Showing 105001 words to 108000 words out of 115646 words
tana tafiya daqyar ga uban hips dinta yasake bajewa babu hijabi ajikinta wani mayafi tad'an yafa hannunta d'aukeda d'ata tanaci, Sai wata me aiki a gefenta tana riqe da wani plate Wanda yake d'aukeda d'ata dakuma kayan marmari, bata lura da zuwansa ba, Alokacin da aka bud'e masa mota yafuto harsun shige part din mama, Shima Kai tsaye part din maman yawuce yana zama a kujera ta kalleshi tace"Uncle sannu da zuwa"
Yace"yawwa Maamah,Ina Baby na?"
Idon mama ta Faka taga hankalinta baya kansu, sannan taja hannunsa tad'ora masa akan cikin tace"tun dazu yaketa motsi"
Qasa yayi da muryarsa cikin rad'a yace"ko yanason jin d'umin Babansa?"
Babu musu ta daga masa Kai, murmushi yayi sannan yajuya ya kalli Mama yace"mama, adena barin Maa-mah tana fita compound Dan Allah, baki saiya kamata, mutane Sai kallon ta suke itama Sai ciye ciye take agaban su"
Aisha tanajin haka cikin shagwa6a ta turo Dan qaramin bakinta gaba,mama ta galla masa harara sannan ta maida Hankalinta kan kallon datake.
Shima da yaga bata tanka masa ba, saiya futo da takardu daga cikin briefcase yabawa Aisha yace"kisa hannu a wannan takardun,Ana qoqarin daukar ma'aikatan dasuka dace a kamfanin ki, idan akwai Wanda kike so kisake d'auka saikiyi musu magana su kawo takardunsu Sai a tantance su agani".
Kallonsa tayi tace"Uncle Dama inaso In fadama Dan Allah inason in koma makaranta kodan saboda aikin Nan, inaso Nima indinga zuwa office, Ina aiki kamar mata ma'aikata"
Lokaci daya yanayin fuskarsa ya sauya, ya kalleta yace"tunanin da kike kenan?"
Cikin sauri tace"emana, to tayaya zan riqe company Bayan ba karatu nayi ba? Ai dole in koma makaranta Uncle"
Cikin daure fuska yace"wannan tunanin ki kenan,idan Zaki cire karatu aranki, toki cire, domin kuwa,ba-za-ki-yi ba"
Yaqare maganar a rarrabe
Wani irin kallo tayi masa, bata Tanka masa ba tatashi ta wuce dinning domin kuwa wata irin baqar yunwa takeji, mama ta kalli yanda Aisha take tafiya daqyar, ta juya ta kalli Shahaab tace"kaje Kaci abinci mana, kosai kagama fad'an karatun tukun?"
Murmushi yayi yace"mama Dan Allah tayaya zan Barta tatafi wata makaranta?Kuma Babyn nawa waye zai dinga bashi kulawar data dace?tunda cikinta ya tsufa Hankali na atashe yake, fatana kawai tasauka lafiya,Amma ita maganar karatu ma take, Ni wallahi tausayi ma take Bani kwana biyun Nan daqyar takeyin komai, har yanzu bata cika shekara Ashirin ba, ko zata Iya haihuwar ma da kanta?"
Mama ta ajiye wayar hannunta wadda take ta gwada Kiran layin Hajja Amma taqi shiga, ta kalli Shahaab tace"tayaya Kuwa zata Iya haihuwa tunda nauyin mijinta ma bata iya daukewa?"(😲🙈)
Shahaab ya kalli Mama da sauri, cikin kunya yasosa qeyarsa, batare da yace komai ba sum sum yawuce dinning din Shima.(😂)
Please kuyi hakuri da wannan bayawa, nagaji ne 🙏🏻
Shahaab littafin kudi ne, ki biya naira 300 ki karanta, idan kika karanta baki biyaba nabarki keda ALLAH
0164549488
Amina muhammad
GTbank
Kokuma katin MTN tareda shedar biya ta wannan number 08033300034
Mrs Usman ce✍🏻
Page 25
Zama yayi a dinning d'in yana kallonta qasa qasa,abinci takeci da hannunta dayan hannun Kuma wayarta take danna wa, ahankali yatashi tsaye yazare wayar hannunta, sannan ya zauna tareda ajiye wayar agabansa, Kallonsa tayi, tace"Uncle fati zan kirafa"
Abincin yasake qara mata yana fadin"kici abincin tukunna"
Batare datace komai ba tamaida Hankali wajan cin abincin, saida taci taqoshi, sannan tafara hamma, kallonta yayi, Adede lokacin itama ta kalleshi, cikin kulawa yace"bacci?"
