Showing 12001 words to 15000 words out of 61919 words
Sam yaki saki gashi yaki canza dayan,Hawayen wahala nafara amma araina nace Allah ya k'ara ubanda ya aikeni.
Dakyar nasamu nasakamishi dayan sannan nafara shafar jikinshi yanda zaisami nutsuwa babu inda hannuna be kaiwa ajikinshi domin gara intemakamishi yasami nutsuwa ko Allah zaisa yabarmu muyi barci.
Irin nishin da gurnanin da yakeyi yasani jin kamar insako fitsari ga azabar zafi da kirjina keyi Wanda bansan ranar sakinshiba.
[4/2, 11:15 AM] Re@l💍 K@usy🌹: Rumana 11
Yinin ranar
nayishine cikin kewar inna shiyasama nakasa hakuri har saida, nakira wayar baba nace yabata mu gaisa.
Cikin shagwabar da sai yanzu nasami damar yinta nace inna kin manta dani ko?
"Dariya tayi cikin jin dadi kamin tace ke kuwa autata ya za ai uwa ta mance da 'yarta guda daya? Wannan ai ba abune me yuwuwaba kina raina wallahi har yanzu gidannan bekoma daidaiba munata gyare gyare ya gidan?
" Lafiya lau innata.
"Yauwa auta babu dai wata matsala ko?
" Babu komai inna ammadai nayi kewarki Allah.
Kuma gyara zamanta tayi kamin tace hakane nima nan har zazzabin rashinki nayi amma nasan ahankali zamu saba karshen watannan insha Allah zaki ganni nida k'awarki dije tunda ita tasan waje,Zanzo inga muhallin diyata, Ya mijin naki kunfara gaisawa dashi ko?
"Murmushi nayi kamin ince eh inna yana kirana duk safiya mu gaisa shima yanada kirki sosai kamar babanshi,Amma kinga da inatajin tsoron wane kalane shi.
"Hakane Ruma ainasan Allah zai tausayama maraicinki bazai barki ki galabaitaba yanzu ki ajiye wayar kije kiyi aikin gabanki sai kuma ankwana biyu dakaina zansa malam ya kiraki saimu gaisa nima ai nasai wayar bandai iyabane shiyasa.
" To inna sai anjima zan jira.
Jin motsinshi cikin daki yacika yawa yasani mikewa na nufi dakin,Watsi kawai yake da shimfidar gadon da filullukan yanawani gunji tare da make make.
Karatun alkur'ani na kunna awayata na lallaba na ajiye gefe nai tafiyata falo na zauna,Tun inajin ifface iffacenshi harnaji shiru shedar sun barshi kenan,Girgiza kaina nayi kamin ince hummmm wallahi bawani hauka aljanune kawai ke kaidamai tunanin,Allah ya sakamaka.
Saida nai sallar magriba sannan Na kira number da Abba yabani ta maman haidar,Kirjina yanata bugawa Sabida tsoron yanda zata tarbeni.
Bani da matsala da kudin waya domin Abban saida yaimin lodi sosai wai Sabida kiranshi ko kiran wani nawa.
Harta yanke ba'a daukaba saida nakuma kira sannan naji muryar wata mata na sallama.
"Jikina har rawa yakeyi Sabida tsoro, Mama ina yini ya aiki?
" Saida tayi Dan jim sannan ta amsa da lafiya lau,Amma bangane me maganaba nadaiga number daga Nigeria ko?
"Muryata ashake nace eh hakane Sunana Rumana.
" Murmushi me sauti tayi kamin tace ah Ashe diyatace sannunki ya kwana biyu ya bakunta?
Cikin jin kunya da mamakin ina tasanni na amsa mata da lafiya lau mama Dan Allah kiyi hakuri ki dawo mama.
Cikin jin dadi tace karki damu Rumana insha Allah inanan tafe kinji ko? Nasan komai akanki domin anyimin bincike kuma babu Wanda yagayamin wata magana ta banza akanki danhaka zandawo gidan nan kodan farin cikinku keda mijinki,Yanzu inashi haidar din yake?
"Yana daki mama amma idonshi biyu.
" Allah yaimiki albarka Rumana Allah ya albarkaci rayuwarku nima nan ba zaune nakeba wallahi kullun addua nakemishi nasan zai warke da yardar Allah ina nan dawowa inda nake aikine sunki bani damar barin kasar amma insha Allah zandawo kedai ki dage da addua sannan ko megadin gidannan kadda ki yadda dashi balle matan gidan idan da halima ki dinga zama bangarenki babu ruwanki da harkar kowa ina k'ara tunamiki karki wasa da ibada domin yanzu duk me harin cutar da haidar tare zai dinga hadawa dake.
