Showing 12001 words to 15000 words out of 115646 words
alqur'ani dazai raba, ko Allah zaisa yasamu Lada saboda gobe za'a kama azumi, Ana idarda sallar magrib din yatashi yafara Rabon alqur'ani, mutanensa suna tayashi.
Limamin masallacin ne yayi masa addu'ah, Sannna yafara yin wa'azi kafin lokacin sallar ishsha'i, wasu mutane ne guda biyu dasuke zaune asahun bayansa, yaji suna zance qasa-qasa, da alama ba'a Garin sukeba, zuwa sukayi, gaba daya Sai hankalin sa yabar kan wa'azin da akeyi, yakoma kansu, dayan yaceda dayan "yanzu Mansur kaduba kagani yanda masu kudi suke jin dadi a wannan Garin? Amma kwata kwata basa taimaka wa talakawan dasuke wasu qauyukan, kaduba kaga haduwar wannan masallacin fa, ni idan nasamu Nan ma ai naji dadi, wannan shi ake kira aljannar duniya"
Wanda aka kira shi da Mansur yace "wallahi hakane zakarai, kaga fa har kyautar alqur'ani ake bayarwa, mukam Bana zamuyi azumi a dadi, tunda ba yanzu zamu koma arewa ba, gashi babu zafi, ga ruwan sama, can Kuma Sai zafi"
Zakarai yasake yin qasa da murya yace "wallahi saida nazo Garin Nan nasan cewa bazan mutu acikin wahala ba, gaskiya kudi yayi, saboda yanzu rashin kudi yayi yawa, marasa qarfi suna buqatar taimako, inda ace masu kudi zasu dinga taimaka musu Aida sun samu Lada, wani ma baisan irin addu'ar da za'ayi masa ba, qarshan ta wani yana masa addu'ah kaga Allah ya amsa masa, saboda kowa da irin baiwar da Allah yabashi, wancen azumin fa, gidan wani maqoci na, kullum gero sukeci, safe rana dare, shine abincin, idan aka Sha ruwa kuwa farau-farau suke hadawa, dayake Ina Dan taba sana'ar qanqara to shine Nima nake Dan taimaka musu, Amma wallahi kafin akama azumi geron ne, haka cikin azumin ma de shine abincin "
Jikin Shahaab yayi Sanyi kalau, yanzu acikin wannan qasar ne za'a samu masu cin gero da azumi? Kuma Ahaka suke rayuwa?
Har aka idarda sallar Isha'i, yana wannan tunanin a ransa, daya koma gida ma suna yin dinner mama taga kamar hankalin sa baya kan abincin, kawai de yana cine
Shikuma tunani yakeyi a ransa, mutum yaci gero da Azumi?
Mama kuwa Kallan sa take,tun daga fuskarsa har zuwa faffadan qirjinsa, tambayar kanta take Anya kuwa Mahmud lafiya kalau yake? Kokuma bashida lafiya? Kwata kwata Bahaka mahaifinsa yakeba,saboda idan de bata manta ba, lokacin da sukai aure idan babansa yafara abu daya saita gudu(🙈)
Kuma idan de Shima ubansa yabiyo, to jarabar sama kadai zatasa matarsa tasamu ciki duk dade haihuwa tsari ne na Allah, to Amma shi shiru kakeji da alama de ba qalau din yakeba, duba da yanda yatsani ayi masa maganar qarin aure.
Ruwa yadauka yasha, Sannna yad'auki tissue ya goge bakinsa, zuwa yanzu yagama yanke shawarar rabawa talakawan wasu garuruwan kayan abinci, ko Allah zaisa Shima wani yayi Masa addu'ah Allah yabashi magaji, Kallan munirat yayi, ya qifta mata ido alamun yana jiranta, Sannna yayiwa mama sallama yatafi part dinsa
Bayan sunyi shirin bacci yaja munirat jikinsa ya rungume ta,ganin kamar baida damuwa yasa ta bijiro masa da maganar ten million din Dayayi mata alqawari zai bata.
