Showing 57001 words to 60000 words out of 115646 words
kanta yana qasa tace "mama jinake Zaki qarasa da kanki"
Cikin sauri mama Tace"A a zauna kibani,saida kika sangarta ni dabani abinci sannan Zaki gudu? Wannan dakike Gani ba Bani zaiyi ba saide ma yafara min shagwa6a nabashi"
Ta qarasa maganar tana nuna mata Shahaab, batayi gigin kallon inda yake ba tace"yalla6ai Ina wuni"
Wani iri yaji, yalla6ai? Me yarinyar Nan take nufi? Jin yayi shiru yasa Mama ta kalleshi tace"narasa meyasa idan Aisha ta gaishe ka bakason amsawa, Karage qiyaiyarka ga mata mana"
Murmushi yayi cikin shagwa6a yace"mamaaah..."sannna yad'ora Kansa a cinyar ta, yazagayo da hannunsa ta hips dinta, ahankali Aisha ta zauna, tana zama taji ya mintsineta Adede kan hips dinta, kallon sa tayi taga Idonsa a Lumshe kamar bashi ba, mama ta kalleshi tace"baka rabo da fitina Mahmud,mekakeso yanzu?"
Wani irin taqaici ne yakama Aisha, tad'an kalli mama taga Sai wani riritashi take kamar wani jariri, tunanin tane ya tsaya lokacin dataji yana shafa hips dinta,gabanta ne yafadi, tasake kallon sa taga Idonsa a rufe, shi ko tsoron mama ma bayaji, Bayan tsoron taji motsin hannunsa, ahankali taji yace"mama nagaji ne"
Mama tace"tun safe kunata aiki ai dole agaji "
Tajuya ta halli Aisha tace"Aisha laifin me kikayi wa Abbanki ne ya turo ki aiki wajena?"
Cak Shahaab ya tsaya da abunda yake, sakamakon tambayar ta mama ta shige shi, shi Kansa yanaso yaji dalilin zuwan ta gidan, yasan idan ya tambayeta bazata kulashi ba, tunda yaga alama har yanzu bata huce ba.
Gaban tane yafadi, cikin sanyin jiki tace"Mama wani suke son su auramin, nikuma Bana sonsa, akwai Wanda nakeso, shine Abbana yace Gara yaturani aiki inyi nesa da gida saboda karna dinga haduwa da Wanda nakeso din"
Mama tace"subhanallah, Aisha ai ba'a bijirewa iyaye, duk abinda suke so shi akeyi, Amma menene laifin shi Wanda suke so subakin?"
Cikin sanyin jiki tace"bashida laifi mama, yanzu ma nakoma sonsa, shizan aura"
Cikin sauri Shahaab yabude Idonsa ya kalleta, lokaci daya fuskarsa tayi kicin kicin 6acin rai da tsananin kishi yafuto qarara, mama kuwa murmushi tayi tace"ikon Allah, har tsuntsun yatashi daga kan Wanda kike so din? To meyasa kika haqura da za6in naki? Inde har yanzu kina sonsa, Sai muje dake har Garin naku inyi musu magana cikin fahimta subarki ki auri Wanda kike so din"
Cikin sauri tace"A a mama, Aina haqura dashi, saboda ya yaudareni, ya6oyemin gaskiyar waye shi, Bayan nagane Kuma naji duk na tsaneshi"(🙆🏻♀️😂)
Runtse Idonsa yayi, cikin 6acin rai ya d'ago Kansa daga cinyar mama ya kalleta yace"kozaki danyi shiru please?, banson jin wannan shirmen "
Mama ta kallashi da tsananin mamaki tace"menene abun 6acin rai anan? Kai take Bawa labarin?"
Cikin masifa yace"mama I'm tired... tazo tasani agaba tanamin wani zancen banza da wofi... "
Idon Aisha yaciko da qwallah, yanda taga ransa ya6acin Nan saita tunada ranar dasuka fara fada yake mata kashedi akan ogonsa Mahmud Wakili, cikin kuka tatashi da gudu ta wuce daki, bayanta yabi da kallo, yanda take gudun yasa hips dinta suke rawa,wani irin jarabben yawu ya hadiye saida yaga shigewarta daki sannan yasaki wani irin tsaki.