"To mama nagode.
" Yauwa sai anjima zan dinga kiranki insha Allah Ammafa banso ki gayama alhaji sai anjima.
Najima ina kallon wayar bayan ta kashe,Muryarta taimin dadi daga gani 'yar gayuce sosai.
Ajiye wayar tayi kamin ta sauke naumfashi lallai Allah ya amsa addu'arta tunda yabawa haidar mace ta gari domin koda tasa akaimata bincike hankalinta be kwantace wai har sai taga ranar dana nemeta sannan zata tabbatar saigashi ko sati banyiba na nemeta lallai dole ta dawo kodan wa innan yara kamin acutar da marainiyar Allah Wadda batajiba kuma bataganiba.
Jin ana kwankwasa kofa yasani dawowa hayyacina daga tunanin dana lula,Wani mutun nagani tsaye Wanda bansaniba.
Kallonshi nake kamin in bude baki saiya rigani da hajiya ina yini Sunana mudi nine mekula da megida kamin akawoki nazo muku sallamane gobe zankoma gida.
Murmushi nayi kamin ince ah sannunka to shigomana.
Zama yai muka gaisa yake kumaban labarin ciwon na megidanshi tare dabani shawarwari nidai inajinshi Sabida dama nasan dole zaifini sanin komai tunda sunjima tare.
Muna nan zaune saiga Abba.
Ah mudi kana nan kenan? Cewar Abban.
"Eh wallahi alhaji nashigo yima amarya sallama da megida insha Allah lokacin da zan dawo megida ya warware.
" To Allah yasa aimungode sosai da temakonka Allah yasaka da Alkhairi ammadai nacemaka ka dinga waiwayomu Dan Allah.
"Insha Allah alhaji kadda ka damu ai anriga anzama daya.
Sai lokacin Abba ya zauna na gaidashi kamin yace Ruma yame jikin anfara samun wani cigaba kuwa?
Murmushi nayi kamin ince kai Abba daga farawa?
Duk dariya mukayi kamin yace to aikinsan mu mutane akwaimu da garaje nidai Allah ya nunamin ranar da zanshigo nan inga haidar zaune cikin hankalinshi.
Da ameen duk muka amsa.
Duk saida suka lek'a sukaga haidar din Ashe barci yayi sannan sukaimin sallama suka wuce nikuma na rufe kofata,Saidai ko zama banyiba naji ana kuma bugawa.
Nayi tunanin ko Abbane yai mantuwa amma ina budewa sainaga wata mata tsaye da kula ahannu tanamin murmushi.
Banyi niyyar bata hanyaba domin tashigo danhaka anan tsayen nafara gaidata.
Itaba bata damu da shigowarba Dan muna gaisawa ta mikomin gashi farfesune nayo muku keda megidan naki.
Saida na duka har kasa sannan na amsa gamida godiya, Tana wucewa nabi bayanta da harara domin haka kawai naji hankalina be kwanta da itaba.
Farfesufa har farfesu domin kamshin da yakema kawai abin dadine amma zuciyata nagayamin Allah kadai yasan surkellen da akai ciki duk kwanakin danai gidan ko ruwa babu wacce ta kawomin kaini yanzu hakama bazan iya bambancesuba amma shine hadda wani yomin to ai ba mayya bace.
Cikin Leda na juyeshi sawu na daukewa najefa cikin babbar bolar gidan nadawo na rufe kofata.
Ayanzu wajan watana daya kenan cikin gidannan babu abinda nanema na rasa na canza naiwani kyau nasamun hutu babu ruwan matan Abba dani balle ince sun dameni,Abba kullun zai shigo so biyu dubamu indai yana k'asar da safe dakuma dare.
Kula da haidar be zamemin wani aikiba domin ayanzu na saba inyimishi wanka da sauran bukatu wani lokacin inacin bugu wajanshi amma wani lokacin sai inyi sati be kaimin buguba tunda abun zuwane.
Ance ko mahaukaci yasan me kuladashi yanzu da kanshi yake zuwa kusa dani ya zauna babudai magana sannan idan yafara kallon waje saiyai kusa minti talatin bedenaba wani lokacin ma saina kaudamishi kanshi.
