Showing 54001 words to 57000 words out of 73204 words
ba'a? Wacece ke, yaushe aka haifeki? Aikin banza dana wofi!! An ga mijina mai kudi an makale mishi kamar maganadisu, ana ta wani shige da fice a gida har da rashin lafiyar karya. To ta Allah ba ta mutum ba wallahi, kuma duk dan iskan da yace zai kara dani wallahi shi zai ji jiki. Haka nan za'a koma gida aci gaba da cin tuwon datsa miyar kuka tsanwa, mu dai mun fi karfin mutum!!".
Na janye robar hannuna gefe ina kallonta, raina ba karamin baci yayi da maganganunta ba, amma na danne, nasan so take take raina ya baci in biye mata. Na fuskanceta sosai, ina watsa mata wani wulakantaccen kallo, babu shiri ta shiga taitayinta. Nace "na farko, ban san abinda na miki ba da zaki zo haka kawai ki hau zagina, sai dai bari in tabbatar miki da wani abu daya, I'm not into your husband! Hakan da kike yi ya tabbatar min da cewa ko dai kema kwacen mijin kika yi, ko kuma dama can kwacen samari da mazaje a jininku yake. Kowanne ne dai wannan matsalar ku ce, don ni ban saba ba, ban iya ba, kuma ba zan yi ba. Ke gida da dukiyar miji suka dama, dama don su kika aure shi. Mijinki baya cikin yan kayana, ki godewa Allah, da ba don haka ba wallahi da sai na sa kin zubda hawaye, don haka baiwar Allah, ki shiga taitayinki. Gida ne, daga gobe idan kika kara ganina a cikinshi ki min duk abinda kika ga dama!".
Ta daga baki zata yi magana, amma ta kasa. Tayi haka yafi sau uku, kafin tayi kwafa a fusace ta juya ta bar kicin din da sauri, na ja tsaki ina furta "sakarkaru" a kasan raina. Raheemah sakara ce, daukar zugar kanne da kawaye yana nema ya jefa rayuwar aurenta cikin garari da matsala. Wani abun ban dariya da takaici shine, zasu zuga ta ta wa miji ko danginsa rashin mutunci, ta hau kai ta zauna, su kuma su koma gefe suna mata dariya da ba'a, me amfanin hakan kenan?
Muna gamawa na koma daki na bar Janan zata gyara kicin din ta kuma hade kan kayan. Na wuce mutanen gidan a zaune su duka, muna kallon-kallo dasu daya bayan daya. Ni har mamaki nake, anya kuwa karatu suke yi? Ita dai Raheemah dama tun daga karatun diploma tace ta yanke karatu, su kuma su Salama da suka zo suka zaune a gidan da cewar karatu suke yi, ba makarantar suke zuwa ba. A sati idan suka je sau uku, to wannan shine highest. Babu aikin da suka iya sai kinibibi da gulma. Ban san daga ina Raheemah take samun idea din wai saboda Yaya nake zuwa gidanta ba, abin is so absurd. Tunanin hakan a karan kaina idan nayi sai inji kaina yana juyawa. Na dauki kudurin daga wannan lokaci, ni da gidan Yaya sai dai ziyara amma banda kwana. Ziyarar ma da ace har in gama karatuna in bar Zaria ban kara yin ta ba, da naji dadi.
Karan wayata ya katse min tunanin da nake yi nayi nisa a tunani ko karan ban ji ba sai daya kusa katsewa. Yana katsewa aka sake kira, na dauka naga Yaya Mudatthir ne, don haka na daga. Bayan mun gaisa da tambayar mutanen gida, yace ya ba wani abokinshi da zai je Kaduna gobe sako zai kawo min, zai tsaya ya kwana a Kano sai ya taho da safe, ina ganin zan iya fitowa bakin hanya in karba? Nace mishi ehh, yace to ya bashi lambar wayata zai kira ni. Nace to, tare da mishi godiya, muka yi sallama.
