Showing 45001 words to 48000 words out of 73204 words
fara cin duniya, gani take yi kamar ita din wata shegiya ce. Ni kuma naga meye abin dagawa akan haka? Akwai masu motoci da suka ninka nata a kyau da tsada da ake zaman lafiya dasu a cikin hostel din, wadanda iyayensu suka fita kudi ma. Ni fa ganina nake daidai da uban kowa, yadda kake sanya sutura mai tsada kayi kyau, haka nake saka mara tsada inyi kyau, har ma a kasa banbance mu. Abinda zaka fini kawai in damu, shine yawan maki, a test, assignment, exam ko result, wannan shine kawai. Itama don ta ita ne da bamu gaisa ba, sai dai ni ba'a zaman gaba dani. Ko sannu sai ta hada mu da kai, in yaso zabi ya rage naka, ko ka amsa, ko kar ka amsa, matsalarka ce, ni dai na fita hakkinka. Esther ce muka fi mutunci da ita dama.
Kafin a kira sallah na dora jollop din macaroni, ana kiran sallah na rage wutar karamin gas din dana saya na tada sallah ta. Murjanatu tana zaune a gefen wayarta tana hira da saurayinta har na gama sallah ta na zuba abinci, tunda nazo dakin na kula sallah bata dameta ba ko kadan. Yau da asubahi dana tasheta sallah, cewa tayi period take yi. Sai da rana ta fito gade-gade, tana kallonta suna kallon juna, wai ta kalli gabas ta tada sallah. Na girgiza kai kawai dana tuno abin.
Tayin abincin na mata ta girgiza kai kawai taci gaba da wayarta, nima na girgiza nawa kan na saka cokali na fara ci. Ko loma uku banyi ba Esther ta shigo dakin, nan ta dauko nata cokalin muka zauna muka ci muka yi nak, har da kari. Na sauka kasa na wanke plate din, na sake dauro alwala na dawo sama.
Kan sallaya na koma na zauna ina lazumi har aka kira sallar isha'i nayi. Karfe takwas saura na dauki dan karamin littafin da nake daukar bayanai idan mun shiga ward, textbook akan matsalar da mata ke fuskanta yayin da suke dauke da juna biyu, sai kuma biro da pencil na sauka kasa. Common room naje na zauna, ba jimawa aka fara hasko diramar da nake zuwa kallo kullum. Ko bayan an gama anan na zauna can wani lungu inda babu hayaniya sosai, na cigaba da bita da karatuna har karfe goma tayi. Na mike na koma daki.
Yanzu kuma Murjanatu ce bata dakin, babu mamaki daya daga cikin samarinta ne yazo.
A rayuwar makaranta, musamman wadanda suke zaune a cikin hostel, babu abinda idanunka ba zasu jiye maka ba. Babu tabara, rashin kunya da banzatar da kai da ba zaka gani ba.
Kai ne iyayenka suka taso ka tun daga wani gari, suka kawo ka wani, domin me? Domin fa kayi karatu ne, idan kuma kayi kai zai yiwa amfani ba wani ba. Amma sai kazo, ka biyewa kawaye da samarin banza ayi ta bushasha da dibar albarka, har ma ka manta da abinda ya kawo ka. Ka ci amanar kanka, ka ci ta iyayenka, ka kuma yaudari kanka. Tunda daga karshe dai, su wadanda ka rike din, zasu zo su maka tawaye, kawaye da suka zuga ka su yaye maka baya su koma gefenka suna maka dariya, samarin banza da suka daure maka gindi su samu wasu da suka fi ka, su kyaleka. A lokacin ne kuma idanu zasu raina fata, an barka da carry overs in ma kayi rashin sa'a da spilling, daga nan idan shaidan ya maka huduba, ka koma bin lecturers domin gyara takardu. Idan kuma hakan bata samu ba, a barka da hamma, kayi babun badinihu, baka ga tsuntsu baka ga tarko, sai zare idanu. Lokacin ne kuma zaka yi dana sani.