Tace"wallahi, bacci nakeji uncle, tunda natashi Dasafe ban sake yin bacci ba"
Abincin sa yakeci cikin kulawa ya nuna mata dinning din yace"kwanta, Bari ingama Sai muje ki kwanta"
Babu musu ta dora akan dinning din, har saida yagama cin abincin sannan ya kalleta yace"muje, ko bazaki iyaba na daukeki?"
Murmushi tayi tace"zan'iya uncle"
Hannunsa takama suka nufi wajan mama, yad'auki kayansa suka tafi, mama tabi bayansu da kallo tana murmushi, cikin ranta tana tunanin wayaga Shahaab da d'a?inajin da zai iya da jikinsa zai dawo da ciwon Aisha, ansan cewa dole a tausaya mata kasancewar ta yarinya qarama ga Kuma halin datake ciki, Amma itama lokacin data haife shi shekararta goma Sha takwas, ita haihuwa aita Allah ce, idan Allah ya sauketa lafiya abunda ake Fata kenan, Amma saka damuwa acikin rai duk ba nasa bane, addu'ah kawai itace mafita.
Suna shiga part dinsu ya maida kofar ya rufe, yasaka hannu ya dauketa cimak, basu tsaya ko'inaba Sai dakinsa, akan gadon ya kwantar da'ita, sannan yafara rage kayan jikinsa, saida yacire komai yarage dagashi Sai boxer sannan ya kwanta tareda janyota yashigar da'ita cikin jikinsa, hannunsa ya dora akan cikinta, sannan yayi kissing din wuyanta yace"Cikin Nan tunda ya girma ya hanani rungume mata ta yanda ya kamata"
Murmushi tayi tace"nan gaba kadan ma tsakanin mu zai dinga kwanciya"
Murmushi yayi Shima yace"idan mace ce to wallahi bata isaba, idan namiji ne Shima wallahi bai isaba,babu Mai shiga tsakanina da matata Sai Allah"
Murmushi tayi tana Lumshe idonta tace"me kakeso mu Haifa uncle?"
Sake Sakata cikin jikinsa yayi sannan yace"ke mekikeso ki Haifa?"
Idonta a Lumshe tace"mace...,inason in haifi 'ya mace insaka mata sunana, sannan Kuma ace tana Kama dakai, Mai dimple irin Naka, indinga yimata kwalliya, indinga yimata vedio, mudinga fita yawo, tazama babbar qawata"
Cikin jin dadi yace"nide nafison ki haifamin namiji, saboda shine jigon gida, Kuma shine idan Allah ya rayashi zan'iya dorashi akan komai nawa, zai taimaka min akan komai Sa6anin mace, Amma Kuma a mahanga ta Hankali saide muce Allah yabamu mafi alkhairi ko?"
Murmushi tayi tace"hakane, Allah yabamu mafi alkhairi" daga Nan ta Lumshe idonta, tanajin yanda yake kissing wuyanta, hannunsa Kuma yana cikin rigarta yana shafa cikinta.
Sun dade suna bacci, bacci Mai cikeda nishadi dakuma jin dadi, shi bai farka ba itama haka, saida suka dauki lokaci sunayi sannan suka tashi, kayanta yacire mata, ya dauketa suka shige toilet, a toilet dinma sun dade acikin ruwa suna murzar jikin junansu kamar karsu rabu, sannan suka futo suka gabatar da sallah,basu je part din mama ba Sai dare, suna zuwa kuwa Aisha taga Hajja tazo, tsaya wa yayi yana waya daga Gefe, ita Kuma ta qarasa wajan su, Hajja ta kalleta tace"meciki"
Murmushi tayi tace"Hajja Ina Ummah, meyasa Baku taho tare ba?"
