Showing 69001 words to 72000 words out of 115646 words
wuyan ta sunsha sarqa da zoben gold, kana ganin ta kasan daula ta zauna, cikin mamaki ta kalleshi Tace"A a, yana ganka anan Kai kadai?"
Cikin sauri ya sunkuyar da Kansa qasa, yadan shafa sumar Kansa yace"mama ai nagama shirya wane"
Murmushi tasaki, ta nemi waje ta zauna tace"tokoma kacire wannan kayan kasako manyan Kaya, haba Mahmud, wajan surukanka zakaje fa ba wajan Aisha ba"
Kansa yadan shafa, sannan yatashi yakoma part dinsu, itama dinning ta nufa tafara cin abinci,don bazata iya wannan azalzalar ta Shahaab ba, Dan idan tabiye masa taga alama abincin ma bazasuci ba.
Tare suka dawo shida Munirat, shadda yasaka fara tareda babbar riga, kayan sunyi Masa kyau sosai fiyeda qananun kayan, Wanda bai saniba tsaf zaiyi tunanin wani sabon angon ne, agogon hannunsa ya daura sannan yaja kujera ya zauna, munirat ma ta zauna tareda gaida mama, cikin kulawa mama tace "Barka munirat"
Abincin suke ci Hankali kwance, mama data gama tana shirin tashi ta kalleshi tace"jirgin karfe nawa zamubi?"
Cikin sauri ya Kalle ta, saida ya ajiye spoon din dayake shan tea sannan yace mata"jirgi bazai tashi ba yau, saboda yanayin hazo, saide mutafi a mota"
Kanta ta Jinjina tace"to ai saimu wuce ko?"
Tissue yadauka ya goge bakinsa, dama kawai yana tura abincin ne, Amma ya matsu sutafi, cikin sauri yace"toshikkenan muje"
Munirat tayi mamakin sa, tafiya zaiyi Amma ko fada mata baiyi ba, batasan meyasa tsakanin jiya zuwa yau, yake share taba, har zata tambayesu Ina zasuje, Sai taga mama ta kalleta tace"to Munirat zamuje jigawa, kinsan yanayin tafiya bamusan Yaya zata Kaya ba, saboda haka kimana addu'ah,idan daga Nan Kuma kinji anyi masa mata acan saiki shirya kar6ar abokiyar zama"
Cikin sauri Shahaab ya kalli mama, baiso ta fadawa munirat zancen auren ba, yasan tanada kishi dole zata daga hankalin ta, shiyasa yaso saiya dawo saiya sanar da'ita ta cikin ruwan Sanyi.
Dam! dam!! dam!!! Gaban munirat yayi wata irin faduwa, hannunta datake cin wainar qwai yad'auki karkarwa har batasan lokacin da fork din yafadi daga hannun taba,ta zubawa mama ido tana kallon ta, mama dataga yanayin munirat ya sauya tace"ikon Allah, menene abun rawar jiki daga maganar kishiya munirat? Dama yamiki alqawari zai zauna dake kadai ne? Banda abinki munirat yanda Shahaab yakeda kyau irin wannan ai kema kinsan dole yanmata zasu so shi,ballantana ma wannan yarinyar kin Riga kinsanta, Aisha ce, idan ya auro tama itade ba baquwa bace awajanki, dama gida daya kuke zaune shikkenan saiku dora daga inda kuka tsaya, may be Rabon muga qananun Yara agidan ne shiyasa Allah yakawo maganar auren, kema ai zakiso ganin yaran Shahaab suna kuka, suna fada, suna Rikici akan sweet..."
