Showing 18001 words to 21000 words out of 73204 words

Chapter 7 - A ZATO NA

30 Oct 2024

1753

daga dakin.

Sai dana bi su daki na musu bankwana, Maryam ta taya ni daukar akwatina muka fita. Na shiga gidan su Inna su ma na musu sallama. Kulsum da Maryam suka raka ni har bakin titi kasancewar babu ababen hawa tunda safiya ce sosai, na tari adaidaita sahu na hau muka tafi tasha. Motar Kano na hau, tana cika muka dauki hanya.














*☆⋆05⋆☆*





Tunda muka isa Kano da misalin karfe goma na safe, muka hau motar Gashua. Sai a tasha na samu yogurt mai sanyi da cake na ci. zuwa karfe sha daya muka dauki hanya. A Hadejia muka tsaya aka yi sallah tare da cin abinci, muka sake daukar hanya. Karfe biyar da yan mintuna muka shiga garin Gashua.

Yaya Mudatthir da kanshi yaje ya dauko ni. Ya kalli yadda nayi wuki-wuki saboda gajiya yayi dariya, "Subhanallah!! Illo! (nick name din da yake kira na dashi), you look like a total mess!".
Nima nayi dariya, "Yaya tafiyar awanni fiye da bakwai a mota ai ba ta wasa bace ba!".
Ya gyada kai, "kwarai kuwa. Sannu da zuwa. Ya hanya?".
Nace "Alhamdulillah". Ya taya ni daukar akwatina ya dora akan mashin dinshi, nima na hau muka tafi.

A gidan Bako ya ajiye ni, ko shiga bai yi ba yace min zai dawo bayan magriba, na mishi godiya. Ya juya ni kuma na shiga gidan wani almajiri ya biyo ni da akwatina.
Inna Fatsu na gaban wuta tana tuka tuwo nayi sallama na shiga cikin gidan. Ta tashi tsaye tare da dago kanta sakamakon jin muryata a kanta. Kafin ta tantance ko ni ce ko ba ni bace ba, na saki jakar hannuna kasa na falla da gudu na fada jikinta. Allah ya taimaka ta dafe bango da sai na kaimu kasa gabadayanmu.
Ta fara kokarin yakice ni tana mitar, "ban san ko sai yaushe bane zaki daina wannan shirmen naki ba Na'ilah. Ina ga dai sai ranar da Allah ya baki sa'a kika buga mu da kasa mu duka kika karya min kugu sannan zaki daina!".

Nayi dariya tare da daga kaina na kalleta, "Fatsu na, kin sake yin kyau wallahi. Me Malam yake baki kina ci ne?".
Ta girgiza kai, amma murmushine akan fuskarta, "tuwon dawa ne da miyar. Idan so kike yanzu in bada nikanta".
Nayi dariya, "Inna kin san wannan ba cima ta bace. Abu zaki bane mai sanyi da mai romo don na kwaso gajiya da yunwa".
Tace "ki fara shiga kiyi wanka, sai ki zo kici abinci".
Nace "haka za ayi". Na fada daki.
Ita ta biyo ni da jakar hannuna dana yasar da akwatina tana mita. Dariya kawai na dinga mata.
Idan ina gabansu ji na nake yi kamar wata karamar yarinya yar shekara goma.

Da nayi wankan sai na dauro alwala kawai. Na shiga dakin Fatsu da aka mamaye da carpet mai laushi. Dakin irin tsarin nan ne na mutanen da, gadon karfe babba da kuma karami na katako, sai wardrobe babba, da kuma tarkace da ba'a raba tsofi dasu. Na zauna na shafa mai tare da lalubo kaya masu karancin nauyi na saka. Ina sakawa sai gata ta shigo dakin da plate da kula.
Na mike kafa akan carpet din tare da amsar plate din, maltina ce mai sanyi har raba yake da ruwan sanyi, kular kuma soyayyar indomie ce a ciki.
Tace "Yayanki yace kada ayi abinci dake, za'a dafo daga gidanshi a kawo miki".

