Showing 102001 words to 105000 words out of 115646 words
ita kanta tasan cewa ba qaramin so yake wa wannan cikin ba, inbanda ciki waye ya'isa yahana Shahaab wannan abun?π€
Sosai ta Jinjina masa, kwata kwata ya kauracewa saka turare saboda ita, yadena kusantarta, bashida aikin komai sai Wanda zai sata farinciki, tsananin kulawar dayake bata ne yasa tasake jin soyaiyar sa tana sake shiga ranta.
Yau satin su hudu da dawowa daga india, watan cikinta uku, daga Saman mararta kuwa ciki harya fara tasawa,tunda Shahaab yaga haka, yahana Kansa sukuni, bata Isa ta kwanta rub da ciki ba zai fara fada, murmushi kawai take tarabu dashi da gyara kwanciyar Tata.
Yau da daddare Bayan sunyi shirin bacci ta kalleshi taga duk jikinsa yayi Sanyi, Idonsa yayi jajir kamar marar lafiya, Kallonsa tayi tace"Uncle lafiya?"
Cikin wani irin yanayi na buqata ya kalleta yace"maamah....inashan wahala, natara dayawa maamah, ni wannan wasan Bana jin dadinsa kamar dayan"
Ajiyar zuciya ta sauke tace"yanzu fa lafiya ta kalau Uncle, idan zakayi kazo kayi, ni banajin komai yanzu"
Cikin kulawa ya kalleta yace"a a, kirufamin asiri maamah, Dr yace cikin ne bayaso, idan Kuma nayi a kazo aka samu matsala fa? Inason cikin Nan kamar raina maamah, banason abinda zaisa yasamu matsala ko yar kadan ce"
Cikin tausayawa tace"to yanzu haka zamu zauna?"
Yace"zan tambayi Dr tukunna, idan naji na gamsu da bayanin nasa Sai muyi"
Tace"to Allah yasa mudace"
Ta kwanta rub da ciki abun ta tafara bacci, Shikuwa yana zaune yana aikin tunani, yana juyowa ya ganta ta kwanta akan cikin, aikuwa da gabansa yafadi, cikin sauri yace"maamah!, maamah tashi mana, wacce irin kwanciya ce wannan?"
Tashi tayi, ta gyara kwanciyar Tata, ta kwanta akan hannunta nadama, Sai a lokacin yasaki wata irin ajiyar zuciya, sannan ya matsa kusa da'ita Shima ya kwanta(π)
Cikin dare tana tsakar bacci taji shi yana fadin"maamah!"
Ahankali ta bude idonta kadan tace"na'am Uncle"
Yace"tashi ki gyara kwanciyar ki,kar Babyn Nan yasamu matsala tunda kika kwanta yanzu karfe biyu ko juyi bakiyi ba, gyara kwanciyar ki"(ππ»ββοΈ)
Babu musu ta sake juyawa ta kwanta akan hannunta na hagu tana mita acikin ranta, sunci gaba da bacci gab da Asuba yafarka ya Kalle ta sannan yace"maamah!"
Tace"Um Uncle"
Yace "tashi kidan gyara kwanciyar ki, maamah tun dazu fa Dana tasheki Ahaka kike"
Runtse idonta tayiππ, sannan ta bude, ahankali tatashi zaune, tasaka hannunta ta kunna fitilar gefen gadon, sannan tace"Uncle"
Yace"na'am"
Akaro na biyu tasake cewa"Uncle"
Yace"Na'am maamah"
Akaro na uku tasake Kallonsa tace"Uncle"
Yace"Na'am"
Tace"dan girman Allah kabarni in runtsa, haba Dan Allah, tun Daren jiya kake min maganar kwanciyar Nan, na kifa ciki na kace a a, na kwanta hannun Dama, kace a a, na kwanta hannun hagu, kace a a, yanzu Yaya kake so inyi? So kake yanzu Kuma in kalli Saman Dakin? Saboda Allah tunda aka samu cikin Nan ka Hana kanka sukuni duk ka fita a hayyacinka kaduba kagani har Rama kafara Amma bazaka kwantar da Hankalinka ba?, haba Uncle"(ππ€£)
Ajiyar zuciya yasauke yajata jikinsa ya rungume ta, sannan yace"toshikkenan yi haquri na nadena, shikkenan?"
