Showing 27001 words to 30000 words out of 63648 words

Chapter 10 - MUTALLAB

Nimcyluv   

08 Nov 2024

3758

Ya ba ki idan babu ranku shi ne zamu kira da sunan uba, zai mana walicci a ko'ina bai kyautu don ?addarar Ubangiji ta kitta a rayuwarsa ku ce za ku juya masa baya ko wofitar da rayuwarsa har haka ba, akwai hak?in iyaye akan yara haka akwai hak?in yara akan iyaye shin kina bu?atar Ubangiji ya tuhume ki da hak?in Mutallab? Allah da kan shi cikin hadisi mai girma ya ce; ?a?anku amana ce kuma kiwo ne a gare ku, lallai za mu tambaye ku wannan amanar da kiwon idan an ce ki faWi inda yake a yanzu ba za ki faWa ba wannan abun da kuke kun bashi dama da lasisin ?ara lalacewa ne idan yaro ya Wa?ko hanyar kangara jawo shi aje jiki a nuna masa ?auna da soyayya"

Mi?ewa ta yi tsaye tana share idanunta "ya zo mini jikinsa duk sara kamar korarre mara iyaye a duniyar nan har na yi na gama magana bai tanka wani kuskuren iyaye ke haddasa shi"

Tana kaiwa nan ta fice abin ta inda ta shige Inna Binta da Mama Zaituna na kokawa akan wani ?anzon tuwon da aka baza ya bushe sai ya yi gwanin sha'awa tana Santara da kaiwa baki ta ce "eh, kya yi kya gama wannan ?anzon sai na bawa Mufee ke ni fa akan abinci ba wani kirki gare ni ba, ba zan zauna yunwa ta yi ajalina a gidan nan ba, tunda mai gidan zuciyarsa a mace take bai san fus na hak?in iyali ba sai auri saki da tare yara kamar ?a?an Seraye kowanne kana kallonsa yunwa zata fara maka sallama a jikinsa haba me ake da hali na..." Da sauri ta yi shiru ganin malam tsaye ta yi mamaki da bai tanka mata ba ya shige.

Safiyyerh ta sakko daga saman bene tana yi tana duba wayarta ganin sa?on da Ashraf ya tura mata cewa ya Wan yi tafiya ba ta yi reply ba ta ri?e wayar. Yaya J ta gani zaune ta juya masa manyan idanunta da suka sake fitowa farare tas ta ce

"Office Win kenan?"

"Ina ni ina zuwa office banga yadda little sis ta farka daddy's favourite" ta girgiza kai tana Wan murmushi iya leSe ta ce "Yaya J kenan, good morning"

"Kin tashi lafiya sai ina?"

"Office, ina da meeting kuma Yaya J ka yi mini addu'a Please da wannan kyakkyawan harshen naka, zan baka labari mai daWi" ya ware hannunsa ya ce

"To ina jira ko na kai ki office Win?" Ta girgiza kai ta juya tana nufar sashin daddy dake ?asa. Fiyya tuni ta manta abin da ya faru ta manta wani Mutallab fresh take jin kan ta, tana ?ar wa?arta ta turanci tama manta ta shigo parlon daddy dake zaune ya zuba mata idanu ta yi saurin rufe ba ki ta ce

"Ka yi ha?uri daddy i enjoying when i sing a song, don Allah ka yafe wa Maama"

"Sai an yi magana idan kin yi laifi kina buWe manyan idanunki kinawa jama'a turancin yaran zamani ke ba kowa naki da yake bature"

"To babana babban laccara ne wanda ake alfahari da shi dukkan matasa ke son shi saboda ?o?ari da iyawar shi" Fiyya ta ce tana zaman ?asan ?afafun daddy "Tiger" sak ta yi jin sunan da ya kira ta da shi, lallai an taSa donganta ta sa wannan sunan na Tiger ta share kana ta gai da daddy.

