Showing 48001 words to 51000 words out of 61919 words

Chapter 17 - RUMANA BOOK COMPLETE BY MAMAN KHADY

22 Aug 2025

259


Zuwan inna da dije yamin dadi gaskiya,Sosai inna kemin wanka dantace bata yarda da kalar Wanda taga anaminba,Sannan tun randa tazo taima umma maganar tanaso idan anwatse suna ta wuce dani yanda zanyi jegona anatse Dan ita gaskiya bata yadda da wannan me idanun atsakar ka ba.




***


RANAR SUNA,Tsaywa fadin irin shagalin da akai bata lokacine nasan ku kanku masu karatu zaku iya hasaso yanda abubuwa suka kasance,Abba yasaki bakin aljihu fiye da yanda kuke tunani haka umma,Shiko oga ai babu magana,Gani yake zai iya bayar da dukkan abinda ya mallaka akan wa innan yara da Allah yabashi.
Sun sami suna Abdurrahaman da Abdurrahim,Kamar yadda Abba yaso Sabida shidai zabi yabawa iyayen nashi bayan yagama tambayata menakeso nikuma nabashi zabi.




Ranar suna da dare,Gidan ya rage mutane sosai saidai na nesa wa inda zasu wuce gobe, wata yarinya me suna fadila diyar k'anwar ummace dasukazo sunan daga Kaduna,Itace tashigo dakin da nake zaune da 'yan uwana wa inda suka sami zuwa sunan,Kusa dani ta matso kamin tace"aunty yaya na kiranki yana bangaren Abba yace kijemai da su Abdul Sabida rabonshi dasu tun asuba.


Fuskata na yamutse Dan gaskiya nagaji wallahi duk da nai wanka amma kaina harwani ciwo yakeyi.
[4/2, 3:09 PM] Re@l💍 K@usy🌹: Rumana 49




Dijee na kalla ina kauda fuska "Dan Allah kikaimishi yaran nan yagansu wallahi nagaji"


K'anwar mamana mesuna inna hasana itace tai magana cikin fada"Haba Ruma da hankalinki kuwa? Ya mutun nason ganin iyalinshi zaki nemi hanawa yanzu nanda gobe zai gankine balle ya nemi ganinki? Inace gobe idan Allah ya kaimu bakori zaki koma?
Dallah tashi ki gyara jikinki kije wajanshi,Gakidai da wayewarki amma sai bak'ar wauta.


Bakina na tunzuru inajin haushin fadan haka na mike nadan shafa turare sannan na dauki yaran wa inda keta barcinsu Sabida wanka dasuka sha. Dansuma sunsha dauka kamar me musamman wajan maza abokan Abbansu da Abba Sabida walimar da Abba ya shirya da yammacin ranar.

Aharabar gidan muka hade dashi dagashi sai farar jallabiya me gajeran hannu,Saiwani kamshi ke tashi jikinshi.
Abdulrahman ya karba hannuna kamin yai gaba nabi bayanshi batare damunyi magana da junaba.
Kwantar da yaron hannunshi yayi saman kujera tare da sumbatar kuncinshi sannan yazo ya amshi na hannuna shima ya kwantar dashi nidai kallon shi kawai nakeyi.
Rungumata yayi cikin jikinshi yana sauke numfashi tare da sauke ajiyar zuciya,Bakina ya laluba yafara tandarshi bansan lokacinda na fara tayashiba,Saida naji abun nashi na Neman wuce gona da iri sannan na rikeshi duk k'asa muka zube muna maida numfashi.

Idanunshi duk sunwani kankance,Saida muka huta sannan ya kalleni sosai yace"nakasa nutsuwa Ruma kewarku ta dameni yau,bansan wani hali zan kasanceba idan kukayi nesa dani,Banso wannan tafiyar takiba wallahi tunda komai anayi anan ma.


Jinai tausayinshi ya kamani danhaka cikin karya harshe alamun lallashi nafara magana"Ka kwantar da hankalinka tunda sunce hakan inaga idan mukai hakuri kamar yaune zakaga mundawo nikaina harnafara kewarka tun yanzu Allah"


Kuma matseni yayi jikinshi yana murmushin jin dadi kamin yace Allah da gaske babyna?


