Showing 114001 words to 115646 words out of 115646 words

Chapter 39 - Shahaab Complete Hausa Novel

12 Oct 2024

9638

matar MAHMUD WAKILI ce, cikin shekara d'ayan Nan tasake murmurewa jikinta ya murje, bata hada qiba sosai ba, Amma kokadan babu alamun Rama atare da'ita, leshi ne ajikinta dinkin doguwar Riga, batayi wani Daurin dankwali Mai wahala ba, Sai sarqar gold da zoben gold dasuke hannayenta, cikin yanayin roqon alfarma tace"Uncle Dan Allah, tunda ankusa fara bada admission Nima Atemaka min mana, in danyi karatun Nan"

Cikin sauri ya kalleta, yayanta biyu, idan tafara karatu babu Wanda zaice tanada aure, yanzu nema girma da Dan Hankali suke sake shigar ta, yanda yakejinta a ransa baya tunanin zai iya barinta ta dinga cudanya tsakanin ta da wasu mazan, kafin yabata amsa Yaron dake kwance akan gadon yafara kuka, cikin sauri yasaka hannu ya tattare babbar rigar jikinsa, sannan yad'auki Yaron yana jijjiga shi, yasaka masa fida a bakinsa yana cewa"sorry sojana, kaida baka kuka, waya tabaka kake kuka? Ko saboda kaji mummynka zata gudu makaranta tabarmu ne, uhm?"

Aisha tana jinsa tayi murmushi tace"Uncle zaka barni?"

Cikin daure fuska ya kalleta yace"meyasa bazaki daina min wannan maganar bane?"

Cikin nutsuwa tace"Uncle ilmi shine jigon rayuwa,kasancewa ta atare dakai inajina kamar ban Rasa komai ba, banida damuwar komai, Ina rayuwa ta yanda nakeso, Amma Kuma ta wani 6angaren nasan narasa wani abu guda daya shine ilmi, kabarni inyi karatu Nima ko kadan ne, Kaga FEENAH saida tayi masters dinta sannan ta auri AHMAD Bayan gwagwar mayar dayasha yana nemanta(DANA SANI).

haka AMAL itama mijinta KARAM,shine yakaita har qasar waje domin ta qaro ilmi kasancewar sa Babban mutum Kuma Dan siyasa yasan cewa dole matarsa zatayi mu'amula da kowanne irin mutane,(BURINAH)

IMAN bata auri ALIYU ba, saida ta kammala degree dinta na farko, sannan ta aure shi Kuma suka zauna lafiya (WAZAN ZABA?)

sannan duk wahalar rayuwa da HANIFA Tasha, Bayan tayi aure HANIF shida Kansa ya maida ta makaranta(SHALELAN BABA) duk saboda suyi yaqi da jahilci.

Haka BABY tana cikin karatun sauyin qaddara tasa ta auri MK, Shima daga baya saida ta qarasa karatun ta(NI DAKE)

sannan duk girma irinna Familyn mazawaje,kaga yayansu mata basa dogon karatu, Amma NIHLA qaddara tasa saida tayi degree dinta a Abuja, sannan ta Auri ABBA, (DANGI 'DAYA)


Haka ASIM, shida Kansa yake koyawa INSAAF, karatu, Kuma shine ya zabi abinda yakeso tayi(INSAAF)

WAHEEDA Bayan Aurenta da NAUFAL tayi karatun ta a qasar waje (BABBAN YAYA).

Meyasa nibazaka barni ba Uncle?"

Ajiyar zuciya yasauke yace"saboda nabarki kiyi karatu duk kika min irin wannan dogon misalin?, to saiki qara da cewa MAHMUD WAKILI, EFCC CHIRMAN, shine kawai baibar matarsa AISHA MAHMUD, tayi karatu ba"

Yana fadin haka yafice daga d'akin hannunsa d'aukeda junior,Mai sunan kakan Aisha wato mijin Hajja, Ismail,suna kiransa da junior.

Qafafunta tafara bubbugawa aqasa cikin shagwa6a, sannan tasa hannu ta dauki wayarta da handbag dinta, tabiyo bayansa, basu zame ko'inaba Sai part din mama.


Suna zuwa sukaga mama da Hajja suma sungama shirya wa, Kai tsaye wajan su yanufa ya ajiye musu Yaron, sannan yawuce zaici abinci, itama bayansa tabi, suka fara cin abincin.


Daddy yana ganin junior yataho da gudu yadawo wajan Yaron yayi masa kiss a kumatunsa, Hajja ta kama baki ta kalli Mama tace"ikon Allah,wacce irin al'adace wannan? Kode awajan iyayen nasa yake Gani?"