Jikin Shahaab yayi Sanyi, yasaki ajiyar zuciya, yaga alama idan bai katse maganar ta mama ba, Tofa bazata dainaba,Wai ahakan ma Dan batasan da case din filayenta da munirat din ta dauke taje ta siyar ba, dama suna yar tsama to idan tasan da batun filayen Allah ne kadai yasan inda rigimar tasu zata qare, ahankali yace"muje mama"
Yajuya ya kalli munirat, fuskarsa babu yabo babu fallasa yace"saimun dawo"
Munirat dai batasan cewa Shahaab yayi mata magana ba, tadaisan yayi magana Amma kwata kwata bata cikin nutsuwar dazata gane meyake fada, wani irin tashin Hankali ne ya wanzu a Saman fuskarta, baqin ciki ya tokare mata maqoshi, suna fita takifa kanta akan dinning table tasaki wani irin kuka maicin rai, dama ashe Aisha baquwar mama zai aura? Kenan ita ya mallakawa company? Ita Mahmud zaiyi wa haka? Dama tasan hakan zai iya faruwa, tunda har uwarsa ta riqe masa yarinyar ya matsa yaji ba'irin na matarsa bane ai dole ya rikice yabibiyi yarinyar. (🙈)
Kuka take me mutuqar cin rai, kwata kwata tunanin ta ya tsaya cak, tarasa Ina zata samu mafita, Amma abinda takeji acikin ranta Gani take dazata samu wuqa Toda tsaf zata Iya da6awa wannan tsohuwar(🙆🏻♀️)
Mota biyu sukayi, daya suna ciki ita dashi a zaune abaya, Sai driver dayake jansu, dayar Kuma securities ne aciki saboda tsaro.
Suna hanya yake turawa Ramadan text cewa suntafi jigawa shida mama, Sai tsiya Ramadan yake masa shikuma yana murmushi.
(nabarki da Allah keda kika karanta batareda kin biyaba)
******
Aisha ta kalli Hajja tace"Hajja meyake damunki ne Naga kinyi shiru, ko bakya jin dadi?"
Ajiyar zuciya tayi tace"inafa jin dadi mesunan qawa, gaba daya yau Jina nake jikina Sanyi kalau, tun asuba gabana yake faduwa, bansani ba ko mutuwa zanyi"
Cikin tashin hankali Ummah tace"Hajja Dan Allah Kidena wannan maganar, idan bakida lafiya tashi muje nakai ki chemist din Mubarak dogo"
Cikin sauri Aisha ta kalli Hajja tace" Ko wani abu kike so kici saina siyo miki?"
Ganin yanda duk suka daga hankalin su yasa tad'an kwantar da Hankalinta tace"lafiya ta kalau wallahi, kawai gaba nane yake faduwa"
Ummah tace"to kidinga addu'ah Hajja, insha Allah Sai alkhairi"
Kallan Aisha Hajjan tayi tace"mesunan qawa, dauki kudi aqasan fillo na kije bakin kasuwa ki siyo mana kaji, da nasan da zuwanki jiya Aida tun safe zanje insiyo miki, Amma tunda bansani ba kije yanzu ki siyo mana"
Cikin sauri Ummah tace"Hajja aiga kudin datazo dashi jiya, kusan dubu talatin dawani abu, ta d'auka aciki taje tasiyo"
Hajja tace"to jeki dauka ki siyo, kudin bironki da'aka siyar ma mamuda fili yasiya miki dashi,Sai Dan gyare-gyare da'aka yi mana a gidan, yace idan aurenki da inusa yatashi Sai asiyar ayi hidimar biki dashi "
Dan qaramin bakinta ta turo gaba ta juya tana Hararar Hajja, cikin lallashi Hajja tace"to uwar masifa, tashi kije Dan Allah, kibiya gidan qawar ki Walida saita rakaki, tunda batasan kinzo Garin ba, kisiyo harda kayan miya, da kaji guda uku, yau Walima zamuyi, jikata tadawo gida"
Cikin murmushi Ummah ta Kalle su, cikin ranta kuwa dadi takeji yanda Hajjan tasaki ranta tadena maganar mutuwa.
******
Sunci tafiya sosai a hanya, Sai yamma suka shigo jigawa, suna kokarin shiga garinsu Aisha mama ta hangi wani Tsoho yana tafiya akan Keke, itace ya'iyo abayan gari, daqyar yake tuqa keken da alama yajigata dayawa,cikin sauri tace"driver tsaya"
Shahaab ya kalleta da mamaki, glass din ta sauke qasa ta kalli wannan tsohon tace"bawan Allah cikin Garin zaka qarasa ne?"
