Showing 66001 words to 69000 words out of 115646 words

Chapter 23 - Shahaab Complete Hausa Novel

12 Oct 2024

9593

aciki,sannan yatura vedio yayi Yan danne danne tsawon lokaci, sannan yatura mata computer gabanta yace"mama, idan kikaga irin wannan vedion nutsuwa yakamata kiyi ki kalla dakyau mama, yanzu duba kigani Bani bane, ba Kuma Aisha bane, dora fuskar mu akayi akan vedio,kiduba jikinsu kigani, mama wannan yarinyar tafi Aisha girma, ki kalli surar jikinta dakyau, sannan ki kalli ta namijin Shima kigani, ga zahiri nan computer ta nuna miki, duba kigani mama"

Ajiyar zuciya tayi, ta share Hawayen idonta sannan tafara kallo, lokaci daya tasaki salati tace"yanzu Dama anayin haka Mahmud?"

Yace"gashi kuwa kingani mama?, bani number da'aka turo miki vedion, zansa ayimin tracking dinta"

Babu musu mama tabashi number, murmushi yayi har dimple dinsa suka futo yace"yanzu shikkenan Hankalinki ya kwanta?"

Sake goge idonta tayi tace"AISHA"

Murmushin yayi, sannan ya shafa sumar Kansa yace"mama nida Aisha mun dade muna tare"

Cikin sauri ta Kalleshi, Shima ya Girgiza mata Kai sannan yace"qwarai kuwa mama,nahadu da Aisha tun cikin azumi,Kuma kece silar haduwa ta da Aisha mama, tun lokacin dakika umarceni naje Jigawa State in bude miki gidan marayu saboda qawar ki, tun Alokacin nahadu da'ita, idan Zaki tuna mama Alokacin banda magana saide ince zanje jigawa, ki gafarceni mama, Amma wani lokacin ba wajan wannan aikin nake zuwa ba, wajan Aisha nake zuwa, nadauki shawarar ki data Ramadan cewa in6oyewa budurwar danakeso kaina, hakan nayi akan Aisha, ban nuna mata inada kudi ba naje mata a matsayin Yaron Mahmud Wakili, ahakan ta amince Dani take soyaiya Dani, iyayen Aisha talakawane mama, suna rayuwa cikin kwanciyar Hankali zuwana cikin rayuwar ta saida hakan yata6a wannan farincikin na ahlinsu, duk abinda nasaka ta shi take min,kudin dan'uwan ta datake aiki take Tarawa tana so Yaron yakoma makaranta shita dauka tamin kyauta dashi mama, A'ina zan samu irin wannan soyaiyar mama?akwai Wanda akeso abata agida tace ita Shahaab take so,dalilin hakane yasa babanta yaturo ta aiki Abuja, baisan cewa gidana yasake turo taba, ranar Dana dawo daga Australia a ranar na ganta a gidan Nan idan zaki tuna Alokacin nashiga cikin wani irin yanayi, kiyi hakuri mama, Amma inason Aisha, bantaba son kowacce yarinya kamar son danake mata ba Bayan ke, inaso Dan girman Allah mama kinemomin Aurenta please"

Ya qarasa maganar yana hade hannayensa waje daya, mama data zuba masa ido tana kallon sa tasaki ajiyar zuciya tace"amma kukan anyi munafukai, daga Kai har Aishan ba qananun munafukai bane, ni Ina zaune ashe ku soyaiya kuke shiyasa kake wa yarinyar mutane ihu saboda tace tadena son Wanda ya yaudare ta? Yanzu ashe Dama dakai take? Yanzu fisabilillahi ka kyauta abinda Kamin Shahaab? Kasan Sarai kanason yarinyar Nan Amma shine lokacin da batada lafiya na riqeta kadinga ta6awa yarinya nonuwa kod'an musu babu? Yarinyar Nan bata so Amma haka nasa ta tsaya saida kagama abinda kaga Dama sannan karabu da'ita,meyasa lokacin ko dukanka zanyi bazaka cemin bazaka ta6aba?"