Yanzu ita Murjanatu da muke magana a kanta, yar spilling ce. Kamata yayi ace yanzu ta gama nata aikin tana internship kamar yadda sauran yan ajinsu da suka gabata suke yi yanzu haka anan Shika din, amma gata nan.
Yanzu haka har nayi shirin kwanciya barci na kwanta, bata dawo dakin ba. Sai wajen karfe goma sha biyu da rabi na dare sannan ta turo kofar dakin ta shigo. Ina kallonta ta cikin dusu-dusun hasken dakin ta kwanta akan katifarta. A raina na nema mata shiriya da ita da sauran masu hali irin nata, Allah ya nuna musu hanya madaidaiciya.
#F.W.A
[17/03 9:38 PM] Jiddah Lawal: 🌟 *⋆☆A ZATO NA...!☆⋆* 🌟
*⋆©Jeedderh Lawals⋆*
*☆⋆13⋆☆*
"Assalamu Alaikum wa Rahmatullah wa Barakatuhu, ina fata kin wayi gari cikin koshin lafiya ya ke ma'abociyar haske dake haskaka fadin zuciyata bakidayanta!".
Kamilalliya, kuma tattausar muryar ta fada, cikin wani irin huskinesa da sexiness da... da... abubuwa da dama.
Jin muryar kadai ya haifar min jin wasu abubuwa, wadanda nafi fahimta a cikinsu shine faduwar babu gaira babu dalili da gabana yake yi, sai kuma wata irin kasala, sauran na kasa fahimtar ko meye kuma.
Karfe tara na safiyar ranar asabar, sai dana kusa tuntsirawa kasa lokacin da vibrating din da wayata tayi ya tashe ni daga daddadan barci da nake yi. Sai dai ba wannan bane yasa nayi suman zaune ba, ko kuwa kwance zan ce? Sunan wanda yake kiran ne da yake tsalle yana rawa akan screen din wayata ya kusa sumar dani. Mamakin ya wuce misali, haka fargabar ta wuce misali, nayi zaton mafarki nake yi, hakan ne yasa na kurawa wayar idanu tana ta ringing, wakar Chainsmokers da cold play ta 'something just like this' tayi-tayi har ta katse. Ba'a dauki wani lokaci ba aka sake kira, nan ma dai naci gaba da kallon wayar. Sai a karo na uku ne na samu kuzarin kifta idanuna, sannan na daga wayar na kara a kunne.
Muryar data fara dakar kunnena rendered me speechless, na kasa magana. Na tabbata a lokacin da za'a dauki abin gwajin bugun zuciya, za aji zuciyata tana gudun fanfalaki.
Na sha ayyana yadda muryar wannan bawan Allah zata kasance, har mafarki na sha yi. Amma muryarshi da naji yanzu, ban taba tunanota ba, ban taba mafarkinta ba, ban taba jin mai kama da ita ba.
Na hadiye yawu mukut! Da kyar na iya warto murya da natsuwata da suka fara shawagi a saman kaina suna kokarin dagula min lissafi.
Cikin rawar murya dana rasa dalilinta, na amsa. Zata iya yiwuwa saboda yadda muryarshi ta sanya zuciyata tsalle ne, ko kuma saboda yadda muryar tashi ta sanyayar min da jiki ne, zata kuma iya yiwuwa saboda yadda abin yazo min a bazata ne, za kuma ta iya yiwuwa duka abubuwan ne.
Yace "wow, Masha Allah, ban taba tunanin muryarki zata kasance haka ba, lallai tsarki ya tabbata ga Ubangijin daya tsara ki, ya baki murya wadda zata iya shagaltar da mutum ga yin abu, shin ko ya zaki kasance a fili?".
Sai naji kunyar maganganunshi sun kama ni, don haka na buge da gaida shi. Ya amsa, ya kara dorawa da, "To daga farko dai sunana Muhammad M.B, ni bahaushe ne sannan ina aiki a Abuja, ban sani ba ko malamar ta ganeni?".