Mama ta kalleshi fuskarta d'aukeda damuwa tace"meyake damunka ne? Yarinya tana bakin qoqorin ta akaina bata gajiya, sannan muna Dan zancen mu kazo kasata kuka ka Koreta, haka kawai badakai take magana ba kahauta da fada, ko tunda kake zuwa falon Nan ka ta6a ganin ta tazauna?"
Cikin kishi yace"mama Kuma saita zauna tanata cewa ta tsaneshi ta tsaneshi kinajin ta bazaki hanata ba? Tace ya yaudare ta kinyi shiru baki dauki mataki ba, tadawo tace ta tsaneshi Shima baki hanata ba, Kuma idan tace bata sonsa fa kwata kwata?"(🤣)
Mama tace"saime? Dakai take? Kai tace ta tsana?"
Cikin kumburi yace"a a "
Tace"to banaso, yanzu kasa tana kuka idan tafara wannan shegen fishin Nata Allah ne kadai yasan ranar dazata sauko, tashi kaje dinning Kaci abinci katafi part dinku"
Cikin shagwa6a yace"mama korata kike ko?"
Tace"nibana korarka,Kai dinne wani lokacin kacika rigima,kabar matarka acan nikuma kazo Nan ka dameni"
Murmushi yayi yace "shikkenan naji zan tafi, tashi muje kibani abinci"
Cikin sauri tace"me amfanin matarka?Nima Aisha ce tabani"
Murmushi yayi cikin ransa yace"aikuwa Nima saita Bani"
Amma a fili saiyace"to Bari in Dan kalli labarai idan zan tafi inkwnta saina ci abincin"
Tace"toshikkenan saida safe zanje in kwanta Nima,tunda ka kori yar hirar tawa,"
Cikin jin dadi yace"to mama saida safe"
Harta juya zata tafi saita dawo tace"yawwa wacece Aisha ne?"
Cikin sauri yajuyo ya kalleta yakasa bata amsa, tace"ka tsareni da ido baka Bani amsar tambaya taba"
Cikin wata irin kunya ya sunkuyar da qansa tareda shafa sumarsa yace"mama ai kece"
Murmushi tayi tace"banason qarya Mahmud, wacece Aisha?"
Cikin kunya yacigaba da shafa sumar sa,saide Kuma yaqi kallon ta, ahankali yace"wata ma'aikaciyar muce"
Murmushi tasake yi cikin ranta tana qara godewa Allah Dan da alama Mahmud din Nata soyaiya yake batare data Sani ba, cikin murmushin tace"ma'aikaciyar takuce zaka iya sadaukar da ranka saboda ita?"
Cikin shagwa6a yace "mamaaaah...."
Dariya tayi tace"to in tayi tsami naji, saida safe "
Cikin sauri yace"to Allah yakaimu mama"
Saida tashige daki sannan yasaki wata irin ajiyar zuciya, saida yayi Zaman minti ashirin shi kadai a falon, sannan yatashi yanufi dinning, yau da Kansa yazuba abincin acikin wani plate Mai kyau.
Sannan yad'auki gorar ruwa guda daya, yad'auki brief case dinsa yawuce Dakin Aisha.
Handle din dakin yakama sannan yashiga tareda rufowa, duhu ne ya wanzu a Dakin da alama ta kashe wutar ne ta kwanta, kunna wutar yayi lokaci daya ya hangeta kwance akan gadon jikinta a rufe ruf da blanket.
Hasken data Gani a idonta ne yasa ta bude idonta, lokaci daya idonta ya sauka akansa yana kokarin ajiye kayan dake hannunsa.
Shahaab littafin kudi ne, nera 300 na kacal
Zaki tura 300 ta wannan account
0164549488
Amina muhammad
GTbank
Kokuma katin MTN tareda shedar biya ta wannan number 08033300034
Mutara zuwa gobe🙏🏻
El Yaqoub ✍🏻
BASAJA TAKU NA BIYU
Ummah da Abba suna tsatstsaye atsakar gida suna kallon ikon Allah, Hajja ta riqe waya a hannu Sai zagaya tsakar gida take tana mita.
