Showing 3001 words to 6000 words out of 63648 words

Chapter 2 - MUTALLAB

Nimcyluv   

08 Nov 2024

3749

Inna Binta ta ji an cauWa mata bulala a Wuwawu ta yi saurin dire tukunyar ta ce

"Kan uba wanne mai tsautsayin ne haka?...," shiru ta yi ganin Malam ya ce "Kina sake magana ina ?ara cauWa muku shasha kawai mara kan gado"

Ya juya wajansu ya ce "Mayu marasa godiyar Ubangiji kawai akan abinci duk ma?ota da unguwa sai anjiku" Inna Binta ta ce "Yaushe rabon da muga sisi taka banda masifar tsiya kana bamu za mu yi haka ne?" Kan ta ya yi da bulala ta yi saurin waftar dambun a hannu ta yi Waki tana "Ohho dai na Wiba na mai da mugun miyau"

Haushin karnuka suka ji wanda rabon da su ji shekaru uku kenan gabaWaya suka juya wani ihu Mama Zaituna ta yi tare da fatali da dambun da ake ta yin masifa akan shi har zaninta na kuncewa zuwa ?asa ta yi saurin juyawa zata Wakko ta zame da Sawan albasa ta faWi dif a ?asa Kasancewar ?atuwa ce sosai ta fasa ?ara da jan Wuwawu ta shige Wakinta hankali tashe. Shi kansa Malam sai da zuciyarsa ta motsa saboda tsoro ya dinga kallon karnukan da idanu yadda suke Waga jela tare da zaro harshe waje jibga-jibga dasu sai zagaye wanda ya shigo suke yi. Da ?yar Malam ya ja numfashi ya ce

"MuWallabi ?anmalam nake gani haka? Ya suka sake ka basu kashe ka ba, ni na Wauka ma tuni ka mutu wallahi, ikon Allah" sosai kansa ke masa ciwo kamar zai rabe ga wani ciwo da jikinsa yake yana jin fatarsa na rawa, ya yi ba?i sosai amma manyan idanunsa na nan kayan jikinsa duk a yage ya zubawa Malam idanu.

"Kai MuWallabi ba da kai nake magana ba? Yanzu da suka sake ka me suke nufi ka kashe ?ar mutane a banza kenan? Ba zan goyi bayan gaskiya ba dole na je wajan jami'an tsaron yanzu na bi ba'asi"
Cikin sauri Ammo ta fito daga Wakinta jin sunan wanda aka kira zuciyarta har rawa take tana fitowa suka haWa idanu dashi ya kafe jikin bango a hankali yaran gidan suka fara fitowa ya dinga bin guntattakin yaran da kallo wasu duk bai san su ba. Ya nufi Ammo ta yi saurin Waga masa hannu ta ce. "Ina jin tsoron kiran ka a matsayin Wana na ji na yi dana sanin haihuwarka wallahi"

Ya buWe manyan idanunsa sai kawai ya ja ya lumshe yana ?ara yun?urin zuwa wajanta kenan ya ji ihu a waje kafin ya motsa Goje ya shigo da sauri yana cewa

"Mai dawa ?an unguwa ne Wauke da makamai wai za su Wauki fansar....." Da sauri MOH ya Wagawa Goje hannu baya son ma a kira sunanta a kusa da shi zuciyarsa buWewa take sosai. Goje ya sake cewa "Ba ?an unguwa kaWai ba har da gajoji da cinnakun layi" kafin Goje ya ?arasa sun ji ana cewa

"Ba iya Mai dawa ba har Malam da babarsa yau sai sun mutu da duka mutanen gidan sai mun Wauki fansar yarinyar daka kashe tunda jami'ai sun sake shi a banza" Mutallab ya kalli karnukansa ya musu inkiya Tiger ne ya fara zuwa ?ofar Wakin Ammo ya tsaya Rainbow ya je ?ofar gidan ya tsaya, Spider kuma ya tsaya yana kewaye Malam. Goje ya ce "Kai ?arfe baya cinka tsine baya ratsa jikinka su Malam sune matsalar" bai magana ba kai tsaye ya nufi waje gaban Ammo ya faWi ganin ba makami a hannun Mutallab. Inna Binta ta fito tana zunduma ihu tana jama'a su kawo musu Wauki tana le?a ?ar ?aramar katangar gidan ganin tarin matasan da suke waje Wauke da makamai ya saka Inna Binta kurma ihu tana faWin "Ya gafilan zanbi waya kashifal gammi...." Bata gama ba aka raWa mata gora aka ta faWo Waga saman katangar ta baje wanwar a ?asa Mufee ta fasa ihu tana yin wajan Inna Binta ganin haka sauran mutanen gidan suka shige Waki banda Ammo da Malam.