Komawa nayi kan katifa na kwanta zuciyata cunkushe da tunanika, har Janan ta dawo dakin hannu dauke da plate shake da abubuwan da muka yi. Ranar su muka yi ta ci ko abinci bamu nema ba.
Washegari talata aka tashi da azumi. Bayan mun shirya, mun saka uniform dinmu, muka wuce asibiti. Allah ya taimaka wanda zai kawo sakon muna fita ya mana waya, don haka muka tsaya muka amsa muka wuce asibiti. Hostel kawai na wuce na ajiye su ko dagawa ban yi ba, muka wuce ward dinmu.
#F.W.A
[23/03 9:40 AM] Jiddah Lawal: 🌟 *⋆☆A ZATO NA...!☆⋆* 🌟
*⋆©Jeedderh Lawals⋆*
*☆⋆18⋆☆*
Azumi bai taba bani wahala irin na ranar Alhamis ba. Muna dawowa daga hutun sallah zamu zana wata irin exams da suke kira 'council exam', wannan exam ita zata yi deciding din kasancewar ka nas a cikin wannan shekarar ko kuma akasin hakan. Don haka hankulan kowa a tashe yake, karatu kowa yake yi babu sassautawa balle takaitawa. Ga projects da suka sako mu a gaba. Kafin mu gama projects uku zamu yi, bayan mun gama TP dinmu munyi daya, yanzu haka preparation din proposal muke yi cikin wannan azumin. Ga kuma wani da muka fara cikin wannan satin. Yanzu haka dawowata daga cikin makaranta kenan ganin supervisor dina, wani inyamuri mai dan banzan rashin mutunci. Allah kadai yasan wahalar daya bani yau. Nayi zarya zuwa department dinmu ta kai sau goma yau, yana cewa inje in dawo, hawa bene ma kadai ya isheni. Cinyoyina masifar ciwo kawai suke yi, ga rana, ga azumi. Tun ruwan ranar Lahdi da aka yi ruwa ya mana duka, ba'a sake yin ruwa ba har yanzu, dama daminar ba karfi tayi ba.
Komawata ofishin Mr. Akafyi a karo na kusan goma, na riga na rantse na kuma maya, wannan karon idan naje ya sake cewa inje in dawo, to warewa ta kawai zanyi, in yaso na dawo washegari. Don na gaji.
Na sameshi da daya dalibar da aka hado mu wajenshi da ita a zaune akan lumtsumemiyar kujerar ofishin suna kwasar hirar abinsu. Dama ina jin kishi-kishin cewa mutumin irin yan adawa da musulmai ne, duk mai saka hijabi da nikabi, apparently shi a wajenshi makiyi ne. Nayi kwafa a kaikaice, wato ita wannan da yake tasha izgar doki aka ta fiddo cinyoyi da hannuwa waje, zai iya bata lokacinshi kacokam a kanta, tunda zai iya taba ta yadda yake so, duba da irin zaman da suka yi. Duk da akan teburi ne, sai da yayi yadda yayi yake taba hannunta.
Na gaida shi ya amsa yana wani cijewa, Allah kadai yasan iya dauriyar da nayi ban sakar mishi tsaki ba. Da ace ina da hanyar da zan bi a canza min supervisor, wallahi da da gudu zan bita, a canza min shi in huta. Sai dai a babbar makaranta kamar wannan, babu wani abu da yake zuwa ta sauki ba tare da hanya ba. Wadanda suke samun wannan garabasar it's either iyayensu suna da kudi, ko sun san wasu da suka san wasu manyan a cikin makarantar, ko kuma ke kinsan wasu manya a cikin makarantar, ta nan ne kawai zaki samu yanda kike so. Ire-iren mu mu ya-ku-bayi, da bamu san kowa ba kuma kowa bai san mu ba, haka nan muke cije duk wani wulakanci ko kaskanci da za'a nuna mana, muyi ladab, domin mu samu mu gama karatunmu cikin sauki ba tare da an janyo mana wata matsala da zata fi karfinmu ba.
