Showing 3001 words to 6000 words out of 115646 words

Chapter 2 - Shahaab Complete Hausa Novel

12 Oct 2024

9576

cikin office din Adede lokacin ne yake cewa "duk kayaiyayin mu dasuke kasuwa asake saukar musu da farashi yanda talakawa zasu iya siya, banaso sukai lokacin azumi" yana gama fadar haka yasaka Dan yatsansa ya danna agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa touch, Nan da Nan wayar ta katse

Wasu file yaduba, ko ten minutes baiyi ba, yad'auki wata takarda, yatashi yasaka suite dinsa,I'd card dinsa ya saqala agaban suite din nasa setin qirjinsa,anrubuta MAHMUD WAKILI, EFCC CHIRMAN.

Kai tsaye d'akin da zasuyi taro yanufa, dogon daki ne Wanda yaji kujeru masu mutuwar kyau tareda dogon table, an ajiyewa kowa gorar ruwa a gabansa, fuskar kowa d'aukeda face maks, office din yayi kyau sosai, gaba dayansu maza ne, Sai mata guda biyu, suna ganin shigowarsa cikeda ladabi suka miqe tsaye, saida ya zauna akan kujerar sa wadda take d'aukeda tambarin hukumar, dakuma manyan rubutu Wanda aka rubuta EFCC ajiki, sannan kowa ya zauna.

daga Bayan kujerar daya zauna sojoji ne guda biyu sun qame waje daya, Sai babbar tutar tambarin hukumar EFCC, dakuma wata babbar tuta ta qasar Nigeria, daga can sama Kuma Babban photonsa ne yayi kyau cikin suit yana murmushi, dakuma wani photon daban na shugaban qasa.


Basu bata lokaci ba suka fara tattaunawa akan abunda ya tarasu, zasu fitar da wani salon na yaqi dacin hanci da rashawa a Nigeria.

Saikuma maganar sunayen wadanda hukumar ta d'auka,a matsayin Wanda zasu bawa horo, zasu fitar da sunayen su zuwa wani watan ta manhajar hukumar, dakuma kafafen yad'a labarai.

Basu dauki lokaci Mai tsawoba suka tashi daga meeting din, daga Nan office dinsa yakoma yafara ganin mutane kowa da irin maganar dayake zuwa da'ita

Sai yamma yayi shirin tafiya gida, yana futowa kuwa mutanan nasa suka take masa baya har zuwa mota, mutum dayane yabude masa mota yashiga, Alokacin har anfara yayyafi kasancewar kudancin qasar sunfi arewacin Nigeria saurin samun ruwan sama, yana shiga motar ya Lumshe Idonsa, ga qamshin ruwan sama me dadi yana busowa cikin motar, yagaji sosai, zaiso ace yasamu anyi masa massage Ayanzu (🤭)
Tafiya Mai Nisa sukayi, kafin su qarasa gida, Alokacin har ruwan yafara qarfi, sojoji ne awajan gidan, dakuma daidai kun Yan sanda, get man nabude musu get, driver ya danna hancin motar zuwa cikin gidan, gida ne babba gari guda, ba zakayi tunanin ma acikin qasar Nan gidan yake ba, acikin harabar gidan ma sojoji ne suke shawagi, motarsa tana tsayawa daga me gadi har sojojin wajansa suka nufa kowa yanayi masa sannu da zuwa, hannunsa yadaga musu kawai,kasancewar Ana Dan ruwa yasa yayi sauri Kai tsaye yawuce part din MAMA.

Yana shigowa falon yafara cire jacket dinsa, tareda necktie din wuyansa, duk da girman falon Nata, wani kafet ne Mai masifar laushi yake malale a falon, ga wata katuwar plasma tana aiki, daga fentin falon har kujerun da labulaye duka milk colour ne, wata tsohuwa ce mai kimanin shekaru sittin da shida a zaune, saikuma wata yarinya a tsugunne a gabanta, tana matsa mata qafafu

Cikin fad'a-fad'a tadubi yarinyar "ke! Kidena matsa min qafa da qarfi mana kamar kinsamu wani dutsi, nagaji dayin complain a kanki, Nan gaba kad'an zan'iya sallamar ki idan baki gyara halinki ba"

Cikin ladabi tace "kiyi hakuri Hajiya"

Cikin muryarsa Mai cikeda miskilanci yace "mama"

Kallan sa tayi tace "SHAHAAB kadawo?"