Moh na fita suka yi masa ?awanya kasancewar akwai shafi a hannunsa duk wanda ya daka sai ya baje a wajan, suna da yawa sosai cike da rashin sanin cewa tsarin jikinsa ya karye ya shiga tsakiyar su Waya ya Wauki dutse ya buga masa aka nan take ya fashe, wani ya Waga wu?a ya soka masa a ciki nan take wu?ar ta shige Goje ya zaro idanu ganin sun yi nasara ya saka suka zagaye Moh suna kai masa sarawa, baya faWa da makami bai san kuma ya ake yi ba, kafin wani lokaci sun kai shi kasa ko'ina na jikinsa jini ke fitarwa daidai lokacin tawagar mafarauta suka ?arasu wajan tare da zugar karnuka faWan ya koma tsakanin ?an unguwa da mafarauta cikin mawuyacin hali Moh ya ja jikinsa a hankali jin wani yana waya da ?an'sanda ji ya yi dama layya zana na wajansa a yanzu haka? Ya dinga tafiya yana jan jiki har ya bar unguwar ya shiga cikin wani waje mai kama da gonaki kuma jeji-jeji. Tana zaune cikin bukkar hannunta ri?e da ?waryar nono ta ji an faWo cikin bukkar a gigice ta mi?e tsaye...




*To ga dai shi nan ban san ya zaku amshe shi ba, amma tabbas zai zama daidai da ra'ayinku musamman iyayenmu mata da maza =?-?da suke wasa akan yaransu. MUTALLAB zai zo da sabon salo in sha Allah za a yi kuka sosai kuma za a yi dariya fatana kar ku yi mini zagin da kukai a MIJIN MALAMA =?-?ku amshi labarin da hannu bibbiyu ku tayani isar da sa?on zuwa ga manya ta hanyar yin sharing saboda Allah*


08164069385
WhatsApp only
[10/2, 8:40 PM] Nanameera: *d'
=?%? MUTALLAB d'
=?%?*



Page 2
Nimcyluv


Bright pens..... Second batch


*=?? Warning... For criminal issues*

Cikin bukkar ya faWa jikinsa jina-jina da jini sara ta ko'ina da ?yar yake iya fidda numfashi, ya zube a gabanta idanuwansa a lumshe har yanzu yana jiyu sautin ihu da kukanta, ya kasa ceton ta, ta sake mutuwa, yaushe zata ci-gaba da rayuwa tana sake macewa akan idanuwansa? Ya cije jajayen laSSansa wanda jini ya Sata sam bai damu da yadda yake shanye jinin yana koma masa ciki ba, a matu?ar fisge ya yi maganar mai sautin gurnani ya ce "Na amince, da gaske na amince Abbasa, zan zama mata maza, ki mayar dani jinsin mace ina tunanin zama macen ya yi daidai da tafiyar ?addarata! Zan zama mata maza, bana iya kwanaki ba, bana iya wa'adin sa'a ba, ba kuma iya na tafiyar sakwanni ba, ba kuma iya na gilmawar kwanaki ko shuWewar watanni da nisan shekaru ba, a'a Abbasa, a'a Abbasa ina son zama mata maza ne na daidai da tafiyar agogo da adadin shekarun da zan yi a duniya"

Yadda furucin ke fitar da kan su, da yadda yake magana idanuwansa na fiddowa waje duka jikinsa rawa yake da Sari yana wani irin tsuma bakinsa har wani haya?i yake yi jijiyoyin kansa tamkar zasu ratsa fata bakwai su keto, ganin halin daya shiga ya saka Abbasa cewa. "Iya zubin tunanin naka kenan? Iya jarumtar kenan? Mayar da suffarka zuwa abi mafi nakasu a rayuwarka? Ka zama mace shin ko ka mace da......"

"Abbasa!"

