Showing 51001 words to 54000 words out of 61919 words
kaga Kaine babba yarinyar nan tanada hakuri da kawaici,Allah yaimuku albarka ya kade fitina tsakaninku.
Rungumeni yayi jikinshi yana sauke numfashi cike da kwadayi da son kasancewa dani,Amma abun mamaki jinai wani irin kunci da damuwa ya dabaibayeni har bansan lokacinda na tureshi daga jikina ba.
Da mamaki yatashi zaune tare da kunna kwai haske ya gauraye dakin,"Lafiya Rumana?
Wata uwar harara na wurgamishi kamin ince"Au wai tambaya kakeyi? To wallahi bazai yuwu in zauna banda aiki saina ciki da rainoba dama nasan yanda kake rarukata babu yanda za ai ciki yaki shiga tunda bawai tausayine dakaiba to wallahi ka zubar dashi danni banso bankuma shiryama wata wahalarba yanzu.
Hasken ya kashe fuskarshi cike da damuwa ganin yanda yau daya kawai duk na yamutse amma bazaiso infaramishi rashin kunyaba.
Matseni yayi jikinshi da karfinshi ya kwanta dani Dan inagama hadda mugunta ya hadamin Amma ko qala beceminba game da maganar danayimishi ta ciki.
Asubama haka ya gwadamin karfinshi haryasami nutsuwa sannan ya kyaleni duk da irin kukan da nakemishi kuwa.
Safiyar lahadi nan ma beje ko ina ba iyakar tashin hankali yaganshi Dan tasashi nayi da kuka da bakar maganana har saida na cikashi ya fallamin wani lafiyayyen mari,Wanda ya tilastamin shiga nutsuwata batare Dana shiryaba ammadai bandaina kukaba.
Cikin wata irin zuciya yafara magana Dan nagama hasalashi"wallahi baby bayan inajin tausayinki dasaina lallasaki gidannan da wanne kikeso injine? Tun jiya kwana nayi Neman mafita amma bansamu yaukuma tunsafe kintasani da fitini kalli yanda yaranki ke kallonki dazu har baki kika fasama abdurrahim babu gaira balle dalili ga kukan banzanki Wanda ke tafasamin zuciya,So kikeyi zuciyata ta bugane ina jiye miki damuwa da tashin hankali kinakuma kai kanki ko? To tashi muje wajan umma tunda ni ban isa dakeba.
Fuuuuu ya yayi waje da yaran harwani huci yakeyi tsabar yanda ranshi yake bace.
Ko sallama beyiba haka ya diremata umma yaran ya fice duk irin kiran da abban kemishi besa yadawoba.
Inda nake ina kuka ya isa wata irin figa yaimin duk irin tirjewar danakeyi besa ya sakeniba saida ya isa falon umma to suma duk tsaye muka taddasu,Wani hantsalani yayi gabanta yana huci.
Wani irin shiru falon ya d'auka sai sautin kukana danakeyi kadan kadan,Yayinda suka zuba Mishi ido ganin yanda yake huci kai koni bantaba ganin fushinya irin na yauba iyakar zamana dashi,Sosai tsoranshi ya darsu cikin zuciyata.
Ruwa umma ta debo tabashi yasha sannan yafara sauke numfashi Ahankali.
"Meya faru? Cewar Abba dake rungume da yaran dansuma sun tsorata tuni suka lafe jikin Abban.
Yajima cikin yin shiru kamin yace" Abba Ruma Sam batajin lallashi ni bansan yanda takeso muyiba sotake dole saitakaini karshe naimata abinda bata zataba sannan hankalinta zai kwanta!!!
"To ai ance meya hadaku har rayuka suka baci haka? Cewar umma wadda ke kusadani zaune.
" Cikine da ita wai dole sai an zubar dashi"
Agigice duk suka mike musamman Abba Wanda har ya kawo kusadani,Batare Dana fargaba ai tuni nai baya atsorace ina kuma sakin kuka.