Abba ya kalleta yace"Hajja da haquri kikai da Kiran wayar nan haka, yanzu karfe goma saura, itama idan kin sameta ma may be basa tare Dame wayar, kokuma sunyi bacci"
Cikeda masifa tace"mamuda kaifa nariga nagama sanin baka damu da yarinyar Nan ba, inda kadamu da'ita lokacin data bugomin waya nace bazan bata kaiba Aida haquri yakamata kabani inhadaka da'ita, Amma saika yi mursisi kakara redio a kunne, nafi sati Ina Kiran yarinyar wayar taqi shiga, tayaya Hankali na zai kwanta?"
Umma ta kalleta tace"Hajja to tunda taqi shiga kibari mana gobe saiki kirata"
"bazan Bari ba Hadiza,kunga banfa riqeku ba, kuje kuyi kwanciyar ku, Amma nikam yau saina ji muryar mesunan qawa zan iya runtsa wa, haba dadewar ai tayi yawa, Yan birni da suka 6aci dason duniya waya Sani ma kohar sunyi tsiren ta"
Ummah ta sunkuyar da kanta tayi shiru, Abba kuwa kujera yaja ya zauna, Ina ya'isa yaje yabar Hajja awaje? Aikuwa da basu wanye lafiya ba gobe.
******
Bayan ya ajiye kayan zama yayi aqasan d'akin tareda daure fuska yace"sauko magana nazo muyi"
Babu musu taja hijabinta tasaka, sannan ta sakko Qasan Dakin ta zauna kanta aqasa hannunta duka biyun suna cikin hijab dinta.
Ajiyar zuciya yasauke yace"ba gaisuwa?"
Kanta aqasa tace"yalla6ai Aina gaisheka dazu"
Cikin sauri ya katseta "ke da Allah banason wannan yalla6ai-yalla6ai din,shikkenan dan abu yafaru bazaki tsaya ki saurari abinda zan fada miki ba, saiki yanke min hukunci, agabana kina cewa Wai wani kike so, ni kin tsaneni ko maaamah?"
Yaqare maganar da wata irin murya kamar zai Fashe da Kuka.
Hakanne yasa zuciyarta ta karye, Nan da Nan tafara hawaye, cikin kuka tace"bakaine ka yaudare niba, kasa Abbana ya rabani da Hajja yakawo ni wani waje aiki,aidama baka sona matarka kakeso tunda Qin fadamin kokai waye kayi" taqare maganar tana turo bakinta gaba
Cikin sigar rad'a yace"Amma nabaki haquri..."
Cikin kuka tace"ainima bance komai ba,kawai de karabu Dani kafita daga rayuwa ta, tun farko ma da nasan cewa kaine Mahmud Wakili bazan saurareka ba, sawun giwa ai ya take na....."
Cikin sauri ya katseta"maaamah.... Tun farko nasan cewa bakya sona, ranar Dana fara haduwa dake ma nasan cewa bakya sona..." matsowa yayi gab da ita, yasaka hannunsa biyu yariqe fuskarta,yasake yin qasa da murya yaci gaba da fadin"amma ni Ina sonki maaamah..."
Lumshe idonta tayi, Hakanne yabawa Hawayen idonta damar zubowa akan kumatunta, ahankali ta bude idonta, sannan tasaka hannu ta janye nasa hannun daga kan fuskarta, ta kalleshi tace"bazai iyu ba, saboda Abba na bazai baka niba, maqocinmu yaganni lokacin dana shiga motar ka, Kuma yaganni lokacin Dana futo, Abba na yayi fishi Dani Kuma duk kaine sila, tun farko inda kayi magana dashi dole zai fahimceni"
Tunda tafara magana ya zubawa lips dinta ido yana kallo, kawai moment dinsu na cikin mota yake tunowa lokacin dayake kissing dinta.
Ajiyar zuciya yayi shibaiga abun damuwa anan ba, ahankali yace "to maaama munshiga mota me mukayi? Meyasa Dan kin shiga motata Abba zaiyi miki wata fahimtar, ai babu abinda mukai..."