Magani dai yi akeyi amma saidai ahankali ni nakeganin saukin tunda inatare dashi amma Abba kullun cewa yake shifa bega wani canjiba
[4/2, 11:15 AM] Re@l💍 K@usy🌹: Rumana 10
Inacan nai nisa
wajan tunanin yanda zanyi mishi kawai saidai naji tallatsin ruwa ajikina,Tsalle nai nakoma gefe ina maida numfashi,Ashe wai fitsarin ya fallatsomin Sabida bugashin da yake da hannunshi.
Addu'a nafara duk kalar wadda nasan ta Neman tsarice tare da kariya daga shaidanu sannan na matsa kusa dashi hadda yin bismilla na mikamishi hannuna so nake inga zaizo wajena.
Yajima yana kallon hannuna kamar me karanto wani Abu sannan ya maida hannuwanshi bayanshi ya kauda kai ga barin kallona.
Janshi nai zuwa toilet din dake dakin na antayamishi ruwa daga sama har kasa sannan na rufe idanuna na zaremai wando nai gaggawar saka mishi na hannuna shidai yana tsaye batani yakeba.
Yayinda nakejin kirjina kamar zai faso Sabida tashin hankali,Oh rayuwa kenan kowane bawa da kalar tashi kaddarar Allah kasa mucika da imani.
Wani dadine ya kamani lokacinda naji alamar katifar dakin me ledace wato idanma zaiyi fitsari saidai ashare,To da sauki nasami saukin aiki.
Sai wajan Tara na dare sannan Abba yadawo kawo magungunan kamar yadda yace.
Rubutune jarka guda sai Wanda za adinga badamishi idan zai wanka sainasha sai kuma wani kamar ruwa amma kamshi yake sosai shine Wanda za adinga shafamishi idan zanyi barci.
Saida yagama nunamin tare damin bayani sannan yadora da cewa"Saifa kin daure Ruma domin jihadi zakiyi sannan Dan Allah kema kadda kiyi wasa da addua Sabida yanzu nidai nafara sakankancewa da sharrin mutun.
Saida ya shafamai na Daren yau din sannan yabashi wata karamar kwaya wacce ke temakamishi wajan yin barci akan lokaci Sabida gudun tashin ciwon,Sannan yaimin sallama.
Tsayawa nai na gyare inda yabata sannan nakoma dakina na canza kaya tare da Alwala .
Harna kwanta saikuma hankalina yaki kwanciya naita tunani kala-kala daga karshedai mikewa nai tare da daukar alkur'ani na na nufi dakin.
Yanata barcinshi kamar me hankali fuskarnan gwanin kyau domin har saida naji kirjina ya buga,Na kalli faffadan kirjinshi mecike da gargasa lallai inbacin yana cikin wannan lalura nasan yafi karfina kilama ko kallona bazai iyayi ba.
Can gefe na rakabe bayan nagama kallonshi nafara karatu cikin tsananin sanyi da Neman temakon ubangiji akan wannan lalaura ta wannan bawa nashi.
Banjima da fara karatunba yafara motsi tare da juye juye kamar na meneman dauki kasancewar nariga nayi hadda kawai saina maida hankalina akanshi nacigaba da karatuna ammafa zuciyata ahautsine take tun yana motsi da mutsu-mutsu har saida yagaji yabari lokacin ina gabda gama bakara.
Saida naga barcinshi yai nisa sannan nikuma nasamu na raba gefenshi na kwanta bayan na tofeshi da addua.
Kwance take tai dai-dai saman lafiyayyen gadonta tana chating da manyan mata irinta,Karamar wayarta dake gefe tafara ring kamar bazata daukaba saikuma takai hannu ta dauka, Da sauri ta amsa ganin me kiran.
"Malam barka da dare ya aiki?
" Da katuwar muryarshi ta mushrikan ALLAH ya amsa da lafiya hajiya saratu ammadai akwai matsala danhaka kome kikeyi kishigo gobe.
Jikinta har rawa yake,Matsala kace malam?
"Kwaraima da gaske kedai kiyi kokari kizo domin asami mafita kamin komai ya cabe.
" To shikenan malam zanshigo goben kome kenan zan kiraka.
Washe gari.
Cikin ikon Allah saina tashi cikin walwala domin zullumin danake fama dashi Sam bantashi dashiba.
Beyi fitsariba haka beyi bayan gidaba hankalina kwance nai sallar asuba sannan natasheshi,Wani mugun mari ya sakarmin Dana matsa saiya tashi Ashe barcin be isheshiba,Ina kuka ina mai Alwala domin na rantse saidai ya kasheni domin babu wata cuta dake damunshi sai miyagun aljanu dake wahal dashi.