Ya amsa cikin kulawa duk motsin da take akan idanunsa Fiyya na da mugun wayo dana da wani experience da Qualities bata yin abun da za a iya following footsteps Win ta, she is a clever girl faWanta har tsoro yake bashi ga taurin kai da miskilanci har addu'a yake Allah ya sassauta mata sai gashi Ubangiji ya gyara komai a lokacin da bai zato ba. Ya Wauke kai yana kallon wani gefen

"Aliyu yaushe ka dawo?" Idanunsa a kan waya yana dannawa, wandon uniform na sojoji ne jikinsa sai fara t.shirt tas wacce ta kama damtsen hannunsa ya saka p.cap ta sojoji fuskarsa kamar ya ce ya shiga uku can ya ce

"Da daddare"

"Dare da yaushe? Aliyu kai kana son shigowar dare kamar mara gaskiya?" Captain ya Wan kalli daddy ya ce "Tun 12"

"Kuma baka shigo ba me ya sa?"

"Kawai daddy" ficewa ya yi yana cilla wayar a aljihu yana jin Fiyya na gaishe shi ko inda take bai kalla ba. "daddy ni ba zan iya Waukan wannan halin ba wallahi bai ishe ni kallo ba zan daina ko gaishe shi ina dalili, Safiyyerh Abdu Marafa na da class babu mai Waga mini shoulder, duk wannan abun da ya yi aure a waje ne yake soja" Ranta duk a Sace ta mi?e tana cewa daddy ta tafi ya ce "Allah Ya tsare Manager ya shirya safiyyerh Abdu Marafa". Kasancewar sauri take yi ta saka ta yi driving kamar zata tashi saman bata wasa idan tana kan titi, tana isa ta buWe office ta shiga fahimtar da sabuwar envelope a table Win ya saka ta sa hannu ta Wauka tare da buWewa ta?aitaccen rubutu ne mai Wauke da jan biro wanda ke nuna rayuwarta na cikin matsala. A hankali ta fara duba consent Win da takardar ke Wauke da shi tana ajjiye waya.

 Jarumtarki bai kai ki tsaya bincike akan FS WORLD INVESTMENT COMPANY ba, kina iya Waukan rubutun matsayin wasa amma gargaWi ne da jan kunne ga yara masu rawar kai irin ki. Ki tsaya da binciken da kike you're nothing but a manager

Ta dinga juya takardar a hannu tana jin confidence nata na ?ara hakan kamar wata dama ce aka haska mata na nuna cewa lallai akwai ?ullalliyya a wannan kamfanin, kuma ta shirya buWe faifai ko da za su yi zubaibai ?warya ne, ko da gaskiyar da take ?o?arin bayyanawa zai yi silar barin ta numfashinta daga ?irjinta. Ta yi Addison na cikin abubuwan da take ?arawa a binciken za ta yi komai ko hakan na nufin fito na fito da surukinta ne. Zama ta yi ta fara duba files na sabbin kayan da aka kawo can ta saka aka kira mata accouter bayan ya shigo ba tare data kalle shi ba ta ce

"Accouter kana bu?atar wani abu ne?"

"Allah Ya taimaki manager kamarya fa?" Still bata kalle shi ba ta yi baya tana duba maganar da aka turo mata yanzu a waya ta ce "kawai kuWi idan kana so na bu?atun rayuwa"

"Ina jiran lokacin albashi ya yi ai nasan za a sallame mu da wuri" ta Wago idanunta masu sanyi ta zuba a kan shi sai ta cillo masa ?aramin file ta ce "na saka hannu ka yi signature as a accouter ka cire 1m a asusun kamfani na baka" da mamaki ya ce

"Ni kika bawa kuWin?"

"E, ko baka so?"