Hannuwana nake shafar jikinshi dasu kamin nace sosai ma nasan yarankama zasuyi missing dinka.


Ba k'aramar murza nasha wajanshiba sannan ya rakoni nadawo daki nidai lallabashi naitayi har muka rabu Dan na lura rikici kawai yake nema.


Kusan kwana mukai hira kunsandai yanda ake baje hajar hira idan an hadu da 'yan uwa,kusan hirar tamu duk na irin daular da Allah ya kawoni cikine,Musamman da hidimarnan tatashi Haidar yaimin akwati set daya na kayan lefena daban gakuma na haihuwa hakama yaran saida na cika gado da kayan arziki kala kala wa inda dangin umma Dana Abba suka kawo ga abokan Abban haka na haidar din ko Harun saida yayo akwati guda na kayan yara.
Kai abubuwan damuka samu gaskiya sai godiyar Allah.
Shinefa kowacce ke fadin albarkacin bakinta nidai dadi yagama kasheni Sabida farinciki harbansan kalar godiyar da zanyima Allah ba Sabida tako ina sai inga tayi kadan,Sai intuna lokacinda aketa Neman kai dani babu Wanda zai iya rikeni Sabida kawai kadda dawainiya ta karu ma mutun yau gani cikin wannan daula,Allah yabani miji me sona na nunawa asa'a ga surukai na gari, yaukuma ga yara har guda biyu kumafa duk nawa ne lallai Allah shine mabuwayi gagara misali.
K'ara rungumar yarana nayi jikina inajin kaunarsu cikin zuciyata kamar yadda nakejin mahaifinsu.
Nidai bansan sanda barci yai awon gaba daniba yo dama ga gajiya da hayaniya su Kansu anshasu.



** ** **




Tun safe muke kintse kintsen abinda yakamata intafi dashi ga soye soye Wanda damma Allah yasa 'yan uwana da yawansu sannan gana shi haidar sunkama aikin sosai yanda yakamata Dan bamazaka gane wa innena nawan ba.
Amma duk da haka sai bayan azahar sannan akagama shirya komai tuni yaran nawajan Abba ya rungume jikoki yanata gayamusu zaiyi kewarsu sosai da sosai yayinda umma ketamishi dariya Sabida tana tunanin ko abban ya mance da kwanakinsu aduniyane da yaketa musu magana.






Yana nanike jikina Dana motsa saiya bata fuska ni kunyama duk tagama kamani daga zuwa sallama kuma sai aga najima shiyasa inna saitaita fada wai indaina likemishi indai bawani cikin nake bukata da wuriba.
Cikin yanayi na shagwaba nace ya haidar lokacifa yana shigemana ko so kakeyi muyi dare yaranka suyi mura?


Sassauta rikon da yaimin yayi kamin yace"OK muje amma nidai gaskiya ankwareni wallahi dannasan bazan iya jurewaba.


Nidai lallabawa nayi mukai sallama duk da cewa shine da Harun zasu kaimu amotoci biyu sai guda daya da zatakaimana kayanmu,Nidai gudun surutun mutane motar harun nashige nida dijee sai matarshi dake gaba Sabida hadda ita za a rakiyarmu.
Har mota umma na nanata insha Allah sati nasama suna hanya zatazo ganin angwayenta.


Tafiyace mukayita mecike da farinciki da kwanciyar hankali ina rungume da abdulrahman itakuma dijee na rike da Abdurrahim hira mukeyi sosai wadda ta dauke hankalina daga tunanin oga dannasan yananan yacika yabatse banshiga motarshiba.




****






Zuciyata cike da zullumin inda inna zata saukeni Sabida nasan dakina Nada bawani girmane dashiba gakuma baki duk da bawani jimawa zasuyiba Sabida dare yariga yashiga.


Shida tayi lokacinda muka isa bakori, Abinda yabani mamaki shine ganin yanda aka gyara gidan gabadayanshi,Sannan dakin baba nan ne yakoma amatsayin nawa, dakin yasha gyara naban mamaki domin hatta gadon jarirai saida aka saka ga wajan kayansu da kuma kayana dakina saikace na gidan Abba.
Salla kawai sukayi suka juya ko sallama haidar be bari munyiba sabida be huceba.


Nidai nabisu da addua tunda nasan duk damuwarshi.