Wata irin matsananciyar kunya ce ta kamashi, yayi sauri ya sunkuyar da Kansa qasa tareda Sosa qeyarsa yace"mama saida nace Miki a a...fa"

Cikin sauri tayi masa daquwa tace"qarya kake Shahaab,cemin kayi dubawa de kake,nasan hakane yaushe zanyi wannan danyan aiki?"

Kansa yana qasa yayi Dan qaramin murmushi, sannan yadan kalleta cikin kunya yace"mama to Zaki nemamin auren Nata?"

Fillon dake gefenta ta d'auka takai masa duka dashi tace"Wato Aisha ta maida Kai marar kunya, aini babu abinda zance, idan kaga zaka iya yiwa munirat kishiya shikkenan, dama kaine kake cewa kaida munirat Sai Allah, yanzu Yaya za'ai Naga Aisha?"

Cikin nutsuwa yace"za'a ganta mama,ki kwantar da Hankalinki,mutuqar agogon Dana daura mata yana hannunta, to dole zansan inda take"

Mama tasaki wata irin ajiyar zuciya tace "Alhamdulillah, Allah abun Godia, to tashi kaje kabawa matarka haquri Dan itama anturo mata wannan vedion, kabata haquri ka fahimtar da'ita cewa videon hadawa akayi"

Cikin ladabi ya amsa mata, sannan yatashi yad'auki kayansa, yawuce part dinsa, yana zuwa falonsu yayi sallama tareda shigowa, tana zaune afalon saide ko kallon inda yake batayi ba, cikin zuciyar yace"fishi kan fishi kenan, Dama da fishin company yanzu Kuma ga wani ya qaru"

Murmushi yasakar mata, sannan yace"Bari inzo inyi lallashi"

Munirat ko kallon sa batayi ba,Shima Kai tsaye dakinsa yawuce yana tunanin irin lallashin dazai mata kozai samu yau tasakar masa jikinta yayi yanda yakeso da'ita, saboda a matse yake, kwana biyun Nan kawai yana daurewa ne,yana shiga Dakin yacire kayan jikinsa,dagashi Sai Dan qaramin towel a daure a qugunsa, murd'ad'd'an jikinsa yafuto fili, fatar jikinsa tayi wani irin fresh, lallausan gashi kwance akan faffad'an qirjinsa,yana shirin shiga wanka kenan wayarsa tad'auki qara, dawowa yayi ya zauna abakin gado tareda daukar wayar yayi sallama, daga dayan bangaren akace "Ranka yadad'e sunana Alhaji Umar Amare, nine mamallakin filayen Nan guda biyu danasa afara ginamin Kuma yanzu Yara sun kirani sun fadamin katuro a rushe ginin, shine nace ai babu Wanda baisanka ba a qasar, na bincika nasamu number ka awajan yaronka Auwali, nace Bari in kiraka inbaka haquri, Dan manzon Allah kayi hakuri, Nima wannan fili, siyarsa nayi, Kuma nadauki kudi nabawa wadda nasiya awajanta da shedu na dakomai, tasa hannu Nima nasa hannu, tabani takardun filaye Nima nadauki kudi nabata"

Cikin tsananin mamaki yace"wacece ta siyar Maka?"

Cikin tabbatar wa yace"Sunanta Munirat Abdul Salam,domin kuwa Alokacin ma ban sayi filayen ba saida ta tabbatar min cewa mijinta ne yabata su kyauta, saboda kasan harkar ciniki da mata"

Wani irin duhu duhu Shahaab yafara Gani, duk bayanin da mutumin yake masa kwata kwata baya jinsa, tun lokacin daya ce masa munirat Abdul Salam, tundaga lokacin yanemi nutsuwarsa yarasa, cikin tashin hankali yace"Kanaji na? Zanbaka kudin filayenka, da kudin daka kashe na aiki, saika Bani takardun filayen"

Cikin sauri Alhaji Umar yace"to yalla6ai babu damuwa godia nake"

Daga Nan yakashe wayar.

Wasu irin hawayene masu mutuqar zafi suka zubo daga idanun Shahaab, cikin ransa yace"munirat?"