Nayi murmushi cike da jindadi, "sai ni yar gatar Yaya da Anty Sailu".
Tayi dariya, "kwarai kuwa, dazu zuwanta biyu nan wai taga ko kin zo".
Nima nayi dariyar. Sailuba itace wadda Yaya Mudatthir ya aura. Wannan shekarar su ta biyo ne kenan. Auren dangi ne suka yi, diyar Iya Lami kanwar Mama ce. Da yake duk tare muka taso da ita da sauran diyan dangi sa'anninmu, kusan duk abokan juna ne mu.
Na sa fork na fara cin indomie, taji maggi da dan taruhu, dama in dai Inna Fatsu ce bana jinta wajen girki. Ta iya hada abinci kala-kala, tun daga na da har na zamani.
Sai dana kusa yin rabi sannan na daga kai na kalleta, "wai ni ina Malam yayi ne? Nayi zaton ma yana dakin soro ne".
Tace "ai Malam wajen jana'izah yaje, nasan kuma daga can zai wuce masallaci. Shi da gida sai bayan isha'i".
Nace "Allah sarki, waye ya rasu?".
Tace "wani abokinshi Malam Mati idan baki manta shi ba".
Nace "ina zan manta Malam Mati? Shi da nake kaiwa rubutuna idan nayi a allo ya wanke min kafin in iya?".
Inna tayi dariya, "Aikuwa shi ne. Rashin lafiya ce yayi wallahi, ya kusa share watanni biyu a aaibiti".
Nace "Allah ya jikanshi, Allah kuma yasa mutuwar hutu ce a gare shi. In shaa Allah idan na fita gobe kuwa zan je inyi gaisuwa".
Tace "yakamata dai".
Ina gama cin abincin aka fara kiran sallah. Na daukesu na fidda waje na koma daki nayi sallah.

Ina gamawa naji wayata tana kara, na tashi a nutse na dauketa daga inda na ajiyeta, lokacin kiran har ya katse. Na duba naga Maryam ce. Murmushi nayi kafin na sake kiranta. Yana fara ringing ta dauka, "Yaya Na'ilah tun dazu nake kiranki baki dauka ba, hankalina har ya fara tashi wallahi!".
Nayi dariya, "ban jima da isowar bane, ina zuwa kuma wanka nayi. Ina ga lokacin kika kira. Na sauka lafiya, ina dakin Fatsu na ma idan abinda kika kira ki tambaya kenan".
Tace "shine dama. Ya hanya? Kin same su lafiya dai?".
Nace "lafiya lau kowa. Ya gidan?".
Mun danyi hira da ita ta fada min yadda su Muneerah da Auwal suka dinga cigiyata a gidan, ina ta dariya. Daga karshe dai muka yi sallama da ita akan cewa zan kira washegari ta hada ni da yaran. Bayan mun kashe wayar Baba na turawa text na sanar dashi na sauka lafiya duk da cewa nasan Yaya zai fada mishi.
Kan abin sallah na koma na zauna gefen Fatsu da take lazumi nima na fara nawa har aka kira sallah.

Sai bayan sallar isha'i sannan Malam ya shigo gidan. Na dauki kwanukan da aka zuba mishi abinci na tafi dakinshi. A bakin kofar dakin nayi sallama, daga can ciki na jiyo ya amsa cikin muryarshi mai cike da kamala da haiba.
Na yaye labulen dakin na shiga, yana ganina ya hau sakin murmushi "Masha Allah, amaryar tawa ta karaso kenan?".
Nayi yar dariya tare da zama a gefen shi, "ni ai nayi fushi, tunda kaki zuwa tarya na!".

Yayi yar dariya, "to, ki ce wannan karon da yan rigimun kika zo kenan?".
Inna data shigo dakin hannunta dauke da kofin ruwa tace "kamar kuwa ka sani!".

Na zauna a gefenshi tare da ajiye kwanukan a gabanshi. A nutse na gaida shi ya amsa tare da tambayata mutanen gida, na amsa tare da mishi ta'aziya.
Inna ta gama zuba mishi tuwon. Ya wanke hannunshi tare da yin bismillah ya fara cin tuwon. Ya kalleni, "yau ba za'a taya ni cin abincin bane?".
Inna tace "yau dai kai kadai zaka ci abincinka. Girkin matar Yayanta take jira".