Daga masa Kai tayi, cikin lallashi yace"Allah ya saukeki lafiya maamah"
Tace"Amin Uncle"
Tasakar masa kiss akan lips dinsa, sannan sukaci gaba da baccin.
Washe gari Bayan sungama breakfast ta kalleshi tace"Uncle Dan Allah inaso Inga Ummah ta, na Dade ban ganta ba, ita Kuma kasan ba zuwa zatayi ba"
Hajja tace"toko nakira ta tazo taganki idan bayason ki fita?"
Mama tace"har wani? Yanzun me suke? Su tashi suje mana"
Shahaab ya kalleta yace"muje to, Amma muna zuwa zamu dawo gidanmu, banason mutane su dinga kallonki"
Murmushi tayi, ta kama hannunsa suka futo compound din gidan, Hajja da mama suka Ta6e baki batare da sun tanka ba, mota ta nufa, suna zuwa yabude mata da Kansa tashiga, Shima yashiga sannan driver yataho da sauri yaja suka bar gidan.
Suna zaune abaya, hannunsa yana cikin Nata, yad'ora dayan hannun akan cikinta, yad'ora bakinsa akan kunnan ta cikin rad'a yace"Ummah zataga jikanta yafara girma....."
Murmushi tasaki, kafin tabashi amsa sukaji wani irin qara garammm anbigi motar su, motar data bigesu tasake tahowa tasake bugarsu, motar su tahadu dawani gida ta bigi bangon gidan, kasancewar basuyi Nisa da gida ba wannan qaran ne yasa sojojin dake gidansa
futowa cikin sauri, tsananin tashin hankalin dasuka ganine yasa suka zuba a guje sukayi wajan motar su Shahaab wadda ta hautsina, wasu Kuma suka doru abayan motar data bigesu wadda ta juya da mahaukacin gudu, lokaci daya aka fara musayar wuta, kowa yana harbi, tun lokacin da'akabigi motar su kan Shahaab ya bugu da dayan gefen, yayinda Aisha Kuma tana daga 6angaren da motar tahadu da ginan, kanta yahadu da bango glass din windon yafashe,kasancewar batada nauyi, Kuma bata saka belt ba yasa tafado Qasan motar, cikinta yabugu da jikin kujera, lokaci daya ta runtse idonta, motar ce tafara hayaqi kamar wani abu yafashe aciki gaba daya Sai hayaqi yarufe motar, cikin sauri sojojin suka bude motar, aka futo da direban Wanda ko motsi ma ba yayi, cikin tashin hankali Shahaab yasaka hannu yadauko Aisha,Bai duba yanda hannunsa yafashe yake zubar da jini ba kawai Tata yake, futowa yayi da'ita waje Sai Alokacin yaga kanta yafashe yana zubar da jini, duk jini ya6ata mata gashinta, fuskarta yariqe yana jijjiga ta,tareda fadin"Aisha!, Aisha!! Aisha!!! Bude idonki ki kalleni "
Amma kokadan Aisha batayi motsi ba, daya daga cikin sojojin ne yace"yalla6ai tana zubar da jini yakamata mutafi Asbiti abata taimakon gaggawa"
Sai Alokacin ya zubawa jikinta ido anan yaga jini take zubarwa duk qafafunta sun 6aci,jini har qasa yake sauka, gabansa ne yayi mummunar faduwa,cikin tashin hankali ya furta "innalillahi wa inna ilaihirraji'un"
kamar mahaukaci haka ya dauketa duk jini ya6ata jikinsa, cikin sauri aka wuce dasu Asbiti, suna zuwa wasu nurses guda biyu mata suka kar6i Aisha, likitan dazata dubata tana ganin yanda jini ya6ata jikinta tace"Subhanallahi wannan tasamu miscarriage ne?"
