Showing 33001 words to 36000 words out of 61919 words

Chapter 12 - RUMANA BOOK COMPLETE BY MAMAN KHADY

22 Aug 2025

268

Ko motsin labule tagani sai gabanta ya buga Sabida tashin hankali tasan cewa tabbas Alhaji be iya fishiba balle irin wannan tasan shirunshi bazai taba zama alkhairiba agareta.
Amma addua daya takeyi Allah yasa kadda ya haramtamata zama dashi.






****************


Ya dade yana mamakin abunda yagani yau lallai wasu matan basu da tunani yanzu Sabida Allah inda yake shiga nan take niyyar ta tura yaronta Wanda bashi cikin hayyacinshi gashinan tatasomai da masifa besan ya matarshi zatai dashiba yanda yake cikin wannan mugun yanayi.


Tun cikin daren yayanke hukunci akanta danhaka jiran wayewar gari kawai yake.


Saida yagama kintsawa sannan ya nufi bangarenta lokacin shadaya nasafe yakusa ma.



Tana ganinshi ta rarrafa gabanshi tana kuka"Ka dubi girman Allah Alhaji kaimin afuwa wallahi na tuba sharrin shaidanne bantabayiba yauma kuskurene.


Bakinshi yatabe kamin yace"Amma baki da tunani bilki inkamaki zakiyima yarona fyade Wanda bashi cikin hayyacinshi sannan ki dinga tunanin wai zan iya cigaba da zama dake? Kema kinso kanki danhaka gashinan dama akwai saki daya tsakaninmu ga biyun na idasa miki kiyi gaggawar barina inba hakaba zntonamiki asiri kowa yasan mugun halinki,Awa uku kadai nabaki.




Kai tsaye bangarenmu ya nufa domin ganin ya muka kwana sannan wayarshi akunne yana kiran umma,Domin yasan awannan matakin itace kawai zata iya kwantarmishi da hankali.


Wani irin mummunan tashin hankali ya shiga lokacinda yaji sheshshekar kukana tindaga falo.
[4/2, 11:15 AM] Re@l💍 K@usy🌹: Rumana 25




Farinciki ya cika Abba yanda yaketa sakin murmushi yana shafar kan haidar.
Shidai haidar yana like kusa dani ko muskutawa nayi shima saiya gyara yakuma komawa jikina danma na hadu da surukai wa yayyu domin Sam bazakace ma suna kallonaba,Amma nidai inajin kunya gaskiya.




Zakuyi mamaki idan kukaga yanda ake jifan juna da kallon love tsakanin Abba da umma, Gaskiya sundace da juna sosai domin shima abban bawani manyanta yayiba sabida kudi, kunsan kudi sukan boye tsufan mutun.

Anan duk mukaci abincin dare,Anayi ana hira,Nikaina nasami nutsuwa da kwanciyar hankali ganin umma wlh sosai nakejin dadin yanda take kulawa dani bunu-bunu zata kamo hannuna ta rike.


Bayan sallar isha'i Abba yace Rumana tashi kuje ku kwanta tunda kunyi sallah.


Dan bata fuska nayi kamin ince Abba sai anjima banjin barcin yanzu.


"A a rumana kuje kodan wannan mijin naki kinga zakimai amfani da magunguna kamin ku kwanta din.


Cikin shagwaba na tunzuro bakina kamin in mike tsaye aiko ina mikewa shima ya mike harwani cimin diddige yakeyi.
Da dariya sukabimu kamin Harun shima yatashi yabimu mukai sallama.






**********


Ina rufe dakin yafara cire kayan jikinshi yana wurgarwar kasa idanuna nabishi dashi kamin ince kaf lallaima ya haidar ka raini to yau bazanyi maka wankaba saidai ka kwanta haka.


Cikin shagwaba ya turomin bakinshi bakinshi yana motsi kamar yanaso yai magana.
Da sauri na matsa kusa dashi tare da rikemai hannu ina kallon idanunshi ya haidar kafarajin magana ne?
Kana gane abinda abinda nake fada yanzu ko?
Gajeran wandonshi yake kiciniyar cirewa na rike,Waikai nace bazanyimaka wankaba ai bakai daud'a ba.


Bedeyi maganaba amma bakinnan nashi adane da alama shima ya iya rigimar.


Dole nashiga na hadamishi ruwan wankan na cudashi inamai wankan amma yana tabe tabe ajikina duk bigewar da nakemai besa yabariba har saida ya jikemin jiki.