Ya kira sunanta a karo na farko a tsawa ce, domin baya son tuna abinda take ?o?arin cewa "Shikenan shikenan, zaka zama jinsi biyu, mai halitti biyu" ya girgiza mata kai yana jin amo da sautin muryarta cikin wutar da suka babbaka ta ciki "Kawai ki nakasta ni" "Tabbas zaka nakasa, zaka zama kamar jaririn da aka haifa yau, zaka zama ri?a??e zaka gagara, ubanka zai alfaharin haihuwarka duk da tsinuwarsa na tattare da kai, zaka sake yi rashi, rashi irin wanda baka taSa yin irinsa ba, zaka samu dukkan wata shahara da Waukaka da kake bu?ata, amma zaka dauwama a matsayin mata maza"

Ihu ya fasa yana ?o?arin mi?ewa tsaye da ya yun?ura gefen cikinsa yake sake buWewa saboda shafcecen saran da aka yi masa, jikinsa bashi da wani gurbin da babu sara.Abbasa ta mi?e ta Wakko wani farin abu a hannunta tana zuwa kan shi ta danne shi da duka ?arfin daya zo mata, ta Wauki garin abun ta fara sha?a masa a hanci yana sha?a da ?yar da sauri ya dam?i hannunta ya kifa fuskarsa da hancinsa gabaWaya, yana ihu da gurnani jikinsa na rawa ya fara sambatu, Abbasa ta ce "A me ka zo waje na?"

"Taya" ya bata amsa a raunace idanunsa na lumshewa. "Wasu sun biyo ka ne?" Ya girgiza kai can ya ce "Cinnaku, Cinnaku na fi ?arfin su" ya dinga juyya kansa can ya ce "Akwai Kimini a tattare dani, ya faWawa ?ashi wani abu, sun nemi asawa da Tsohuwa....!" Ya kasa cewa komai idanuwansa har yanzu na hango yadda gangar jikinta take ci a wuta.

Ita dai Abbasa ta kasa cewa komai ta zuba masa idanu, ta dinga kallon yadda jikinsa je rawa a hankali kuma ya fara saki idanunsa ?ur a saman bukkar cikin fitar hayyaci da yanayi irin na maye yake sambatu tare da kiran sunayen da ita kanta mata sani ba. A hankali ta ce "Mutallab" bai amsa ba sai zuciyarsa kawai dake rawa ta hango hakan ne a yanayin yadda ?irjinsa ke Wagawa. Ganin ya zama kamar matacce tsoro ya kama Abbasa ta tuna ashe bai taSa sha?ar abin da ta bashi ba a yanzu, maganin ?arfe dana tauri kawai yake sha gashi kuma zaman da ya yi na shekara uku a hannun jami'an tsaro ya sa tsarin ya karye.

?warya ta Wakko ta ji?on wani magani tare da ruwa mai zafi ta fara danna goge masa jinin jikinsa sai a lokacin ta lura da gabaWaya farcen yatsun ?afafuwansa dana hannu babu ga jikinsa duk alamar an jona masa shokin akan tilasta masa amsa laifin da babu wanda yake da masaniyar komai akai, sun yi masa haka ne da nufin ya amsa laifin kashe matarsa da ya yi. Ta sauke numfashi tare da kallon bakinsa a hankali ta kara kunnenta a tausashe yake cewa.

"Ina son ta, ina son ta zuciyata zata fito ita ce wajan ta uku me ya sa.... Ina jinta a ?asan zuciyata" Tunda suke bai taSa yi mata zance Wiya mace ba, haka bai taSa magana mai tsayin da ya yi a yanzu ba, duk abin da ya saka Mutallab magantuwa ba ?aramin abu bane ba. Mi?ewa ta yi ganin kamar ya samu yin bacci ta fita waje zuciyarta cike da sa?e-sa?e.