Hajja Tace"ina Hadiza Ina zuwa gidanki me sunan qawa?Nima yanzun zuwa nayi muna magana akan yajin da za'a miki"
Shahaab daya qaraso falon ya zauna agefen Aisha yace"Hajja wanne irin yaji Kuma?"
Kallan sa tayi tace" d'an yajin daddawa mana da akeyi, haihuwa tana tafe ai muma Gara mufara shiri,wannan yarinya Allah de ya saukeki lafiya"
Ta qarasa maganar cikin alhini,Aisha ta harareta tace"ji Hajja,Dan Allah ni karkisa naji tsoro, mama kinga Hajja ko" ta qarasa maganar tana kallon mama
Mama tayi dariya tace"rabu da'ita takwara, kalau Zaki haihu kinji,keda kike da likita atare dake, babu ruwanki da shan wahala"
Shahaab yayi murmushi, zai iya yiwa wani komai Amma baya jin zai iya ta6ukawa Aisha wani abu, kwata kwata bashida qwarin gwiwa inde Aisha tana cikin tashin hankali, gaba daya rud'ewa yake yarasa meyake masa dad'i.
Har qarfe Tara Hajja tana gidan, tana zaune suna Dan ta6a hira itada mama, tana Kuma Kiran mutanan Chamo suna ta magana akan shirye shiryen haihuwar Aishan, Sai wajan karfe goma sannan tatashi zata tafi mama tasa hannu tajata ta zauna tace"ai kinzo kenan,narasa me kike yi acan gidan idan kinje wallahi, ki zauna anan mana mudinga Dan zantukanmu"
Hajja tace"ko? To ai can dinma Hadiza tana zaune ita kadai babu dadi, Kuma idan muka zauna din muna Dan ta6a hirar mutanan mu nacan"
Shahaab yayi murmushi yace"kiyi zamanki kawai Hajja, itama ba mijinta yana Nan ba"
Cikin sauri Aisha ta kalleshi tareda mintsi ninsa, murmushi yayi yana shafa wajan yace"yi haquri, ni bada wata manufar nafada ba"
Mama tace"ai Gara dakika mintsine shin kozai tuna akan surukansa ake magana"
Hajja tace"to Bari in zauna, idan na kwana biyu anan Sai inje can itama namata kwana biyu"
Haka sukaci gaba da Zaman su afalon suna kallo suna hira, har shadaya na dare sannan suka koma nasu part din, acan dinma Bayan ta kwanta shi computer ya dauka yadan rage wasu ayyukan sannan shima ya kwanta.
Haka mama ta dinga yaudarar Hajja ta hanata tafiya sukaci gaba da zamansu a gidan cikin kwanciyar hankali har cikin Aisha Yacika wata Tara cif, tun daga Nan Kuma hankalin kowa yadawo kanta, ma'aikatan gidan ma kowa ido yazuba mata yana jira yaga mezata Haifa, sunsan cewa uban gidan nasu Sai yafi kowa murna akan haka.
Tun Ana tunanin haihuwar akan lokaci har suka daina, saida ta qara sati biyu, Alokacin ma basuyi tunanin haihuwar zata zo ba, itama Kuma kasancewar haihuwar ba sanin ta tayi ba, Sai hankalin ta bai kawo mata haihuwar ba, yau tunda safe yafita wajan aiki, Alokacin tana bacci bata tashi ba, tun shekaran jiya take danjin ciwon baya, saitayi tunanin ko yawan kwanciyar datake ne, ga mararta tana mata nauyi, babu Wanda ta fadawa wannan sauyin yanayin nata
Baccin Nata yayi dadi sosai, kad'an kad'an mararta tana mata ciwo, tasa hannunta akan marar taci gaba da bacci, can bacci yayi Nisa taji wani irin ciwon Mara yataso mata, cikin azaba tafarka, yatsina fuskarta tayi, sannan ta sakko da qyar ta wuce toilet tafara fitsari, anan taci karo dawani irin ruwa yana zuba ajikinta,hakan yasa tacire kayanta tafara wanka, kafin tagama wankan taji marar Tata tasaki, ahankali tagama komai tafuto tayi sallah, sannan tasaka wata doguwar Riga me fadi ta nufi part din mama, ahankali take takawa ma'aikata Sai sannu suke mata, mamaki yasake kamata jin wannan ruwan yana sake bin jikinta, tana saka qafarta a part din mama, taji gaba daya qafafunta sun riqe, mararta ta d'aure dawani irin ciwo na fitar Hankali, cikin azaba ta tsugunna awajan tana runtse idonta, mama da Hajja suna zaune kwata kwata hankalin su baikai bakin qofar ba, Aisha kuwa idonta a runtse yake wani irin gumi ya tsatstsafo mata, jitayi wani irin abu yana neman rabata gida biyu, tsananin azabar dataji ne yasa tasaki wani irin qara tareda fadin"mama!!!"