Ina fitar dashi nasamu nima na watso ruwan,Tawul din na daure sosai ajikina gudun kadda ya kuccemin, Sannan nafara shafamai maganin da ake shafawa idan za a kwanta,Sabida naga jikinshi yai laushi da yawa kadda yai barci kamin ingama shiryawa.


Idanunshi arufe harna gama murzamishi sannan na yunkura zantashi yawani jawoni jikinshi yana
[4/2, 11:15 AM] Re@l💍 K@usy🌹: RUMANA 23



Besan lokacinda yafara addu'ar Allah yasa ba yaga diyar mutane yayiba Allah kada kabashi ikon kusan marainiyarka harsaika dawo dashi cikin hayyacinshi.


Zaune ya ganni na hada kai da guiwa ina kuka shima haidar din na gefena Amma hankalinshi yai mummunan tashi sai wuki wuki yake da ido gashi yarasa yanda zai temakamin.


Subhanillahi sannu yanke hannu kikai?
Sannu sawo hijab dinki muje agyara wajan koda yake bari nakira Harun idan yana kusa saiyazo ya gyaramiki hannun sannu,To garin yaya hakan ta faru ma kodai shine ya yankeki?
Kallon haidar nai Wanda yai tsumu tsumu duk beji dadin ganina hakaba sannan na kauda kaina gefe,Batare danayi maganaba.
"Karamin tsaki abban yaja kamin yace ainasan bazai wuce shidinba,Amma haidar yakamata ka rangwantama yarinyar nan haba duk irin wahalar da takesha Akanka be isaba saika dinga raunatata yanzu daka yanke hannunta dame zata dinga kula dakai kamar yadda ta saba?
Matsawa yayi jikina tare da shigewa jikina ya daina kallon Abban.


Murmushi nayi shima Abban gwanin farinciki fuakarshi yace Ummu Rumana kinga haidar ko? To koyafara fahimtar me akace ne?

Da murmushi afuskata nace kila,Amma bashine ya yankeniba naje hadomana abin karine shine ya dauki wukar garin in amshe shine na yanzu hannu.
To Allah ya sawake bari inje indawo so nake intabo ummanku inji idan bazata dawoba inaga kuma binta zanyi nikaina hankalina yafi kwanciya idan inaganinta kusa daku,Ki kuma hakuri kinji Allah yaimuku albarka.


Ina cikin bashi tea Harun yashigo da sallama.
Hijab din jikina na maida sannan muka gaisa hannuwan haidar yaso rikewa Amma yawani lafe jikina saikace yaro me kiwa.
Dariya mukayi kamin ince ai dazuma Abba namishi fada boyewa yayi jikina.

"Ah Alhamdulillah inaga yafara fahimtar me ake nufi Allah dai yabashi lafiya kuma yaimishi sakayya nasan haidar beda matsala da kowa wacce ta cancanci ai mishi irin wannan azabar,Amma ai Allah baya barci da sannu zamuga sakayya ga macuta.




Dakanshi ya gyaramin hannun bama wata yankace me yawaba jinin daya zuba sosaine yasa nai tunanin babbace.


Gyara zamanshi yayi kamin yacemin Amarya meya farune naga can bangaren hajiya bilkisu ana kwashe kaya ko wani abune yafaru gidan?


Idanuna na fiddo waje kamin ince kai haba dai? To wallahi ban saniba Allah dai yasa lafiya.




*********


Kwance nake saman doguwar kujera ina kallo idanuna lumshe domin tuni nai nisa da tunanin yanda zamu kasance idan yasami sauki tunda gaskiya yanzu inajin tsoron samun saukinshi banso inrabu dashi wallahi ina sonshi nasaba daduk halin dayake ciki,Ina matukar bukatar son zama dashi.
Jin anayimin waiwayi akafa yasani kallonshi yana zaune da manyan idanunshi daya zubomin kai gaskiya haidar ya hadu wallahi.
Lokaci guda na k'aremishi kallo INA mamakin yanda 'yan kwanakinnan yake kuma wani murjewa fatarshi harwani sulbi take sannan sajen fuskarshi yakuma yin lumf harwani sheki yakeyi.




Wani murmushi me kyau na sakarmishi kamin in janye jikina in koma jikinshi,ina rikeshi yana lumshe ido,Hannuna nasaka cikin rigarshi daidai cibiyarshi ina wasa da yatsana ciki.
Wata Ajiyar zuciya ya sauke tare da sakin numfashi har wani k'ara dannmin kaina yakeyi lokacinda yaji ina saka harshena ciki.