Ba maganar sallah domin ana gama alwalar yasako fitsarinshi kuma atsaye.
Tunanin idan yayo bayangida ya zanyi nasashi zaunar dashi akan masan,Na juyamishi baya.
Koda zan juye yana leken kashin da yayi,Wani dadi naji lokacinda na fahimci yayi kashin.
Banji komaiba wajan yimai tsarki saidai gabanshine ban iya tabawa Dan wallahi tsoroma nakeji kosai daya ban yadda idona ya kalli wajan ba.
Sai misalin goma saura saiga Abba yashigo,Cikin kunya na gaidashi yayinda ya amsa cike da farincikin ganinmu Sabida lokacin nagamaba haidar abinci kenan yanata kokarin kama jelar gashina.
Bansan ya akai yaga shatin hannun haidar din afuskataba saidai naji yana subhanillahi bugunki yayi?
"Kauda fuskata nai batare danayi maganaba Sabida ya Riga yagani balle ince a'a.
Kiyi hakuri insha Allah zakiji dadi nan gaba komai lokacine,Nidai fatana kidage damai amfani da magungunan mukuma munata addu'a komai zaizama tarihi insha Allah.
" Cikin girmamawa nace ai inagama aljanune Abba domin jiya da dare danafara karatu bakaga abinda yaitayiba kamin yai barci.
Baki bude yace"ahaf ni kaina nafara zargin haka wallahi Sabida wani lokacin saikiganshi kamar me hankali amma idan abun ya motsa saikace tsohon mahaukaci,Allah yaimiki albarka ammadai kidingayin nesa kadda ya makeki babu kowa kusa,Nizan wuce nema idan kina bukatar wani Abu saiki gayamin.
Hajiya gaskiya aikinnan inaga zaibada matsala.
"Kuma muskutawa tayi kamar zataimai sujjada tsabar biyayya,A'a malam kadda kace haka nidai fatana haidar ya dawwama cikin lalurarnan har zuwa lokacinda zaibar duniya konawane zanbada Amma banso inji ana kiran matsalar nan malam.
" To gaskiya bazan bouemikiba kamar yadda nacemiki bake kadaibace meyin aiki akan wannan yaro to hakanne domin aljanin dakikasa na turamishi Wanda zandinga tsikarinshi yana zabura to jiya yadawomin nan yana kuka wai dakyar yasha Sabida masifar daya shiga cikin dakin shi yaron.
"Da mamaki tace malam banganeba?
" yauwa to gaskiya yace bazai komaba Sabida akwai wadda zata koneshi cikin dakin yanzu ba kamar daba Sabida besan ta inda zaikuma shigarshiba Dan babu inda bata shafeshi da addu'a,Danhaka saidai acanza wata mafitar duk da cewa bafa warkewa yayiba domin suma sauran sunacan suna kuma shiri kamar yadda kema kike niyyar wani shirin.
"To nidai malam nabaka wuka da nama kome ka yanke daidaine agayamin abun sadaka kawai,Hajiya saude kenan mugu beda kama.
Kauyen dogon dutse." Uhumm malam duk naji abinda kace shine nace to kodai kasheya za ayi kawai kowa ya huta?
"Hahhhhahhaha hajiya saratu kenan wannan yaro ya debo shekaru da yawa danhaka babu me kasheshi sai lokacinshi yayi kima daina wannan maganar.
" Idanunta ta runtse kamin tace to malam acanza mishi wasu wa inda zasuje su haukatashi kaba daya mana.
Zane zanenshi yayi kamin yace ansami mafita hajiya kawo sadaka.
Jakarta ta zage ta kwaso kudi me yawan gaske kamar batasan ciwonsuba.
Kullin magani biyu ya mikomata,Wannan wanka tsakiyar gida babu sutura sannan kadda ki yadda kiyi magana kuma kadda kibari kowa ya ganki,Wannan kuma kisan yanda zakiyi kisamusu a abinci dashi da matar tashi,Zakiga sakamako.
[4/2, 11:15 AM] Re@l💍 K@usy🌹: Rumana 14
Tun inajin sukur
-sukur dinshi harnafarajin saukar numfashinya,Ajiyar zuciya na sauke me karfi kamin ince Alhamdulillahi yasami barci.