Azabure suka juya itada Hajja, suna ganin Aisha a tsugunne suka fita a guje sukayi kanta, Hajja tana duddubata ta kalli Mama tace"Aysha inajin haihuwar ce tazo"
Mama da jikinta yakama rawa tace"eh gashinan Kam Naga kamar akan gwiwa take"
Cikin sauri suka d'ago ta Hajja ta riqeta tana mata sannu, hawaye ne yafara bin fuskarta tana yarfe hannu, mama kuwa a guje tashige d'akin da suka adana kayan haihuwar ta Dauko wasu kayan, sannan tafara Kiran wayar Shahaab, yana d'auka tace"kana inane"
Yace"ina office mama,meeting muke"
Tace"to yarinyar Nan ce babu lafiya, Ina tunanin haihuwar ce tazo, gashinan Nan de zamu tafi asbi..."
Kafin tagama magana taji ya kashe wayar, wayar ta kalla kawai ta jefata cikin Jakarta, Alokacin har Hajja sun qarasa gaban mota, gaba daya ma'aikatan gidan kowa mamaki ne ya kamashi ganin yanzu yanzu ta wuce ta gabansu Amma har naquda tatashi, suna shiga cikin mota driver yaja a guje suka fice daga gidan.
Ko Nisa basu yiba suka hadu da Shahaab, yana ganin motar su ya tsaida su, yafuto daga motar dayake, yakoma cikin motar su mama, yashiga gaban motar sannan driver yaja, juyawa yayi ya kalleta kwata kwata ma bata cikin hayyacinta, mama da Hajja sun sata atsakiya Sai sannu suke mata, yayinda Hajja take goge mata Hawayen idon Nata, shikam Idonsa ne yayi zuru zuru kamar marar lafiya, baya cikakken minti daya, batareda ya juya ya sake kallon ta ba, suna zuwa asbitin aka kar6eta, Hajja tafara Kiran wayar Ummah da Abba zata sanar dasu, Shahaab ya zauna yad'ora Kansa akan hannayensa, abun duniya yataru yayi masa yawa, yayinda mama take zarya takasa tsayuwa haka Kuma takasa zama waje d'aya,suna jiyo yanda Aisha take kuka tana salati, har kusan awa daya bata haihu ba, ahankali yatashi yacire suit din jikinsa, yacire agogon hannunsa ya ajiye su anan, Kai tsaye yashige cikin d'akin, mama da Hajja suka bishi da kallo, yanayin da yaga Aisha yasa gabansa faduwa, ba kowa ne yafado masa Arai ba Sai mama, itama haka Tasha wahala kafin ta sameshi, kasancewar sunsan cewa Shima yasan aikin shiyasa babu Wanda ya hanashi, sun dauki tsawon lokaci Ana abu daya, sannan haihuwar tazo gadan gadan, shida Kansa ya qarata, sannan ya kar6i haihuwar ta da Kansa, shi Kansa yayi mamakin yanda yasamu wannan qwarin gwiwa, lokaci daya su Hajja sukaji kukan Baby Yacika falon, hawaye mama tafara, tana zubawa Allah kirari dakuma godia agareshi, acikin d'akin ma Shahaab yana ganin Babyn a hannunsa wani irin hawaye me dumi ya zubo daga Idonsa, nurse din dake gefensa tasa hannu ta kar6i Babyn sannan tace masa"yalla6ai congratulation, Baby boy ne"
Hannu yasa ya goge Hawayen, sannan yafara cire safar hannunsa, yakoma ga Aisha yana kallon ta, wadda tuni baccin azaba yayi gaba da'ita, sauran nurse din Kuma suka fara gyara mata jikinta, saida aka gyara baby tsaf, aka saka masa kayan Sanyi farare masu mutuqar laushi, sannan suka Bawa Shahaab shi, nurse din tace"yalla6ai gashi,Bari mu qarasa gyara madam"
Babu musu ya kar6i Yaron Wanda yakasa dauke Idonsa akansa, Yaron yana bala'in kama dashi sosai, babu abinda yabari nasa, fari ne tas 6ul6ul dashi kamar ba Aisha ce ta haifeshi ba.