Hannunshi yake niyyar sakawa cikin rigata mukaji an banko kofar domin dama ban rufetaba.
Da sauri na mike,Ina kallon kofar,Nafeesa ce tashigo ranta bace.


Kauda kaina nayi ga barin kallonta naja wani tsaki danni gaskiya haushinta nakeji yanzu musamman datacemin da haidar yaji sauki zai sakeni ita ya aureta,Maganar nan fa ta tsayamin arai.


"Banza sakarya Mara zuciya anyimata kora da hali amma taki tafiya saikace akuya.
Murmushi nayi kamin ince uhum sannunki fa wama kike da suna? To bari kiji ingayamiki har yanzu banga Wanda kemin kora da halinba balle inyi zuciya in tafi amma kema ai inaga kinyi shige da akuyar tunda gashi kinzo gidan da bana ubankiba kin zauna kuma kin kasa tafiya.
Tashi nai nayi tafiyata daki nabar haidar din shima Dan wani irin haushinya naji.


Kwanciyata nai agado ina sauke nunfashi.

Afalon kuma tanaganin nabar falon itama tafice da sauri shikuma mamaki ya kasheshi domin Sam yama manta dawata nafeesa.
Haushi ya kamashi ganin yafarajin dadinshi tazo ta yankemishi.






Bayan sati biyu
[4/2, 11:15 AM] Re@l💍 K@usy🌹: Rumana 19






Fatima kidubi
girman Allah da soyayyar da kikeyima Annabin rahma kizo mukoma gida tare insha Allahu b azaki kuma ganin abinda beyimikiba wallahi zan kiyaye Dan Allah.
Abbane yai maganar cike da roko domin yau tunda suka tashi yakejin hankalinshi yayi Nigeria sannan yasan koyaje hankalinshi bazai kwantaba tunda dai ita tana nan musamman yanzu dayasami kanta.


"Naji zan dawo amma gaskiya batare dakaiba kayi gaba nan da sati biyu lokacin nagama shiryawa saina biyoka tunda kaga ko asbt danake aiki dole sainayi da gaske sannan subarni.


" cikin farin ciki yace eh naji babu komai indai zaki dawodin bari intashi in shirya hankalina yanakan yarannan kinsan tunda haidar yafara ciwonnan ban iya koyin sati daya awata tafiya amma gashi yau kwanana goma.


Itadai da ido tabishi tanason mijinta matsalar matanshi ke damunta domin tasan shi zato beda kyau amusulunci amma tana zaton sune silar ciwon haidar musamman intai la'akari da irin wulakancin dasukasha nunamata tare da nanata saidai itama tarasa kamar yadda suma basu da yaran.
Tana zaune harya gama kintsawa ya fito da kanta ta rakashi saida taga tashin jirginsu sannan takoma gidanta cike da kewa sai yanzu tafara tunanin komawa gida kodan taya surukarta kula da tilon danta.








Yana kwance saman doguwar kujera amma kanshi yanakan cinyata da alama barci yakesonyi domin yanzu beda aiki saina barci,Kanshi nake shafawa ahankali tare da sosamishi kunnenshi.


Kasancewar ban rufe kofar ba kawai saidai naji anturo kofar.
Kaina na daga sainaga nafisa tuni ta samarma kanta wajan zama.
Kauda kaina nai ga barin kallonta Dan kaddama tau tunanin zan iya tsayawa sauraranta.
"Mutun banza abanza kawai kai ba kowan kowaba amma kazo kawani share duwaiwai gidan mutane.


Nidai banza nai da ita tunda dama ita arziki be shigo da ita nan saidai tsiya.
Wajan kakafun haidar din takoma ta fara shafar tafun kafanshi tana wayyo my sweety Allah yabaka lafiya musha soyayyarmu lokacin wasu andade da komawa gidan iyaye makwadaita.


Motsi yafara kamar zaitashi danhaka saina kalleta kidaina tabashi kadda yatashi sabida bejin dadin jikinshi.


Wani tsaki taja kamin tace " kedin banza harkin isa yimin iyaka da mijina kodan kinga nabaki dama to bari kiji zamanki dashi na lokacine idan yau naga dama tabbas zanzama matarshi kuma kisani zamana matarshi daidai yake da barin gidannan.