Suma dangina na maska alokacin suka wuce sabida dare.
Gida yakoma dagani sai inna da dijee itama tanagama tayani gyara kayan taimin sallama bayan nacikata da shatara ta arziki Dan sosai naji dadin zuwanta wajena wlh.


Saidama zamu kwantane sannan baba kemin bayanin ai haidarne yazo da masu aiki akayi wannan gyaran yau kwana uku kenan,Sannan kayan abinci babu kalar Wanda ba ajiyeba.
Nidai sainabishi da addua kawai Dan gaskiya haidar mutunne kuma yaimin halarci fiye da yanda nazatama.




Dagani har yaran kwanciyarmu mukayi Dan angaji gajiya duk ta bugar da kowa.





****






Ranar danayi sati guda agida saiga umma da Abba da uban gayyar domin shine ya kawosu.
Saiwani ciccin magani yakeyi sabida kawai takalen fada,Dama tun tafiyarshi saidai yakirani ya yaranshi danace lafiya lau shikenan saiya kashe.
Nidai bandamuba tunda nidai nasan bawani Abu naimishiba.


Suna rungume da yaran suna mamakin kuma wayansu kamarsu sai kuma fitowa takeyi da ubansu.
Inna kebasu labarin ai yanzu kukan dare sukeyi gabadayansu.


Dariya Abba keyi kamin yace to da alamadai basuson zama dake gidansu sukeso.


Duk dariya akai kiran sallar azahar yasasu barincikin gidan da baba Dan zuwa masallaci daganan su wuce gidan yayan Abban.



Saida nai wankana dayake da wuri inna kesamin ruwan shiyasama bancikayin na yammaba sabida sanyi, Sabanin wasu da zasuyi wankan jego amma sai bayan magriba ko daf da yinda sannan ashiga wankan.


Yaran barinsu nayi wajan inna tunda sun koshi nikuma idan nai salla in kwanta indanyi Dan yanzu sungane rikicin dare.


Ina cikin yin sallar naji sallamar haidar cikin dakin,Kirjina naji yai wata irin bugawa kamar yadda shima abangarenshi hakanne lissafin kwanakina da haihuwa yafara kamin yafara sakin wani munafikin murmushi.
[4/2, 3:09 PM] Re@l💍 K@usy🌹: Rumana 51




Kwance nake akan gadona yayinda na Dora abdurrahman saman cikina ina Dan jijjigashi sama sama yau yatashi da ciwon ciki shiyasa rigimarshi tai yawa.
Wayata dake gefe ta dauki ring babu wani jinkiri na dauka sabida nasan waye.
K"asa kasa nakumayi da muryata kamin na rangad'a sallama.


Wata ajiyar zuciya ya sauke kamin ya furta"Nayi kewarki babyna"


Cikin yanayi na lallashi na furta sorry!! Dadynsu ai munkusa dawowa gareka insha Allah danagama yawon Arba'in kamar yadda iyayenmu suka tsara ko?


"Hummm,Shine abinda ya furta kamin ya Dora da fadin" aikema haka kikeso kuma wallahi duk wannan wahalar danakesha saina famshe abuta akanki tunda kinaji kuma kinagani amma yanzu ko yaranama anhanani zuwa gani sabida kadda naimiki wani abu, Sabida anmaida Dan iska ko?


Muryata har rawa take na furta Dan Allah kayi hakuri haba mana kai yanzu shikenan haka zamu dingayi dakai kullun ka kira bazamu rabu cikin dadin raiba sabida fitina irin taka Dan Allah da wanne kakeso inji? Da kai kokuwa da yaranka ?

Tashi yai daga zaunen da yake cike da mamaki lallai Ruma tagama rainashi shi takema fada haka?
"Ke dakata kadda kimin shirme Dan kinga ina binki shine zaki nemi ki tainamin wayau ko? To bazan dauki rainiba idan kuma Dan wannan abun naki kike Neman ki wulakantani to ki rike abinki dan Allah karma ki dawo saiki kwada ki cinye.
Kashe wayar yayi yanajan dogon tsaki toma da wanne zaijine? Amma ai laifin dukna umma ne tamaidashi wani bunsuru ta toshe duk wata hanya dazaibi yaje ga iyalinshi gashi itama yanzu tana nema tafara biyemishi suyita masifar kullun.


