ofar. A hankali Captain ya nemi waje ya zauna a gefen gadon ya zuba mata idanu sosai, a nutse a kamo hannunta ya ri?e cikin nasa jin jikinta zafi sosai ya saka ya saki hannun ya Wakko towel da ruwa ya dinga goga mata a goshi har lokacin yana ri?e da hannunta har sai da zafin ya ragu, bai tashi ba yana zaune aka fara kiran sallar farko cikin sauri saki hannunta ya mi?e tsaye yana haWe fuska J ne ya shigo a hankali ya bi Captain da idanu har ya fice daga cikin bedroom Win na Fiyya.

*****
Cikin gidan ya faWo babu ko sallama Inna Binta na zaune har za ta yi magana ganinsa tsaye ya saka ta yi shiru da bakinta. Yau ranta fari tas an yi musu rabon abinci Malam ya basu ya Soye sauran. ?akin Ammo ya nufa yana Waga labulan Wakin ya ganta zaune tana Waura kuSewa tun kan ya shigo jikinta ya bata yana hanya saboda gabanta daya tsananta faWuwa.

Ya shiga Wakin ya zauna ita dai bata kalle shi ba, sai kallon ta ya ke yi can ?asa da murya kamar ba shi ba ya ce "Ina yini Ammo?"

Mi?ewa ta yi maimakon ta amsa masa, ya cije bakinsa yana rufe idanu kwanon abinci ya jenyo ya buWe yaga taliya ce jallof ta ji albasa nan da nan yawunsa ya tsinke ya tuna rabon shi da abinci har ya manta.

"Alhaji Wada ya bawa Malam, idan da zuciya ai ba za ka ci abincin daya bamu ba" cak ya tsaya yana kallon abincin kamar zai tashi sai kuma ya nutsa hannunsa ciki ya Webo lauma zai kai bakinsa cikin sauri aka ce "Allah Ya isa ban baka ba ida ka ci abincin nan" Malam ya kalli Ammo ya ce

"Bana ce kar ki yarda ya shigo gidan nan ba? Wato har abinci kika bashi ko?" Ta girgiza kai ta ce "?auka ya yi"

Jiki a sanyaye Moh ya mi?e ya fice daga cikin Wakin yana saka ?afa ya banko ?ofar da ?arfin gaske yana zuwa daidai inda Inna Binta ke gyara shinkafa ya saka ?afa ya yi fatali da farantin shinkafar ta tarwatse ya yi waje kamar zai tashi sama. Ta dafe ?irji tana rafka salati "?ar gwamnati ce fa Allah ya isa wallahi".

Goje ya dubu Mangal ya ce "Me ka bashi wai? Yake wannan sambatu da mimmi?ar haka?"

"Sha fara kaga aljan ce, ita za ta yi aiki a jikinsa, daga sama aka bani ita" Goje ya juya ya kalli Mai dawa ya sauke numfashi cikin damuwa ya ce "Dole sai ka koya masa shan waWannan abubuwan ne?"

"A'a ina zaune ya zo mini kamar an koro shi yana huci ya ce na bashi irin abin da na bashi kwanaki saboda damuwar zuciyarsa ta kau ya manta da komai ni kuma na bashi sha fara kaga aljan"

"To gashi nan yana ganin aljanin ai" da ?yar ya samu ya yi bacci a wajan. Bayan ya farka Mangal ya bashi abinci ya girgiza kai "Mai dawa idan kuWi kake so ina da hanyar da zan yi maka ka dinga samun kuWi sosai cikin sau?i har ma ka taimaki wasu" tunda ya farka sai lokacin ya Waga kai ya kalli Mangal alamar ina ne? "Bangar siyasa kasan yanzu muna gab da fara shiga sabgogin siyasa uban gidana cikakken Wan siyasa ne, shima yana da uban gida kuWi zaka samu sosai a sabgar nan ina faWa maka"

"Kai ni" kawai ya iya cewa yana mi?ewa tsaye.

Suna zaune a wani haWaWWan parlo inda suke karSe wa su yi meeting na sirri. GabaWaya suka kalli MUTALLAB TAHHB SCORPIO Waya daga cikin su ne ya ce.

"Mene sunanka"

"Mai dawa"

"Kai mafarauci ne?" Ba tare daya kalli mutumin ba ya ce "Darr" babban mutumin ya jinjina kai sosai ya zaro wani photo a aljihu ya ce "Kafin mu yi maka bayanin su waye mu, me muke bu?ata da kai, fara ganin wannan ka saka dai a ranka mu ?an siyasa ne"

Shi dai Mai dawa bai ce komai ba, aka ajjiye masa photon a gabansa "?auki ka buWe ka gani mana"

Wani daga cikin mutanen ya ce "Manager ce a FS WORLD INVESTMENT COMPANY aiki za ka yi mana a kanta kafin mu faWa maka aikin mene ka fara Waukan photon kaga wacece" a sanyaye ya Wauki photon kafin ya kai idanunsa kai....



08164069385
For more information
WhatsApp only
[10/8, 7:59 AM] null: *d'
=?%? MUTALLAB d'
=?%?*


Page 5

"Safiyyerh Abdu Marafa Manager ce a Kamfanin FS WORLD INVESTMENT COMPANY kuma ?a a wajan tsohon leccara, muna bu?atar ka yi mana kidnaping Win ta" Moh Kallo Waya ya yi wa photon da suka bashi ya Wauke kai
"Ka santa?" Shi dai bai ce komai ba.