Unguwar ta yi shiru saboda zuwan ?an'sanda wanda da ?yar suka raba tsakanin mafarauta da jama'ar da suka zo Waukar fansan wacce aka kashe zai ya zama kamar an saka kafiyo ne kasancewar babu wanda bai san labarin kisan rashin mutuncin da aka yi wa yarinyar ba. Tiger, spider, rainbow sune suke ta kai kawo a ?ofar gidan Malam saboda basu tsaro kamar yadda Moh ya saba musu ya raine su tamkar mutane hatta mara gaskiya suna ganewa. Da sauri suke tafiya hankali tashe gabaWaya basa cikin nutsuwa Waya sai Waga hannu sama take ba'a jin maganarta sai sautin murya. "Ki yi ha?uri"

Sa'adah ta ce tana shafa hannunta a ?irji alamar ban ha?uri da yaran kuramen da zata gane ta girgiza kai tare da sunkuyawa tana buga ?asa ta Waga yatsa sama alamar rantsuwa. "Allah Ya kyauta, da kin bari mun ?arasa gani ai ya kori ji Bafullatana" daidai nan suka ?arasu ?ofar gidan ba kowa a rumfar Almajiran sai allonansu da rubar tadawa da ?an rubobi na bara. Tiger ya ?are musu kallo yana shinshina su sai kuma ya ja da baya yana Waga ?afa ya basu hanya suka shige cikin gidan.

Da Inna Binta dake yashe a ?asa suka fara cin karo jini na zuba a gefen goshinta Wan tofinta a bankaWe Allah Ya sa ba yara a wajan cikin hanzari Sa'adah ta nufeta tana girgizata ta juya ta yi wa Bafullatana alama data bata ruwa bata fahimci komai sai kawai ta kinkimo ruwa bokici guda ta kwarawa Inna Binta ajjiyar zuwa ta sauke a firgice ta mi?e zaune tana furta "Dambun Mufee, a kawo Wauki jama'a dambun Mufee ?an ta'adda za su kashe ni" ta ?an?ame hannunta jikinta ya ji?e jagab amma har yanzu dambun na hannunta ta mi?e ganin Sa'adah da Bafullatana sai kuma ta ja tsaki "Irin bala'i wallahi Ammo ta haifawa unguwar Birget masifa Wai-Wai da Wai-Wai zai dinga kashe mu yana zu?e jininmu ku duba wannan yarinyar ma ya kashe ta kari na uku"

Idanun Sa'adah ya cika da hawaye amma ta Wauke kai ba tare data tanka Inna Binta ba. Inna Binta ta watsawa Bafullatana harara wacce ke ta ihu tana taSo Sa'adah ta ja tsaki "Kurman banza da wofi gayya masifar, daga haihuwar kurma sai ta Wan jagaliya" tana kaiwa nan ta shige da?inta ta samu Mufee tana bacci ta yi maza ta tashe ta, tura mata Wan guntun dambun ta yi a baki bayan ta cinye ta ce "to sha ruwa kiji abin da kika samu sai kuma gobe, ki yi addu'a ki goge Allah ki gode Muhammadur Rasulullah. Banda ina buWe ido a gidan nan kema mutuwa za ki yi saboda yunwa kamar taki ?ar'uwar" sai kuma saka dariya sosai "Inna mene?"

"Tukunyar dambu ta kife dan ubanki da tuni ba ki lasa ba kema" Mufee dai ta buWe manyan idanunta irin na Mutallab tana kallon Inna Binta.

Ammo ta dinga bin Sa'adah da idanu ganin yadda take kuka kamar ranta zai fita, Bafullatana kuma ta haWe rai sai girgiza kai take "Ammo don Allah ina Mutallab yake? Da gaske ya dawo an sake shi? Sun wanke shi daga zargin da ake masa, yana ina?" Ammo ta Wauke idanunta zuwa can gefe tana kallon wani waje daban a Wakin nata can ta ce "Ki daina kira mini sunansa sallamamman yaron nan a kunnena Sa'adah, ki yi hankali watarana zai iya kashe ki"

"Ba zai taSa kashe ni ba, duk lalacewar shi jinina ne Wan'uwana ne a wannan halin da yake ciki na Wauka za ki yi murna Ammo? Za ki ja yaronki jikinki ki nuna masa kulawa gudun kar ya sake lalacewa, kar ki ce za ki yi abin da kikai a baya duk lalacewar Mutallab kece wacce kika haife shi, tun yana ?aramin kin san zuciyarsa yadda yake da zafin nama taurin kai. Kin san yadda yake da ?ulafucin uwa kodayaushe yana manne dake, me ya sa za ki yi haka?" Mi?ewa Ammo ta yi ta nunawa Sa'adah hanya ta ce "Tashi ki tafi gidan mijinki, banga dalilin zuwanku ba ni bani da wani Wa Mutallab kuma na sani kuskurena ya saka na haifeshi. Wallahi kika sake yi mini maganar tsinannen yaron nan sai na daina amsa gaisuwar ki har abada" tana kaiwa nan ta fice ta bar musu Wakin, fuuu Bafullatana ta fice daga Wakin zuciyarta na yi mata zafi Sa'adah ta yi shiru ita dai tana mugun son ?annin nata ai da ba haka yake ba, ya kamata su amshi hakan matsayin ?addara!

