Showing 6001 words to 9000 words out of 73204 words
ta bada a ajiye min.
Shi yasa nake matukar girmama matar. Ko ba don alkhairin da take yi min ba, don yadda take daukata kamar diyarta. Idan nayi wani abu da bai dace ba, zata kira ni ta zaunar dani, ta bani duk wata shawara da uwa ta gari ya dace ta bawa diyarta, ta tsaya daram, akan kafafunta, wajen dora ni akan hanya, duk da cewa bamu hada ko digon gumi ni da ita ba.
Ko a hakan kadai aka tsaya, wallahi ta gama min komi. Balle kuma ayi zancen irin alkhairanta a gareni.
Duk abinda zata yiwa Janan, ba ta taba bambanta mu, sai dai ko kala da tsayi.
Na kalleta ina murmushi, "Madallah da wannan sako, lallai Umma ta gano ni. Bari in koma sai in latsa mata kira inyi godiya. Na gode kwarai".
Tayi dariya, "ai fa! Yanzu ke dai mu tafi, kada Yaya ya gaji da kira".
Kamar yana ji, sai ga kiranshi ya shigo wayar. Ta daga tana ce mishi gamu nan fitowa, ban san me yake ce mata ba, na dai ji tana cewa "minti daya!". Ta ja hannuna muka tafi.
Sai da na leka ta dakin Anty Raheemah muka mata sallama, sannan muka fita ni da Janan.
Yaya Bilal yana cikin motarshi a zaune, ya zuro kafarshi daya waje. Kyakkyawan takalmin D&G baki, budadde na fata yana ta sheki a kafar tashi. Na gaida shi kafin na zagaya ta daya gefen na shiga gefen mai zaman banza.
Janan ta leko tana min Allah ya kiyaye, yayin da Yaya ya tashi motar muka fita daga gidan.
Tafe muke a cikin motar, babu wanda yake furta uffan. Sai sautin wakar "earned it' ta weekend dake tashi a nutse. A hankali nake bin wakar, ba lallai ka sani ba sai idan ka kalli bakina sosai, inda zaka ga yana motsawa kawai ba tare da sauti ya fita ba.
Idanuna suna ta tagar gefena suna kallon cikin garin Zaria. Na dinga jin alamun idanu a kaina, nasan cewa zargin hakan ne kawai nake yi a cikin raina. Da abin ya girmama, sai na juya a hankali cikin dabara, na kalli inda Yaya Bilal yake, idanunshi straight suna kallon gabanshi. Na girgiza kai, dama sai da nace zargine nake yi.
A kofar Bitmas Bakery naga yayi parking motar. Ya kashe tare da fita daga motar yana muttering "excuse me!". Wanda ba don na juya a daidai lokacin idanuna sun sauka akan fuskarshi, na ga bakinshi ya motsa ba, ba zan ji mai yace ba.
Na zaro wayata a cikin jaka ina dubawa don in rage kadaicin zama.
Bayan kimanin mintuna biyar da fitarshi, naji an kwankwasa gilashin tagar motar, gefen inda nake zaune.
Na daga kai, naga Umar a gefen a tsaye.
Nayi murmushi tare da sauke gilashin kasa, "hey handsome, me kake yi anan?".
Shima yayi murmushin, "wai mun tsaya ne zamu sayi fruits fa, ina jiyowa kuma sai na ganki. Daga ina?".
Nace "daga gidansu Jan. Tare muke da Yaya Bilal, zai sauke ni a makaranta".
Ya gyada kai, "uhmmn... Ya shirye-shiryen tafiya gida? Jibi zaki tafi ko?". Nace "ehh!".
Yana nan a tsaye muna hira, Yaya Bilal ya dawo. Kwata-kwata ban ga wucewar shi ba, sai da ya bude motar ya shigo. Na kalli Umar ina murmushi, "handsome, bari mu wuce ko?".
Ya gyada kai, "Ok Sweety, zamu yi waya ko?".
Na jinjina kai, "in shaa Allah. See you!".
Har ya juya ya tafi, sai kuma ya juyo da sauri, "hey, bari in miko miki fruits".