Da alama zancen lallashi ya rushe 🤣🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️



Shahaab littafin kudi ne, idan kika karanta baki biyaba nabarki keda mahaliccin ki,inde ubangiji yana sakayya na tabbatar zai Sakamin

300
0164549488
Amina muhammad
GTbank


Ko katin mtn

Shedar biya ta wannan number 08033300034





Amnah El Yaqoub✍🏻



Page 37








Gaba daya saiya nemi 'yar sha'awar data addabeshi yarasa(😂)

Kansa yariqe da hannunsa guda biyu yafad'a Kan gadon tareda furta"innalillahi wa inna ilaihirraji'un"
Wani Hawayen ne suka sake zubo masa,yaji duniyar tayi masa zafi gaba daya, Dame yarage ta? Meta nema tarasa awajansa?meyasa zata masa haka? Har tasan tad'auki takardun filaye ta siyar, me zatayi da kudin? Meyasa mutumin daka daukakeshi fiyeda kowa yake cin amanarka daga baya?menene baiyiwa munirat ba? Haduwarsa da Aisha ne kad'ai yasan cewa yaraba soyaiyar dayake mata gida biyu yabawa Aisha d'aya,jin wayarsa tana ringing ne yasa yayi saurin goge Hawayen Idonsa, a fili ya furta, "dole zan dauki mataki akan munirat".

Wayar dake shirin katsewa yayi saurin dauka, daga dayan bangaren mama tace"Shahaab kaduba kagano inda Aishan take?"

Saida ya daidaita muryarsa yanda bazata gane yana cikin wani Hali ba, sannan yace"ban dubaba mama"

Cikin sauri Tace"A a, Tome kake nufi?shikkenan daga shiga wajan matarka harka manta da batun yarinya?yarinya qarama tafice tabar gidanka kacemin zaka duba Amma kayi biris harka samu munirat ka manta da Aisha,?Anya kuwa Shahaab zan'iya nema Maka auren yarinyar Nan? Tun yanzu ma kana shiga wajan matarka ka manta da batunta, tayaya za'a yi maganar aure tsakani da Allah?"

Duk da yana cikin halin damuwa saida ya danyi qaramar dariya yace"mama wanka zanyi saina duba nagani, karki damu mama, Aisha bazata 6ata acikin qasar nan nakasa dubo taba aduk inda take"

Cikin sauri tace"to hanzarta kayi wankan"

Wayar ya kashe, batareda tunanin komai ba ya lalubo number Hajja, wannan ne kiransa na farko wayar Hajja tun Bayan zuwan Aisha gidansa, kamar jira Hajja take, wayar tana shiga ta d'auka tareda sallama, cikin ladabi yace"Hajja barka da wannan lokaci"

Hajja tace"yawwa barkanmu dai, dawa nake magana?"

Murmushi yayi yace"Sunana Shahaab"

Cikin sauri Hajja tace"kacewa? Shahaab koba Shahaab ba?"

Cikin sauri Shima yace"eh haka nace, nine Shahaab, dama Ina neman Aisha ne"

Hajja tayi ajiyar zuciya tace"wacce Aisha?saida ka salwantar min da jika zaka debo jiki kana tambaya ta Ina Aisha? Nan kazo har gida ka hure mata kunne yarinya tayi tsalle ta dire tace Nan duniya saikai, kasa mamuda yaturata aiki har yau bansan inda jikata take ba, wallahi Shahaab idan Namutu bansake saka jikata a'idona ba hakuma ce zata rabani dakai...." daganan saita Fashe da Kuka

Runtse Idonsa yayi,cikin ransa yace"kuka!,kamar de Aishan"

Cikin nutsuwa yace"kinga, kiyi hakuri, insha Allah zata dawo gida lafiya, kiyi hakuri Dan Allah"

Cikin masifa Hajja tace"zaka rufemin baki ko saina wankeka da Mari? Kashe waya!"