[4/2, 3:09 PM] Re@l💍 K@usy🌹: Rumana 52
Nai mamakin ganin kiranshi domin idan ban mantaba to lallai inaga munfi sati bamuyi waya dashi ba saidai ya kira inna su gaisa ya tambayi yara amma bazai nemeniba,Yayinda nima na tattareshi na watsar sabida haushin fushin daya dauka dani babu gaira balle dalili.
Ina kallonta harta yanke wani kiran yakuma shigowa,Nan ma banza nayi da wayar haddama harara tasamu kamar haidar dinne ke gabana alokacin.
Wani huci ya fitar me zafi kamin ya kuma danna kiran kenan harya gama kure hakurinta,Lallai idan hakane be kyautaba,Kuma inda ya dauki shawarar harun da abin bekai hakaba.
Saida na mula na mulmule sannan na d'aga wayar kuma nai shiru abuna,Jira kawai nake inji yaukuma dawata masifar yazo.
Ajiyar zuciya ya sauke kamin ya furta"Babyna kinyini lafiya ya twins?
Bakina na tabe kamar yana gabana kamin nace "Lafiya lau ya aiki?
" Lafiya lau babyna ya maskan?
Hararar Abdurrahim dakeshan nono nayi kamin jin yanda yake janshi kamar sai janye ruwan dake ciki duka,Kamin nace "Uhumm Ashe kasan munzo maska?
Ganin dai yanda hirar tamu take duk sai ahankali sai kawai ya kuma tambayar yaran yaimin sallama.
Tagumi ya zabga yana mamakin fushin danake dashi saida yai dogon tunani saikuma yaga ai duk laifinshine tunda shi yafara,Amma yasan ahankali zai shawo kan komai.
Niko murmushi nayi dannafahimci jikinshi yai sanyi sosai,K'wata nayi kamin ince dani kake magana wallahi ni bazan dauki wannan zuciyar takaba.
Satinmu daya amaska muka koma bakori da kayan arziki niki niki.
Koda muka dawo bawani zama mukaiba sabida shirye shiryen komawa kullun umma saita tambaya to nadai sami wadataccen gyara ko? Nidai sai dai inbita da eh cike da kunya.
Kuma gaskiya inna tai kokari dan ko farfesun kaji inaga naci yafi na kaza shabiyar haka caccabi ni kaina inaji ajikina dan gaskiya ni kaina nasan na gyaru.
Magunguna kuwa wa inda inna ta daka da kanta sannan sune suka zama kamar yajin cin abincina kai innafa tasan takan duniya.
** *** **
Irin gyaran da bangarena ya diba sai mutun yai mamaki kullun cikin gyare gyare yake yahana kanshi sakat tsabar zumudi duk da cewa yana zullumin haduwarmu tunda yasan cewa fishi nakeyi dashi,Ammadai ya k'udure komadai menene yasan zan huce indai nadawo din.
Ranar da zandawo kuwa ai hana Harun sakat yayi tun safe yadameshi da kira dayake shine Wanda zai daukomu.
Nagama shirina tsaf haka inna tagama kintsamin duk abinda tasan zan buk'ata duk da umma da Abba sun gargadeta akan kadda taimin wata wahala daban amma ina saida ta hadamin kayan da ake raka mejego dasu da yawa hadda dan akuyanta ta yanka aka soyeminshi.
Dijee na hadama kayana sosai da wasu danabarma inna din da atanfofi kozata dinka hakama baba nabashi kudi sosai dan tuni ansaimin fili da kudin danasamu wajan haihuwa gakuma ragowa da inna tace sai azuba kiwo.
Anshiryasu cikin kayan sanyi sabida iskar mota yaran sunyi wayau fiye da tunanin me karatu har wasa sunsani dan sunfara dariya sunyi wata irin kiba kamar sunyi watanni hudu ko biyar nan ko watansu biyu da yan kwanaki kawai.
Jinai kamar insaka ihu lokacinda harun ya iso,inna ta tarbeshi sosai saida ya huta sannan ya shirya kayanmu cikin motar har baya dole saidai wajan zamana ya kasance gaban motar dan sosai kayan sunyi yawa waifa damma narage sosai nace abawa mabukata.
Rungumar yaran yayi yanata murna da santin yanda suka koma ko wannensu idanunsu k'yar tsabar wayau sai dariya yakeyi dajin dadin ganin yaran balle dayaimusu wasa yaga sunyi dariya.