Kamin nai magana sainaga ya bude idanunshi fes akanta dake wajan kafafunshi tana shafarshi,Bata fuska yayi domin besanbata, Kamin muyi wani tunani yaimata wani mugun harbi Wanda yasata hantsilawa k'asa.
Da sauri na na mike zan gudu amma kamin inmike din ya hardoni kanshi wani karo muka gabza dashi na saki ihu,Da gudu tabar falon ko waiwaye niko komawa yai jikina ya kwanta batare da wata damuwaba.


Hawaye na share kamin nace ammadai Allah ya tsinemiki nafisa yaushe rabon da yai bugu amma zakijamin masifa ina zaman zamana.Hannunshi yafara kokarin sakamin cikin Riga jinai kamar in wurgashi gefe wallahi,Amma tsoro yasa na rabu dashi danbansan ko masu bugun na kusaba.
Yajima sosai sannan barcin yaigaba dashi Niko na lallaba nabar falon ma.




Da yamma likis ina zaune INA tsifa shikuma yana gefena dana daga hammata ta saiya saka hannu nikuma sai in kyalkyale da dariya danni Sam banson cakulkuli.
Jin ana kwankwasawa yasani mikewa ina dariya shima yana biye dani.


Yeee Abba oyoyo sannu da zuwa.
Da farinciki ya amsa kamin yashigo yana Alhamdulillahi nasameku lafiya ko?Koda yake ga alama ma nagani.


Hannuwan haidar din ya rike yana fadin hello son ya kk ya jikinka?

Kwace hannuwanshi yayi yakoma jikina ya lafe yana leken abban.


Mungaisa sosai kamin kamin abban yaimana sallama akan zaije ya huta amma zuwa dare zaishigo saiyaimin albishir sannan yatahomana da tsaraba.
[4/2, 11:15 AM] Re@l💍 K@usy🌹: RUMANA 21








Innalillahi wa
inna ilaihirraji'un ikon Allah waye nan kuma?
Malam yai tambayar zuciyarshi cike da tunanin wane tantirine haka da tsakar daren nan.
Ganin babu amsa saima kuma haskesu da akeyi da tocila me hasken masifa,Sai kawai malam yacigaba da watsa ruwan addu'ar yayinda Abba ya kasa hankalinshi waje biyu nan wajan malam din da kuma son gane ko waye ya dallaresu da haskennan.


Saida malam ya tone waje uku sannan aka kashe abinda suke hasashen tocilace.Ajiyar zuciya abban ya sauke zuciyarshi tacika da damuwa kenan da cikin sihiri suke kwana kenan.


Tsakanin shida malam din babu Wanda ya runtsa,Shidai malam addua yaketa shararawa yayinda shikuma Abba yaketa nafilfili Sabida yanda yakejin wani irin tsukewar zuciya.



*************


Sai asuba na motsa bansan abinda ya rafkemin jikiba saidai ina juyawa najini jikinshi sannan harwani huci yakeyi Sabida zafin zazzabi.


Da sauri na mike tsaye ina nanata innalillahi waikai yanzu baka da aiki saina zazzabine? Duka yaushe kayi zazzabin da yanzuma zaikuma rufeka?
Tashinai na nufi toilet inata mita nikadai shiko sai lumshe ido yakeyi daga gani bejin dadin jikinshi.


Saida nai sallah sannan na gogemishi jikinshi,Idanunshi sunyi jajir jijiyon kanshi duk sun tashi Allah sarki!!Allah ka kawowa wannan bawa naka sauki hakika haidar yanajin jiki wlh.
Saida naga yakoma barci sannan nima naraba gefenshi na kwanta idanuna akanshi jinake kamar inciremishi ciwon jikinshi ya huta koda nawani Dan lokacine.


Bansan barcina yai nisaba saida naji wayata nata ring koda na duba ai goma nasafe ya wuce.
Da sauri na mike ina salati kallon haidar nayi sainaga idanunshi biyu hasalima kallona yakeyi.
Murmushi naimishi kamin ince sannu yayana Aliyu haidar Allah yabaka lafiya me dorewa bari inbude kofa inzo inyimaka wanka.
Sam ban lura da yanda yake bina da kallon mamakiba da nakasa fita.


Wanka!wanka ya dinga nanatawa aranshi kamin yace ammadai wannan yarinyar ta rainani nizataima wanka toma wacece ita?
Kai dole tsayawa zaiyi yaga iyakar gudun ruwanta.