Cikin sauri ya tsaya ya kalleta yace"hakane Hajiya,ciki zan shiga"
Tace"toshigo mota saimu qarasa dakai"
Tsohon ya kalli motar yaga mota Sai sheqi takeyi tana daukar ido, yaji tsoro karyaje Yan yankan kaine, cikin tsoro yace"a a Hajiya, nagode, Aina qaraso ma, nagode sosai"
Murmushi tayi, ta bude Jakarta tad'auki kudi Yan dubu dubu tabashi tace"to ungo wannan kasai itacen dayawa kadena zuwa da kanka"
Jiki na rawa tsohon ya kar6i kudin hannunsa Sai rawa suke, cikin jin dadi tace"nagode Hajiya, Allah yasaka da alkhairi, Allah yahadamu a aljanna mafificiya, ubangiji yabiya miki buqatunki na alkhairi, Allah Yacika miki burinki"
Cikin jin dadi mama tace"Amin ya Allah, kasan ni wacece?"
Tsohon yace"a a Hajiya saikin fada"
Tace"amma ai kasan Mahmud Wakili ko?"
Cikin sauri yace"ranki ya dade duk qasar nan waye zaice baisan Mahmud Wakili ba? Ko baka sanshi a'ido ba ai zaka sanshi a suna"
Murmushi tasake yi tace"toni mahaifiyarsa ce, sunana Aysha Yakubu Sagagi, qawar Aysha Sulaiman Bompai"
Cikin sauri tsohon ya tsugunna yana zuba mata addu'ah, mama tarufe glass din motar suka cigaba da tafiya, Shahaab ya kalleta yayi murmushi tareda Sosa girarsa guda daya, mama kuwa tunanin qawarta Aysha Sulaiman ne yafado mata, rayuwa kenan, yaude gata acikin jigawa Amma batada Hali ko hanyar dazata hadu da qawarta, lokaci daya jikinta yayi Sanyi, tana wannan tunanin batasan har sun qaraso kofar gidan su Aisha ba, Shahaab ya kalleta sannan yace "mama ga gidan Nan munzo"
Kallonsa tayi tace"mekake nufi? Futowa zakayi muje tare dakai kabawa iyayen ta haquri akan abubuwan dasuka faru abaya, Nima nabawa Aisha haquri akan abinda yafaru"
Cikin kunya Shahaab yafuto daga cikin motar, securities sukazo da sauri suna gyara masa babbar rigar jikinsa, aka budewa mama kofa itama tafuto, manyan motocin dasuka tsaya a qofar gidanne suka dauki hankalin Yan qauyen, Wanda suka sanshi Nan da Nan suka fara qus-qus suna nuna shi da hannu anaso a tabbatar Mahmud wakilin daya ta6a aiko musu kayan abinci ne, kokuma wani ne daban?
Wani yaro ne dayazo wucewa mama ta tare tace"shiga Nan gidan kace Ana sallama Dame gidan"
Yaron yajuya yashiga gidan, Sai gashi sun futo daga gidan shida Abba.
Abba yana ganin Shahaab sai mamaki ya wanzu a fuskarsa, cikin mamakin yace"sannunku da zuwa, kamar yalla6ai Mahmud nake Gani ko?"
Shahaab yayi murmushi tareda sunkuyar da Kansa qasa cikin kunya irinta surukai, cikin ransa yana mamakin mahaifin na Aisha ashe ma yaro ne kamar shi,Mama tayi murmushi ganin yanda Shahaab yake sunkuyar dakai tace"kaine mahaifin Aisha?"
Cikin sauri Abba yace"Eh nine Hajiya, sannunku da hanya, nace Allah yasa de ba wani laifin tayi muku tataho gida ba?, mu munata qoqarin zuwa har gida muyi godia akan abun alkhairin da yalla6ai yayi mana Kuma saina ganku kunzo?"
Mama tayi murmushi Tace"A a Aisha batayi laifin komai ba, mune ma mukai laifi mukazo bada haquri, Yaya sunan Kane?"
Cikin murmushi Abba yace"sunana Mamuda Hajiya"
Cikin farinciki mama tace"Mahmud de ko?"