Daya daga cikin nurse din tace"Dr. Bamu saniba yanzu de aka kawo ta"
Yana jin haka ya Lumshe Idonsa hawaye me zafi ya silalo daga Idonsa, hannunsa biyu yasa yadafe goshinsa dashi, baisan lokacin daya fara shashshekar kuka ba, kokadan ya manta da ciwon dake hannunsa, sojojin dake tsatstsaye awajan duk jikinsu yayi Sanyi ganin yanda Mahmud Wakili yake kuka da Kansa, wasu sojoji ne guda biyu suka shigo cikin 6acin rai suka tsaya akansa daya daga cikin su yace"yalla6ai munyi nasarar samun Wanda suka aikata wannan laifin, Yanzu haka mun miqasu hannun hukuma, Kuma kafin mu kaisu ma saida muka motsa musu jikinsu, sun kuma tabbatar mana da cewa Hajiya Munirat ce ta turosu"(ππ»ββοΈ)
To.... ko Yaya zata kasance tsakanin Shahaab da munirat yanda yad'ora wa wannan ciki rai? π€
Ina labarin Mama da Hajja ne dasuka niqi hanya suka bar qasar sukaje suka siyo kayan Baby?π€
Muhadu zuwa Anjima ππ»
SHAHAAB LITTAFIN KUDI NE, IDAN KIKA KARANTA BAKI BIYABA NABARKI DA ALLAH BAN YAFEBA
300 NE KACAL
0164549488
Amina muhammad
GTbank
Mrs Usman ceβ
Page 23
Cikin sauri ya d'ago Kansa ya kalli sojan dayake masa wannan bayanin, lokaci d'aya yanemi kukan dayake yarasa, kafin yayi magana su Hajja da Mama dakuma Ummah da Abba suka shigo asbitin cikin alhini,Ummah tasamu waje ta zauna ta Lumshe idonta,addu'ah take acikin zuciyar ta akan Allah ya dubi wannan bayi nasa yasa kar wannan ciki yafita, Abba kuwa wajan Shahaab yaje ya zauna yana bashi haquri, Hajja da mama kuwa, kuka suke wiwi, mama Sai salati take tana fadin"inna lillahi wa inna ilaihirraji'un,shikkenan yanzu babu ciki yatafi,abinda muka qwallafa rai akansa ashe bamuda Rabon ganinsa"
Hajja tace"wannan tsinannun mutane Allah ya kwashe musu Albarka, su Rasa wazasu kawowa Hari Sai wannan bayin Allah, yanzu shi ciki menene nasa daza'a hallakashi tun kafin yazo duniya"
Ramadan yashigo asbitin a fujajan sakamakon labarin daya watsu agari, Shima anan yaji, saida yafara zuwa office din Yan Sanda yaji bayanin komai, sannan yataho asbitin, gaba daya yahada uban gumi baima lura da mutanan wajan ba yana zuwa yace wa Shahaab "Wai ita wannan yarinyar metakeji dashi ne? Yaza'ai ta nemi ta wulaqanta mu agari haka kawai saboda tana so ta huce haushi? Idan yarinyar mutane ta mutu tana tunanin za'a Barta ne?"
Shahaab yadago Idonsa Dayayi jajir ya kalli Ramadan yace"wallahi tallahi illa daya idan maamah taji, itama munirat saita jishi"
Cikin sauri mama ta kallesu yace"munirat Kuma?karka cemin itace ta turo su?"
Ramadan yace"yaran sunyi magana sun tabbatar da cewa itace ta saka su,but a yanda sukai bayani kawai tasa suzo suyiwa Aisha illa ne,da alamun batasan cewa tanada ciki ba"
Hajja ta dora hannun ta aka tace"laaaa ilaha-illallahu....mahammadurrasulullahi, s.a.w"
Mama tace"Yanzu munirat Bayan kokarin kasheni datayi hakan bai mataba saita sa andauki haqqin yarinyar da bataji ba bata Gani ba? Aikuwa yau zamu raba raini tsakanin nida ita, yanda tasa cikin Aisha ya zube wallahi itama yau saita zube"(ππ»ββοΈ)
Tana fadar haka tamiqe da nufin fita, itama Hajja ta d'oru abayanta, likitan datake duba Aisha tafuto,Shahaab yana ganin ta yatashi tsaye, ahankali yace"Dr. Yaya jikin Nata?"