Kallona yayi yana dariya gaskiya madam haidar yaimiki wayau yo ai naga babu ta inda yarannan sukaimiki kara ta dauko wani kamanni naki kin lura da hakan kuwa?
Nidai murmushi kawai nayi,Dan ni kaina ina mamakin irin kamannin yaran da mahaifinsu.
Saida yaima inna kyauta ta girma sannan mukabar garin bakori munbar inna da sharar hawaye bata taba tunanin zanjawomata arziki irin hakaba,Saigashi dabata haihuba Allah yabatani kuma tanajin dadi.
****
Tafiya tayi nisa na sakasu cikin hijab sabida iska amma yarannan sukace ba hakaba saima uban ihun da suka sakamin lokacin guda gashi nasaba da inna na temakamin aduk lokacinda suka fara rikici.
Jinai kamar insakamusu kuka lokacin dole saidai ya faka motar ya rikemin daya sannan naba na hannuna nono saida ya barci sannan na lallaba na kwantar dashi ajikina na amshi na hannunshi,Kusan atare muka sauke ajiyar zuciya nida Harun din lokacinda yaran sukai barci kamin yacemin "Sannu da k'okari madam Allah yasa masu jin kammune!
Da murmushi na amsa da ameen ya Allah sannan yacigaba da tafiya jefi jefi muke fira kusanma duk firar matarshine datake fama dalaulayi yanzu.
Muje katsina
[4/2, 3:09 PM] Re@l💍 K@usy🌹: Rumana 54
Saida ya mula dan kanshi sannan ya furta"Amma umma dan Allah tun yanzu za'a fara batamusu cimarsu? Tunda tanada wadataccen nono jikinta abarsumana har zuwa ko watanni shiddane ko?
Wani kallon banza taimishi kamin tace sannu ubana' To bari kaji insha Allah nanda wata shida summa kama abincin gaske danhaka kaje ka tasota tazo ta sallamesu kaikuma ka fice nemo madara kamin ranka yabaci kaji ko?
Bakinshi ya turo gaba yana nanata kai umma.
Tarairayoni jikinshi yayi yana tashina,Idanuna da sukai ja kuma sun kankance na saukesu akanshi,Ina yamutsa fuska dan wallahi nagaji fiye da yanda za a hasaso wannan fitina dame tai kama dan Allah?
Wata muryar tausayi yayi tare da cewa"Ga ruwa can na hadamiki kikuma gasa jikinki kuka sukeyi duk yunwa sukeji.
Naji dadin jikina sabida ruwan zafin daya ratsa jikina sannan na nufi falo dan can nakejin sautinshi Dana umma kamar dai fada take mishi.
Cikin mutunci muka gaisa sannan tabani Abdurrahman dan dama yafi korafi,Kamin wani lokaci yai luf jikina yana shan nonan,Ganin fuskarshi cidin cidin yasani kallon umma sainaga Ashe harararshi taketayi,Jinai kamar insaki dariya wlh.
Shima abdurrahim saida yasha sannan nasamu nima nacika cikina.
"Wai zaman me kakeyi haidar? Kobakaji abinda nagayamakaba kai banfasan shirme wlh.
Fuuuuu yatashi yabar falon kuma har umma takoma da yaran be fitoba.Zamana nayi falon dan wani irin tsoronshi naji inaji wallahi gaskiya ya iya mugunta,Kokuma dan hadda uban gyaran danasha ne oho dai amma dai naji jiki yanda ya kamata.
Tuni barci yafara surata saidai kamin yai nisa naji yai sama dani yana dariya,Lallai yarinya wato inacan ina jiranki kekuma kina nan zakiyi barci ko?
Banza nayi dashi dannaga alama soyake inbiyemishi ya halakani.
Kan gado ya kwantar dani tare da shigewa cikin jikina alokacin jinai kamar in yankashi in huta da saida yakuma biji biji dani sannan yai shirin fita office lokacin ko motsin kirki sainayi da gaske nake iyashi.