Nayi yar dariya, "na gane ka mana, Mr. Mysterious!".
Ya saki wata irin tattausar dariya data sa na kara narkewa akan katifata, jin muryarshi nake kamar ana min busar sarewa a kunne, yace "da gaske nayi zaton sai na zauna dogon bayani, shi yasa tunda gari ya waye nake ta hardar abinda zan fada miki, ki ce da ban wahalar da kaina ba?".
Na gyada kai ina dariya kamar wata sakara, "gaskiya kam, da ka kira tun da wuri".
Yace "yadda zan katse miki barci? Yanzu ma naji kamar daga barci kika tashi, sorry, na katse miki barci. Na kasa daurewa ne wallahi. Ina fata banyi laifin komi ba?".
Na girgiza kai kamar yana kallona, "ko kadan baka yi laifi ba, zan ma iya cewa kayi daidai!".
Ina jin ajiyar zuciyar daya sauke, "good. Don ba zan so ace daga wayar farko ba na fara yin laifi ba gaskiya". Duk muka yi dariya.
Daga nan duk muka yi shiru, baka jin sautin komi sai karar dake fita daga cikin wayar kawai. Zuwa can yayi gyaran murya, yace "to Malama Na'ilah, kamar yadda nasan cewa kin san dalilin da yasa na tunkareki tun farko har ya kawo ga wayar da muke yi yanzu, magana ce ta so. Wadda nake so, kuma nake fatan idan Allah ya yarda ya amince, zata kaimu ga aure na sunnah. Magana ta gaskiya ban fito da wasa ba, kuma nayi niyar dana bayyana a gareki, muka samu fahimtar juna ni da ke, ba zanyi sanya ba zan fara zancen aurenmu, in samu in killace ki a dakina kafin kwado ya min kafa, me kika ce?".
Daga jin sautin muryarshi da yadda yake fitar da haruffa daya bayan daya, kasan cewa kaji mutum wanda yasan ciwon kanshi, wanda yasan me yake yi, ya kuma san yadda duniya take ci. Naji ya kara shiga raina. Nan nayi mishi bayanin cewa yanzu dai karatu nake yi, sannan kuma akwai wanda muke tare dashi a halin yanzu dai, ban boye mishi komi ba, na fada mishi komi da komi. Shi kuma ya burgeni daya saurareni tunda na fara magana har na gama bai katse ni ba. Hakan ya kara min wata martabar shi a cikin idanuna.
Sai dana gama, ya nisa yace "naji dadi kwarai da baki boye min komi ba game dake, sannan maganar karatu a wajena ba matsala bace, koda ace baki fara ba, zan iya daukar nauyinki har ki gama, balle kuma duka-duka Allah na tuba menene ya rage a cikin karatun naku yanzu? Sauran kadan ne. Zancen wanda kuke tare kuma, wannan ai lokaci ne zai nuna mana ko ke din ta wacece. Illa iyaka, mutum ya zage damtse, ya shiga filin dagar neman ki sai aga wanda yake da nasara!".
Nayi dariya sosai da maganganunshi, da alamu Allah ya hore mishi iya sarrafa maganganu matuka. Shima ya biye min muka yi ta kyakyatawa kamar wasu kananun yara. Sai dana nutsa sannan nace mishi, "to Allah dai yayi mana zabin mafi alkhairi".
Ina dire aya ya cafe da; "in shaa Allahu ma kece alkhairin", ko yawu bai bari na gama hadiyawa ba.
Nace "to Allah ya yarda".
Yace "ameen... Tunda yanzu mun yi wannan magana, ina fata mun fahimci juna ni dake? Kina da wata tambaya da kike son yi game dani?".
Nace "na fahimci komi, tambaya kuma bana tunanin a yanzu akwai ta, amma idan ina da ita nan gaba, zan yi maka".
Yace "zaki iya yi a koda yaushe, tunda yanzu na ji muryarki, ina tabbatar miki da cewa sai kin gaji da ganin kira na a wayarki, don zan so ace kullum cikin sauararen muryarki nake!".