Na daga baki da niyar cewa na gode, Yaya Bilal ya katse ni ta hanyar yiwa motar key. Ya kalli Umar, "ta gode, sauri muke". Da wannan yaja motar. Ina hango Umar ta cikin gilashi yana daga kafada.
A main gate na kalleshi nace "Yaya ko zaka ajiye ni anan kawai, sai in karasa ciki?".
Yadda kasan bango, haka ya maida ni. Bai ma nuna alamun yaji abinda nace ba, sai ma ya karawa motar wuta ya shige ta cikin makarantar.
A bakin hostel ya samu waje yayi parking din motar, na fara yunkurin bude kofar ina jera mishi godiya,
"na gode Yaya, a gaida Anty Ameerah".
Sai da na fita, ina kokarin maida kofar in rufe, naga yana miko min leda mai dauke da tambarin Bitmas, na kalleshi fuskata dauke da alamun tambaya, kafin inyi magana ya riga ni, "karbi mana, kina bata min lokaci!".
Nasa hannu biyu na karba, nace "nagode, Allah Ya amfana". Yace "Ameen" a kaikaice, yawa motarshi wuta ya kara gaba. Ni kuma na shige cikin hostel.
Sai bayan sallar magriba dana gama komi, na bude ledar. Bread ne da roll cake da suke yi a wajen guda biyu, da ice cream biyu shima. Na dauki daidaya na mikawa Ayla, tana ta min tsiya, wai "lallai yau Umar ya tuna damu!". Dariya kawai na mata na koma gefe ina cin nawa. Sai da na gama ci sannan na tashi na hau hada kayan tafiya gida.
Bayan na gama, na turawa Baba sako akan cewa zan taho ranar Asabar, ya turo min kudin motar tafiya gida.
Washegari muka je asibiti muka yi bankwana dasu. Daga nan muka yi bankwana da Janan, itama ranar Lahdi zata tafi Kaduna wajen Umma. Ni da ita kuma sai idan mun dawo hutu.
Na dawo hostel na karasa shirya kayana, wadanda zan bari anan kuma na hade su waje daya tsaf na rufe da mayafai saboda kura. Na share waje na zauna ina jiran kudin mota.
_*NA'ILAH!*_
Mahaifana su duka biyun, asalin yan garin Gashua ne. Mahaifina, Alhaji Al-Hassan Hannafi, cikakken haifaffen garin Gashua ne. Iyayenshi hausa/fulanin dake cikin garin ne, duk da cewa sun rasu tun ma kafin a haifeni, sai sauran dangi na nesa-nesa kawai. Yayin da mahaifiyata, Yana, ta kasance ruwa biyu. Mahaifinta Barebari ne, mahaifiyarta kuma Shuwa Arab.
Kakana Bako Audu, shahararren malami ne, Kakata Fatima da muke kira da Fatsu, ta kasance mai sana'ar sake-saken kaya, a cewarta tun tana budurwa.
Mahaifiyata ta kasance kyakkyawar mata, fara, doguwa, mai dogon hanci da dogon gashi da dara-daran idanu masu tsari. Babu abinda ta bari na Fatsu. Allah Ya hore mata hakuri, Kawaici da kawar da kai. Aurenta da mahaifina ya kawo yar matsala a tsakanin danginsu ta fannin mahaifiyarta, su a sonsu ta auri dan uwanta ta fannin uwa, ko Barebari, amma ta kafe. Sai kuma matsalar rashin aiki, don a lokacin da suka yi aure, ya gama kammala degree dinshi akan banking and finance, amma bai samu aiki ba. Jajircewar Bako ce kawai tasa aka yi auren, suma kuma dangin nata suka hakura.
Bayan auren nasu da kadan, ya samu aiki da bankin GT, anan cikin Gashua din, ya fara zuwa aikinshi.
Yaya Mudatthir shine 'Da na farko a wajen iyayenmu. Shekaru biyar cur ya bani.