Sumbatar goshina yayi tare da cewa Allah yaimiki albarka ni zan wuce amma idan anyi sallar azahar zandawo insha Allah.
Kaina kawai nadagamishi,Sannan na maida na rufe bayan yabar dakin.Bansan lokacinda barci yai awongaba daniba dan inata tunanin farkon aurena da yanzu wanne nafishan wahala saidai bankaiga gano amsarba barci yai awon gaba dani.
Kai gaskiya umma ba k'aramin kaunata takeba wallahi ko girki haka ta hanani inyishi ayinin sannan ko yaran idan har ba kuka sukafaraba to bazata kawosuba,inko ta kawosun dasunsha nono take komawa dasu.
Tunda taga bezo da madararba bayan magriba kawai saita kyaleshi saidai ta kudurce dakanshi zai siyota idan yaji uwar bari.
Da dare.
Nagama sallar i'sha,I kenan saiga umma da yaran kuma gaidata nayi sannan nakoma na zauna muka fara hira domin yau koso daya banfitaba.
"Uhum kinga Ruma mijinki wani irin murdadden mutunne wallahi yau tunsafe nake fama dashi akan yasiyoma yarannan madara amma ya kiya kinga ko dawowa gidan ma beyiba kuma nasan hadda maganar danhaka amatsayinki na matarshi kuma saukinnan ke ake nemarmashi danhaka saiki dage wajan ganin fin fahimtar dashi tunda da gaske yake beson ahadama yaran wani Abu da nono yakasa fahimtar nono ba lallai ya wadatar dasuba tunda kullun wayau sukekuma yi indai baso akeyi aga kinata tsotsewaba danhaka yau zan barsu nan ku kwana tare dasu nasan idan suka hanashi rawar gaban hantsi zaisai abinyi kuma kice nace kadda akaimin su matukar kinga yanaso ya kaimin su kinji ko?
" To umma zanyi komai insha Allah.
Sallama taimin tabar falon tare da tambayata nako shanye tsumin dataimin?
Nidai amsawa nayi da eh amma kofi daya kawai nasha nazuba sauran cikin frij haka kawai intashama kaina abinda zai wahal dani.
Ina rungume dasu duk ajikina sunata wasansu ina biyemusu sosai yaran sukai wayau idanun nan kyar idan suna kallonka daga gani kasan zasuyi wayau na gasken gaske.
Da sallama ya shigo idanunshi na kanmu fuskarshi cike da walwala da farinciki.
Sannu da zuwa naimishi tare da tashi zaune shikuma yaran ya kwashe gabadaya daga jikina bayan na karbi kayan da yashigo dasu, Sosai yakemusu wasa suna bangale baki oh ni wai harsun San wasa🤔 Koda yake yaran yanzu da wayansu ake haihuwarsu.
Gefenshi na zauna ina ragemishi kayan dake jikinshi da safa da takalmin kafarshi dan babu abinda ya cire hasalima hankalinshi kacokan yanakan yaran.
Shigewa nai bedroom dinshi da kayan sannan na had'amishi ruwan wanka saida na d'aukomishi marasa nauyi wa inda zaisa inya fito sannan nakoma falon.
Dady ga ruwan wanka can,Kasancewar tun bayan Dana haihu haka nake kiranshi dady ko dadynsu dan banso sutaso suji ina kiran sunanshi.
Rungumoni yayi jikinshi yana murmushi"Babyna kinga yarannan dariyar da suke ko?
Nima murmushin nayi tare da nunamishi yaran da yatsana yanda suka zubamishi ido suna kallo ni tsoroma naji bazasuyi kiwaba dan da alama kallon sani zasufara daganan kuma sai kiwa.
Dakyar nasamu yatashi zuwa wankan kamin yadawo nagyara naman da yashigo dashi dan dama banyi girkiba.
Dawani kallon soyayya nabishi kai gaskiya dady karshene wajan kyau da gayu sai k'amshi yakeyi.
Kusan cin abincinma ashirice akayishi dan hankalinshi nakan yaranshi wa inda keta haurinshi da kafafunsu batare da sanin mesukeyiba,Shikuma hakan da sukeyine shine yakejin dadi.