Cikin sauri yakashe wayar yana Girgiza Kansa, da alama rikitacciya ce kamar mama, ajiyar zuciya yasauke, hakan yana nufin bataje gidaba kenan, dole zai bincika yagani, cikin sauri yatashi yashiga wanka


(idan kika karanta baki biyaba nabarki da mahaliccinki)
******

Bayan gwagwar mayar da Tasha, daqyar da d'an turancinta tasamu aka kaita inda zata shiga motar dazata kawo ta kano,suna cikin tafiya tana share hawaye daga idonta kad'an kad'an, waye yayi mata wannan sharrin? Abinda take tambayar kanta kenan, tun tana share hawaye harta Dena,tana addu'ah tana kallon garuruwa da dajujjukan dasuke wucewa har Allah yakawo su kano lafiya,yamma tayi sosai kasancewar hanyar akwai go slow, anan ma bata Sha wahala ba kawai napep ta tare tafada masa tana so yakaita inda zata hau motar dazata kaita dutse, yafada mata kudin, ta d'auka tabashi, sannan tashiga suka tafi, can ma tana zuwa tashar ake tambayar ta Ina zataje? Tafada musu dutse zataje, suka nuna mata wajan da ake lodin motocin dutse, taje tashiga, mutum biyu ne suka shiga Bayan shigar ta, aka kar6i kudin kowa, sannan driver yaja suka tafi, basu zo dutse ba Sai wajan karfe biyar da rabi, zuwa wannan lokacin duk ta gama galabaita, qafafunta sun dauki ciwo, ga yunwa, tunda tataho babu abinda tasaka acikin bakinta, ko tayi niyyar siyan wani abun idan ta tuna irin sharrin da aka mata saita ji duk duniyar ma tafita akanta, yanzu wannan vedio idan aka turawa wasu awaya shikkenan ita Kuma tagama watsuwa a duniya, lokaci daya, taji wani irin hawaye yasake zubo mata, cikin sauri tasaka hannu ta share, sannan ta nufi inda zata hau motar dazata kaita cikin garinsu, wato Garin CHAMO.


******


Bayan yagama wanka ya shirya, yad'auki computer sa, Adede lokacin munirat tashigo Dakin nasa, fuskarta babu walwala ta Wulla masa wayarta wadda ta kunna vedion da aka turo mata itada mama,wayar ya kalla yaga de irin vedion da mama ta nuna masa ne dazu, yasake kallon vedion ya kalleta, sannan ya Ta6e bakinsa yara6a ta gefenta yawuce, har yanzu idan ya tuna irin ta'asar data masa, wani irin qullutun baqin ciki yakeji a ransa, tabashi mamaki yanda baya zato, ko kadan bayason sake ganin ta, hakanne yasa daya futo zuwa falon su ma bai tsaya anan ba, Kai tsaye yafice zuwa compound din gidan cikin yar qaramar rumfarsu ta hutawa, wadda aka gama qwatata da tsari Mai kyau, ya zauna, sannan ya ajiye computer sa a gabansa yafara binciken location din da Aisha take, fuskar Nan tasa ahad'e, babu alamun farinciki ko walwala atare dashi, fatansa daya, Allah yasa bata cire agogon daga hannun taba, ko minti uku baiyi da zama awajan ba, Mai aiki tazo da sauri ta ajiye masa fruit da Kuma gorar ruwa tareda glass cup a gabansa ta juya cikin sauri.

Munirat kuwa mamaki da taqaicinsa ne suka sake kamata, tunani take a ranta me Mahmud yataka dayake mata wannan abubuwan?tana tunanin ai ayau din ta cancanci yayi mata komai domin ya lallashe ta saboda wannan vedio din, Amma sai gashi yagani, Amma yawuce yarabu da'ita, harda cewa zaizo ya lallashe ta ashe duk qarya ce Da yaudara, dama tariga tasan muddin yafara shiga wajan waccan tsohuwar, to Sai abinda ta kitsa masa, dama can ai itace tabashi lasisin iskanci da yarinyar, tunda itada kanta ta kama yarinyar ta riqe masa, yake ta6a mata nono, to yanzu kuwa dan ya aikata Zina da'ita ai ba zatayi masa fada ba, lokaci daya tasake jin tsanar mama acikin zuciyar ta, Fata take Dama ace ta mutu, kowama ya huta, tunanin da munirat ta dinga yi kenan Bayan fitar Shahaab daga cikin dakinsa.

Acan compound kuwa Shahaab baima kalli abinda aka gabatar masa ba, nutsuwa yayi yakafa Idonsa a computer yana aikin bincike, wata irin ajiyar zuciya yasauke Mai karfi, cikin tsananin farinciki ya furta"Alhamdulillah"sannan ne yad'auki inab guda daya yafara Sha ahankali, saida yasha fruit din sosai, sannan yatashi yanufi part din mama.