Cikin kuka ta daga murya tace"basaida ka tsotsi bakinaba, Kuma aina hanaka Amma shine kaqi denawa"
Murmushi yayi, yace"ni nama dade da mantawa maaamah, jinake kema kin manta, maaama akwai dalilin dayasa na 6oye miki kaina, mama da Ramadan sune suka sakani hakan"
Cikin sauri ta d'ago ta Kalle shi, jijjiga Kansa yayi yace"yes.... Saboda wani dalilin su Wanda nikaina banga amfanin saba, Sai Bayan nahadu dake ne Naga amfanin hakan tunda gashi nagane kina sona da gaskiya, ba kudina kikeso ba, bakisan waye niba Ina dashi banida shi Amma ahakan kika saurareni, maaamah...Ramadan koda yaushe bashida burin yaga naqara aure, mama kuwa tayi maganar tayi maganar harta gaji,kiduba shekaru na maaamah har yanzu banda yaro ko daya, mama kullum burinta shine taga naqara aure ko Allah zaisa na haihu, Amma naqi yarda saboda inason matata munirat banason nayi abinda zaisa hankalin ta yatashi har tayi tunanin nadena sonta, naje Asbiti andubani, doctor's dayawa sun tabbatar min qwayoyin halittana lafiya suke, zan iya haihuwa a kowanne lokaci, Amma munirat bataje ba, koda yaushe tana fadamin haihuwa ta Allah ce,yafimu sanin halin damuke ciki, Kuma ita gidansu sunada gadon haihuwa tunda ba'ita kadai mamarta tahaifa ba, muma idan mukai haquri Allah zai bamu watarana, tafi tunanin rashin lafiyar daga nine, hakanne yasa na shirya har qasar waje naje akan hakan suma sun tabbatar min lafiya ta kalau, hakan Dana fadawa mama da Ramadan shine yabasu damar da suka sake damuna akan maganar aure.
Bayan haduwa ta dake, ban 6oyewa Ramadan komai ba, saboda a ranar ma dashi muka fara zuwa garinku, har fadan mu saida nafada masa, daga lokacin da nabar garinku ban sake tunanin komawa ba, saida tunanin ki yamin yawa sannan, tunda Ramadan ya lura da tunanin danake nakuma fada masa komai daga Nan yafara cusa min ra'ayin ki araina daga qarshe harna gane Ina sonki, kullum Ramadan fadamin yake karna kuskura nafada miki koni waye, yakamata ace nagama sanin halin ki, shin zamuyi abota dake ta Amana kokuwa? Banta6a tunanin akwai soyaiyar gaskiya a duniya ba Sai ranar dakika Bani kyauta kika fadamin kudin karatun qaninki ne da kike Tarawa kika siyomin agogo dashi, kin sake shiga raina a ranar, kin birgeni yanda bakya zato, na fadawa Ramadan komai, shine yasake Bani qwarin gwiwar dazan tunkareki da maganar soyaiya, inba hakaba to shi zaizo har gidanku yace yana sonki, hakan ne yasa nafada miki Ina sonki, Sai Bayan kin amince da soyaiya ta shine Zaki gujeni?"
Sauran Hawayen idonta ta share, sannan tace"kaine kaje super market akano koba kai hane? "
Ahankali yace"nine, kuma tun a ranar nayi DANA SANI akan rufe miki koni waye danayi, inda kinsan cewa nine Mahmud Wakili da tuni na bayyana a gabanki na tambayeki waye wannan Yaron dayake tare dake?"
Cikin shagwa6a ta turo bakinta gaba tace"niba saurayi na bane, saurayin fati ne"
Cikin kishi yace"koma waye maamah banason kisake sauraren kowanne namiji, Rasa control din kaina nake, Bana son sake ganinki da kowanne namiji this is the first and last kinji ko?"
Cikeda yarinta tace"um"
Wayarsa yadauko dake gefe, yayi Dialing wata number, yasaka ta a hands-free, ringing hudu aka amsa cikeda nutsuwa, kallansa tayi tarasa bakin magana, ahankali ya jijjiga mata Kai yace"your brother..."
tareda bata wayar.
Cikin mamaki ta kar6i wayar tace"jabir...."
Saita Fashe da Kuka
Shahaab ya Girgiza Kansa, cikin ransa yace"Yarinyar Nan batada damuwa, abu kadan kuka na farinciki Dana baqinciki"
Daga d'ayan bangaren cikin wani irin farinciki jabir yace"takwarar Hajja,Wai kece?"