Tanuna masa Shahaab da Kansa yake qasa tace"shima wannan danane, kamar yanda kasani Mahmud Wakili sunansa, Amma Ina kiransa da SHAHAAB..."
gaban Abba ya yanke yafadi, cikin sauri ya kalli Shahaab, cikin daburcewa Shahaab ya russina tareda Bawa Abba hannu yace"Barka da yammah"
Kan Abba gaba daya saiya kulle, dama Shahaab shine Mahmud Wakili? Wannan shi ake kira an yanka tatashi....,kenan shine yake zuwa wajan Aisha? Kuma shine yasake tura Aisha gidansa aiki? Shine yakaishi Umarah, yakai jabir qasar waje karatu?cikin son sake tabbatar wa Yace"Shahaab-shahaab de Danakeji awajan Aisha?"
Shahaab yayi shiru ganin lokaci daya surukin nasa ya d'agoshi, Dan haka yayi saurin yin qasa da Kansa yana 'Dan Sosa qeyarsa.
Mama tayi murmushi tace"shide,idan babu damuwa ka bamu wajan zama Dan maganganu muke tafe dasu dayawa"
Cikin sauri jikin Abba yad'auki rawa, Wai yau Mahmud Wakili ne da Kansa a kofar gidansa, Mahmud Wakili ne yake zuwa wajan 'yarsa,cikeda mamaki yace"a a, to hajiya ku qaraso ciki mana, ku shigo daga ciki kawai..."
Mama Tace"toshikkenan Takwaran Mahmud mushiga"
Abba yajuya cikin gidan da sauri, mama da Shahaab suka doru abayansa.
Hajja tana sunkuye tana gyara hadaddan kunun ayar data zuba acikin fridge, Aisha tana zaune da abinci agabanta tanaci kamar bataso, Ummah tana Gefe da pure water ahannunta tanasha,saiji sukai Abba yana cewa "kushigo Hajiya, ku qaraso, sannunku da zuwa"
Shahaab yana daga Kansa Idonsa ya sauka akan Aisha, tana hada ido dashi gabanta yayanke yafadi, ta tsaya cak tadena cin abincin, yayinda gaban mama ya yanke yafadi ganin fuskar da bazata ta6a mantawa da'itaba a tarihin rayuwar ta,lokaci daya handbag din data riqe a hannun ta tafadi qasa, qaran faduwar jakar ne yasa Hajja tarufe fridge din ta d'ago kanta, gabanta ne yafadi, hannunta yana karkarwa tafara nuna mama,cikin rawar murya tace"Aysha Yakubu?"
Jin sunan data kirane yasa gaba d'ayansu suka maida kallon su ga Hajiya Mama.
Masha Allah, mutara zuwa gobe🙏
Littafin kudi ne, nera 300 kibiya ki karanta kada ki karanta abun Allah ya'isa
0164549488
Amina muhammad
GTbank
Kokuma katin MTN
Shedar biya ta wannan number 08033300034
Mutara zuwa gobe🙏🏻
Mrs Usman ce✍🏻
Page 24
Wani Irin hawaye ne yazubo daga idon mama,cikin rawar murya tace"Aysha Sulaiman? Aysha kenake Gani haka kokuma idonane?Dan Allah kifadamin kode irin mafarkan danake yi ne?"
ta qarasa maganar hawaye na gudu daga idanuwanta.
Ahankali Hajja tatako tazo gaban mama, tace"nice Aysha"
Cikin sauri mama ta rungume ta,kuka Hajja tasaki mecin rai, mama kuka, Hajja kuka, cikin kukan Hajja tace"Aysha, ashe da Rabon zan sake ganinki a doron duniya?"
Cikin sauri tasaki mama ta daga hannunta sama tace"ya Allah nagode Maka, Allah Ina qara yima Godiya bisa nunamin qawata dakayi wadda na Dade Ina nema tsawon shekaru masu yawa"
Hajiya Mama ma Hawayen ta share, itama ta daga hannunta kamar de yanda Hajja tayi tace"ubangiji na gode Maka, yau Naga Aysha Sulaiman bompai,Babban burinmu guda daya Yacika, saura Kuma d'ayan, Allah nagode maka"
Cikin sauri Ummah ta goge qwallar idonta, itade batasan wannan baqi ba, Amma duk da babu bayani tariga tasan cewa wannan matar itace qawar Hajja, yaude ga qawar Hajja tazo har gida, ikon Allah kenan, kullum labari-labari yau gashi Allah yahadasu.