Bai bata amsa ba saida ya zauna yana fadin "wash! Allah na mama nagaji"

Yarinyar datake matsawa wadda aka kira da mama qafafu, cikin tsantsar ladabi kanta asunkuye, batare data hada ido dashi ba tace "yalla6ai barka da dawowa"

Bece da'ita uffan ba, Sai mama ce data watsa mata wani irin kallo tace "saiki tashi kije, zan gana da Dana"

Cikin sauri yarinyar tatashi tabar wajan har qafafunta na hardewa

Kallan sa tayi tace "Shahaab ya aikin? Kadawo lafiya?"

Kafin yabata amsa agogon hannunsa ya nuna alamun Ana kiransa, ta6a agogon yayi ya amsa Kiran dake shigowa, daga dayan bangaren muryar wani mutum ne yake tashi "ranka yadade kanada baqi daga bayelsa"

Dafe Kansa yayi, kwata kwata ya manta da Zuwansu, ahankali ya kalli mama, shide yasan be'isa yasake fita yanzu ba, cikin muryarsa Mai dadi yace "kafada musu muhadu dasu gobe misalin karfe goma nasafe" daga Nan yakashe wayar, ya maida dubansa zuwaga mama

Hankalin tane taji ya kwanta Bayan taji bazai sake fitaba, taqi jinin ta ganshi nesa da'ita

Tafison kullum ta kasance tareda dannata qwaya daya tal a duniya, batason yawan rashin zamansa agida ko kad'an, cikin kulawa yace "waye yata6aki mama? Keda waye?"

Ajiyar zuciya ta sauke tace "ai kasan damuwa ta, rashin dawowarka ne gida dawuri, saikuma batun qawata Aysha Sulaiman bompai, dakamin alqwari zaka nemomin ita"

Kansa ya sunkuyar qasa, wannan qawa ta mama! Wannan qawa ta mama!! Da yanada halin dazai mantar da'ita wannan qawar Tata datuni yayi, saboda babu Wanda yasani tana Raye har yanzu kokuma ta mutu, ahankali ya d'ago Kansa ya kalleta, yakama hannayenta yariqe yace "za'a duba agani"

Shiru mama tayi tana Kallan sa, tarasa meyasa Shahab baison maganar qawarta, tun lokacin data fada masa inde taga qawarta Aysha to zata hadashi aure da 'yarta idan mace ta Haifa, tun daga lokacin yaqi jinin tayi masa maganar qawar Tata, saboda bashida ra'ayin yin wani aure yanzu, idan ba bayason Nemo mata qawar Tata ba yaushe zata yi masa maganar amma yace Wai za'a duba, hakan yana nufin Bama shine zai dubaba kenan, ko meyasa yake gudun yin wani auren? Kokuma baida cikakkiyar lafiya irinta maza oho masa, rashin haihuwar sa yana damunta, ga Kuma rashin qawarta wadda take Fata, take Kuma burin tahadu da'ita kafin Takoma ga mahaliccinta, wadannan burikan Nata guda biyu su take Fata su kasance, yau ace taga jinin Shahaab, sannan Kuma taga qawarta Aysha Sulaiman

Ajiyar zuciya ta sauke tace "Yaya labarin Munirat? Har yanzu haihuwa shiru babu ciki bare ayi tunanin labarin haihuwa ko?"