Kallan ta yayi, "idan kina buqatane yanzu, to nayi Miki izni kibude loka ki dauka, ten million din Kuma tunda nayi Miki alqawarin baki to zan baki, but ba yanzu ba, akwai abubuwan dasuke gabana yanzu"
Rantane yayi baqiqqirin, Amma dayake yar duniya ce, bata nuna masa ba, saima kissing din wuyansa data hauyi, alamun furucin nasa yayi mata dad'i, dayaga tana neman janyo masa ruwa, saiya rungume ta yayi mata rad'a a kunne, yasan cewa idan tatada masa Hankali ma wahala kawai zaisha, saboda kwana biyun Nan gaba daya tasauya masa, jinta yake tamkar abinci ce medadi Amma Kuma babu Maggi da gishiri acikinsa(😲)
daga Nan yayi bacci, munirat kuwa, kasa baccin tayi, baqin ciki ne fall ranta, Sai gab da lokacin sahur bacci me dadi ya dauketa, shi kuwa tun qarfe uku da rabi yatashi yafara nafilfili, yana roqon Allah yasadashi da alkhairin dayake cikin wannan wata Mai Rahma daya kama yau
Sai shine yatashe ta tahada musu abunda zasuyi sahur dashi, shikam kawai baqin tea yasha, Bayan ankira sallah yafice masallaci.
Dasafe yana tsaye gaban mirror din dakinsa, agogo yake daurawa ahannunsa,kamar kullum yana Sanye cikin suit wadda ta kar6i fatar jikinsa, ya maqala waya a kafadar sa yana magana cikin aji
"Ramadan kayi magana da MD na company yahada manaTrella ta macaroni da taliya guda goma "
"yanzu ake buqatar trella goman?"
"no, cikin satin nan nakeso agama hadawa, Sai kayi magana da Baba yahuza, zai hadaka da mutanan dazasu dauka, Sai araba duk garuruwan daya kamata"
"ok to shikkenan, jiya naje ganin sabon company, komai yayi kyau sosai Abokina, Sai aiki ake wuta-wuta,da alama kana buqatar sa yanzu ne cikin qanqanin lokaci"
Murmushi yayi, Bayan yagama daura agogon yace "A a, ni Bani zanyi amfani dashi ba, akwai wacce zan Bawa, zan Bawa wata wadda Takeda mutuqar muhimmanci awajena"
Munirat data qaraso cikin Dakin nasa hannunta d'aukeda brief case dinsa, tasaki wani murmushi Mai qayatar wa Sannna tashigo cikin Dakin, tasan cewa itace, ta Kuma San Bayan ita, babu wadda Shahaab zaiyi wa wannan kyautar, Nan da Nan taji duk wani 6acin rai datake ciki yakau, bacin ran Data kwana dashi Daren jiya taji yatafi.
Ganin munirat din tashigo dakinsa yasa yakashe wayar, bayaso ko kadan tasan shirin dayake akanta, yafi son saide taga yabata takardun companyn
******
Hajja ce zaune cikin inuwa tana wanke jarkokin kunun Aya, tunda ankama azumi yau, tofa tarufe yin kunun Aya Kuma, Aisha na gefenta tana tsefe kalbar da'akayi mata wadda duk jelar tagama warware wa, ta kalli Hajja tace "Dan Allah Hajja kimin kitso, kullum saide amin kalba, ni wallahi nagaji kitso nakeso"
Hajja tace "haba 'yar Nan, kika Bari saida muka dauki azumi Sannan Zaki kama Kai ki tsefe saboda kina tutiya Hajja A'i ta'iya kitso, aikuwa saide kije maqota a miki"
Kafin Aisha tayi magana wani yaro yashigo gidan yace "Hajja A'i Wai inji jummai idan kinada yar ashana kibata zata hura wuta"
Hajja tace "wacce irin ashana Kuma da wannan safiyar ko bata dauki azumin ba ita?"