Cikin sauri Kuma tasaki dariya tace"Dalla nice"
Cikin mamaki tace"amma Yaya akai Naga kin kirani da number Yaya Mahmud?"
Cikin sauri tace"yaya akai kasan shi?"
Yace"muna waya dashi sosai, amma ban fada masa yayata tana aiki a gidansa ba, yacemin ogansa ne yad'auki nauyin karatu na"
Hararar wayar tayi, sannan ta juya ta harari Shahaab, cikin sauri tace"bawani ogansa, shine, Kuma idan nakoma gida ma saina fadawa Abba da Hajja da Umm...."
Kafin taqarasa maganar Shahaab yayi sauri zai qwace wayar, itama tafara kokarin hanashi,basusan sun kashe wayar ba Garin kokawa kowa yanaso ya kar6i wayar, saida ya Kar6a sannan yace"miye haka? Meyasa Zaki fada masa?"
Hawaye ne yasilalo daga idonta, cikin kuka tace"to meyasa Shima zaka masa irin nawa?"
Wayar yasakar mata, sannan yariqe fuskarta da hannu biyu yace"sokike nafada masa nine na dauki nauyin karatun sa? Menene abun birgewa to? Nayi ne Dan Allah,sannan Kuma danke, dakika dauke kudinsa da kike Tarawa zai tafi makaranta kika min kyauta dashi, to gashinan nahutar dake, Saudia Kuma Dama ai kece Zaki kaimu ko...?"
Yaqarasa maganar cikin sigar tsokana, cikin farinciki takai masa Dukan wasa a hannunsa, sakinta yayi yana murmushi, sannan yadauko abincin sa ya ajiye akan cinyarta yace"dazu kinbawa mama, nikuma kika hanani, yanzu saiki Bani Nima"
Cikin sauri tace"kaje Kaci afalo, kaga yanzu goma da kwata, dare yayi, baka tsoron matarka tasan kana zuwa dakina?"
Fuskarsa yadan daure yace"kinaso na kwana da yunwa?"
Cikin sauri ta Girgiza masa Kai, yace"to bani"
Kallan abincin tayi tace"to ai babu spoon"
Cikin shagwa6a yace"da hannu"
Cikin ranta tace"nashiga uku"
Afili kuwa saita Girgiza masa Kai tace"um um ni bazan iyabb....."
Kafin ta qarasa maganar cikin sigar rad'a yace"please"
Badon tasoba tasaka hannunta tafara bashi abincin, duk lokacin dazata saka masa a bakinsa saiya Lumshe Idonsa sannan zai fara ci, mamaki ne ya kamata ganin yanda yakecin abinci kamar bayaso, har qaguwa tayi yagama saboda ita Bahaka mama take cin Nata ba, wanne irin cin abinci ne wannan saikace mace.
Saida yaci yaqoshi, sannan yariqe tsintsiyar hannunta, yafara tsotsar Yan yatsun data bashi abincin, Idonsa a Lumshe suke yana tsotsar yatsun kamar wanda yake shan sweet, kallansa tayi tanajin gabanta yana faduwa, wani irin yanayi yana shiga jikinta, ahankali tazame hannunta daga bakinsa, babu musu yasaki, cikin wata irin murya yace"Albishirin ki"
Cikin sauri tace"goro"
"to menene Goron albashir dina?"
Fari tayi da idonta tace"duk abinda kake so"
Yace"kinyi alqawari?"
Tace"inde baifi qarfi naba"
Briefcase dinsa yabude, yad'auko wasu takardu yad'ora mata akan cinyarta yace"kyauta ce daga masoyi zuwa masoyiyarsa, kyautar amsa tayin soyaiya ta dakikai, fatana ki kasance tare dake da dadi ba dadi,da kudi ba kudi,kici gaba da sona fiyeda kowa a duniyar Nan Bayan iyayenki, kibani kulawa fiyeda wadda Zaki Bawa 'ya'yanki,kijani ajikinki, muyi rayuwa tare har abada, kyautar sabon company n Dana bude yau ne"
Yad'ora hannunsa akan takardun tareda bude wani shafi, can qasan page din ya nuna mata yace"kinga sign dinki daga yau, a ko'ina haka Zaki dinga yi,Ash-hab sunan yamiki dadi ko?"