"Ana Addu'ah de"

Shine abinda yafada mata

Kallan sa tayi dakyau Kai tsaye tace "inaso kafin namutu, Inga qawata Aysha, sannan Kuma Inga yayanka, Qawata Aysha de Ina Nan Ina nemanta, Kuma nasan insha Allah watarana zan ganta, Amma Kai haihuwa bakada tabbas,matarka ba haihuwa zatayi ba, yakamata kayiwa kanka fada, saboda haka yaushe zaka sake aure? "

Gabansa ne yafadi,cikin sauri ya d'ago Kansa ya kalleta, Dan qaramin bakinsa ya bude kamar Mai shirin cewa wani abu, Amma Kuma yakasa magana, ganin yazuba mata ido yana Kallan ta yasa taci gaba da fadin "yakamata kabi shawara ta, ka 6oye kanka kanemi aure, kafuto a matsayin SHAHAAB kanemi aure da soyaiyar tsakani da Allah bata kudi ba, muddin kace zakaje wajan yanmata a matsayin MAHMUD WAKILI,to bazaka ta6a samun soyaiyar gaskiya ba"

Tamkar Wanda zai Fashe da Kuka yace "mama itama Munirat din tana sona, nida ita ai sai Allah mama"

Batace dashi komai ba saboda taqaici kawai wayarta ta d'auka dake Gefe, tawuce dakinta tabarshi anan, hakan yana nufin shiru ma amsa ce game Hankali.

Yana ganin shigewarta daki yaji kamar ya kurma ihu kozaiji dadi, tayaya mama zatace yayi aure Bayan irin dunbin soyaiyar Da Munirat take nuna masa?

Jikinsa a sanyaye yamiqe yanufi part dinsu, duk ruwan dayake sauka akansa ko kad'an baya jinsa, yasan cewa idan yabi Bayan mama ma to bazata saurare Shiba, yana zuwa falon ya hangota gaban TV da remote a hannunta, Riga da siket ne ajikinta dinkin ya zauna Das ajikinta,munirat chocolate beauty ce, Amma hutu, dakuma jin dadin datake samu, da shafa mayuka masu mutuqar tsada yasa gaba daya bazaka ce mata chocolate ba, fatarta tayi wani irin luwai luwai kamar ka latsa jini yafuto, mace ce har mace, Mai aji dakuma wadatar ilmin boko,Daurin ture kaga tsiya tayi, hakan yabawa gashin dokin data saka damar futowa sosai Kai kace halalinta ne, falon bashida wani tarkace, kujerun falon Kala biyu ne, akwai yellow, dakuma ash colour, Sai aka hadasu akayiwa falon qawanya dasu

Tsayawa yayi yana qare mata kallo, haqiqa yana qaunar munirat, Kuma itama ya tabbatar tana mutuqar sonsa, babu abinda ta rageshi dashi, sannan tana mutuqar qoqarinta wajan ganin ta kyautata wa mama, Amma mama bata Gani

Jin alamun kamar Ana kallon ta ne yasa tajuya, tana ganinsa tatafi dawani irin taku me daukar hankali, ta qarasa wajan sa
"barka da zuwa my Dear"

Cikin damuwa ya Lumshe Idonsa ya bude, alamun amsawa, murdaddan dantsan hannunsa ta kama tace "muje kayi wanka, meyake damunka ne Naga kamar kana cikin damuwa, gashi katsaya ruwa ya ta6amin kai"

Ta qarasa maganar tana janshi ciki, ahankali ya janye jikinsa yace "kije kiyi kallonki, yaude na hutar dake, idan nagama zan futo"

Murmushi tasaki, ta rungume shi tasakar masa kiss a kumatu, sannan tasake shi tajuya, saqon Nata yashige shi sosai, har saida hakan yasa shi Lumshe Idonsa, batare daya shirya ba

Washegari da safe bai tashi dawuri ba, sakamakon gajiyar da yayi cikin dare,tun kafin yatashi daga baccin munirat ta silale tatafi part din mama,yau tana so tayi wa mijin ta girki Wanda zaisa yaji dadi sosai kamar yanda yajiyar da'ita dadi adaren yau, ma'aikatan part din ta had'a gaba d'ayansu tasakasu su girka mata irin abunda takeso, cikin qanqanin lokaci suka kammala komai suka jereshi a Babban dinning din na mama, Wanda aqalla zai dauki mutane samada mutum takwas

Har zuwa lokacin Hajiya Mama Ana daki bata futo ba, munirat kuwa zama tayi akan kujera ta sallami masu aikin, wayarta ta d'auka tana chatting da qawayenta, dayawansu tallar magungunan mata suke mata, Wanda ita kanta batasan Dame aka hadasu ba

"menake Gani haka?!!!"