Yana nan kwance asheme naje na budema Abba da malam kofar sannan nadawo cikin dakin.
Bina yai da kallo kamar yadda nima nake kallonshi,Saida nagama hada ruwan wankan sannan nadawo wajanshi taso ya haidar muje ga Abba can na jiranka.


Biyoni yayi kamar yadda yasaba ammafa tsabar mamaki kamar zaiyime.
Manyan idanunshi ya fiddo ganin na kwalemishi kayan jikinshi ina cudashi kamar wani baby.
Wata ashariya ya lailayo ammafa cikin zuciyarshi lallai akwai bala'i wajannan shikenan tagama kallemin sirri.
Da kaina na dauramishi alwala domin yanzu koda yaushe da alwala nake barinshi.


Shafamishi mai nayi bayan nagama gogemishi jikinshi,Saibina da kallo yakeyi nikuwa bamatashi nakeba sauri kawai nake nagama shiryashi in tadda Abba da malam dake jiranmu afalo.
Dakyar nasamu yasaka wandon yau da alama beso,Da lallashi da komai nasamu nasakamishi saikace irin babyn nan.
Cikin zuciyarshi dariya kawai yakeyi yana kallon ikon Allah.


Hannunshi na rike sai gaban malam sannan na gaidashi nakoma gefe.
Kan haidar malam ya dafa yacigaba da zubomishi addu'ah Abba na amsawa da amin nima amsawar nake cikin zuciyata.

Karku damu insha Allah komai yakusa zuwa karshe babu sauran wani abu jikinshi saidai adage Dana Neman tsari kuma domin duk Wanda yai wancan to lallai daya fahimci jikinshi yafara kyau zaikumayin wani.
"To shikenan malam insha Allah zamu kiyaye sannan yanzu saika tunama ita rumana yanda zataimai amfani da wa innan daka kawo din,Cewar Abba Wanda farinciki ya lullube musamman yau dayaga yaron nashi yafi ko yaushe nutsuwa.


Manyan idanunshi ya lumshe mamaki yana dawainiya dashi towai meya sameshi hakane kamar Wanda yatashi daga ciwon makanta ko hauka.Dam kirjinshi ya buga da kalmar hauka ta diromishi,Shiko bazai tambayaba zaicigaba da shirun nan harya fahimci komai to Amma ina ummanshi?
Tambaya Mara amsa kenan.


Tashi nai na nufi kitchen domin hadomai tea sukuma sukaci gaba da tattaunawa akan matsalar kusan anan yafara fahimtar lalurar data sameshi.
Innalillahi yaitaja cikin zuciyarshi atsorace yake sosai.


" Amma malam maganar maganarshi har yanzu shiru?Cewar Abba Wanda yakatse Dan shirun da akayi na wucin gadi.


"Karka damu alhaji idan Allah yaso komai zai warware ahankali ahankali kasan ciwone ke shiga faraddaya amma waraka sai ahankali.


Tea din na ajiye gabana kamin in matsa kusa da haidar din Dan har lokacin yana gaban malam zaune.
Zokasha tea din kamin inyi girki,Ganin ko motsi beyiba yasa naja hannunshi muka matsa nan da nan ya shanye tea din kamin ya nemi kusa dani ya kwanta.


Sallamar Harun tasa duk muka kalli kofar muna amsawa.
Saida duk muka gaisa sannan ya matsa wajan haidar ya shafi kanshi kai oga barki zakai da safennan,Amarya ya wannan megidan naki?
Murmushi nayi kamin nace Alhamdulillah jiya bakazoba?
Eh wlh tunda na aje malam saina wuce aigashi yanzu zan maidashi.


" Kaima Ai kana kokari Haruna Allah yaimaka albarka yabawa abokinka lafiya lallai kacika aboki nagari,Cewar malam liman.


Abba saida yacika malam da shatara ta arziki sannan yasa Harun ya maidashi maska.



********






Tagama shirinta tsaf daduk wani Abu zatasan zatayi zagaye kawai take takosa dare yayi sosai ta aiwatar da nufinta domin wannan karan ta rantse saita dandani kalar zumar haidar.


Saida nagama shiryashi kamar yadda nasaba sannan ya kwanta nima kwanciya nayi gefenshi ina yimishi addua kamar yadda nasaba.


Yauwa yayana na kaina kai kwanciyarka nan Dan Allah inje in gyara jikina sai inzo mu kwanta kaga jikina yana baci bakaga duk yau fashin sallah nakeba? To abunmu na mata nakeyi danhaka kai kwanciyarka inje

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login