Eng Ali wali ya dinga kallon Moh yana tunanin abubuwa da yawa a ransa kafin ya ce "baka gama ganin photon bane, ko da yake yana da kyau da ?are mata kallo maybe ka zama silar mutuwar ta ko ka kashe ta da hannunka, ka ya zama dole ka gane kamamminta"
Goje ne ya Wago kai da sauri yana kallon Eng Ali wali kafin "Sai da kai mai gida wannan aikin ai ko ni zan iya yin shi ba sai Mai dawa ba, ka huta ka sarara mai gida"

Eng Ali wali ya yi murmushi yana jingina da kujera ya Wauki ?afarsa ya Wora akan Waya ya kalli Mai dawa wanda ko motsi bai yi ba sai jujjuya photon da aka bashi yake. "Ko Mangal ba zai iya aikin nan ba da ya fika wayo a sabgar balle kai da na sani yanzu, shi wannan Mai dawan idanunsa na kalla na san zuciyarsa za ta iya aikata komai"

Ya yi shiru sai kuma ya ce "Ni Wan siyasa ne babu mamaki ka taSa ganin poster na ko bana, shekaruna takwas ina ri?e mu?amin ?an majalisa na tarayya a jam'iyyar da nake ta kara, bani da ra'ayin ha?ura da kujerata kamar yadda ake yi mini kirarin idan na yi na gama na karya kujerar. Siyasa jinina ce Mai dawa, bana jin akwai wani dalili da zai zo ya saka na ha?ura da kujerar na amma wannan karon na yi karo da muruci wanda yake shirin yi mini wahalar dafawa ko ta halin yaya ne dole na sake hawa kujerar nan a karo na huWu. Hon MaWatai yana tare da manya wanda suka san kan siyasa ciki da bai dole mu fito da salo na musamman wanda zai kai su ?asa. Hon MaWatai shine Wan takarar jam'iyyar hamayya kuma yana da ?arfi har yanzu ba'a san mene rauni ko aibun shi ba amma akwai jita-jitar data zo kunne na domin tabbatar da gaskiyar al'amari ya saka na kawowa cikin jama'ata"

Sai a lokacin Mai dawa ya Wago kansa ya Wan kalli Eng Ali wali kamar ba zai ce komai ba sai ya cije baki yana karkatar da kai gefe ya haWa hannayensa biyu suka bada sauti mai ?ara cikin wata murya ta izza ya ce

"Mene haWin ta da maganar yawar ku?"

Eng Ali wali ya ce "Wa kake magana"

"Ita Wawar mai Wan kwalin?"

Cikin rashin fahimta Eng Ali wali ya ce "Meye Wawa da Wan kwali kuma?" Mangal ya yi murmushi yana "Ka fice Mai gida, Wawa da mai Wan kwali mace kenan ake kwafa maka zancen" Ya ce "Yaran naku sai ku"

Mi?ewa Mai dawa ya yi tsaye yana Wora ?afarsa a saman farar kujerar dake parlon kallonsa kawai Eng Ali wali ya yi bai ce komai ba. Sai wani ya ce "Mai dawa farar kujera ce fa?" "Ko takaddar jikinka zan Wora ?afa akai" wanda ya yi maganar ya yi saurin kallon farar shaddar dake jikinsa fara tas da ita sai ya ja bakinsa ya yi shiru. Moh ya kalli gefe yana furzar da iska daga bakinsa ya ce

"Me ya sa ka neman, bayan kana da gajojinka?"

"Saboda kai ne ba?uwar fuska a cikin wannan sabgar tamu, ba wanda zai gano cewa a tsagina kake za ka yi aiki mai kyau hankalina ya kwanta da kai Mutallab" wani irin kallo Mutallab ya jefa masa idanunsa sun sauya kala ya yi murmushi ya ce

"Oh Mai dawa da jeji, ya batun yarinyar ka santa ne ko ka taSa ganin fuskarta?"

"Na santa ko ban santa ba ina jin bashi kake bu?ata ba. Yaushe kake so a kawo maka ita?" Girgiza kai Eng Ali wali ya yi ya Wauki ruwa ya kurSa ya ajjiye kana ya mi?e tsaye yana zagaye parlon hannunsa a baya "Ka jira umarni na, kawai ka zama cikin shiri a koyaushe zaka iya jin kira. Akwai gidan dana samu a bayan gari zan baka makullin ko ka Wakko ta can zaka ajjiyeta kai ne zaka dinga kula da ita har yanzu lokacin da muka shirya abin da mukai niya, a cikin gidan akwai kayan aiki irin naku wanda za su sama muku nutsuwa"

Goje ya jinjina kai cike da jin daWi kafin ya ce "Mai gida za a siya mana mota mai iska kamar yadda muke ?a?an iska?"

"Za a yi muku komai, ku ri?e amana. Sai dai kawai sharaWi ko da wasa kar ku nuna kun sanni idan ina bu?atar ganin ku a wannan gidan zamu dinga haWuwa, ku buWewa kowa idanu kar ku ji tsoro da shakkar komai ni zan tsaya muku har zuwa ci zaSe" Moh ya ce "Bayan cin zaSan fa?"

"Kamarya?"
Ya

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login