Aisha kuwa gabanta ne yafadi, duk wannan dramar dasuke idonta yana kan mama, Tun lokacin da Hajja tace
Aysha Yakubu, daga Nan wani irin shock yakamata, yanzu dama Hajiya Mama itace qawar Hajja?.
Shikuwa Shahaab wata irin wawuyar ajiyar zuciya yasauke Mai karfi,domin kuwa abinda ya lura dashi shine Abban Aisha bashida qanwa mace bare Mama tace dole saiya aure ta Yacika mata burinta, dama abinda yake gudu kenan, mama tadage muddin taga Aysha Sulaiman Tofa Sai sun hada yayansu aure, Kuma Alhamdulillah shi bai taba jin Aisha tace abban ta yanada qanwa ba bare abashi, Gara de ita Aishan, ahakan ma tunda gashinan Allah ya hadashi da Aishan cikin hikimar sa ai shikkenan Shima de dan'uwan burin maman ne, tunda jikar qawarta ce.
Abba kuwa ajiyar zuciya yasaki ahankali, cikin sauri ya goge qwallar Idonsa,sannan yayi gyaran murya yace"Alhamdulillah....,Hajja kuyi hakuri kudena kukan Nan haka, ku qaraso ku zauna"
Yajuya ya kalli Aisha da abincinta ke gabanta ta gagara ci, cikin fada yace"ke tashi ki Dauko babbar tabarmar Nan ki shimfida mana, kinfi awa daya kina cin wannan abincin, ga baqi sunzo ko abun zama baki shimfida musu ba"
Cikin sauri Shahaab yayi qasa da Kansa tareda Sosa qeyarsa
Ummah ta kalli Aisha Tace"Ai inta fara dora abinci a harshe saikace basarakiya, na hanata irin wannan cin abincin taqi ji "
Cikin sauri tatashi ta wuce Dakin Ummah tad'auko babbar tabarmar ta shimfida musu.
Ummah ta kalli su Hajja tace"ku qaraso ku zauna"
Tajuya ta kalli Shahaab da batasan waye shi dinba, ita de taga Sai sunkuyar dakai yake yaqi kallon idon kowa, tace"bawan Allah qaraso mana"
Cikin sauri Shima Abba yace"bissmillah yalla6ai"
Yanda yace yalla6ai dinnan Sai abun yayiwa Shahaab nauyi, ahankali yace"to nagode"
Suka qaraso suka zazzauna a tabarma,Aisha tana daga Gefe, duk jinta take a takure, saboda yanda Shahaab yazuba mata mayun Idonsa, ko tsoron su Ummah su kamashi yana kallon ta ba yayi, duk motsin datayi akan Idonsa.
Hajja ta kalli mama, sannan ta nuna Aisha da hannu tace"kinganta Nan,? Babu abinda tabari naki,masifa,rashin kunya, yanga saikace yar wani, wannan cin abinci dakike a makaranta haka itama takeyinsa kamar kin zauna da'ita kin Koya mata yanda kike yi, lokacin da aka haife ta uban yadage sunana zai saka, nikuma nace a a, munyi alkawarin zamu sakawa Yayanmu Aisha, idan Kuma maza muka haifawa to zamu saka musu suna Mahmud, to Alhamdulillah, Dana guda daya ne a duniya gashinan mamuda, ban haifi mace ba bare nasaka mata sunanki, shiyasa Ana haifar ta daya ce sunana zaisaka nadage nace a a, saide yasaka sunanki, to daqyar de mamuda ya yarda, saboda kallon ta6a66iya sukemim Alokacin, tayaya qawar daban masan inda take ba, bansan a'ina zan ganta ba, zan dage ince sunanta zan saka? To dayake de sunan naki duk irin nawa ne, shine yasa mamuda yasaka mata sunanki,idan masifar ta tatashi fada mukeyi akan wannan suna Nata, fada takeyi tana min sababi kawai natashi nasa mata sunan qawata qilama ta mutu, ban'isa ince tanada masifa ba saitacemin ai nice nace asaka mata sunan qawata, danhaka halin qawata ta Dauko..."
Cikin sauri Aisha ta sunkuyar da idonta qasa, wannan tonon silili na Hajja har Ina? Da alama batasan waye wannan yake tareda mama ba, da tasan shine Shahaab dabata mata wannan tonon asirin ba.