"To na ga ban yi wani aikin da na cancanci 1m ba kin sa na fara jin tsoro ba zan iya cin abin da ba ha??ina ba" ta Wan yi murmushi ta janyo files Win ta yaga ta ce "meye cikakken sunanka ma?" Rainin hankalin Manager mamaki yake bashi sai kawai ya ce Wazeer" da hannu ta ce ya je yana fita ta saka aka kira mata MD abin da ta yi wa Accouter shi ta yi wa Md cikin sauri ya ce

"Yanzu kika Wakko hanya manager da za ki ha?a ramin da za ki iya binne kan ki ciki ai duk sai na raina wayonki wallahi da ajin nan naki ko mene a ?asa ba ruwanki mind your own business rayuwar nan kana kallon wasu abubuwan kake yi kamar baka sani ba, to a haka cibiya ta rai ne mu kuma yanzu hankalin jama'a da yawa na kan siyasa, matasa na neman hanyar karatu, wasu na can suna bautawa ?an siyasa, wasu sojan baka wasu rayuwar social media wasu bangar siyasa wasu kasuwanci. Safiyyerh da yawa ana yin abin da ya samu ne ko yazo hannu ba wanda kake ganin cancnatar shi ba, ba a duba capacity na abu ko a siyasa kana ji kana ganin wanda ya dace amma kake rufe idanu ka Wauki baragurbi saboda yana watsa maka hatsi mu Win kamar ka ji suka Wauke mu, think big Fiyya ke macace babu mai ce miki don me, akwai kuWin da shi kan shi Alhaji Baiha?i bai sani"

"Kana son siyasa"

Md ya yi murmushi ya ce "Safiyyerh siyasa yanzu ai kusan a jinin kowanne matashi take, kinga muna da jam'iyyu uku Waya ce mai ?arfi saboda ita ke ri?e da mu?ami ma'ana ?asar a nan Hon MaWatai yake neman takarar kujera, sai jam'iyyar su Eng Ali wali sai last jam'iyya wacce mutumin cikin ta ya fi kowanne nagarta kuWi masu dame shi ba, da ?yar aka taushi zuciyarsa yake mu?amin kusan matashi ne matasa na son shi amma kasancewar yana cikin jam'iyya ?arama kusan sabuwa ya sa ba a yin maganar shi ma kuma da ba musulmi bane" Safiyyerh ta jinjina masa kai ta ce "Ka bawa accouter ya yi signature a baka 2m, enjoy yourself MD, but sunan wanda kake bani bayani yanzu?"

Ya washe bakinsa ba ?aramin jin daWi ya yi ba ya ce "Abraham Denial David, shine Wan takarar"

"Yana da hannun jari a nan ne?"

"A'a, i don't think zai saka hannun jari a nan gaskiya" a hankali ta ce "Me ya sa?"

"Kar ki zurfafa a bar maganar, za mu yi aiki tare" sallamar shi ta yi tana jin zata yi amfani da Md da accouter Md zai taimaka wajan sanyawa ta san sirrin kamfanin cikin sau?i accouter zai taimaka wajan bayyana komai. A gefe guda tana jin kamar ta shiga batun siyasar Abraham Win kawai ta ji ya yi mata she just want to help him.

****
Su da kan su sun kwana biyu basu saka shi a idanunsu ba, ba kuma su samu labarin inda yake ba sai yanzu da suka ganshi kamar wal?iya kwance a ?asa idanunsa buWe yana kallon sama Darma ya ce "Sai godiya wanda ya ce zai bi sawunka ya wahala, Wan malam ya?i halin malam dafinka ?arinka masifa ne idan ka taSa mutum da shi"

"Darma"

"Ka dake Mai dawa ka jima ka yi lastin irin na dabino, wa kake so a taka a kashe ko a yi masa fiWa" Darma ya ce yana buWe hannu sama tare da karkatar da baki hannunsa ri?e da ledar pure water ya nannaWe a hannu yana kaiwa baki tare da zu?a. Mutallab ya sake buWe idanu a sama ya kasa cewa komai tunaninsa ya tafi wani wajan. Goje ya ce "Sai godiya matsalar goge ce ko wato ka kayan lantarki"

"Zaman gidan yari ba daWi,amma na ji daWi"

"Ka ce ka tuna na jakuna nan cinnaku tsakaninmu da su sai ?arfe ba ma'ana ka tuna na jakin da suka haWa maka kenan"

"Ina jin zafi a ?irjina farcuna na da suka cire mini sun ?i fitowa, zan Wauki fansa Goje"

Kafin su yi magana an yi sallama an ?arasu cikin sauri Mutallab ya rufe idanunsa jin muryar zabuwa. Goje ya dinga kallon wacce take tsaye "Bayin Allah sallama nake muku fa" Mangal ne ya kalleta sosai ya ce "Yi batu" ta Wan rausayar da kai gefe ta ce "Amma dai ku musulmai ne amsa sallama wajibi ce"

"To alaiki, mene sagin aiki kike so a yi miki?"

