Showing 6001 words to 9000 words out of 61919 words

Chapter 3 - RUMANA BOOK COMPLETE BY MAMAN KHADY

22 Aug 2025

262

tace.


''Naji zan fita daga rayuwarka gaba d'aya ba gidan kaba ma, amman dan girman Allah ka barni da yarona kaga dai halin da yake ciki babu kuma wanda zai kulamin dashi kamar yadda zai samu agareni, dan Allah kaimin wannan alfarmar kaji Alhaji.''

Alokacin kallon banza ya bita dashi kafin yace mata.


''Wallahi koda mutuwa nayi yaro na ba zai koma hannunki ba ballenta ina raye.''


Sautin kukanta ya dinga ji akunnuwan shi kamar alokacin ne take yi masa kukan. Hawayen idanunshi ya share kamin yace a fili.


''Allah ka kawo min mafita.''


Yana cikin wannan halin yana tufka da warwara saiga matarshi ta shigo, Hajiya bilkisu,Idanunshi ya lumshe bayan yai mata kallo guda.

"Alhaji barka da wannan lokacin?''

"Yauwa sannunki da gida.'' Cikin yanayi na kwarkwasa da iyayi tace dashi.


"Alhaji dama cewa nayi ko Haidar yaci abincinsa kuwa?'' Kallonta yayi kamar yana son gano wani abu a fuskarta sannan yace.


"Na bashi tun d'azu harma Dr. yai mishi allurar shi yayi bacci, amma wallahi hajiya kun bani mamaki matuja wallahi, ace wai idan bana gida a cikin ku babu wacce zata iya kula da gudan jinina ko? amma idan anyi magana kuce wai kuna sona ta yaya zan yadda bayan kun bar gudan jinina babu kulawarku? ai shikenan na gode lalurace dai kuma Allah zai iya jarabtar kowa.'' Harara ta bishi da ita bayan ya wuce tana cewa.

''Allah ya kyauta naba wannan katon saurayin abinci a baki balle ai maganar wankin kazantar shi, Allah ya tsare ni dama ka samu nake ta yi maka addu'a Allah yasa ya mutu kowa yama ya huta.'' Fuuu ta tashi tabar falon ta nufi b'angaren ta tana ta faman sababi a cikin zuciyar ta.


Gefen Haidar d'in ya rab'a ya kwanta har lokacin tunani nukurkusar zuciyar shi yake yi wanda har wani zafi-zafi yakeji daga cikin zuciyar shi ya rasa wane kalar ciwo ne wannan da duk wata k'asa da take takama da manyan asibitoci da likitoci ya kai shi amma a banza babu wani cigaba da aka tab'a samu ballantana ace ai an gano abinda yake damunsa ko kuma ace da sauki.

Zubawa fuskar Haidar d'in ido yayi yana kallon yanda yake ta baccin shi haka kamar mai lafiya amma yana tashi shikenan kuma wannan nutsuwar duk zata kama gabanta.


Wani tuna nine ya fad'o mishi, nan da nan ya mike addu'a ya tofawa Haidar d'in sannan yabar gidan bayan ya kuma duba d'akin ya tabbatar da cewa babu wani abu da zai iya zama makami a gareshi.


Kai tsaye wajan wani abokin shi ya wuce dake can wata unguwar daban, ya koyi sa'a domin yana zuwa ya ganshi ya fito da mota da alama shima fita zai yi. Da dariya ya fito daga cikin motar yana yi tare da cewa.


"Abban Haidar baka kirani ba sai dai kawai na ganka? da ka tarar da bana nan ai da kaji babu dad'i.''


Kai tsaye cikin falon mutumin suka wuce, hira suke yi sosai cike da kaunar juna daga gani abokai ne na gaske. Sai da ya huta kafin yace.


"Wato alhaji aminu akan maganar Haidar ce na dawo gareka domin tabbas na fara lura da abinda kake gaya min game da matana, tabbas sud'in ba masu kaunata bane, toh amma kasan hidima irin wannan tunda har ba kama su nayi dumu-dumu ba bazai yiwu na titsayesuba da zargin.''