Lokacin kwanciya nayi na shirya yaran na shayar dasu yana zaune dan kaddama sufara rigima yace laifinane danhaka agabanshi duk saida sukai taf dasu sannan na kwantar dasu atsakiyar gadon dadynsu ya kwanta farko nikuma k'arshe🤣.
Manyan idanunshi ya zubamin kamin yace"babyna yanaga haka? Yau bazasuje wajan umman bane?
Cikin alamun rashin damuwa nai shirin shiga wanka tare da cewa"Aiko yau tacemin bazasuje kwana wajantaba dan bata da abun basu.
Bece komaiba yaci gaba da jijjiagasu koda nafito wankan har sunyi barci abinsu kamar suyita barcin su Amma nasan anjima kadan labari zai canza.
Saida nagama jamishi rai sannan naje gareshi,Yaudin madai kamar koda yaushe yi yake kamar zai cinyeni tsabar zalama,Saidai yanayin gurnanin da yakeyi da uban nishin da yake saki gakuma sheshshekar kukan da nakesaki nima yasa yaran tashi kamin yasami nutsuwa.
Yanajin kukan yaran amma yakasa sakina har saida yasami nutsuwa,Mikewa yai dani kawai muka gyaro jikinmu kamin mudawo nacigaba da kula da yaran,Yanaso ko rungumeni yayi amma ina ko yaya ya motsa suma yaran saisun motsa.
Da asuba ma saida tafiya tai nisa sannan abdurrahim Yakama ihu dole saidai ya kyaleni ammafa beji dadiba dan sosai yaita jan tsaki.
[4/2, 3:09 PM] Re@l💍 K@usy🌹: Rumana 53
Wani farinciki ne naji ya lullubeni lokacinda na hangi mijina kuma uban yarana,Saidai tuni na gimtse fuskata karma yai tunanin naji dadin ganinshi dan har yanzu ina tuna maganar daya yabamin na inje in k'wada abuna in cinye danhaka sainagama wanashi akan hakan.
Tsakanin umma da Abba har rige rigen daukar yaran suke yayinda nikuma takaicin batani sukeba yasani turo bakina gaba cikin yanayi na shagwaba.
Ummace ta rungumoni jikinta tana dariya tare da cewa"ke Kyalemu munga jikoki mun manta da diya yi hakuri diyar albarka sannunku da hanya Harun!
Shigewa mukai bangaren umma cike da farinciki musamman Abba Wanda hakoranshi sunki rufuwa ganin yanda yaran sukai manya dasu kuma nono kawai sukesha.
Harun da haidar muka bari tsakar gidan duk wani Abu daya danganci tsaraba sai harun yayi wajan umma dashi sukuma kayanmu sai haidar ya nufi bangarenmu dasu jikinshi har rawa yakeyi tsabar murna da farinciki sannan gashi ya ganni nawani canza yasan ba k'aramin jin dadi zaiyi ba.
Kasancewar yanzu ban wasa da cikina shiyasa ina hutawa na lodi dadd'adan girkin umma sannan ta hadamin da lemon kankana Wanda yaji madara,Nadaisan da biyu akaimin wannan hadin.
Har karfe Tara na dare ina wajan umma yayinda oga harya gaji da lewa ya zauna hirar shima sai tsomoni cikin hirar yake nikuma ina basar dashi,Dan so nake yagane yaimin laifi ko yayane.
Umma tai musu wanka tare dayimusu shirin barci,Kasancewar nayi sallolina yasani cewa umma bari inje Indan watsa ruwa jikina duk ciwo yakeyi idan zaku kwanta sai inzo in karbesu.
Abbane ya amsa da shikenan ai saimungama hira zasuyi barci,Ya idasa maganar yana dariya kallo daya zakaimishi kasan yaufa yana cikin kwanciyar hankali da farinciki.
***
Sam Bambi ta kanshiba duk da yanda yaketa wani takalata da magana hasalima shigewata nayi bayi danyin wanka.
Saida na gama wankan sannan na fara lekenshi ta kofar makulli aiko can na hangeshi zaune bakin gado ya zubama kofar bayin ido.
Wani irin shegen murmushi