Yaqarasa maganar tareda Dagowa yana kallon ta, tunda yafara maganar Aisha take kallon sa, wanne irin mutum ne Shahaab? Dama haka halaiyarsa take? Duk wannan abun dayake saboda kawai tana sonsa ne? Yakai mahaifin ta umara, yakai qaninta karatu qasar waje, duk wannan abubuwan da wannan facaka da kudin dayake bashida d'a nashi na Kansa, tausayin sane ya kamata,itakam Dame zata sakawa wannan mutumin a rayuwa? batasan lokacin da hawaye ya wanke mata fuska ba, dama ita Aishan yake nufi? Ashe sunanta yasaka Bana matarsa ba, Bana mahaifiyar saba, wacce irin soyaiya ce wannan?
Cikin kuka tafara Girgiza masa Kai Tace"A a, ban cancanci haka daga gareka ba, matsayi na baikai Nan ba, abun yayi yawa, ka barshi Dan Allah"
Matsowa yayi jikinta, kamar wanda zai rungume ta, Cikin sigar rad'a yace "haba kekuwa,menene abun kuka Kuma? Kinaso kimin asarar Hawayen ki kooo?" yaqare maganar cikin wata irin murya me cikeda fitina,
Matsowa yasake, ahankali yad'ora hannayensa a fuskarta, yariqe fuskar, sannan ya matso da bakinsa dab da fuskarta yad'ora harshansa akan kumatunta, yafara lashe Hawayen datake zubar wa, jin abinda yake ne yasa tarufe idonta ruf..., ta nemi kukan datake tarasa, saida yaji tadena kuka, sannan yahade bakinsu waje daya,al'amarin daya saka duka zukatan masoyan cikin wani Hali na shauqi da begen juna, hakan yasa wannan Karon batasan lokacin data bashi hadin kaiba,Dan qaramin lips dinsa take Sha ahankali, hakan datayi ne yasake gigita Shahaab, cikin fitar wani irin numfashi da tsantsar soyaiya, yake yimata wani irin kiss,gaba daya ya manta acikin dakinta yake, zuciyar sace take zigashi akan yata6a abubuwan Nan guda biyu masu dadin shafawa, wata zuciyar Kuma tana hanashi, daqyar ya'iya zare bakinsa, gudun kada ya aikata abun kunya acikin gidansa yasa cikin mutuwar jiki, yasakar mata kiss a goshinta, tareda miqewa ya fice daga d'akin cikin sauri.
Haka yakoma part dinsu Idonsa cikeda jaraba, yayi mamakin ganin munirat zaune afalo ta dora qafa daya Kan daya, yana sallama ko d'ago kanta batayi ba bare ta amsa, cikin mamaki ya qaraso wajan ta ya tsaya yace"munirat bakiji Ina sallama bane?"
Kamar da dutsi yake magana haka munirat tayi masa banza, ajiyar zuciya yayi, yarasa dalilin yin fishin ta, yace"meyafaru kike fishi?"
Nanma batace masa komai ba tayi shiru, Kansa ya Girgiza kawai yawuce dakinsa, idan ma akan rade radin dayake ji ne matarsa tana fishi saboda yabawa mama company ai yana ganin hakan ba zaisa tayi fishi ba, tunda shide bai futo fili yace budurwarsa yabawa ba, Yan kalamai yayi sannan Kuma yabayar da company, yanzu inda maman yabawa ma kenan haka zata yi fishi? Hakan na nufin idan mama yabawa munirat tana daga cikin Wanda zasuyi fishi akan yayiwa mahaifiyar sa kyauta, maimakon itama tayi kokari tasamu abinda yafi company awajansa, Girgiza Kansa yayi yashige toilet ya watsa ruwa,domin yanayin da yakeji ajikinsa Sai ahankali, Bayan yayi wanka yafuto ya shirya sannan ya kwanta tareda rungume fillo tsam a qirjinsa ya Lumshe Idonsa.
Bayan ya idar da sallar asuba yana dawowa part dinsu yakoma ya kwanta, Bai dade da kwanciya ba akayi masa Kiran gaggawa daga kamfanin su dake lagos, cikin sauri ya shirya ko sallama baiyi da munirat ba yafita yayi part din