Mama ma da mamaki ya kamata tace"oho musu, jarabar uban kadai ma ai zatasa wataran yayiwa uwar agaban Yaron, anan zai Gani"

Ta kalli Daddy tace"Daddy na karfa ka cijeshi"

Juyowa yayi ya kalli Mama yace"Mama Baby ne?"

Tace"eh"

Yasake cewa"mama Baby ne?"

Tace"eh Baby ne"

Dariya yasaki yace"Baby nane"

Mama tace"nikwa nasan Babynka ne, tunda uwarku daya ubanku daya"

Hajja tayi dariya jin hirar mama da Daddy, tad'auki wayarta takira jummai, Bayan sun gaisa tace"to jummai gamunan zuwa, yanzu zamu dauko hanya kiyi mana kunun Aya Mai dadi de"

Daga d'ayan bangaren jummai tace"to Hajja A'i, Allah yakawo ku lafiya"

Hajja tace"Amin"sannnan tafara shirin kashe wayar, cikin sauri jummai tace"nikam Hajja A'i gulma ajali inba'ayi ba amutu, tun rannan kike cemin zakuzo nace ganin gida zaku zo ne kokuma wani abunne yataso?"

Hajja tace"kai jummai da gulma kike, to zamu zo taro ne, mijin Mai sunan qawa zai bude gidan marayun daya gina"

Cikin sauri jummai tace"oho, to, tona gane yanzu, to saikun zo, Bari naturo a siyomin kwatar aya, Sai ayi muku"

Hajja ta kashe wayar, Adede lokacin su Aisha suka gama cin abincin, suna zuwa Aisha ta dauki Junior, suka futo gaba dayansu, motoci biyu suka yi, suka wuce Airport,acan suka hadu dasu Abba da Ummah, basu dade da zuwaba, jirginsu yatashi.


Bayan sun sauka agarin ko zama basu yi ba, jummai tataho gidan, daga Nan manyan gari suma suka shishshiga mota sukai ayari gaba dayansu, suka wuce wajan taron, waje Yacika maqil da mutane, Gwamnatin Jihar ta basu hadin Kai yanda ya kamata, har akai taron bude gidan marayun lafiya, aka gama lafiya, su Aisha Kam gida suka iyo, Amma mazan duk suna can,kasancewar baqin da suka zazzo basu gama tafiya ba.


Acikin gidansu Aisha Bayan kowa yayi wanka gaba dayansu bajewa sukai a Babban falon Hajja wadda aka qawata shi da kayan more rayuwa, yaji kujeru kamar ba'a cikin Garin CHAMO, gidan yake ba.

Jummai ce tayi sallama takawo musu kunun ayar da Hajja tace ayi musu, mama Tasha Dan kadan ta ajiye, Aisha kuwa waya ce a hannunta tana turawa Shahaab saqo,Yayinda junior yake bacci akan kujera, Daddy kuwa daga shi Sai Dan qaramin wandon Yara tareda singlet yana wasa da ball a Dan qaramin tsakar gidan nasu, Hajja tad'auki kunun ayar Tasha, cikin sauri ta ajiye ta kalli jummai tace"jummai wannan aiba kunun Aya bane, kwata kwata babu gardin ayar abaki, wannan ai ruwan daurayar nawa kunun ayar ne, ni Dama tunda naji kince Zaki siyo kwatar Aya nasan cewa Sai ahankali"

Jummai ta gyara zamanta sannan tacire mayafin kanta tace"ke kwantar da Hankalinki, na yanzun ne nake zunduma masa ruwa, Aida Ina murna kin Bani firji na kama kunun Aya inayi ka'in da na'in, Ina farinciki zan samu kudi, to wallahi inayi jikokina suke shanye wa, baifi in samu ribar nera talatin ba, itama talatin din inbawa Dan talla ita, nikam Aina Dena yima"

Daddy yabugo ball tafado d'akin, yace"goooo, Hajja bugo"

Hajja tace"inani Ina ball Daddy?"

Jummai ta kalli daddy, sannan tajuya ta kalli Hajja tace" Hajja A'i gulma ajali....."

Kafin ta qarasa mama tayi dariya tace" fadi maganar da kike so kawai jummai"

Jummai tasake kallon Daddy, sannan ta kalli Hajja tace"shi wannan Yaron Jikan ki, zance ne kokuma Dan ki, bashine Yaron da Aisha ta Haifa ba?"

Mama tayi murmushi tace" shine mana, Daddy ne"

Jummai ta Jinjina Kai sannan ta kalli Daddy tace"kai yaka zonan"

Babu musu Daddy yazo wajan ta, ta kalleshi tace"yaya sunanka?"

Kai tsaye yace" Daddy"

Tasake cewa "shekarar ka nawa?"