Kinal ta fito da littafi da biro ta ce "Sunana Kinal ni mawa?iya ce, har zan shige na hango ku na ji ina son tambayarku na ji ina son na yi wa?a akan ku kasan mu da mu da marubuta kusan aikin mu Waya muna da son bin ?wa??wafi" Goje ya ce "To ina ruwan mu? Fece kafin na yi miki lahani"

"Ku ba ?an shaye-shaye bane? To akan shaye-shayen zan muku tambaya ina yin wa?ar zan kawo muku ku ji, idan kun yi shaye-shayen me kuke ji mene dalilin daya saka kuka fara shaye-shaye kuma kuke harkar daba"

Moh na jin su ya juya musu baya zaka Wauka bacci yake, ransa duk a Sace saboda jin muryar mace da ya ji ya san daya juyo zai iya kashe ta tsaf don bashi da wani business da mata. Darma ya ce

"Yanzu yadda muke ji za mu faWa miki kenan?" Kinal ta yi saurin cewa "E, wallahi na iya wa?a ina da murya sosai babu mamaki idan na yi wa?ar na saka a YouTube ta je viral na saka a tiktok ta yi trending" Darma ya ce "To ni dai tun daga sanda a gida na yi...,"Da sauri Goje ya tsayar da shi yana cewa "Kai amma Wan tsinanniya ne kai, ba haka ake bayani ba"

Mi?ewa ya yi ya ce "bari na faWa miki" wu?a ya zaro a ?ugunsa Kinal ta zare idanu tana yin baya cikin sauri Mangal ya tare bayan jikinta na rawa ta fasa ihu jin yadda Goje ya yanke ta da wu?a a fuska,ya danna mata ledan wiwin a baki ta fara zare ido tana ihu. Sai a lokacin Moh ya juyo yana kallon yarinyar ya cije bakinsa tare da juyawa exactly irin ihun da Safiyya ta yi lokacin zata mutu.

"Gani ya kore ji, idan kin rero wa?ar muna dakon ki a nan sata ?ar munafuka"

Darma ya dinga tuntsira dariya sosai yana ri?e ciki "Amma Goje baka da imani kamar fa fitsari ta yi a wando gaskiyar kurciyar nan akwai jan ido ga bayani nan kin gani ganin idanunki ai" ya juya ya kalli Moh ya le?a ga wata cukurkuWaWdiyya takarda yake karantawa shi ba wani karatu ya yi ba "Wai wannan takardar mece kamar ta asiri kodayaushe tana wajanka, kamar numfashin sha?a ka faWa mana ta mece" cikin sauri ya Soye yana dam?e ta a hannu Goje ya ce

"Nima sai fakon farar nake na mata karatun makarantar allo, na rasa wacce tsiyar ce a ciki"

"Goje"

"Sai godiya"

"Zan saka maka tsini idan ka taSa takardar nan ko na saka su tiger cinye ka Wanye, wallahi zan iya kashe ka akan takardar nan"

Kafin su yi magana an zo da babur an cillo wata takarda da sauri mai babur Win ya juya, Mangal ya mi?e tsaye ya Wakko ya buWe cikin sauri ya kalli Mai dawa dai kuma ya mi?a masa amsa ya yi ya duba, photo na gudu biyu ne Waya zanen fuskar wata kamar dai mahaukaciya sai kuma photo jira-jirai, photo me mai magana ga wanda yake da cikakken lissafi a gefe an rubuta FS WORLD INVESTMENT COMPANY.