******

Lokacin datazo Garin duk mutane sun shiga sallar magrib, kasancewar Adede lokacin ta sauka, Garin take kallo kamar wanda tayi shekara bata cikin sa, wani irin farinciki ne ya kamata, jitake kamar tayi ihu, har gudu-gudu take hadawa dashi domin tayi sauri ta qarasa gida, tana shiga gidan kuwa ta kwasa a guje, Adede lokacin Hajja tana Zaman tahiya a sallarta, Ummah Kuma ta idar da alwala kenan ta miqe zata shige daki, cikin wani irin ihun murna ta daka tsalle ta d'ane umman ta, cikin jin dadi tace"Ummah...."

Cikin sauri Ummah ta juyo tana kallon ta baki bude, mamaki ya hanata yin magana, dariya tayi ta ce"ummah nadawo"

Hajja datayi sallama cikin tsananin mamaki tace"me sunan qawa?"

Cikin sauri tasaki Ummah tafada jikin Hajja tace"Hajja nah"

Sai a lokacin Ummah tayi magana tace"Wai kece Anya kuwa kokwade mafarkin Dana saba ne?"

Cikin sauri tace"Ummah nice mana, Zona mintsine ki kiji" taqarasa maganar cikin sigar tsokana.

Ummah tayi dariya ta Girgiza Kanta,tad'auki hijab tatada kabbarar sallah.
Hajja kuwa hannu ta daga sama ta kalli gabas tace"Alhamdulillah....Allah nagode Maka daka dawomin da jikata gida lafiya,su jummai Yan baqin ciki saide su mutu"(🤭😂)


******


Cikin farinciki mama tace"ikon Allah, ashe tana Jigawan, ninama Rasa Yaya akai kayi dabarar saka mata agogo me d'aukeda na'ura Shahaab,kodan kasaba yin dabara kana kama 6arayin gwamnati shiyasa yanzu ma kayi dabara kakamo 6arauniyar zuciyar ka?"

Cikin sauri ya sunkuyar da Kansa qasa saboda wata irin kunya data kamashi, saida yadan Sosa kansa, sannan ya kalleta yaga ita zuciyarta daya tayi maganar ko ajikinta, ahankali yace"a a mama, ainasan batada waya a hannun ta, nasaka na'urar a jikin agogon ne saboda idan inason ganin ta, zan duba Inga halin datake ciki, banyi hakan da wata manufa ba, Amma Kuma gashi cikin ikon Allah hakan yayi amfani, Bari inkira kakarta inji Yaya ta sauka, dafatan ta'isa lafiya, dazu nakira ta tanata fada, mama bakiji yanda ta rufeni da fada ba, halin ta sak irin na mamanah"(😂)

Cikin dariya mama takai masa duka tace"d'an mutum wasa ne Shahaab? Ai tanada gaskiya, karabu da'ita karka kirata, kabari gobe mushirya mubi jirgi, Sai muje a basu haquri, daga Nan Kuma Sai ayi maganar aurenku, kaga hakan zaifi, suma zasuji dadi Susan cewa sun turo yarsu gidan karamci"

Cikin jin dadi yace"to mama Allah yakaimu, saimu tafi sassafe ko?"

Mama ta kallashi,Shima kallon ta yayi, Sai a lokacin yaga kallon Fassara take masa, cikin sauri yatashi yabar falon Nata cikeda kunya, Sai aikin shafa lallausar sumar Kansa yake.

Mama data bishi da kallo tana ganin fitarsa tasaki murmushi, ta daga hannunta sama tana yiwa Allah godia daya karkato mata hankalin danta yake son aure yanzu, tana fatan ace anayin wannan aure Aisha tasamu ciki ko Allah zaisa itama taga jikokin ta kafin tarasu.


******

Gaba dayansu su ukun atsakiya suka saka Aisha sunajin yanda take basu labari, Abba ya kalleta yace"amma qawar Hajja banda Shirman ki Dan kun samu Sa6ani da uwar Dakin naki saiki niqo irin wannan hanyar kitaho ke kadai? Bakya tsoron asaceki a hanya?"