Tana rufe baki sai ga sallamar Yayan a tsakar gida. Na tashi da sauri na fita tsakar gidan. Wani dan ihu nayi na dafe Sailuba dake gefen Yayan. Ya girgiza kai kawai ya shige dakin Malam ko tunanin yi mana magana bai yi ba, don yasan in muka hadu sai a hankali.
Sai da muka gama murnar ganin juna sannan muka shiga ta gaida su Malam.
Na dauki kwandon da suka shigo dashi na ja ta muka koma dakin Inna. Da yake da wuta kar a garin, na kara mana gudun fanka.
Farfesun busasshen kifi ne ta kawo min da chips din doya. Na zuba iya wanda zai ishe mu na ciccibi sauran na kaiwa su Inna.
Dakin na koma muka dasa dandalin hira ni da ita, bamu san dare yayi ba sai da Yaya ya leko yace mata ta tashi su tafi. Na raka su har kofar gidan muka yi sallama dasu.

Dakin Fatsu na koma nayi shirin kwanciya barci na. Ina zaune Fatsu itama tayi nata shirin ta tafi dakin Malam. Wutar dakin na kashe tare da sakaya dakin, na kara ware iskan fanka na fada kan karamin gado na kwanta.
Sai dana kira Janan muka gaisa na fada mata ina Gashua sannan na dannawa Umar kira.
Yana dauka ya tare ni da, "haba Sweety na, ina kika shiga ne tun safe nake nemanki?".

Nayi murmushi, "hello to you too, and yes, lafiya lau na wuni!".
Ina jin sautim dariyar daya saki, "Lols.. Da gaske nake fa. Har na fara shirya kayan tahowa Kt gobe idan baki amsa kira na dama".
Nayi murmushi, "lallai ma, yanzu kawai sai ka taho Katsina?".
Yace "ai ba kawai bane, ina lafiya bugun zuciyata bata daga kira na?".
Nace "ba kin daga wayarka nayi ba, ina tunanin matsalar netwok ne. Kasan ina Gashua fa!".
Yace "hope komi lafiya?".

Dadina da Umar kenan, kulawarshi a gareni na matukar tafiya dani. Nace "lafiya lau fa, kawai nazo ganinsu ne!".
Yace "good. Shine kuma sai yanzu kike fada min ko?".
Nayi dariya sosai, rigimar Umar watarana tafi karfin mai rai.
Mun dauki kusan mintuna goma muna sa'insa akan ban fada mishi ba, daga baya dai ya saki zancen muka shiga wani kan yanayin aikinshi.
Sai dana fara jero hamma sannan muka yi sallama dashi, "goodnight dear, dream of me fa! Zan kira ki gobe ki bani labarin kalar mafarkin da kika yi". Abinda yace kenan kafin ya kashe wayar.
Nayi murmushi kawai tare da ajiye wayar a gefen gado. Nayi addu'ar kwanciya barci tare da jan abin rufa zuwa jikina tare da rufe idanuna.



*



Funkasu muka ci a matsayin abincin kari. Ina gamawa nayi wanka na shirya na tafi gidan Yaya. Naci sa'a yana gida bai kai ga fita ba. Yana aiki ne da wani research institute. Na gaida shi ya amsa. Sailuba ta fito daga daki tana murmushi, "yanzu nake cewa ya kira ki kizo ki ci abinci".
Na kalli inda take nuna min, kuloli ne a shirye akan ledar cin abinci. Na shafa cikina, "abincin nan sai dai ko anjima don yanzu dai kam cikina a cike yake".
Tace "to ai shikenan".

Yaya ya mike zai wuce, na mishi Allah kiyaye, ita kuma ta bishi zata mishi rakiya. Yace "kada dai a yi nisa Na'ilah, na san ki da yawo. Duk ranar da kika zo haka zaki ja matata ku shiga gari sai na nemo ku".
Nace "Yaya sau daya ne fa ka taba nemo mu".
Yace "oho dai. Idan dai kuka dade, babu fita gobe!".
Nayi dariya "matar ka zaka ja wa kunne kuma wannan, ita ce mai son yawo bani ba".
Yace "ni dai na fada muku!". Daga haka ya fita.

Ina zaune a inda suka barni ina wasa da kan wayata ta dawo, tace "bari in shirya sai mu fita ko? Abincin sai mu tafi dashi gidan Yaseerah mu ci".
Na gyada kai, "haka za ayi".
Ta shige can kuryar daki ni kuma na cigaba da danne-danne na har ta fito sanye da riga da zani na atamfa, hannunta rike da jaka da hijabi. Na bita da kallo kafin inyi sequeling na fara tsalle akan kujera, "ke matar Yaya sai kice kin kusa sauke mana baby!".