Yawancin rayuwar yarintata a gaban su Fatsu da Bako nayi ta. Ba kamar Ya Mudatthir daya dauko kamanni da suffofi da halayen Mama kamar tayi kaki ta tofar, ni babu abinda na dauko nata sai yanayin idanuwanta da kuma dogon sassalkan bakin gashinta. Bayan haka, gabadayana Bako Audu ce. Ina da tsayi na daidai-wa-daida, da zubin halitta mai daukar hankali. Shi yasa bana shiga mai fitar da surar jiki. Kalar fatata baka ce, wasu kuma su kan ce wankan tarwada. Ko ma dai wace iri ce, ina jin dadi da alfahari da kalar fatata. Kalata mai sheki ce, sannan fatata mai taushi ce.
A halayen Mama kam, zan iya cewa tsafta da wasu halayen na dauko nata. Hakuri na kadan ne, sannan bana daukar wulakanci ko kadan, ko daga wajen waye kuwa. Bako ya kan ce shi duk cikin danginsu bai ga mai hali na ba, zafin kai, kafiya da taurin kai. Ina da rikakken ra'ayi, idan nace zan yi abu, to zanyi. Idan kuwa nace ba zan yi ba, mai canza min wannan magana kam sai ikon Allah.
Munyi zama mai dadi da iyayenmu, a dan abinda zan iya tunawa na rayuwarmu da wanda Mama ko Ya Mudatthir suke bani labari, Babanmu ya so mu, mutum ne mai son iyalanshi da kuma kyautata musu. Duk da cewa bashi da wani hali na azo a gani, amma rayuwarmu Alhamdulillah, babu abinda muka nema muka rasa.
Wannan kafin ya auro bakar ashana Ramata kenan. Lokacin da aka yi auren, Ya Mudatthir yana makarantar maza ta kwana a cikin Yobe. Ni kadai ce a cikin gidan, sai su Mama.
Tunda aka yi auren wannan, muka nemi walwala da kwanciyar hankalinmu muka rasa. Muka nemi Babanmu, Mama ta nemi mijinta, duk muka rasa. Rayuwar gidan ta koma kadaran-kadahan, yau daci gobe b'auri. Babu wani armashi. Ance wai ba'a kure mai hakuri, amma ni na gani akan idanu na, ranar da aka kure hakurin Mama a gidan nan, ranar da ta daga baki tace hakurinta ya kare.
Ranar ce Baba yasa belt ya zane mu ni da ita a tsakiyar gidanshi, akan naman kaji.
Ya kai mata nama ta soya, aka nemi naman a dakinta aka rasa. A cewarshi, satar nama take mishi idan ya kawo, dama kullum idan ya kai nama a soya sai ya ga babu wani bangare.
Mama tace "haba Malam, in rasa abinda zan daukar maka a gida sai nama? Tunda muke zaune da kai, na taba daukar maka abu ba tare da saninka ba?".
Budar bakin amaryar Baba sai cewa tayi, "kenan kina nufin ni na dauki naman ko kuwa me?".
Mama tace "ni ban ce ba, amma haka bai taba faruwa tsakanina da mijina ba, sai da kika zo!".
Kawai ba sai mata ta dora hannu aka ba? Ta hau ihu, tana kururuwa, ita wallahi ba zata yarda ba, ance mata barauniya, zata bar wa Babanmu gida, sai yaci gaba da zama damu tunda yana zaune a gabanshi aka zageta bai ce komi ba.
Daga nan sai saukar duka kawai Mama taji, nayi tsalle na rungumota. Bai damu ba, ya hada mu mu duka ya mana lilis, kuka ranar haka muka shiga daki muka sha, babu mai lallashi.
Daga ranar dai bamu kara ganin nama a idanunmu ba, an haramta mana shi, duk wannan bai dameni ba, sai ganin an fiddo kwanon da Mama ta zuba naman da aka nema aka rasa daga dakin matar Baba, da tsakiyar ranar Allah Ta'ala. Babu kunya balle tsoron Allah. Wani karin abin haushi ma, da naje na yiwa Baba maganar, saboda Mama taki zuwa ta fada mishi, wai bata son wata rigimar ta sake tasowa, sai ya hau fadace-fadace, abinda na kira borin kunya.
Daga ranar muka kullata da ita. Ban kara ganin idanunta da kwalli ba, ban sake kallon kanta da gashi ba, ban kara mata magana cike da ladabi ko girmamawa ba.