Mama da Hajja cikin sauri suka fasa fita suma suka dawo wajan Dr, mama tace"likita cikin yagama zubewa ko?"
Dr. Ta kalli Shahaab tace"jikinta da sauqi Alhamdulillah, saide tasamu rauni akanta, sannan Kuma ta zubar da jini da yawa, muna buqatar me irin jinin ta yazo mu dauka Sai aqara mata"
Sai Alokacin yasaki ajiyar zuciya, Ummah kuwa har lokacin tayi shiru kawai addu'ah take acikin zuciyar ta,Dr. Ta dubi mama tace"cikinta yana Nan bai fitaba, saboda ankawo ta Asbiti akan lokaci, da andauki tsawon lokaci ba'a kawo taba, to da tuni yazube, yanzu de muna buqatar jinin"
Ummah ta daga hannunta sama tana godewa Allah, Hawayen farinciki dakuma tausayin yartata yana tsiya ya daga idonta, Shahaab ya juya ya kalleta cikin sauri ya kauda kansa Gefe, matar tanada alkunya sosai, tunda suka shigo asbitin yaga bata cewa um bare um um, ya tabbatar duk yanda suke jin ciwo aransu basu kaita ba, tafi kowa jin ciwon abinda yasamu Aishan, Amma gata a zaune ta nutsu tana mata addu'ah, saiya sake jin Hankalinsa ya kwanta akan auren Aisha, koba komai tasamu tarbiya ta 6angare guda biyu, Hajja da Kuma mahaifiyar ta, kafin yagama wannan tunanin yaji Abba yana cewa"muje a dauki nawa agani ko zaiyi mata"
Cikin sauri Shima Shahaab yace"muje Dr."
Duka su ukun ne suka bita lab, aka dauki na Abba da Shahaab, dakuma Ramadan, Ana dubawa a kaga na Abba da Ramadan ne yayi daidai da Nata, na Shahaab baiyi ba,nasu aka dauka aka saka mata, sannan Shima Shahaab sukaje aka duba nashi hannun, inda yaji ciwo.
Bai kwanta ba, Ana gama masa sukaje suka duba jikin driver Wanda yaji ciwo harda karaya a hannunsa, sun dade a d'akin sannan suka futo, kan kace me Asbiti Yacika kowa yana zuwa dubashi, banda masu kiransa awaya suna masa jaje kasancewar labari ya watsu ko'ina, ba'a basu damar ganin Aisha ba Sai dare,gaba dayansu d'akin suka shiga, Alokacin itama ta farka Shahaab yana gefenta yana bata tea marar madara kamar yanda ta buqata, ansaka mata bandeji a goshinta, mama tace"Takwara ga abinci kici saiki Sha magani ki kwanta ko?"
Yatsina fuska tayi, sannan tace"mama banason cin abincin Nan"
Shahaab yayi qasa da murya bakinsa gab da Nata yace"mekike so?"
Kai tsaye tace"fruit zansha"
Cikin sauri yatashi yadauko mata fruit din dake ajiye agefe, ya zauna yafara bata,Ummah da Abba suka hada ido sukai murmushi, Ummah tace"to Allah yasawaqe, Bari mutafi gida"
Hajja tace"to saida safenku Hadiza, Allah yakiyaye hanya"
Aisha ta kalleta tace"Ummah idan zakizo gobe kimin kwad'on zogale, Amma karki sa suger aciki, kawai kimin haka"
Cikin sauri Shahaab yace"zogale Kuma?"
Kallonsa tayi, tayi kalar shagwa6a da fuskarta batace masa komai ba, Girgiza Kansa kawai yayi, baice komai ba
Ummah tayi murmushi tace" to zan kawo miki"
, sannan suka fita, Ramadan Kuma yabisu abaya domin rakiya.
Mama da Hajja ne suka zauna da Aisha, Shahaab da Ramadan kuwa basu tafi gida ba Sai wajan karfe goma Sha biyu saura, a hanya Ramadan ya kalleshi yace"yanzu menene abun yi? Yaya za'ai da mutanan Nan?"