Yaron yace"bansani ba "
Tace" kace mata banida ashana, saide kwalin ashanar idan tana so saikazo ka kar6a mata, saita nemi ashanar awani gidan "
Aisha tace" Hajja Dan Allah nikiji Dani "
Tace" ke bazan miki kitso yanzu ba, kanki yayi santsi dayawa, tsautsayin dayasa kika tsefe shi zaisa ki kitse abinki da kanki "
Aisha bata qara mata magana ba, tagama tsefe kanta, Sannna tadaureshi da Dan kwali, Dan batada ribom ko daya
******
Zaune suke shida mama dakinta, yanda Dakin ya tsaru, saika rantse Dakin wata budurwa ne, Kansa yana kan cinyarta, so yake yafada mata yanaso idan yagama ginin companyn yabawa munirat to Amma yana tsoro, danhaka saiya sauya shawara yace "mama akwai kayan Azumi dazan raba, idan akwai Wanda kike so akaiwa saiki fadamin Inyi musu magana"
Mama tace "A a Shahaab, banason komai, abu daya nakeso awajanka kawai"
Cikin Sanyi jiki ya kalleta, yana tsoro karta ce masa yaqara aure, yace "mekikeso mama?"
Tace "nariga na fitar da rai da ganin Qawata Aysha,inajin Sai a darussalam zamu hadu,lokacin danaje gidansu neman ta, mutanan unguwar sun fadamin babanta yakoma jigawa da aiki,danhaka inaso kasamu lokaci, kaje jihar kaginamin gidan marayu acan, inajin Aysha tarasu, bansan Kuma tayaya zan taimaki wani Nata ba, qila tarasu tabar marayu, idan Allah yasa yayanta suna daga cikin Wanda za'a kawo su gidan marayun shikkenan kaga Nima na taimaka mata, qila haka Allah ya qaddara mana nida ita, Allah baiyi zamu cika alqawarin mu, muhada Yayanmu aure ba"
Shahaab ya Lumshe Idonsa, yabude, shifa wannan maganar hadin auren ne yasa bayason aga matar Nan, to Amma Yaya zaiyi? Ahankali yace "to, za'ayi"
Tace "yaushe?"
Kallan ta yayi yakasa magana, Nan da Nan ranta ya6aci tace "nifa Naga alama bakasan nemomin qawata Shahaab, Kuma muddin a kaga Aysha, saika auri yarta inde mace ta Haifa, saide in ta aurar da'ita ne, daga min cinyata tunda ban'isa insaka kayi ba"(😅)
Sake rungume mata cinyoyi yayi,tamkar zaiyi kuka cikin shagwa6a yace "Allah bazan tashi ba, to yanzu ni mama yakike so inyi, aiki yamin yawa, da wanne zanji? Ga company's, ga office dinmu, ga gida"
Kallan sa tayi yana magana kamar zaiyi kuka, ahankali tace "Shahaab, koba Dan qawata Aysha ba, zaka samu Lada kaima idan kayi"
Cikin gajiya da maganar yace "zansa ayi"
Cikin damuwa tace "to yaushe zakaje? Zanbaka kudin ma, nide fatana kawai ayi"
Jikinsa ne yayi Sanyi lokaci daya, lalle mama da gaske take, sake rungume ta yayi yace "mama kibar kudinki, awanne gari kike so ayi a Jigawan? Wanne Gari qawar Taki take?"
Tace "bansan garinda takeba Shahaab, kawai kayi a inda kaga ya dace"
"to mama zan shirya naje cikin satin nan tunda zan raba kayan Azumi, zanyi magana da Ramadan acikin jerin garuruwan da za'a raba kayan azumin, su saka da Garin jigawa, ni sai naje Jigawan da kaina, in raba musu kayan azumin, inyi maganar gina gidan marayun da Gwamnatin Jihar "
Ahankali mama tasaki wata irin ajiyar zuciya tace"nagode MAHMUD, Allah yayi Maka Albarka"
Tamiqa hannunta Qasan fillo, tad'auki kudi bandir daya tabashi tace "ungo wannan nakane"
Murmushi yayi, dimples dinsa suka futo, yatashi daga kan cinyarta, yayi kissing kumatunta, sannan yace "nagode mama" yatashi yatafi part dinsa cikin murna yana jin dadi kamar tayi masa kyautar miliyoyin kudi.