Shekaru shida da karin auren da Baba yayi, shekaru uku da muka rasa walwalarmu. Muka yi rashin da har yau bamu samu mun cike wannan gurbi ba. Mama ta rasu wajen haihuwa. Nakuda ta kamata, cikin dake jikinta yana wata takwas da yan satika a lokacin, haka ta rasu, bata kai ga haihuwar abinda yake cikin nata ba, Allah ya karbi ranta. Munyi kuka, kuka ba kadan ba, Allah kadai yasan tashin hankalin da muka shiga ciki a lokacin.
Muna tsakiyar karbar ta'aziyar Mama, muna cikin wannan yanayi na jimami, tashin hankali da kunar zuciya, kwana biyu kenan da rasuwar mahaifiyata, har zuwa lokacin ina jin zafin rashinta kamar a lokacin ne hannunta ya silale daga cikin nawa, babu rai. Sai ga Ramata ta fito daga dakinta, taci kwalliya ta sha gyale sai zuba kamshi take yi, tana rike da hannun Aliyu dan data haifa dan kimanin shekaru biyu, Yayarshi Maryam mai kimanin shekaru biyar tana binta a baya. Babu wanda ta kalla a cikin yan karbar gaisuwa, ta tafi wajen bikin kanwarta. Da yake duk dai anan cikin unguwarmu suke dama, layi daya ne a tsakaninmu, muna iya jiyo sautin karar kidan da suka saka na biki kamar a tsakiyar gidanmu aka sa kayan.
Har yau dake motsi, matar nan bata yi min gaisuwar rasuwar Mama ba.
Har yau kuma, ina jin zafin hakan, sai dai idan ban kalleta ba.
Ita ta gwada min cewa kishiya ba karamar masifa bace, kuma kishiya, ba mutuniyar arziki bace, shi kanshi kishin, ba abu bane mai dadi. Na fara neman tsari da kishi irin nata, a ganina bashi da amfani. Da wannan tunanin, na girma na tashi.
Rayuwar dai gata nan sai godiyar Allah. Bayan yan gaisuwa sun watse, gida ya koma sai ni sai ita don Yaya ma ya koma makaranta saboda jarabawa, sai na kasa zama a gidan. Saboda haka na kwashi kayayyakina na koma wajen Fatsu. Na dauki lokaci mai tsayi a wajensu, kafin in koma gida.
Kafin in saba da sabuwar rayuwar wannan na jima.
Da rayuwa nayi mai dadi, ruwan wanka sai an kai min bandaki, abinci sai an zo ance min in ci, makaranta sai an zo an ce min in tafi, kayan makaranta sai an wanke an goge min. Amma yanzu wadannan duk sun zama tsohon tarihi. Abinci sai na je na nema, an wulakanta ni kamar ba gidan uba na ba. Kai sai da ta kai ta kawo, sai kannenta sun je gidan sun ci abinci, sannan za'a bani sauran inci.
Kullum ina hanyar gidan su Bako, cin abinci, kullum. Na fadawa Baba ya fi sau shurin masaki, ko maganar bai taba mata ba. Ni kuma na gaji.
Idan nace ta bani abinci ta ki, sai in shiga har kuryar dakinta in zubo abina. Idan Baba ya dawo ta fada mishi, inyi kyar da idanu ince hana ni tayi, baya da yadda zai yi dani.
Cikin haka Yaya ya dawo gida. Gabadaya taso ta maida mu yan aiki a tsakiyar gidannan. Kayan fitsari da kashin Aliyu da nata har ma dana Maryam haka zata libgo mana su tace mu wanke, Yaya ne yake zama yayi aikin wankin nan, watarana yana gamawa ma zata ce sai ya sake wai bai yi ba. Idan nace ya daina mata, sai yace wai ai bamu da yadda zamu yi, matsayin mahaifiyarmu take. Sai inyi tsaki in ce Allah ya kiyaye. Kuma fa kada ku ce hakan shi yake hana ta zage mu, ko kadan. Haka kawai zata hau zaginmu, watarana ma haka har sunan Mama zata kira ta kare mata zagi, a gabanmu kuma.