Shahaab yasaki ajiyar zuciya yace"zanyi musu waya su lallasa musu jiki sannan su kaisu gidan kurkuku su rufesu, ciki harda ita ogar tasu, inda ace cikin Nan yazube, wallahi saina makata a court"
Ramadan yace"yanzun ma ai dole Sai an tura case din court,Amma yakamata kasanar ayi Maka tsakani kaida munirat, saboda yanzu da abun yazo da qaran kwana da tuni cikin da muke murna dashi yazube, sannan driver yamutu, kaga rayuka guda biyu ace a dauki haqqin su abun babu dadi, kawai ayi muku tsakani kaida ita"
Shahaab yayi murmushi baice komai ba,shi kadai yasan me yagama shirya wa a ransa, haka suka qarasa gida Ramadan ya ajiyeshi, sannan yatafi gida, shi kadai ya kwana a gidan Bayan yayi wanka, Dasafe Ramadan yakai matarsa asbitin ta duba jikin Aisha, sannan yawuce gida yadauko Shahaab Wanda yake shirin futowa domin tafiya asbitin , Kai tsaye yace"muje wajan wadancen masu laifin"
Babu musu Ramadan yajuya kan motar sa zuwa police station, suna zuwa mutanan wajan suka fara bashi girma Ana gaishe shi,Sarai yaga momy a zaune agefe itada yayun munirat su biyu, Sai share hawaye suke, Amma yayi mursisi yarabu dasu yayi kamar bai gansu ba,Kai tsaye d.p.o yawuce dasu zuwa office dinsa,Bayan sun gaisa dakuma jajanta abinda yafaru Shahaab yafuto dawasu takardu guda biyu daga cikin aljihunsa yabawa d.p.o sannan yace"kabawa munirat wannan takardun, sannan atura case din court, ayi musu hukunci daidai da abinda suka aikata, Badon Allah yakiyaye ba, da yanzu driver na, da matata dakuma abinda yake cikinta sun mutu"
Cikin sauri d.p.o tace"Angama ranka yadade"
Ramadan yasaka hannu a aljihunsa ya ajiyewa d.p.o damin kud'ad'e sannan suka futo daga office din.
Ahanya Ramadan ya dubi Shahaab ysce"nayi tunanin zakace ayi muku tsakani kaida ita, sannan ayi musu duka gaba dayansu, Amma sainaga kace abata wasu takardu menene amfanin hakan?"
Shahaab yayi murmushi yace" wannan takardun danace abata, tafi Dukan da zance ayi mata, wannan takardun danace abata Sai ta gwammaci ayi mata duka akan ta gansu, babu wani abu dazaka yiwa mace,macen ma wadda take sonka, irin ka saketa, munirat tayi min abubuwa qarshe nasaketa saboda idan nabarta agidana ma to na budewa fitina da tashin Hankali qofa,takardun danace abata Kuma results din maamah ne na samun cikinta, wannan ma kadai ya isheta"
Ramadan yayi ajiyar zuciya yace"abun de babu dadi, Allah yasa mudace ya kiyaye gaba"
Shahaab ya Lumshe Idonsa yace"Amin"
Bayan tafiyarsu Shahaab , d.p.o yabawa wani kofur takardar da Shahaab yabashi yace"abawa waccen matar"
Kofur yakar6a yawuce yabawa munirat da idonta ya qeqashe ko d'igon hawaye babu,taso ace taji labarin mutuwar Aisha, saboda ta kowanne ganni Gani take itace tayi mata katanga tsakanin ta da Shahaab, haqiqa taso ace ta mutu saita ga Ina zai Kai rawar jikin dayake akan ta, shikkenan yayi biyu babu,itan dayake qi yasake ta, Aishan dayake so tamutu, tana budewa taci Karo da result din cikin Aisha na farko Wanda akayi mata test a Nigeria, sannan ta duba dayar taga Wanda akayi mata test ne a India, ihu tasaka tana kururuwar kuka, tayi watsi da takardun, lokaci daya numfashinta yafara yin sama, tasa hannu ta dafe qirjinta, cikin sauri su momy suka qarasa suka dauki takardun domin ganin abinda yasa ta cikin wannan hali, suna Gani jikin momy yad'auki rawa,hakan yana nufin Shahaab de lafiyarsa kalau abun daga 'yarta ne, hawaye ne yazubo mata, cikin tashin hankali tafara roqon Yan sandan su taimaka su futo da munirat daga magarqama domin taga halin da yarta take ciki.