Kusan mintuna na talatin a ofishin shi, yana min bayani amma rabin hankalinshi yana kan yarinyar dake gabanshi, abin ban takaici shine daga gani yayi diya da ita in ma ba jika ba. Nayi Ala-wadai a cikin zuciyata, na samu ya sallameni ni dai na bar musu ofishin, in yaso ma su cinye kansu kowa ma ya huta.
Bayan na fita daga makaranta na tsaya a banki da niyar cire wata naira dubu daya da nayi tanadinta a cikin akawun dina. Abin ban haushi da takaici sai da layi yazo kaina bayan na sha uwar rana da jira, wai kuma suke ce min 'insufficient balance', haushi yazo min iya wuya. Na gwada ciro naira dari biyar, shima a lokacin suka ce babu. A matukar fusace na karasa hostel. Na san ko hauka nayi ba zan cewa Baba ya turo min kudi ba. Ni yanzu haka taraddadin yadda zan ce ya turo min kudin jarabawar da zamu yi nake yi. Kudi ne kusan naira dubu hamsin da doriya.
Na haye kan katifa na kwanta kawai na lumshe idanuna, gajiya, tunani, yunwa, zafi kai komai ma, suka taru suka min rubdugu sai dana rasa ina zan jefa kaina inji sauki a ciki. Sai da yamma tayi likis, ban ma sani ba sai da Esther ta fara tambayata wai yau ba zan yi dafe-dafen karya azumi ba? Sannan na mike ina dingishin wahala. Sauran kayan miyar da suka rage min basu da yawa, dama nufina idan na ciro kudin in tsaya a kasuwa in siyo kayan miyar in kuma karo wasu abubuwan, to kuma ga abinda ya faru. Sauce nayi, na dafa farar spaghetti da zan ci da ita. Nasan zasu isheni in sha ruwa in kuma yi sahur.
Na sauka kasa dakin wata student da take saida ruwan sanyi da kankara, na sayo. Zobon dana yi saura jiya na kara gyarawa na juye a cikin jug. Naje na dauro alwala na dawo na zauna akan abin sallah ina lazumi har aka kira sallah. Na dauko dabino kwara uku da Yaya Bilal ya bani ranar talata, irin yan makkah dinnan gida hudu, nasan har azumi ya kare ina ci, na ci. Sai da nayi sallah sannan na ci abinci.
Ina gama sallar isha'i naji wata irin gajiya da kasala ta saukar min, haka nan na daure nayi tarawihi. Zuciyata na rada min in kwanta kawai in huta, it has been a long day, yayin da wata take kara karfafa min jiki akan in dai daure in tafi karatu. Bayan dogon nazari da saka da warwara dai na daure na warci wayata da littafai na tafi aji. Kwana biyu ko zaman kallon ma bana yi. Yawancin fina-finan da nake kallo kafin, ko lokacin sallar tarawihi ake yinsu, don haka na ajiye su gefe. Idan na samu lokaci ina hawa YouTube in kalla dai. Yanzu ma nasan idan na shiga common room ba karatun zanyi ba, shi yasa na fara zuwa class.
Karfe sha daya tana yi, na fara haramar hada kan kayana. Na rungumi littafan dana dauko na fito daga cikin theatre hall din. Yanayin wajajen musamman da dare, zaka ji shi shiru, babu zirga-zirgar komi sai ta ababen hawa da basu cika yin wajen hostel din ba sai da can babban titi sai kuwa dalibai da suke zuwa aji ko kuma masu dawowa. Na kan ji yawancin mutane suna korafin tsoron wucewa ta wajen da dare, sai dai ni ban taba ganin dalilin da zai sa naji tsoron ba. Naga a cikin waje mai tsaro muke, idan ba wani Iko na Allah ba, babu abinda zai faru da mutum.