Da naga ya matsa kuma ya ki saurarena, sai na kyale shi yake ta mata aikace-aikacen. Ni dai na ki. Koda ya koma makaranta, idan ma ta kawo kayan wankin sai in tsere abina, watarana ma fakat zan ce ba zan yi ba. Idan an gayawa Baba naki yin aiki, ince yankewa nayi, ko yatsa ta take ciwo, ko kuma wani abu dai. Na dai zame mata karfen kafa kiri-kiri kamar yadda nima ta zame min. Koda wasa ban bari ta juya ni ba.
Wannan yana daya daga cikin manyan dalilan da yasa kullum nayi sallah sai na daga hannuna sama na roki Allah Ya kareni daga sharrin kishiya. Allah ya kiyaye ni da haduwa da ita a gidan aure.
A cikin haka aka wa Baba kari da kuma canjin wajen aiki. Dama lokaci zuwa lokaci ana mishi canjin wajen ayyuka, amma kuma ba mai nisa bane. Wannan karon Katsina aka kaishi. Saboda haka muka fara shirin kaura zuwa Katsina. Yaya yana ajinshi na karshe lokacin a sakandire, don haka aka barshi a can. Ni kuwa da nake aji daya, aka min canjin makaranta zuwa Ulul-Albab.
Babu yadda banyi ba akan a barni a gaban su Bako, fir Baba ya ki. Ranar da za'a tafi din kam da kuka muka rabu. Da kyar aka tura ni cikin motar da Baba yayi shata ta kwashe mu zuwa Katsina.
Mun dauki lokuta kafin mu saba da yanayin sabon garin da muka je. Musamman gari inda babu dangin Uwa balle na Uba kuma ko abokai, yana da wahalar sabo, amma a hakan dai muka zauna muka fara sabawa dasu din. Anan kusa da inda muka koma, wata Ummu-Kulsum, itama kimanin shekaru na ce, mun fara sabawa da ita da mutanen gidansu nake jin labarin itama a Ulul-Albab din take, nan na makale mata sosai. Nan da nan abota ta kullu a tsakaninmu. Ya zamana na gwammace in yini cur a gidansu maimakon inyi gidanmu, saboda idan ma na zauna a gidan me zanyi? Habaici ne nake sha da bakar magana, sai kace ni ce kishiyar ta ba diyar kishiyarta ba.
Da na samu ma baba ya sai min form din islamiyar da Kulsum take zuwa shikenan, sai muka kara gamewa da ita.
Suna kare hutunsu na bita muka tafi. Duk da ba wasu kayan azo a gani aka hada min ba, naji dadin dan abinda yayi din, ban raina ba. Allah Ya taimakeni term daya kadai nayi missing, dana maida hankalina kan karatuna sosai, tuni na wuce aji biyu.
Mun koma gida hutu, na tarda amarya Alawiyya a gida. Abin ya bani mamaki, ko kadan ban ji labarin auren ba, wanda a yadda ake fada min, kusan watanta uku kenan a gidan.
Kodayake, daga bakin wa ma zan ji labarin? Tunda aka kaini aka ajiye a makarantar, ban kara ganin kowa ba. Ni da visiting dama sai in su Inna - mahaifiyar Kulsum sun je, sannan nake ganin na gida. Ni da Baba dama sai dai in ina bukatar wani abu, in ari wayar wani malami in kira shi in fada mishi. A hakan ma sai ya dauki lokacin shi kafin ya turo abinda zai turo din, kudi ne ko kuma abin bukata. Watarana kuma sai dai ya ba su Inna su kawo min kam.
Na sha shigewa bandaki in shaki kukana, ko kuma in haye can kan gadona in yi kukan. Abin yana da matukar cin rai da ban takaici, na rasa dalilin da yasa ni hakan take faruwa dani. A kaika makarantar kwana na wata da watanni amma ka rasa naka wanda zai leko ka ko da wasa? Rashin uwa ne ya janyo haka ko kuma rashin dangi? Saboda na tabbata cewa da a gaban su Bako nake, da lallai sai na ma gaji da ganin dangina. A hakan nake ta cijewa ina danne komi a cikin raina, har muka koma gida hutu.
Amarya ko in ce bazawara Alawiyya ta shiga da rawar kai da jiji da kai, sai dai bai je