(littafin kudi ne, idan kika karanta baki biyaba nabarki da ALLAH)
******
Zaune suke a d'akin da aka kwantar da Aisha, Shahaab yazuba mata ido yana kallon yanda take cin kwad'on zogale kamar marar gata, daya gaji da kallon ta saiya dauki wayarsa ya turawa Dr da sukaje wajan sa India saqo ta email dinsa dangane da matsalar cikin Aisha shin yanzun zai iya kusantar ta? Dr Kuma ya tabbatar masa zuwa yanzu Kam babu matsalar komai, Kuma yin hakan zai sake taimaka wa abinda yake cikinta yazama Mai lafiya da Kuma kuzari, idan bayayi dinma akwai matsala, jin wannan bayanin ne yasa Shahaab farinciki, yayi masa godia sannan sukai sallama ya maida wayarsa cikin aljihunsa.
Satinta d'aya a Asbiti aka sallameta, duk wata kulawa data dace anbata, sosai jikinta yayi kyau saide fari data sake yi, tunda suka dawo gida Nan ma mama da Hajja basu Barta Takoma part dinta ba, saida tasake murmurewa sosai sannan Hankalinsu ya kwanta sukai maida ta part dinta, zuwa wannan lokacin an yanke wa su munirat hukunci inda aka tura su gidan kurkuku tsawon wasu watanni.
Ranar da Aisha Takoma part dinta a ranar Shahaab yasake zama ango, domin kuwa tsawon lokacin Nan daya dauka baiyi ba saida ya fanshe shi, Kuma abinda yasake bashi qwarin gwiwa shine yanda yaga Aishan itama tanaso, a ranar basu zo part din mama ba, suna can manne da juna suna soyaiya kamar zasu cinye kansu.
Washe gari suna zaune a dinning suna fara breakfast,Aisha ta miqe tana cewa"bari in sake shan tea dinnan naji yamin dadi sosai"
Mama tace"bari inhada miki takwara, yi zamanki"
Babu musu ta zauna, mama Kuma ta had'a mata tea din Wanda yake turiri sosai saboda zafi, Aisha tasa hannu zata kar6a Shahaab yayi wuf ya kar6e cup din yace"mama wannan ai yayi zafi dayawa"
Hajja tace"to d'aga mata shi zakayi?Dan Allah kudena sangarta yarinyar Nan,kubarta ta dinga aiki da kanta saboda haihuwa ce a gabanta"
Cikin damuwa Shahaab yace"ni ban hanata shaba, Amma wannan de yayi zafi dayawa idan kuma yaqona min Baby fa?"(π€)
Hajja ta tuntsire da dariya tace"idan batasha ruwan zafi ba, ai zatasha a wankan jego, zamu gauraya ne"
Shahaab baice komai ba saida yaga tea din yadena turiri sannan yabawa Aisha, mama kuwa murmushi tayi tana jin dadin yanda Shahaab yake Bawa Aisha kulawa.
Haka rayuwar tasu take tafiya cikin kwanciyar Hankali,idan Aisha tayi fada da Shahaab to akan cikin tane,bata Isa tadanyi gudu ba kokuma wani aikin saiya fara yimata fad'a yana masifa zata kashe masa Baby,hakan dayake mata saiya sake harzuqa ta tabiye masa su dinga fada, daga qarshe Hajja tayi mata fada da nasiha akan ta dinga yimasa uzuri akan cikin, abinda yadade shekara da shekaru ne yana nema yanzu Kuma yasamu, fadan Hajjan ne yasa take haquri dashi Ahaka har Cikin Yacika wata takwas, a Asbiti aka bata umarnin ta dinga yin tattaki saboda jikinta, cikin yafuto sosai ya girma duk Wanda ya ganta zaiyi tunanin haihuwar tazo yau ko gobe ne, Nan kuwa akwai sauran kusan wata daya, yau ma tagama Dan zazzagaya compound din Adede lokacin Shahaab yadawo daga wajan aiki, daga nesa ya hangota