Idan nayi addu'ata na shafa ni kam shikenan, sai in jona earpiece in done kunnena, in rufe komi kwata-kwata sai karatun da nasa, ko kida ko kuma wa'azi. Babu irin yanayin da nake matukar so irin wannan. Na kan ji ni free, without worries.
Yanzun ma abinda nayi kudirin yi kenan, musamman yadda ranar yau ta kasance min. Ji nake kamar inyi tsuntsuwa in ganni akan katifata. Sai dai banyi nisa da fara tafiya ba, kiran Muhammadu na ya shigo wayata. Ina jin wannna muryar tashi yana ambatar "baby na!", I was a goner. Mantawa nayi da komi dake cikin duniyar nan, har ni kaina kuwa, sai shi kadai. Rakiya ya min har cikin dakin da nake, muna ta hirarmu cikin raha, kafin muka yi sallama dashi. Na cire kayana na sa na barci na dauro alwala nazo na kwanta.
Karfe uku alarm din dana sa ya buga na tashi, na fita na dauro alwala na zo na fara nafilfili har lokacin sahur yayi, nayi na sake tado wata sallar har dai aka kira sallah nayi na zauna ina karatun Al-Qur'ani kafin lokacin fara shirin shiga cikin asibiti yayi.
Kamar yadda nayi tunani, maganar kudin jarabawa bata zo min da dadi ba. Yadda Baba ya rufe ido yana masifar shi bashi da kudi, ina nema in tatuke shi, abin ya bani mamaki. Tun bayan kudin school fees daya turo min, naira dubu goma ta sake hada ni dashi. Yanzu kusan wata na biyu kenan a Zaria, amma ba halin in daga baki inyi maganar kudi sai ya hau zagina. Ko provision yawanci Yaya ne yake turo min su, sai kuwa kudin da yake turo min jifa-jifa, dasu nake amfani in sayi kayan bukata. Bayan doguwar wayar da muka yi dashi a ranar Assabar kenan, daki na koma na kwanta. Esther ta tafi weekend gidan kawunta, Maimunah kuma bata ma dakin tun jiya, babu wanda yasan inda ta tafi. Don haka ni kadai na kwana a daki.
Nayi lamo akan katifa cikin tunani iri-iri, kala-kala, ban taba jin karatun nan ya fita a raina ba sai yau. A raina na raya wai da wanne ake so inji ne? Abu ne da bai taka kara ya karya ba, wanda na tabbata yafi karfin Baba, amma kullum cikin ja wa kanshi babu yake, kullum babu, kuma babun a kaina kadai take.
Yawancin matsaloli irin haka idan suka taso dama sai dai in tuntubi Yaya da maganar, idan bata fi karfinshi ba ya maganceta, in kuma tafi sai ya kai ga dangana da su Malam. To ita kuma rayuwa ba zai yiwu taci gaba a haka ba, ba zai yiwu ace kai kullum cikin bani-bani da a maka-a maka kake ba, kowa ma dama zai ji ya gaji.
Sai dai idan nayi duba ta wani bangaren, sai inga yaushe na cika bani-bani kamar yadda Baba yace? Tsakanina dashi kawai kudin handout ne, sai abinda yaga dama ya dan lafo min ciki kawai. Dama can yawancin hidima da dawainiya Yaya ne yake yi, idan aka samu ya biya school fees da kyar, ya hado min provision, to sauran fa sai dai yadda hali yayi, sai na sha matukar wahala ya kuma yazga ni yadda yaga dama sannan zai turo min na bukatun yau da gobe. To maganar gaskiya na gaji yanzu, yanzu haka kwanciyar da nayi ina tunani, tunanin hada kan kayana nake in koma gida kawai, azabar ta isa.
Sai kuma naga idan ma na koma, ni zan kwari kaina, babu wanda zai ji a jikinsa dai sai ni. Don haka naci gaba da tunani ina laluben mafita. Nasan mafita daya itace in fadawa Yaya, amma gani nake kamar abin yayi yawa. Shi shikenan kullum cikin ji da matsalata, kullum babu hutu?.