Bayan Ansha ruwa yana zaune agaban mama, munirat na Gefe tana danna waya kamar kullum, wayar Ramadan yakira, cikin zolaya Ramadan yace"kaga Angon munirah ita kadai "
Murmushi yasaki yace" Ramadan, a cikin kayan daza'a raba na dinnan, atura mota biyu zuwa jigawa, a Kwai aikin da zanje inyi acan, Nima inaso inshiga cikin masu rabawar araba Dani, inason in Dan wara jinin jikina"
Hakanan munirat ta tsinci kanta da faduwar gaba, batasan dalili ba, har saida ta daina danna wayar datake tazuba masa ido tana kallon sa, menene Kuma zai kaishi wata jigawa? Waye nashi a jihar?
Ganin babu Mai bata amsa Sai shi, shiyasa tabar maganar har zuwa lokacin da zasuje kwanciya.
Cikin murmushi Ramadan yace "Tofa, yauda kanka Abokina? Amma dakayi zamanka, duk abinda kakeso umarni kawai zaka Bani, zanje inyi ma shi, meyasa zaka wahalar da kanka kana Rabon abincin sadaka?"
"inason yine Ramadan, may be wasu suyimin addu'ah Allah ya amsa"
Ramadan yace "hakane, Allah yasa mudace, idan Kuma Rabon wata ne zai kaika shikkenan"
"babu wannan maganar"
Abinda yace kenan.
Ramadan yace "to ai shikkenan saika koyi cire suite, tunda kace da kanka kakeso ka bayar, kaga bai kamata kayi aiki da suit ba ranar"
"okay" shine kawai abinda yace Sannan yakashe wayar
Washe gari yana gab da barin office aka kawo masa wani file akan case din gidan man fetir din wani bawan Allah da'aka kama akano,Me Kai ashirin,Bai tsaya ya duba file din yanda yakamata ba,ya turashi zuwa wani office din,suje suyi aikin komai
******
Hajja da Aisha suna tafe, rana Sai dukansu take, ga azumi, dawowarsu kenan daga gidan Alhaji Audu maqocin su, Wanda suka je masa jaje sakamakon qwace masa sabon gidan mansa da hukumar efcc tayi, daga Nan Kuma suka biya suka gaisa da jummai, Sannna suka taho gida, Hajja Sai mita take "Kai wannan bawan Allah, Allah kadubeshi su sakar masa gidan mansa, mutum Mai mutunci, me sunan qawa kiduba kiga yanda yake dawainiya da duka mutanan unguwar Nan, akawo mana wannan akawo mana wancen, Allah yasaka masa, Allah yakwato masa haqqin sa, Dan baka Isa fada da Gwamnati ba, saide ka hadata da Allah "
Aisha tayi shiru tana tunani a ranta, tasan cewa de idan ba wannan Mahmud wakilin ne yakama ba to tabbas Shima zai iya sakawa akamawa Alhaji Audu gidan mansa, tunda shi kowama kamawa yake, bashida wani motsi saina kama kayan mutane, to gaba-gaba ma tsaf zai iya kama babansa, tunda kowama tuhumar sa yake. (🙆🏻♀️)
Ranar haka ta wuni tana tunanin wannan mutumin, ko abincin shan ruwa bata iya dorawa ba, shi kuwa wannan wanne irin mutum ne?
******
Yau azumi anyi sati daya kenan, Sai yanzu ne Kuma abubuwa sukayi masa d'an sauqi, duk garuruwan daya ce aza6a araba kayan Azumi ko'ina anbasu banda jigawa, Shima Dan yace yanaso yaraba da Kansa ne, yanar gizo, gidan TV, dakuma gidajen redio Sai maganar sa ake, Ana Jinjina wa namijin qoqorin Dayayi,su Hajja Kam dasuka ji Ana fada a gidan redio cewa tayi
"mukam Rabon Naka baizo mana nanba mesunan mamuda"
Aisha kuwa haushi hajjan ma tabata, Wai mesunan mamuda, ko Yaya ma za'ayi ta had'a wannan mutumin da baban ta?(🤔).