Yace"hudu, biyar, shida"

Jummai tajuya ta kalli su mama tace"kaiiii, wannan Yaron bashine Aisha ta Haifa ba, yaro shekara biyu yake wannan surutun mu idan anan ne ai Musanta shekarun nasa zamuyi, ai wannan saide muce yabawa shekara biyar baya"

Adede lokacin Shahaab da Abba suka shigo,Shahaab yana jin abinda jummai tace yayi murmushi sannan ya tsugunna yana gaishe ta, cikin mutunta wa ta amsa tana sake tayaashi muryar bude gidan marayun da akai, cikin nutsuwa yatashi yawuce Dakin dasuka sauka, Shima Abba dakinsa yawuce Dama agajiye yake.


Aisha tana ganin shigar sa daki ta wuce kitchen tadauko masa awarar qwai, da damammiyar fura ta wuce Dakin, tana zuwa kuwa ta ganshi a kwance alamun hutawa yake, zama tayi akusa dashi tace"Uncle tashi Kaci awara da fura"

Babu musu yatashi, tafara bashi awarar abaki, yanaci yana hadawa da fura Mai Sanyi, saida ta tabbatar ya qoshi, sannan ta maida kayan kitchen tadawo Dakin Daddy yana biye abayanta

Shahaab ya kalli Yaron yace"Daddy zonan"

Yana zuwa yaja shi jikinsa cikin wayo yace"kanason sweet"

Daddy yace"Eh inaso"

Cikin sauri Shahaab yace"yawwa, to kaje Abba yabaka, yanacan da sweet dayawa awajansa, idan kagama Sha ka tsaya acan katayashi wasa, tun dazu yake nemanka"🙊😲

Cikin gudu daddy yafice daga d'akin, Aisha ta kalleshi, kafin tayi magana ya fuzgota jikinsa, hararar wasa tayi masa tafara nuna masa falo da hannunta, cikin tsananin buqata yace"to menene?"

Tace" Uncle, kaji tsoron Allah kaji tsoron mutum ukun Nan, Hajja, mama, dakuma iya Jummai"(😂🤣)

Idonsa a Lumshe, cikeda jaraba yace"idan bamuyi Bama bazasu daina mana surutu ba, kawai Gara muyi abunmu, munci abinci munsha ruwa, ba aikin komai zamuyi ba to menene yarage?"

Ya qarasa maganar yana yi mata wani irin kallo Mai kashe jiki, kanta ta Girgiza tafara kokarin raba jikinta da nashi, sake rungume ta yayi cikin shagwa6a yace"nide kibani Abuna, ya kamata anemawa junior qanwa, dama kina cewa kinason Baby girl, toba saimu samo masa Baby girl yar jigawa ba?"

Cikin shagwa6a tace" Uncle kaima fa kasan cewa bazaka iya control din kanka kayi shiru ba, sannan..... "

Cikin sauri ya katse ta yace" tayaya zan'iya control din kaina a wannan yanayin? But tunda ke kina iya control din kanki, Saiki rufemin baki, OK?"

Cikin shagwa6a ta kalleshi, saide kafin ta furta wani abu, yahade bakinsu waje daya.






TAMMAT BIHAMDULLAH🙏



Anan nakawo qarshan littafina na Shahaab, idan akwai Wanda na 6atawa rai sanadin wannan rubutun to Ina roqonsa yayafe min saboda Dan Adam ajizine, abinda Naga yamin daidai ba lalle ne yayi wa kowa daidai ba, tun muna rubuta abu Mai amfani karkuma mu dawo muna rubuta shirme,duk lokacin danake rubuta labarin Shahaab inajin kamar karna tsaya saboda nikaina inajin dadin labarin, to Amma Kuma babu yanda zamuyi dole haka zamu dakata saboda kar Kuma tun muna marmarin labari mudawo muna shirme, a tunani na Gara a taqaita labari tunda dadinsa, ta yanda masoya zasu dinga jajensa.

Masoyana Wanda suka nunamin soyaiya suka Sai littafi na banida bakin dazan muku godia,haqiqa kun nunamin soyaiya wasu soyaiyar dasuke min ce tasa suka Sai littafin fiyeda abunda nake saida shi,nasan soyaiyar dakuke min ne yasa hakan, Ina sake godia agareku, Ina fatan yanda muka hadu acikin wannan littafi Allah yasa muhadu a aljanna baki daya🤲🏻
Alhamdulillah duk shekara Ina rubuta novel guda biyu, wannan shekarar nayi BABBAN YAYA da SHAHAAB, Sai mun shiga wata shekarar Kuma in Allah ya Ara mana lokaci.

Littafi na Kuma na kudi ne 300 ne ba free bane,idan kika karanta baki biyaba nabarki ALLAH ban yafeba


0164549488
Amina muhammad
GTbank



My number
08033300034





Amnah El Yaqoub ✍🏻

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login