Ban tashi daga kwanciyar ba sai da aka kira Sallar azuhur, ashe wani wahalallen barci ne ya daukeni. Wani irin barci mai dauke da wasu irin sarkakkun mafarkai. Na tashi ina mika da hamma, maimakon inji gajiyata ta tafi, sai naji kamar an dauko gajiyar duniya ne an dora min aka. Haka nan na lallaba na watsa ruwa a jikin nawa ya dan min karfi, sannan nazo nayi sallah.
Ina cikin karatu Janan ta kirani. Roko na ta dinga yi akan inje in mata weekend, kai tsaye nace mata a'ah, ta dawo tana magiyar to inje in tayata shan ruwa, nan ma nace a'ah. Ni dai tunda na samu nayi sa'a, Allah ya taimakeni na baro gidan, ai an wuce wurin. Ta gaji tayi fushi ta ajiye wayar. Da yake ba a cikin yanayi mai dadi nake ba, kyaleta nayi kawai.
Yinin ranar haka na yi shi sukuku, can da yamma wai sai ga Maryam, mun gaisa da ita gari-gari, wai in na shiga kasuwa in sayo mata sarka da yan kunne idan ma naga da halin takalmi in karo, naji kamar in hau rusa mata ihu na dai cije nace mata to kawai, na ajiye wayar.
*
Dole kanwar naki haka na dage na kira Yaya zuwa ranar talata, domin duk ta inda na buga abubuwan babu sauki, babu wata mafita. Na zayyane mishi matsalar da muke ciki da Baba, Yayan yayi shiru yana tunani, kafin daga baya yace zai kira shi sai yayi mishi bayani. Na mishi godiya nace to, na kashe wayar.
Allah ya taimakeni cikin satin aka turo mana kudin scholarship da aka saba bamu. Kuka ne kadai banyi ba ranar saboda murna, dama nayi karaf, bani da ko sisi. Haka kayayyakin da suka rage min duk sun tasamma karewa. Yawanci idan aka turo min ina fadawa Baba, amma wannan karon da yake a wuya nake da kowa, babu wanda yaji labari. Kasuwa kawai na fada.
*
Abu wasa-wasa, tun ana yau azumi, har gashi mun zo mun ci tsakiyar shi. Yaya ya samu ya shawo kan Baba da kyar ya turo min kudin, naje na biya. Allah ya taimakeni basu kai ga rufewa ba. Abubuwa zuwa yanzu sun yi min sauki nesa ba kusa ba, ba kamar satin daya gabata ba. Ban bar wannan abin ya dameni ba ko kuma ya hana ni aikata abubuwana na yau da gobe. Allah ya kan jarabci bawanshi ta kowace irin hanya. Zata iya yiwuwa ta kankanin abu, ko babba, ko iyaye, ko 'ya'ya, ko cuta, ko kuma sauran abubuwa. Na yarda hakan yana daga cikin jarabawata, don haka ban damu ba sosai. Fatana Allah ya bani ikon cinyeta. Nasan watarana idan da rai, hakan zai zamo tamkar ba ayi ba. Don haka nake godewa Allah a kullum, kuma a koyaushe.
Jiya Yaya Bilal ya tafi Umarah shi da Anty Ameerah. Ba'a tafi da Raheemah ba saboda last year da ita aka je a cewar Janan. Bata ji dadin hakan ba, saboda haka sai da suka dan yi rikici da Yayan akan wai yana gwada mata rashin adalci kafin ya tafi. Bayan tafiyar tashi kuma sai abin ya koma kan Janan, tsangawamar yau daban, ta jibi daban. Wai kicin ma suke rufe mata yanzu, bayan da Yayan zai tafi sai daya cika kicin din ya batse shi da duk kayan amfani. Nace ta kira shi a waya ta gaya mishi mana, tace wai bata son ta dinga tada musu zaune tsaye, nace "ai sai kiyi tayi!".
Kawai sai ganinta