Kwantar da yaron nayi gefena ganin yai barci sannan nasaka kuka,Sai yanzu nake kuma sanin halayen haidar,Ashe masifaffene na nunawa ataro ga bak'ar zuciya da fishi Wanda zamana dashi ba haka yakeminba amma yanzu kullun zai kira kuma bamu rabuwa lafiya hakan kuma bazai hana gobema ya kiraba ko bayan wasu awoyi,Narasa kalar lallashin da zanyimishi yaranshi su hanani sukuni da nutsuwa shima ya addabeni da fitinarshi ai shikenan saiku hadu ku kasheni ku huta kuma wallahi tunda kace in kwad'a abuna incinye zanga yanda zaka kuma rabarshi.


Jin sautin kukana ya shigo da inna goye take da abdurrahim Wanda yai barci abayanta.
Yaron dake gefena tafara dubawa taga barci yakeyi sannan ta kalleni "Ke rumana lafiyarki kuwa kike kuka haka kawai ko yauma fadan kukayi?


Kaina kawai na dagamata tare dayin wata sheshsheka.


Haba takama tana kallona kamin tafara sababi" To sakarya zauna kita kuka tunda kika ganin kukan shizai zama mafita agareki banda iskanci bance kidaina biyemishiba? Toma ai yayi hakuri yau kwananki arba'in harda uku lokacine daya kamata ace kin koma amma mahaifiyarshi ta rantse saikinyi kwanaki sittin kodan yara sukuma kwari to tunda anyi haka aisaikita lallabashi ki daina biyemishi tunda shima fitinannena amma inba hakaba duka menene akwana 60 Dan Allah?
Yanzu tashi ga wancan tsumin can yadansha iska ka kafa kai ki shanye anjima kadan Laminde zata aiko da ragowar caccabinki ki cinye Dan wallahi sainaimiki shiri sosai akan wancan sarkin zalamar,Gobema kaji zandafa miki dahuwar amare Dan idan bakiyi shirin gaskeba to inaga kina zuwa zaikimiki kwaf daya.


Gwanin kunya natashi nafice bayan Nagoya yaron abayana sabida yamma tayi.

Ni har mamakin irin gyaran da inna takemin nakeyi,Sabida ita gabadaya kallon fitina'u takema haidar.



Hada kayanshi yafara da niyyar tafiya gida dan dama cikin office yake yagama aiki yace bari yakira,Shi kanshi besan abinda ke tunzura zuciyarshi yanamin masifa ba.


Harun ne yashigo da sallama yanemi waje ya zauna yana kallon yanda haidar din duk yagama yamutsewa gawani uban tsaki dayake jerawa akai akai.


"Haidar wai meya farune duk ka yamutse haka? Cewar harun yana kafe haidar din da idanuwanshi.




Wani huci me zafi ya saki kamin ya kuma yamutsa fuska gamida lumshe idanunshi" Harun baby tafara rainani yanzu wallahi,Wai har ita zatacemin nacika fita nida yarana da wanne zataji!!!


Shima harun din numfashi ya sauke kamin yace gayamin dai meya faru?


"Ka ganene harun kewarta ta dameni wallahi ko barcin kirki bansamu inayi sosai,Ga umma ta rantse saitayi wata biyu sannan zata dawo gashi ta hanani zuwa ganin su dan Allah da wanne akeso inji? Itakuma kullun na kirata saita batamin rai sabida wulakanci kalar nata.




" Kaga haidar wannan duk ba abin damuwa baneba indai kasa kanka,Amma rumana bata da laifi gaskiya itama umma bazamuce tanada laifina dannasan akwai manufarta tayin hakan Amma dan Allah ka tausayama yarinyarnan itace abar tausayi yara biyufa haihuwar fari koda tsotsarsu aka barta ai aikine sannan inaji humaira tacemin basu barinta barcin dare sabida rigima yaukuma babban yatashi da ciwon ciki saida takaishi asbt kaikuma ka kirata ka rufeta da fada mezaisa zuciyarta bazata kuntataba harta gayamaka wata maganar daban?
Yakamata kaimata uzuri dan Allah yarinyace karamafa kuma nasan tunda umma tai wannan tsarin wallahi akwai zalamar daka nuna haka haka kawai amaido yarinya kakuma kunsamata wani ko hutawa bataiba.