Mama data futo daga daki tafada, Bayan taga abinda aka ajiye a dinning, ta qarasa maganar idonta nakan munirat, fuskarta kuwa shimfide take da 6acin rai

Cikin sauri munirat ta kalleta, gabanta yafadi, da sauri ta sakko daga kan kujerarar ta tsugunna har wayar hannunta na faduwa, cikin ladabi da rawar murya tace "Barka da futowa mama, Ina kwana?"

"daban kwana ba kya ganni? Munirat yaushe Ina cikin gidannan har Zaki shigo min part dina kina bada umarni? Kinyi hauka ne?"

Adede lokacin yashigo part din, yashirya cikin suit kamar kowacce rana

Munirat da idonta yakawo ruwa, qwalla tataru tacika idon, ta girgiza kanta batare da tayi magana ba

Nunata mama tayi da d'an yatsa, tace"maza maza tashi kije tas ki cinye abinda kikasa aka girka, tun kafin ranki Dana iyayenki ya6aci.... "

Cikin sauri ya qaraso falon, cikin ladabi yace"mama kiyi hakuri Dan Allah"

Kallan sa tayi tace "Alhamdulillah... Gara da Allah yakawo ka"

Ta nuna masa munirat da hawaye ya wanke mata fuska tace "tun kafin namutu matarka ce mebada umarni...., to gatanan kasaketa"

Jiyayi kamar mama ta doka masa guduma a qirjinsa, munirat kuwa tanajin wannan furucin, tafice daga falon da gudu tana kuka.


LABARINSU:

Hajiya Mama, sunanta Aysha Yakubu Sagagi, tun Bayan rabuwar su da qawarta Aysha Sulaiman bompai Sai iyayenta suka rasu, daga Nan mijinta ya dauke ta suka tafi Nijar wajan dangin sa, sun dade acan yana kasuwancin sa, daga Nan suka sake dawowa Nigeria, ahankali ahankali har Allah yasa Arziqinsa yasake ha6aka, Bai Barta tayi maraicin iyayenta ba, janta yayi ajiki, ya dinga Koya mata harkokin kasuwancin sa, ahankali harta gane komai, lokaci zuwa lokaci yana tura ta wasu qasashen sarin kayaiyaki, har Allah yasa Shima yabude kamfanoni dadama, anan Nigeria da Kuma Nijar inda danginsa suke

Lokaci daya, sunansa yafuto acikin jerin sunayen masu kudin qasar Dama Africa baki daya, akwai wata Rana daya shirya zaije yataho da danginsa na Nijar, su dawo Abuja da zama gaba daya, yaje yataho dasu a hanyar su ta dawowa jirginsu yayi hatsari suka mutu gaba dayansu.

Mama tayi kuka tayi kuka kamar ranta zai fita, har kwantar da ita akayi a Asbiti, anan ne aka Gano tana d'aukeda ciki na wata uku, haka taci gaba da Kula da cikinta,tasamu mutane amintattu suka tayata kula da dukiyar mijin Nata,kamfanin sa dasuke Nijar tasa akai gwanjon su,Alokacin da cikinta yakusa haihuwa saita shirya tatafi Saudia,acan ta haifi danta namiji kyakykyawa Mai Kama da mahaifinsa sak, ranar suna taso sakawa Yaron sunan mahaifinsa, to Amma data tuna alqawarinsu itada qawarta Aysha Sulaiman bompai, saita sakawa Yaron suna MAHMUD, mutane suke kiransa da MAHMUD WAKILI, ita kadaice bata fadar sunansa, saboda Dan fari ne, Sai take masa alkunya take kiransa da SHAHAAB.