Tayi sauri ta ja rigarta kasa tana hararata kasa-kasa, "ni kada ki min ihu anan. Don mayuntaka har kin hango abinda ko wata uku bai rufa ba!".
Na daga mata gira ina dariya, "haba mata, kada kiyi underestimating dina ta wannan fannin!".
Ta shafa cikin tana dan murmushi, "ku dai taya mu da addu'a dai kawai, Allah yasa mai tsayawa ne".
Murmushin tsokanar kan fuskata ya dusashe, sau biyu tana yin barin ciki, likitoci sun ce mahaifarta bata da karfin da zata dauki ciki ne, saboda haka aka mata daurin mahaifa.
Na dafa kafadarta ina murmushi reassuringly, nace "da yardar Allah babu abinda zai faru, zaki haifo mana babynmu lafiya lau, in samu takwara!".
Hakan yasa ta saki dariya a tausashe, ni kuma nayi murmushi, tace "muje, Yaseerah har ta fara danno min flashing".
Nayi dariya tare da ciccibar kwandon da ta saka abincin data ajiye mana, muka fita.

Yaseerah diyar Baba Adama kanwar Mama ce. Su hudu ne a wajen su Bako duka mata, Inna Talatu ita ce ta farko, tana aure a Damaturu, sai Mama na, Iya Lami da Adama, su duka suna nan Gashua ne. Yaseerah, ni, Sailuba, Ma'u kanwar Sailuba da Lawisa kanwar Yaseerah duk tare muka taso dasu, kusan duk sa'annin juna ne mu. Yaseerah a shekara daya aka aurar dasu ita da Sailuba. Yanzu har tana da yar diyarta Hafsat.

Gidan Yaseerah muka fara zuwa, a shirye muka sameta tsaf tana jiranmu. Bayan mun gaisa da yin yar hirar yaushe gamo, muka ci abinci, daga nan muka fita.
Gidan Iya Lami dake nan unguwar su Yaseerah muka fara shiga muka gaidata. Daga can muka biya gidan Marigayi Malam Mati muka yi gaisuwa.
Yinin ranar dai a haka muka gama shi. Shiga nan fita can, sai wajen karfe biyar muka koma gidan Sailuba.

Yaseerah da Ma'u suka koma gidanta, ni na tsaya wajen Sailuba. Sai da na taya ta tayi girkin abincin dare, sannan na mata sallama na tafi, lokacin har an gama sallar magriba.
Nayi sallama na shiga dakin Fatsu. Tana zaune akan abin sallah tana lazumi a tsakiyar daki, ta bini da kallo lokacin da nake ajiye hijabin dana cire akan gado.

Tace "wato Na'ilah kina nan da yawon nan naki ko? Yanzu saboda Allah ace kin fita tunda sanyin safiya amma sai yanzu zamu ganki? Saboda kin raina mu ne ko me? Idan a gaban mahaifinki kike kina wannan yawace-yawacen ne na babu gaira babu dalili?".
Nace "haba Fatsu, ya zaki ce wai ina yawo? Ziyarar yan'uwa ce fa nayi, zumunci. Kuma a gida yawon me zanyi? Bani da kowa acan sai nan din dai, kin san haka".
Tace "ai sai kiyi tayi, tunda bakinki bai iya bada hakuri ba balle ya iya amsa laifin da yayi!".

Na koma gefenta na zauna ina yar dariya, "to naji Fatsu na, Allah ya baki hakuri, na tuba na bi Allah na bi ki. In Allah ya yarda gobe babu inda zan je, a kugunki zan wuni. Kinji dadi?".
Ta dan harareni cikin wasa, gefe daya kuma tana kokarin danne murmushin da take yi, tace "Allah yasa, kullum ke dama maganar ki daya, amma baki cikawa!".
Nace "in Allah ya yarda wannan karon da gaske nake, I'll be all yours gobe!".