Yana futowa mama da Hajja da Kuma Ummah da Abba Wanda Zuwansu kenan sukayi Kansa, gaba dayansu kowa kokari yake ya kar6i Babyn, Hajja ce tayi nasarar kar6arsa, ahankali yasaka hannu yasake goge Hawayen Idonsa,yace"nagode mama"
Mama tace"godia tame Kuma Mahmud?"
Saida yasake goge Hawayen sannan yace"dakikasa nazama likita, duk da baki barni nayi aiki ba yau gashi dalilin karatuna na temaki matata"
Murmushi tayi ta kalleshi Tace"to naji, yanzu de kayi shiru kuka Kuma ya qare Mahmud, saide ka godewa Allah bisa kyautar Dayayi ma"
Cikin sauri Hajja tace"um um Aysha barshi ya koka, irin wannan Baturen d'a haka ai dole ubansa ya koka harda shashsheka..."(😂)
Gaba dayansu dariya suka saka, Shahaab yayi mata wani irin kallo me cikeda harara, sannan ya goge Hawayen idon nasa, mama Tace"Ashe zaka iya kar6ar haihuwar? Yaya jikin nata to?"
Ahankali yace"tana bacci, bansaniba Kota farka, nafuto zasuyi mata dinki"
Hajja tace"oh wannan yarinya tana ganin dinkuna, gana Daren farko gana haihuwa"
Shahaab yaji wata irin kunya ta kamashi kamar ya nutse awajan, kasancewar Ummah da Abba suna wajan, Sai akai sa'ah Adede lokacin aka kira wayarsa, cikin sauri ya matsa Gefe yafara wayar, daga office dinsu ne, sunyi tunanin zai dawo aci gaba da meeting din, Sai yafada musu labarin haihuwar, yakuma nemi excuse awajansu,Bayan Nan Kuma yakira Ramadan, yana dauka yace"Albishirinka"
Ramadan yace"goro"
Shahaab yace"Maamah tasauka,Nima nasamu Baby boy dina"
Ramadan yace"Alhamdulillah, Allah abun Godia, kuna Ina yanzu?"
Cikin farinciki yace"muna Asbiti"
Ramadan ya kashe wayar, shikuma Shahaab yakoma wajan su Hajja, yana zuwa yaga Yaron yana hannun Ummah, Adede lokacin nurse ta futo tafada musu cewa sun maida ta Dakin hutu idan anjima zasu iya shiga su ganta.