A India yayi degree dinsa na farko, ya karanci bangaren medicine

Haka mama ta hanashi aikin asbiti duk da yanaso, ta dorashi akan harkokin mahaifinsa, kasancewar yanada hazaqa hakan yasa Nan da Nan yasan kan harkar, dukiyar Kuma tasake ha6aka,daga baya Kuma yatafi malesia yayi karatu akan harkar kasuwanci, hakanne yasake bashi damar gogewa akan harkar kasuwancin nasu,sannan ya dawo Nigeria yayi wani karatun afannin economic, daga Nan yafara aiki da hukumar efcc, yafara da matakin karamin ma'aikaci, har Allah yasa sukaga kokarin sa akan aiki dakuma jajir cewarsa,shugaban qasa ya nad'ashi shugaban hukumar, baya had'a kasuwancin su da aikinsa, aikinsa daban, harkar kula da dukiyar da mahaifinsa yabar masa Shima dabam, Kuma yana kula da hakan yana taka tsantsan akan duk wani abu dazai hada aikinsa dakuma kasuwancin sa, yana samun wannan matsayi yahadu da munirat, tanada samarinta sosai, Wanda suka sota tun tana qarama, suka Sha wahala Akanta, suka hidimta mata, Amma tana ganin Shahaab yafuto a matsayin jerin masu neman aurenta saita liqe masa, harma soyaiyar datake masa ta danne tashi soyaiyar, ta Kuma zabeshi a matsayin Wanda zata aura, acewarta yafi sauran samarin Nata nagarta.

Mama bataso yanemi yarinyar ba,taso ace yasamu yarinya da batasan waye Shiba, batasan kudinsa ba, itace zatayi masa soyaiyar gaskiya, Amma tana ganin idon munirat tasan cewa idon yarinyar abude yake akan son kudi, ta fahimtar dashi Amma soyaiyar munirat din data Gani acikin Idonsa yasa tarabu dashi ya aureta, abokan mahaifinsa suka shige masa gaba, Nan da Nan aka bashi ita, kasancewar sa Babban mutum Kuma sananne a qasar.

shekarar su Tara kenan da aure, haka Kuma a tarihin aikin nasu shine matashi na farko daya dade a matsayin shugaban hukumar, ba'a dade da dorashi ba ya auri munirat,a dadin shekarun sa a matsayin shugaba, a dadin shekarun aurensa, gaba daya shekarun sa 39, yayi aure yanada shekara talatin a duniya, Amma babu Wanda zaice yayi wannan shekarun kasancewar yanda yake motsa jiki, yake Kuma kula da jikin nasa, yasan cewa da yana candy yayi aure to tabbas da yanzu yarinyar sa kokuma yaronsa zaikai shekara Ashirin kokuma shatara,to Amma gashi har yanzu shiru babu haihuwa, Kuma yaga munirat abun baya damunta, shikuma yanason yaga yanada yaronda zai gajeshi koda ace baya Raye, kamar yanda Shima yagaji mahaifinsa.
Shahaab bai iya soyaiya ba, idan yanason mutum Tofa yana sonsa, da gaske yake saka mutum acikin zuciyar sa, shiyasa munirat tayi Kane Kane acikin tasa zuciyar, yanason mace Mai gashi, asali ma shine abinda yagani awajan munirat haryaja ra'ayin sa akanta, Bayan sunyi aure yagane gashin dokine take sakawa, maimakon ya hanata saiya qyale ta taci gaba da sakawa saboda Shima yanaso.