Washegari Malam na zaune a rumfa yana sauraren karatun wani sabon almajirin shi. ?anyaro ne zauna gefe kusa da Malam yana lissafa sabbin kuWin hannunsa ?an dubu-dubu sai she?i yake ya duba yaga dubu biyar cif ya mayar aljihu ya zaro ba?ar leda mai cike da gurasa da nama ya ya fara ci yana ajjiye lemo fanta a gefe. Ajjiye bulalar Malam ya yi ya ce "?anyaro ina ka samu kuWi da nama haka?"

"Bani aka yi Malam" kafin Malam ya sake magana ?anyaro ya mi?awa Malam ba?ar leda guda mai Wauke da gurasa a ciki da nama ya haWa masa da dubu biyu ya ce "A yiwa su Mufee girki Malam"

Jiki na rawa ya amsa yana buWe bakinsa "Da kyau yaron arzi?i, ina ka samu kuWi fal haka sana'ar me ka fara?" ?anyaro ya girgiza kai kawai can kuma ya kalli Malam ya ce "Bana yin sana'a, kyauta ake bani kullum, bani kaWai ba har Muhajeed da Iro" Malam ya yi sak tunani fal ransa ya sake kallon ?anyaro shekarunsa goma rak a duniya a hankali ya mi?e ya yi cikin gida.

****
A kusan tare manyan motoci biyun suka tunkaro babban gate Win ganin ya rigata kai hancin motarsa ya saka ta rage ta fiya, hannunta Waya a saman sitiyarin motar Wayan kuma ta Wan ri?e fuskarta a hankali ta lumshe idanunta gajiya ce a jikinta sosai da ?yar take buWe tu?a motar don dai bata san wahalar driver ne.

"Fiyya" Ya kira sunanta a hankali cikin muryarsa mai cike da nutsuwa ta buWe idanunta da sukai mata nauyi ta kalli wayarta ta manta video call suke yi ma suna haWa idanu da shi ta Wauke kan ta gefe tana ya motsa fuska "Fiyya na miki wani laifi ne? Kin sauya"

"I am sorry ina driving we'll make a call later" ya zuba mata idanu cike da so da ?auna yana jin ina ma a janyo ranar aurensu da Fiyya a ce gobe ne? Ya sauke numfashi zuciyarsa na buWe a hankali ya ce  I adore you Fiyya" ta buWe idanu ta kalli cikin idanunsa sai kuma ta murguWa masa baki ya buWe idanu sosai sai ya girgiza kai yana dariya ya matso da fuskarsa dab da camerar "Na ji kamar ina sha?ar numfashinki...."

Ya yi shiru jin ana knocking ?ofar motar da take ciki, itama ta juya ganin wanda yake tsaye ya saka ta Wan yi murmushi baya ganinta saboda duhun gilas Win motar amma murmushi mai kyau ne a fuskarsa. Ta cikin wayar ya ce "Waye?" Tana Waukar jakarta a ta?aice ta ce "Yaya Junaid ne"

"Ok" ya yi sai kuma ya ce "Fiyya" ta Wago idanunta da sukai laushi ta kalle shi dasu can ?asan ma?oshi ya ce  I love you Fiyya" da sauri ta kashe call Win tana haWe fuska ta Wauki wayar ta fita daga motar.

"Yaya J" yana murmushi ya ce "Manager" ta Wan yi murmushi kawai ya amshi jakar hannunta "Me kika zo da shi"

"Ba kyau bincike J" ya jinjina kai suka nufi shiga gate J ya kalli driver ya ce "Ka shigo mata da motar, she left the key inside the car" Fiyya ta marairai ce fuska tana mannewa jik??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????in J ta ce "Yaya J na gaji sosai"

"Sannu Manager, ko goyaki zan yi?" Ta buWe idanu sannu yake ta yi

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login