Zuwa yamma mutane sun cika asbitin, mutanan dayake meeting dasu, dakuma Wanda Ramadan ya faffadawa kowa kokari yake yazo yaga Yaron Mahmud Wakili, gaba dayansu suna cikin ke6antaccan Dakin da aka Kai Aisha, tana zaune kalau da'ita kamar ba'ita ce tagama kukan haihuwa ba, tea ne a hannunta tanasha Sai murmushi take, Shahaab ne yabude Dakin yashigo hannunsa d'aukeda Babyn, ya qarasa wajan ta ya zauna tareda ajiye mata Babyn yayi qasa da murya yace"kibashi nonon yasha"
Harararsa tayi, babu Wanda yaji me yace mata,kawai de duk mutanan d'akin sunga yanda ta zuba masa wata irin harara me kama da kallon luv, Hajja tayi dariya tace"me sunan qawa yau an dandani ciwon haihuwa,ta gaba Kuma Sai yanbiyu insha Allah"
Mama tace"haihuwa yaqin mata kenan, Allah de ya raya,yi sauri kigama shan tea din kibashi nono yasha"
Da daddare aka sallamesu,acan gida ma falon mama cika yayi da mutane, mutanan Shahaab suna zuwa ganin baby, mutanan mama suna zuwa, Ummah ma bata koma gida ba, Sai wajan shabiyu saura sannan Abba yazo suka tafi, Alokacin kuwa Hajja tahada mata kunun kanwa tanasha, banda farfesun kaza da mama tahada mata da kanta, zuwa wannan lokacin Kam labari yagama ko'ina, shugaban EFCC Mahmud Wakili, yasamu qaruwa, har gajiya yayi da amsa kira, wasu daga bangaren kasuwancin sane, wasu Kuma daga office dinsu ne, banda turawa dayake mu'amula dasu Yan wata qasar kowa Sai ala sanya Alkhairi yake masa kasancewar sun San cewa ya dade bai samu haihuwar ba.
Ramadan kuwa yakawo matarsa gidan itama anan take shirin kwana, a Dakin mama Aisha ta tare, anan suka kwana itada baby da Mama, su Hajja Kuma suka koma wasu dakunan, tunda akai haihuwar mutane suke sallama a gidan, wani ma zaiyi tunanin wani Dan qaramin biki ake, kullum cikin dora tukunya ake, Ana saukewa, hakan kuwa Sai yayiwa mama dadi, saboda inda babu mutanan da tuni Shahaab ya hanasu sakat, Dasafe kafin yatafi wajan aiki yana shigowa ya gansu itada Babyn, haka mama take kafawa ta tsare saiya tafi, sannan itama take barin Dakin, kulawa take Bawa Aisha yanda ya kamata, banda Hajiya zaliha datake mata Dan gyare gyare daga Gefe, abinci suke dura mata tanaci tana qoshi babu alamun yunwa atare da'ita, shiyasa danta yake samun wadataccan ruwan nono ko madarar ma ba'a bashi, kwanansu shida da haihuwa gida Yacika da mutane, mutanan jigawa duk sunzo ciki harda Walida, faty ma tabiyo ayarin kano itama tazo, gida yayi maqil ko lokacin auren ba'ayi wannan taron ba, Shima yana can ayyuka sunyi masa yawa saboda dinner dasuke shiryawa shida mutanan sa, kwata kwata yau din tun safe daya fita, Bai dawo gida ba Sai wajan Sha biyu na dare Alokacin anriga angama tsara komai, yana zuwa gidan yawuce part din mama, yaji dadin yanda baqin gidan sukai bacci, shiyasa Kansa tsaye yawuce Dakin mama, Adede lokacin mama zata shiga toilet,Hajja Kuma tabawa Aisha Yaron ta miqe itama zata tafi dakinsu ta kwanta,Adede lokacin shikuma yaturo kofar yashigo, mama ta kalleshi tace"Daga Ina kake da wannan Daren?"
Zama yayi akan gadon yana gaida Hajja, sannan yace wa mama"ina taredasu Ramadan awaje ne,mungama shirye shiryen dinner ne,nagaji wallahi mama, babu abinci ne?"
Mama tace"bari in futo daga toilet saina hadama wani abun"
Ledar daya shigo da'ita yabawa Aisha yace"ga wannan"
Cikin ladabi ta Kar6a Tace"to Angode"
Sannan tafara budewa, leshi ne me launin baqi da golden, an dandatsa mata dinkin Riga da siket Mai kyau, Sai Babban mayafi da takalmi me tsini, dakuma wata sarqa babba, tana duba kayan tabawa Hajja tace"Hajja kingani"
Hajja ma tafara daga kayan tana fadin"masha Allah, Amma kayan nan sunyi kyau sosai wallahi"
Mama tafuto daga toilet taga kayan itama ta d'aga tace"sunyi kyau sosai, Allah yaqara budi"
Tajuya ta kalli Aisha tace"saiki saka su goben, shi Dama wannan angon na Hajja