Bangaren munirat Kam Bahaka bane, rashin haihuwarsu baya damunta, kullum qawaye take biyewa suna kawo mata magungunan mata Kala Kala, dayawa daga cikin su batasan Dame aka hada akayi suba, kudi Kuma duk lokacin data so samu tana samu awajan mijinta, wani lokacin saita tsokano masa sha'awar sa cikin kissa zata Fashe da Kuka, yana tambaya abinda take wa kuka zata fada masa kudi takeso Kuma gashi account dinta yayi qasa, shikuma jinsa cikin wannan yanayin yasa zai bata kudade, Sannna ne zata bashi hadin Kai su Raya Sunnah yanda ya kamata

Shahaab yana yiwa mama biyaiya, tun tasowarsa yana qarami ita yake Gani, itace take masa komai,baisan mahaifinsa ba, mama itace komai nasa, tana sadaukar da Nata farincikin akan nasa, yana kiyaye duk wani abu dazai sata 6acin rai, yasan cewa Sarai batason munirat, akwai lokacin daya tambayeta meyasa batason munirat Kai tsaye tafuto tafada masa cewa matarsa kudinsa tagani shiyasa ta aure shi, sannan akwai alqawarin dasukai itada qawarta cewa zasu hada yayansu aure, Kuma yasani muddin Aysha ta bayyana Tofa saiya auri yarta inde mace ta Haifa, idan Kuma ba mace ta Haifa ba shikkenan.

Tun daga lokacin idan tasashi yayi wani kokari akai Dan agano qawarta, Sai yayi mursisi da batun, saboda bayason maganar hadin auren Nan datake yi kokadan.

Akwai lokacin data dameshi akan maganar, Amma Shahaab yaqi yayi mata binciken, tayi zuciya tafice tabar gidan a hanya kidnappers suka saceta (😂)

Saida yasha wahala kasancewar sa sannane yasa hukumar tsaro ta qasar tabashi hadin Kai har saida aka kamota daga hannunsu, tundaga lokacin ya zubawa gidansa tsaro, sojoji ne suke gadin mama, banda Yan sanda dasuke Gefe suma suna nasu aikin.

To dayaga de mama da gaske take, shine yabada sanarwa a kafafen sadarwa dakuma yanar gizo, ganin yanzu harkar yanar gizo kowa yanayin ta, shiyasa yayi tunanin za'a iya samun labarin qawar ta mama, abinda bai saniba shine Hajja A'i Kam vivo gareta itama screen din duk ya Fashe, wannan gidan ta abincin dazasuci sukeyi, bata yanar gizo ba(â˜šī¸)

To ganin haka yasa hankalin mama ya kwanta, Amma idan ta tuna qawarta, ranar haukace masa take, tun yana bata haquri harya dawo Shima yazama kamar ta, ya dinga zigata, to saita sauko su zauna lafiya.

Tsawon wannan shekarun munirat ko 6atan wata bata taba yiba, data fahimci hankalin mama dakuma shi Kansa Shahaab din yana kan haihuwa, saita shiga damuwa, akan yanda suke nuna son haihuwar, danhaka Sai take jinyar qarya, dasu amai, mama da Shahaab hankalin su yatashi, suce taje Asbiti taga likita ko ciki ne, saita kar6i maqudan kudade awajansa daga baya Sai tace ai ba ciki bane, tayi haka yakai sau uku, mama kuwa tariga tagane kawai kudin yarinyar takeso, bawai Shahaab din ne da haihuwar suka Dame taba

Tarasa Yaya zatayi, aure tsawon shekara Tara babu ciki, but ita hakan bai dameta ba saboda tana cikin daula, ko neman magani batayi, shikuma duk lokacin daya shirya yatafi Saudia Tofa addu'arsa daya ce akan Allah yabashi haihuwa, ita kuwa mama burinta guda biyu ne, nafarko taga qawarta, na biyu Kuma taga Shahaab ya haihu.

Duk juma'ah Ana bada abincin sadaka a gidan, kunu, abinci, dakuma bread tareda nera Dari biyar, wannan Kuma aikin mama ne, tana bada sadakar ne saboda Allah yakaiwa mijinta dakuma ahlinsa ladan.
Ta bangaren Shahaab kuwa lokaci zuwa lokaci yana yin tasa sadakar, Amma yafiyi lokacin zuwan azumi, yana sauke farashin kayan da kamfanonin sa suke sarrafawa domin talakawa su iya siya.

Back to story 👌đŸģ

******

Jigawa

Aisha ce take sallah, Hajja na gefenta tana Jan carbi, ta kalleta tace "mesunan qawa

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login