Kamar kullum Sanye yake cikin suit Tayi masa kyau sosai, munirat dake fesa masa perfume, gabanta Sai qara tsananta faduwa yake, batasan meyasa ba haka kawai itade batason tafiyar Nan tashi, ta Kalle shi cikin kissa tace "my dear, nifa banson tafiyar Nan taka,I don't know why"
Fuskarta yakama yariqe ta tafukan hannunsa biyu yace "bafa dadewa zanyi ba, kema kinsan banson yin nesa dakeda mama, Amma nayi Miki alqawarin duk inda nake, kina Nan acikin zuciya ta,"
Cikin shagwa6a tafara yimasa wani irin kuka, baisan Yaya zaiyi mata ba, rarrashin ma kamar 6ata lokaci ne, lokaci daya yahade bakinsa danata, wayarsa dake kan gado ce tasa yadaina abinda yake, sakamakon Kiran Ramadan daya shigo.
Cikin kunnan ta ya rad'a mata "ki gyara min abuna sosai kafin nadawo"
Cikin kunya tasake boye fuskarta a qirjinsa.
Shi yana nufin tasake gyara yanda ya kamata tadawo kamar da, ita Kuma kunyar dataji tayi tunanin yaji ta yanda yakeso ne,magungunan datake Sha sun kar6eta, shiyasa yake fadar hakan
hannunta yakama cikin murmushi suka futo falo, daga Nan yayi mata sallama yatafi
Saida yabiya wajan mama yamata sallama, tayi masa addu'ah Sannna yatafi.
A Airport suka hadu da Ramadan, duk Wanda yasan shi saiya yi masa gaisuwa kafin yawuce, yau baisaka I'd card dinsa agaban suit din tasaba, a tsaye suke ko wajan Zama basu nema ba, kafin jirgi yatashi wasu daga cikin ma'aikatan efcc dakuma folice suka ruqo wani mutum kana ganinsa kasan badan qasar bane, Sai magana yake musu da Harshan turanci Amma yanda suka maqala baqin glass a'idon su babu ma Wanda yake saurarensa,hayaniyar datake tashi ne yasa suka juya shida Ramadan, suma ma'aikatan ganin MAHMUD din yasa cikin ladabi suka nufeshi, kudaden dasuke cikin jakunkunan suka juyesu aqasa, sun kamashi ne da kudi zai fita dasu wata qasar kimanin million Dari biyu na Dalar amurka cikin jakunkuna, me Yan jarida zasuyi inba dauka ba, shikam Shahaab kasa magana yayi, saboda da alama wani 6arawon Gwamnatin ne yayi amfani da Yaron domin a turashi da kudin yakaishi wata qasar.
ya kalli Yan jaridar yaga sun taru anaso yayi magana Kai kace Dama awajan suke suna jiran akama mutumin
Haquri ya basu yanemi uzuri tafiya ta kamashi, yanada ganawar da zaiyi tareda gwamnan jigawa nanda awa uku, wannan Kuma wani Babban case ne, idan ya dawo zasu zauna suyi tsatsauran bincike akan case din
Yana fadar haka yayi gaba, yana jin yanda Yan jarida suke kira "yalla6ai tambaya daya, please tambaya daya yalla6ai kawai"
Suna cikin jirgi Ramadan yana gefensa yana duba jarida, shikuwa Shahaab Lumshe Idonsa yayi, Qalubalen dasuke gabansa akan wannan matsayin dayake ciki shi yake tunani, yasan cewa tabbas baza'a Rasa masu shirya masa gadar zare ba, duba da yanda yake kama duk wani Mai sa hannu akan cin hanci da rashawa.