A zuci so nayi in ce, "ai nima hakan take", amma a fili sai nayi dan murmushi kawai.
Yace "yanzu dai bari in barki ki karya, nasan baki karya ba kika fara waya da ni. Bayan kin gama cin abincin zan kira ki mu dora daga inda muka tsaya, ki huta lafiya Baby na!". Daga haka ya tafi.
Na bi wayar da kallo kamar shine a gabana, ina nanata kalmar 'baby na!' a cikin kaina kamar wata bakuwar kalma da ban taba jin kamarta ba sai yanzu. Gabadaya sai naji cikina ya cika, bana marmarin komi. Don haka na koma kan katifa na kwanta ina kara maimaita hirarmu da Malam Muhammad M.B a cikin zuciyata kamar wani shirin film da yake matukar kayatar dani, ina zabga murmushi kamar wadda ta fara zarewa.
Amma dan saurara, wani hanzari ba gudu ba., me yasa muryarshi take min kama da wani wanda na sani? Ban tabbatar ko waye ba, amma naji kamar na taba jin muryar nan, inda na taba ji dinne na kasa tunawa.
Ban san iya lokacin dana dauka a cikin wannan hali ba na tsananin bege, sai dana ji an daka min duka a cinya. Nayi firgigit! Na mike zaune ina sosa wajen. Esther dake gefen katifata a zaune dangargar ta kalleni tana murmushi, "Babe, tunanin meye kike yi ne haka? Hala oganki ne?. Ta fada cikin harshen turanci kamar yadda ta saba magana dashi.
Nace mata "nothing o...".
Tace "na lie... Kada kiyi tunanin ban ga yadda kike ta murmushi ba kina dariya lokacin dana zo fita". Na zaro ido ina kallonta, da gaske har fita tayi ta dawo ban sani ba?.
Ta kyalkyale da dariya ta dauki wata bakar leda da ban kula da ita ba, ta miko min, "dama kina ta soyewa ta ina zaki ji motsin mutane bayan kinyi nisa a duniyar da daga ke sai shi? Na tabbata za'a iya ciccibarki a lokacin baki ma sani ba!".
Harara kawai na jefa mata cikin murmushi. Na daga ledar, kamshin masa ne ya fara bugo ni tun ma kafin in ga masar. Sai a lokacin na tuna da cewa jiya da dare kafin mu kwanta na fada mata idan zata je siyan masar yau da safe ta tashe ni koda ina barci ne, don marmarin cin ta nake yi sosai.
Nayi murmushi ina kallonta, "nagode kwarai Esther, ta nawa ce kika sayo?".
Tace "ban san ko ta nawa kike bukata ba, sai na sayo ta dari biyu".
Nace "tayi, nagode fa".
Tace "babu damuwa!".
Tashi nayi na dauki purse dita na bude na bata kudinta, na kara mata godiya, sannan na sauka kasa naje nayi brush na koma dakin. Bowl na dauka karama ta plastic na juye miyar da aka daure a cikin leda, na fara cin masar.
Ina cikin ci ne na dauki waya na kira Janan, finally, abinda muke ta jira, mysterious dina dai ya kira waya. Nan muka sha ihun murnarmu da maida yadda aka yi. Wani labarin ma ai sai ta shigo ranar Monday sannan za ayi shi baki da baki.
Yinin ranar wannan gabadayanshi, Allah ne kadai yasan farincikin dana yini dashi, wata irin far'ah dana rasa dalilinta, nishadi dana rasa dalilinshi. God, I'm so whipped, totally!!.
Yini aka yi ana ruwa duk da ba mai karfi bane, amma yanzu da nake kudundune cikin bargo a dakina da dare, sanyin da ruwan saman ya haddasa da kuma kamshin ruwa da jikakkiyar kasa da yake tashi, da kuma tsananin taushin muryar Mysterious dake ratsawa ta cikin dodon kunnena a daidai wannan lokacin, sai naji babu wata damuwa a raina. Babu kowa, kuma babu komi a wannan lokacin sai ni sai shi kawai. And nothing matters!.