Dakyar nasamu na janyeshi daga jikina sannan natashi na wanke jikina,Idona nakan kyakykyawan fuskanshi idanunshi duk sunyi lema da alama kuka da hawaye yayi kamin yasami barcin.
Barcin danayi kusan raba da rabi nayi domin mafarkin da nayi nayau yafi na kullun muni,Watakil hakan Nada nasaba da zuwan da zanyi gida gobe.
Da kaina naimishi wankan tsarki da asuba sannan na dauramishi alwala kallona yake kamar idanunshi zasu fado Wanda hakan yakuma dauremin kai sosai,Nifa wani lokacin Saina dinga tunanin kamar yafara jin sauki.
Karfe Tara da rabi na safe harun yaimin sallama lokacin tea nakeba haidar sai bata jikinshi yakeyi.
Cikin farinciki ya k'araso"Amaryarmu ya kk ya kwanan oga?
Alhamdulillahi ya harun yasu umma?
"Lafiya lau. Abba yace kin shirya zamu wuce ko?
"Eh na shirya ya haidar na tsaya gyarawa dayake jiya yai zazzabi shikenan tunsafe da fitina yatashi ji hannuna wani cizo da yaimin har yanzu ciwo wajan yakeyi.
" Subhanillahi wayyo sannu yo me kikaimishi haka?
Sadda kaina nayi k'asa alamun kunya domin kin yadda nayi ya sakamin hannu cikin riga Sabida azabar zafin da kirjina keyi shinefa yaji haushi yaimin wani mugun cizo.
Ganin bance komaiba yasashi cewa"to bari mujira abban yace zai fita dashi yau kamin muje mu dawo Sabida beson zaman kadaici ya dameshi.
"Mikewa nayi tare da cewa bari ingama shirya kayanda zanje dasu aini shanake da wuri zamutai ma.
Bina haidar yayi zugui zugui ko kallon harun dake kiranshi beyiba.
" dariya yafara kamin yace lallai mutumina jiki yafara kyau wato yanzu kasan me kula dakai ko? Aiko yau Abba zaisha rikici Dan kilama sai gobe.
Goma da wani abu Abba yazo hadda kayan tsaraba ya shirgomin wa inda zankai gida tunda wannan shine zuwana na farko.
Aiko godiya naitayi hadda hawayena Sabida tsabar farinciki.
Dakyar yasamu ya janye haidar domin dama ya tsara zai kaishi gun memaganinshi yaganshi yau tunda dama so daya yataba ganinshi zaidaiyi kokarin ganin ya daukemishi hankali kamin mudawo din.
Munyi nisa da gari sosai Sabida uban gudun da yake shararawa hirar haidar yakemin kala kala wani inyi dariya wani inyi murmushi wani kuma da auna labarin da halin dayake ciki yanzu sai inji kwalla tacikamin ido.
Bakori muka tsaya saida ya tsaya wajen gari na warema inna tsarabarta sannan muka k'arasa sabida nasan halinta na hadama duk da dai ana nan ana shirin tafiya makka domin kwana kin bewuce watanni ukuba yanzu da wasu yan kwanaki.
Ihun murna taitayi sabida farinciki rasa inda zata sakani tayi sabida jin dadi bunu bunu ta shafi fuskata"ah lallai hankalinki kwance yake rumana kinga yanda kika koma kuwa?
Nidai saidai inyi murmushi kawai sabida harwata kunyarta nakeji.
Sai la'asar sannan na shirgamata karya akan cewa zanje maska indubo kakana na wajan uwa tunda yasha ciwo kuma yau zamu koma katsina sabida megidana gobe zai dawo da azahar.
Bakin inna har keya take ah lallai gara ku hanzarta Allah yayi albarka kya gaisheshi ai ina nan dai inasa idona akan hanya daya dawo ki kawoshi yaga dangi kinji ko?
"To inna insha Allah.
Tsarabarta nabata me yawa tare da bata ta dije nasandai zataba baba tunda suna tare sannan mukaimata sallama bayan ta hadani da kayan gyara musamman dataji nace gobe zai dawo.
Har muka isa maska harun beyi shiru ba yanamin hira sabida shidai da alama tausayina yakeji sosai.
Tsayawa fadin murnar da kakannina sukai bata lokacine domin sosai sukaita nan nan dani,Hakama harun saidai ko jimawa bamuyiba akayi sallar magriba lokacin na k'arasa gidan kakannina na wajan uwa.
Malam liman naso infara gani amma dayake yanayima magidanta karatu tsakanin magriba da isha'i dole na