Kamar yadda nayi alkawari, washegari a gidan na yini, ko nan da kofar gida ban leka ba. Da yake ba wasu ayyuka muka yi a gidan ba, na shiga dakin Malam na fiddo kayan ciki gabadaya na sharo dakin tas, na maida na sake mishi wani sabon shirin.
Da yamma bayan nayi wanka, na dauko littafaina da textbooks dana taho dasu ina bita. Nasan cewa nan da sati daya ne zasu fara zancen mu koma makaranta. Bana bari koda wasa in shantake a gida idan naje hutu, ina da lokuta na musamman da nake warewa, lokaci zuwa lokaci na kan dauko littafaina inyi bita musamman akan courses din da zamu yi a semester ta gaba ko kuma wadda muke cikin yi.

Da dare bayan isha'i muna zaune akan tabarma a tsakar gida. Bura-busko muka ci, (tuwon biski/tuwon tsakin masara ko na gero), wannan karon na masara ne muka yi, da miyar kuka da man shanu. Kamshin tuwon ma kadai ya isa yasa yawun mutum tsinkewa balle dadin da yayi. Malam yayi baki, tare suka ci abincin shi da bakin a dakin soro inda ya saba ajiye baki na nesa.
Bayan mun gama cin abincin, na koma na zauna ina taya Fatsu hade kayan sakar da tayi da zare, kasancewar babu wutar lantarki, hasken farin wata ne tar ya mamaye kafatanin tsakiyar gidan, sai kuma hasken wutar candle dana kunna daya kara taimakawa wajen kara haskake wajen.
Ita tana gaban murhu tana zubawa almajirai abinci. Malam ya dauki nauyin ciyar da kananan almajirai wadanda karfinsu bai gama kaiwa ba. Yanzu ya daina karbar almajirai na nesa ma, sai wadanda suke cikin Yobe kawai, kuma garinsu bai yi nisa ba.
Manyan tsofin almajiranshi kuwa tuni ya yaye su, wasu sun koma garuruwansu. Yayin da wasu suna nan cikin Gashua, wasu sunyi aure, wasu suna sana'o'insu, su da garuruwansu sai dai ziyara.
Da ta gama zuba musu, ta dawo gefena ta zauna muka cigaba da yin aikin tare.

Wani almajiri yayi sallama ya shigo, duk muka amsa mishi. Ya durkusa a gefen Fatsu, yace "wai ance ana sallama da Na'ilah a waje!".
Nayi kasake da zare a hannu ina kallon yaron baki a dage, wa na sani da zai yi sallama dani a garin Gashua ne? Inna ce ta tambayeshi inji wa? Yace "yace wai ace Magaji ne".
Sai lokacin naji na sauke ajiyar zuciyar da ban san dalilinta ba, nace "kace mishi ina zuwa".

Bayan fitarshi Fatsu ta kalleni cikin yin kasa da idanu, murya cike da gargadi tace "kinsan dai Yayanki ba zai ji dadin wannan magana ba ko?".
Na kada idanu, "gaisawa ce fa kawai ba wani abu ba. Beside, babu wata magana a tsakanina da Magaji sai zumunci kawai da girmama juna".
Tace "ai shikenan!". Hijabina na saka na fita.

Magaji kusan zan iya cewa abokin Yaya ne, duk da dai ba aboki bane na kut-da-kut, they were more like classmates. Shekaru kusan uku da suka wuce ya nuna yana da sha'awar aurena, tun ma kafin mu hadu da Umar. Na sanar dashi ban shirya yin wani relationship ba a lokacin, yace ya yarda zai jira ni. Ni dai na fito fili na sanar dashi cewa bani da ra'ayin yin wata alaka data wuce ta mutunci dashi, yace babu laifi, ya amince. Amma lokaci zuwa lokaci ya kan yi min tuni, ko kuma nuna alamun har yanzu fa yana so na, ni kam sai dai in banzatar da maganar kawai.

Yanzu ma gaisawa kawai muka yi, ya sanar dani dama wucewa yazo yi, da yake jiya ya ga wucewar mu ta kofar shagon dinkinshi, shine yace bari yazo ya min barka da zuwa.
Muna tsaye anan Yaya yazo wucewa, na dan duka ina gaida shi, hararar daya daka min kadai tasa naji diyan cikina suna kadawa. Ya ba Magaji hannu suka gaisa yana ta wani basarwa, ya shige cikin gida.
Yana bada baya Magaji ya dube ni yana dan yin

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login