Kamar yanda yafada hakance ta kasance, suna sauka Kai tsaye Tahir guest palace (Annex) suka sauka, Sai lokacin dazasu ga gwamnan Sannan suka tafi, basu dauki lokaci Mai tsawo ba ya tabbatar musu za'a samu Dajin daya dace agina gidan marayun, acan kusa da Garin Kiyawa, saida aka nuna musu komai a photo dakuma wasu garuruwan ma daban, suka Kuma tabbatar masa kamar yanda ya za6a din, ayi adajin kiyawa Amma wajan da zai kasance kusa da cikin Gari suke so.
sunji dadin yanda aka kar6esu,Kuma abun yazo musu da sauqi kasancewar filin na Gwamnatin Jihar ne,Bayan sungama akayi musu photo Sannna suka koma masauqinsu
Suna zuwa Shahaab ya daura towel yashiga wanka, Bai dade da futowa ba aka kira sallar magrib, shida Ramadan suka tafi masallaci Bayan sun dawo suka Sha Fruit da sauran abubuwan buda baki
Bayan sun dawo daga sallar tarawih sun dade suna kallon labarai shida Ramadan, saida matar Ramadan din ta kirashi awaya Sannna yayi masa sallama yatafi dakinsa, shi kuwa da mama kawai yayi waya, yafada mata yanda sukai, taji dadi sosai, munirat kuwa wayarta akashe, tunda yayi try bata shigaba saiya haqura ya kwanta.
Washe gari sukaje sukaga wajan, aka auna yanda abubuwan zasu kasance, suka tsara yanda aikin zai dinga gudana, dakuma mutanen da aka damqa aikin a hannun su
Awajan suka wuni Sai gab da shan ruwa suka koma hotel, washe gari aka fara tono, manyan motoci suna kawo bulo, wasu yashi, wasu siminti, saida yaga aikin yafara kankama Sannna suka tafi, da magrib suna shan ruwa Shahaab duk tunanin matarsa ya isheshi, duk rashin dadinta yana rage zafi da'ita a hakan, cikin kwana ukun Nan da sukayi shi yasan yanda yakeji, wata irin sha'awa yake ji kamar zaici babu, sauqin sa daya yataho da qananun wandunansa masu kamar pant, yana sakawa, Amma badan hakaba ya tabbatar wataran idan yafita Sai yaji kunya,saide yadinga tafiya yana bude qafa saboda tsaro(😎)
Saboda haka Gara suyi abinda yarage musu kawai yakoma gida, yajuya ya kalli Ramadan yace "yakamata mu raba kayan azumin Nan Ramadan, yau ankai azumi na goma kenan,sonake gobe mu wuce gida"
Ramadan yace "Dasafe zamu raba kayan ne?"
Girgiza Kai yayi "da nayi niyyar mu raba da safe da yamma saimu tafi gida, to nariga nasai mana tickets Dasafe jirgin mu zai tashi"
Cikin sauri Ramadan yatashi zaune yace "Wai kana nufin yanzu daga shan ruwa zamu fara daukar kwalin taliya da macaroni muda yakamata ace mun huta?"
Murmushi yayi yace "ba Lada muke nema ba? Yazakayi?"
Kamar zaiyi kuka yace "to yanzu Yaya zamuyi?"
"kira mun Wanda kayan yake hannunsu kagani" cewar Shahaab
Babu musu Ramadan yakira su, yasaka wayar a hands-free sannan ya ajiye ta a tsakanin su
Cikin aji Shahaab yace "yawwa kana Jina, muna sone muwuce gida gobe insha Allah, so kayan Nan za'a rabashi yanzu, Wanda basu qare ba saiku qarasa gobe, Ramadan zai kar6i account number ku, insha Allah Zakuga saqona"
Cikin ladabi Yaron yace "to yalla6ai, yanzu Yaya za'ayi Rabon kenan?"
Shahaab yace "akai trella daya yankin Hadejia da gumel, dayar Kuma abarta anan yankin dutse,ku dauki Rabin trella ku raba a wasu qauyukan saiku saka mana Rabin acikin mota, direban yazo Nan Tahir guest