Ahankali kuwa ya kalli Hajja yace"nima haka tamin Hajja, ranar Dana kawo muku abinci da Azumi rashin kunya ta dinga zubamin, saura kadan ma ta dungure min kai na...."yaqarasa maganar cikin sigar tsokana.
Aisha ta d'ago ta daka masa harara da fareren idonta tareda murguda masa d'an qaramin bakinta,yana ganin abinda tamasa yafaki idonsu Hajja ya motsa fatar bakinsa yasakar mata kiss ahankali,karaf akan idon Abba (🤭🙆🏻♀️🙈)
Aisha kuwa tana ganin abinda yayi tayi sauri ta sunkuyar da idonta, Abba kuwa cikin sauri ya kawar da Idonsa yayi murmushi cikin ransa yace"dole yarinya tadinga bijiremin tadage lalle Sai Kai"
Ummah da mamaki yagama kamata ta kalli Shahaab tace"wanne irin abinci kake magana bawan Allah?"
Abba ya kalli Ummah da Hajja yace"wannan fa Mahmud Wakili ne, Wanda yaturo da Azumi akayi Rabon abinci agarin Nan?"
Hajja ta kalli mama tanuna Shahaab tace"wannan shine Mahmud dinki?"
Cikin sauri mama ta daga Kai tace"shine Aysha, shi kadai nahaifa, inde kinji Ana cewa Mahmud Wakili to Mahmud dinane, ashe de alqawarin mu nasaka sunaye ya tabbata, Rabon abinci Kuma babu Wanda yaturo, shida Kansa yazo, a lokacin nariga na fidda rai da ganin Aysha Sulaiman, sainayi masa magana akan yazo jihar Jigawa yagina gidan marayu, ko Allah zaisa watan watarana Yaya, kokuma jikokin Aysha zasu kasance a gidan, ta wannan hanyar ne zan iya taimakonta saboda bansan inda zan ganta ba, Nasaka anyi cigiyar duk a banza,Bayan yazo sunyi maganar aikin shida Gwamnatin Jihar, saiya raba kayan abinci, to kunji dalilin zuwansa Nan Garin, dama shine Wanda nake dashi Wanda zai tsayamin akan nemanki, toshi tunda yaji nace masa muddin naganki Sai na aura masa yarki, Tofa shikkenan yayi biris da maganar neman naki, saboda bayason nabashi wadda bayaso, yad'auki son duniya yad'ora wa matarsa, shi Dan boko, ba zaiyi wa matarsa kishiya ba, Amma dayake Allah yaso kamashi, saiya saka masa son Aisha, soyaiya ta kamashi dumu-dumu, Idonsa yarufe,ya manta da batun Qin qarin aure,Sai gashi da Kansa yazo min da maganar inzo in nema masa auren Aisha, inkikaga yanda yake son Aisha saikiyi mamaki, harfa company yabata, Alokacin da akayi kyautar na tambayi abokinsa wacece Aisha? Nasan tare suke qulla komai, Amma Shima saiya 6oyemin, akace mama ai jinake dake yake, waini za'a yiwa wayo, Amma da aka 6oyemin din Sai gashi de anzo wajena inzo neman aure, to Dama mun samu Sa6ani da takwarar tawa, sainace zanzo inbata haquri, ashe ni Allah ne yayi zan hadu dake...."
Tajuya ta kalli Shahaab tace"idan baka auri yar qawata ba ai gashinan zaka auri jikar qawata"
Cikin sauri Hajja tace"kamfani fa kikace Aysha?shiyasa da yarinyar Nan tadawo tazo da kudi ajakarta tace mana Wai me gidan ne yabata naji tsoro, saboda kar ace daga zuwa aiki yarinya ta qwacewa matar gida Miji, saide Kuma bakisan wani abu ba, ai ita takwarar Taki akwai Wanda takeso, tad'auki son duniya ta dorawa wannan jarababban yaro(😳)
Uban Nata har dukanta yayi akansa, saboda Dafarko akwai Wanda mukeso mubata inusa, yarinyar Nan tunda tahadu da wannan saurayi ta bijire tace lalle saishi, ita batason inusa, to yanzu ma idan muka bata Mahmud din naki muna Nan dake wannan Yaron zai dawo