Ummah tace"hanya Kam babu kyau, yanda ake diban mutane kamar wasu dabbobi,qasar nan anmaida rai ba'a bakin komai ba"

Murmushi tayi tace"wallahi Ummah Ina mata komai,Bana mata rashin kunya saboda tsohuwa ce, yanda kikaga Hajja itama haka take, Amma idan ta rikice saiki Rasa gane kanta, shiyasa Nima nataho gida, dama nagaji,ga sauran kudina ma kuyi amfani dashi Ummah"
Ta qarasa maganar tana bude handbag dinta, duk sauran kudin dake ciki ta fitar dashi ta basu, Hajja ta kalli kudin tace"me sunan qawa wannan kudin ai yayi yawa,duk na menene haka? Ko kudin aikin naki ne?"

Kanta ta Girgiza Tace"A a Hajja,me gidan ne yabani kudin da Kansa, ban roqeshi ba"
Abba ya Jinjina Kansa, Hajja tace"yawwa nikin tuna min ma, dazu wannan saurayin naki ya kirani, Wai sunansa Shahaab, ke yake nema in baki waya idan kina kusa, na qare masa tatas nace idan yasake kirana sainaci masa mutunci, shida yayi silar barinki gida?"
Murmushi tayi tace" Hajja Aida baki masa haka ba"

Kafin Hajja tayi magana Abba yace"har yanzu de baki rabu dashi ba kenan, bamu Isa mu fada miki magana ki saurari maganar mu ba, ai shikkenan Allah yabada sa'a"

Jikin Ummah yayi Sanyi jin furucin Abba, ta kalli Aisha taga yarinyar tanata Fara'ah, Sai can Aishan ta d'ago kanta ta kalli Abba Tace"Abba Bahaka bane, Amma kayi haquri, duk bayanin dazan Maka ba lalle ka ganeba"
Daga Nan bata sake cewa komai ba tafada duniyar tunani
batason taga yanda Abban ta zaiji kunya, Amma data fada masa cewa Shahaab din de dayake qi shine Mahmud Wakili, Shahaab din dayake qi gidansa yasake tura ta aiki, tasan Hajja zata masa wankin Babban Bargo, ahankali tasake cewa "Abba jabir bai fada muku Mahmud Wakili ne ya turashi qasar waje karatu ba? Bai fada Maka shine yatura ka umara ba?"

Cikin tsananin mamaki Abba yace"mahmud Wakili Kuma?"

Hajja tace"jabir bai fada mana koma ba, Amma menene dalilin yimana wannan abun? Keda kike gidansa bai fada miki saboda me yayi mana haka ba?"

Murmushi tayi ta Girgiza, sannan tace" tunda nafada muku yanzu saiku shirya kuje kuyi masa godia, saiya fada muku da dalilin da Kansa"

Hajja tace"tokode daga zuwa yaganki ya qyasa? Fadamin gaskiya"

Hararar Hajja tayi, tatashi tashige Dakin Hajjan tafara shirin wanka, Hajja tatashi tabiyo bayanta taga harta daura zani da alama wanka zata shiga, kallon ta tayi tace"mesunan qawa Habujan Nan ta kar6eki, jikinki yayi wani mulmul kamar matar kansila, kode kaji kikeci ne kullum?"

Cikin dariya tace"kullum sunake ci, abinci Kala Kala Hajja Sai Wanda naza6a, nama kuwa kamar abun banza"

Hajja tace"ikon Allah, kice naman kaji yana Nan kayan qarfi..."

Aisha tayi dariya tace" karfin ne kawai bakida shi Hajja da kinje kema kinci"

Murmushi Hajja tayi ta qaraso Dakin, ita Kuma ta juya tashige wanka.


******

Yau yariga mama futowa falo,tun sassafe yafuto su kansu ma'aikatan sunyi mamakin ganinsa afalo, yad'ora kafa daya Kan daya yana kallo, yayi mutuqar kyau cikin suit, Sai qamshi yake zubawa, Sai wajan karfe takwas mama tafuto, ta shirya cikin less Mai ruwan golden, hannunta da

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login