Murmushi haidar din yayi yanajin yanda zuciyarshi ke kwanciya tare da tausayin rumanan to Amma meyasa shi batagayamishi yaron beda laifiya ba?Koda yake yasan laifinshine tunda betsayawa ya fahimceta.
Tare sukabar office din yana kuma lallashinya tare da nunamishi duka saura kwana nawa yanzu duk tsiyadai bazata kuma kwana ashirinba batare da tadawoba.




*** ***




Kwanana hamsin daidai muka nufi maska,Anan ne nazaga dangina na uwa Dana uba kowa sai nan nan yake dani,Yayinda 'yan uwana suketa k'aramin gata da kayan gyara irin namu na mutanen kauye.
[4/2, 3:09 PM] Re@l💍 K@usy🌹: Rumana 56




"Kinga tashi muje asbt yanzu in aunaki nan bani da abun awo ko daya tunda bankawo hakan nan kusaba.
Wani irin sanyi jikina yayi danhaka saida ya temakamin sannan na shirya yana gaba ina bayanshi ko umma bamuyima sallamaba inaga saidai taji tashin mota.
Kuka na dinga saki cikin motar shiko ai dif yayi jiyake ko kwarin lallashina bedashi.


Kai tsaye key din office dinshi yasa yabude yashiga sannan yafita ya nemo abinda hake bukata yau babu wani cikowa ko likitoci tunda yau asabar,Danhaka anace yaimin komai cikin hukunci na lillahi saiga ciki harna sati biyar.


Zaman dirshan nayi gabanshi na bude bakina gaba daya ina kuka hadda murza k'afafuna Dan Allah yasani nagama rudewa da tashin hankali.


Rungumoni yayi jikinshi yana rufemin baki,Amma ina fisgewa nake kokarin yi Dan inyi kukana sosai.


" Wai kiyi shiru mana ko kina tunanin kukan zai samar da mafita ne nace kiyi shiru amma sai kuma bude baki kikeyi saikace su Abdul"


"Nidai koma menene wallahi bazan yaddaba kaga babu Wanda yasa dashi ka temaka ka zubarmin kamin asani Dan Allah.
Bedece komaiba yana rungume dani Saima tunani daya tsunduma yasan tabbas abun zaimin yawa ga shayarwa ga ciki sannan ga dawainiyarshi danshi kanshi yana jinjinama k'okarin danakeyi wajan daukar lalurarshi domin shi kanshi saidaga baya ya tantance kalarshi,Yasan ina kokari dashi sosai tunda ban gudunshi duk wuya saidai idan nagaji inyimishi kuka,Da kuma ya lallasheni shikenan.
To Amma idan yace zai zubar da cikinnan yana hango tashin hankalin da Abba zai sasu ciki bama wannanba idan kuma garinzubar da cikin matsala tataso sai yace me? Kai akwaidai matsala.


Allurar tsayar da amai yaimin yace intashi muje gida, Tuni na daina kukan Dan tunanina Allurar zubar da ciki yaimin.


Ajiyar zuciya naketa saukewa cikin motar yayinda shikuma yake kallona akai akai Sabida tare dajin tausayina.
" Akwai abinda kike buk'atane in tsaya insaimiki?


Kaina na girgizamishi kawai batare danai maganaba.


Umma taso ta fahimci akwai matsala amma dayake uwace ta gari Sam bata matsamanaba saima yaran datahana suzo su damemu.


Bunu-Bunu zanje induba jikina amma babu jini babu alamarshi saima tashin zuciya daya addabeni,Shidai yana kallona amma koso daya bemin maganaba.


Haka na yini cikin kunci da damuwa awannan rana Wanda shima rashin walwalata yanashi sukuni.


Da dare bayan nagama shayar da yaran ya kwashesu ya kaima Umma,Lokacinne takasa hakuri ta tambayeshi"Haidar mekaima rumah yau gaba daya bata cikin walwala?


Miyau ya hadiye kamin yace "Umma mundan sami sabanine amma nabata hakuri.


" To shikenan Allah ya kiyaye gaba Dan Allah ka dinga hakuri

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login