****
Kwana biyu Safiyyerh ta yi busy duk wani family sun zo saboda gobe ne ake Waura auren, kamar auren munafurci ba wata gayya ko shagali Waurin aure ne kawai ana yi kuma Ashraf zai Wauki matarsa su tafi. A daren ranar Safiyyerh ta riga data gama accepting auren Ashraf ta yarda bata da wani miji sai shi zata sawa zuciyarta yadda zata zauna da shi tunda tana son shi ko ba can ba. Waya suka yi da Ashraf ya dinga tsokanarta "Har na hango idanun Maama a Wakin miji, mijin na kuma Ashraf ta yi nasarar samun kyakkyawan saurayi" ta murguWa masa baki ta ce "Zan fasa" ya yi saurin cewa "Idan ki kaga ba ki auri Ashraf to mutuwa na yi ko ke kika mutu, da gaske Fiyya ina son ki Allah shine shaida duk da ina dalilin auren ki ko saka ni akai na yi hakan amma na yi you're my life partner har janna in sha Allah"

"Kamarya? Mene dalilin auren?"

"Ke ba ki da wani favourite words ne sai kamarya, zan faWa miki komai a daren ranar da kika zama halaliyyar Ashraf zan faWa miki, zan sau?a?a miki binciken da kike akan Company" a ruWe ta ce "Ta ya ya kasan ina bincike akan Company"

"Safiyyerh kenan, that's is the difference between man and woman, ina da ba?i sai goben idan na zo ganin matata a wannan lokacin dole na rungume ki halal runguma zan miki Safiyyerh" hankalinta duk a tashe waye Ashraf ne me ya sa daddy ya amince da auren shi? Ta kasa magana har ya kashe kiran sai ya ?ara kiranta video call ?ura mata idanu ya yi taga yana shiri cikin sauri ta ce "Kuma sai ina?" "Inda kika aike ni" ta buWe idanu

"Kamarya?"

"I miss you Fiyya shine abin da na manta na ce miki, a nan nake jin motsin ki" ya nuna mata saitin ?irjinsa, daga nan ya kashe wayar. Daga ?arshe ta yi zamanta cikin bedroom Awais har bedroom ya shigo ya dinga mata shira "Yaya Aiwas ka Wan yanke mini farce" "to ban taSa ganin amarya irin ba tunda nake a duniya" ya jawo ?afar ya fara yanke mata farce ta rufe idanu.

Washegari da sassafe Fiyya na bacci daddy da kan shi ya tashe ta, ta farka da ?yar saboda kan ta dake ciwo mamaki ta yi ganin kusan family a Wakin ya kalleta ya ce "Kin dai yi sallah ko?" Ta Waga masa kai "Daddy lafiya?" Ya yi shiru ya ce "Junaid je ku fara yin gaba, Captain an kira shi yanzu daga can headquarter, Ummi Wakko mini hijabin Maama" Hijab ya karSa ya saka mata ya ri?e hannunta Anty Turai ta yi gaba tana zabgawa Fiyya harara har harabar gidan suka je, abin mamaki gidan shiru ta rasa meke faruwa a motar daddy suka shiga yana baya ri?e da ita Awais na jan motar da Ummi. Motar Fiyya kuma da ita Captain ya yi using wajan fita saboda shi bai Fiyya Waukan tashi ba. Fiyya ta yi shiru kan ta a ?asa,har suka ?arasu cikin babban gidan mai tarin jama'a daidai lokacin aka fito da shi daddy na ri?e da hannunta ya ce "Mamana je ki masa addu'a"

"Addu'a? Daddy waye?" Ta furta muryarta na rawa ta juya ta kalli makarar da aka ajjiye gabanta Wauke da gawa, ya sake ri?e hannunta da kyau ya jata zuwa gaban makarar ya du?a tare da yin namijin ?o?arin buWewa. Fiyya numfashinta ta ji ya Wauke lokacin da idanunta ya yi arba da gawar Ashraf dake kwance cikin makara, jira ya fara Waukar gangar jikinta da gaske Ashraf ne kwance ba yau aka ce za a Waura musu aure ba shine zai mutu anya gawar Ashraf ce numfashinta ya tsaya cak tana daga tsayen suka ji ta yi wani irin ajjiyar zuciya tare da yin baya cikin sauri a tare daddy da J suka tare ta,

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login