Tuni mun riga mun sabarwa junanmu jin muryar junanmu a kowace rana. Muryar dayanmu zamu tashi da ita, texts zasu mana rakiya duk inda zamu je a yinin ranar, haka kuma zamu ji muryar juna kafin mu kwanta da dare.
Da asuba tun ma kafin alarm dina ya buga, Muhammad zai kira ni ta waya, nan kira kawai zai yi in tashi, to idan na gama ne zamu yi wayar minti biyar zuwa goma, sai muyi sallama. In shiga wanka in shirya, in karya, in fita. Kafin in karasa ward ya turo min text mai cike da kalamai dadada da zasu sa in yini ina kallon wayata cikin murmushi, ina kara karanta shi over and over, sai in tura mishi amsa. Kafin yamma ta fadi at least zamu yi musayar messages sau uku ko fi, sannan da dare dole ne sai ya kira ni kafin in kwanta barci, watarana ma muna cikin hirar barci zai daukeni sai dai ya kashe wayar in yaji shiru.
Ni kaina nasan cewa na canza, kamar wani abu yayi snapping a jikina ne. Duk wasu makamai da katangu dana sa a jikina, daya bayan daya Muhammad ya bisu ya sassare, kamar basu taba wanzuwa ba.
Wani abu ne da bai taba faruwa dani a tarihin rayuwata, da shekaruna dai-daya har ashirin da hudu a duniya ba. Ban kuma taba zaton zai farun ba. Amma yanzu daya faru, sai nake jin ina zargi da tuhumar kaina, me yasa tun farko ban bar kaina nima naji dadin wannan abu ba? Na dinga takura kaina, ina matsawa kaina? Kodayake, komi yana da lokaci, kuma kamar yadda Janan take yawan cewa, _'idan lokacin ki kamu da so yayi, baki da yadda zaki yi, kina so ko ba kya so, zaki fada tarkon ko, kin sani ko baki sani ba!'._
To yanzun ma ina tunanin abinda ya faru kenan, lokaci na ne yayi. Na kamu da soyayya, soyayyar Muhammad mai zurfi. Zurfin da ya kai naji ina so inyi kugi da karaji, wanda duk duniya da mutanen cikinta zasu ji cewa ina cikin zazzafar kaunar mutumin da ban taba sakawa a cikin idanuna ba!.
* * *
"Kyawunta ace wannan azumi da zai zo, wani mutumin kirkin zai zo ya dauki dubu ko hamsin ce ya baka, ya hada ka da buhun masara, gero, sukari ko rabin buhu ne! Kai ai da kakar ka ta yanke sa'a!! Sai ka nemi inuwa mai ni'ima kawai ka fuske, ka yini tun safe har dare a kwance Malam, babu ruwanka!!".
Wani kwandastan mota da muka hayo daga asibitin Shika zuwa kasuwar Samaru yake cewa. Duk cikin motar aka saka dariya.
Wani mutum daga baya yace "wannan duk mafarki ne kake yi, wanda baya zama gaskiya. Abu mai yawa da zaka samu daga hannun manyan nan shine kwanon masara ko gero, ba'a hada maka guda biyu ma. Sai ka samu wani mai tsoron Allah shine zai kawo wata lalatacciyar dari biyu ya dora maka yace kayi nika. Ai yanzu wannan alherin a tsakanin masu kudi kawai ake yi, ka dauka ka kai gidan mai kudi, shima idan ya tashi yin nashi sai ya maido maka. Su kuma talakawa sai suje su nemo da karfinsu".
Wani ya cafe zancen, "ai sai dai kawai Allah ya kara rufa mana asiri. Wata irin rayuwa ake yi ta danniya da rashin tsoron Allah, mai shi ya dannewa mara shi, masu kudin namu kuma basa taimakon talakawanmu. Kowa kanshi ya sani ba wani abu ba, Allah dai yasa mu dace!". Duk muka amsa da ameen.
Har motar ta tsaya