"Haka ne alhaji Yusuf shi yasa ai tun farko nace maka kafara bincike tukunna, domin ni wallahi ban yarda dasu ba gaba d'aya dan son duniya ya gama rufe musu ido, nasan zasu iya aikata komai, toh amma yanzu me kake tunanin yi?''


"To nidai a tunanin da nayi cewa nayi inda zan sami wanda zai kular min dashi tsakani da Allah to hankalina zaifi kwanciya tunda kaga yanayin kasuwancina bana zama bane yau bana wannan kasar gobe bana waccan kaga sai hankalina ya tsaya waje d'aya amma wallahi dana tafi hankalina rabuwa biyu yake yi shi yasa kaga bana iya jimawa yanzu duk inda naje zan kokarta na dawo da wuri.''


"Eh wannan gaskiya ne, toh amma alhaji aikin ne da wahala wallahi shi yasa duk wanda aka nema sai ya zille musamman daya kasance yana duka wani lokacin, toh da nayi tunanin ko aure zai zama maslaha agare shi musamman danaji kace kana ganin yanayin tashin sha'awarshi wani lokacin to inda matsalar take matar da zata aure shi din...!''


Duk shiru sukai na wani lokaci kowa da tunanin da yake sak'awa cikin ranshi, kafin alhaji Aminun ya kuma gyara zama yana cewa.


"Amma ka koma gidan su Fatima kuwa?''


"Eh wallahi na koma amma babu wani bayani wai tama koma wajan kanin mahaifinta dake zaune a kasar India harta koma makaranta.''


"kai Abu beyi kyauba wallahi kaga inda tana nan ai da duk ba'a yi wannan doguwar wahalar ba, toh amman duk da haka zancigita kaima saika cigita, ammafa namiji za'a samu ba mace ba kamin Allah yasa asamu wadda zata aureshin a haka.''


"Toh shikenan insha Allahu nima zan cigita bari na koma kafin ya tashi daga bacci ya hargitsa d'akin nasa.''


Har ya koma gidan bacci Haidar yake yi, lokacin har anyi sallar magriba yaje yayi shima, sai da ya sai mishi fura mai kyau da dad'i a hanyarsa da dawowa sannan ya shiga d'akinshi. Ido ya zuba mishi ganin yanda yake ta mutsu-mutsu amma yaki bud'e idanunshi, dafashi yayi yana cewa.


"Haidar...! Kai haidar..!!'' D'agoshi yayi yana kallon fuskarshi kafin yace.


''Yanzu haka fitsari zaka yi kaketa wannan mutsu-mutsun...,Yauwa ai dama na sani.''


Maganar shi ya yanke lokacin da yaga fitsari na biyo kafar wandon Haidar d'in dake kwance. Wasu irin hawaye ne yaji sun zubo mishi kamin kuka me sauti ya biyo baya yana furta.


''Innalillahi wayyo Allah ka kawo min d'auki.''

Sai da ya gyara mishi jikinshi sannan ya bashi furar yasha ya koshi, sannan ya bashi magungunan shi wanda kusan duk na bacci yafi yawa a ciki sabida yanayin ciwon nashi hankali yafi kwanciya idan bacci yake yi.


Fuskarshi yake kallo duk tayi gashi sam baya yadda a aske mishi shi yasa duk sai yai wani irin duguzun dashi sai dai farar fatar shi tana nan yanda take saima k'ara sheki da take yi sabida zama waje d'aya.


Bugun da yaji afuskar shi ne ya katse mishi tunanin da yake yi, ya maida kallonshi akan Haidar d'in yana zaune yana kallonshi shima yana dariya irin dai ta marasa hankalin nan. Gorar da ya gama shan furar ce ya kwalama uban ganin ya zuba mishi ido amma yai nisan kiwo a wajan tunani. Jawoshi yayi jikinshi ya rungume yana shafar bayan Haidar d'in zuciyar shi fal addu'ar Allah ya bawa yaron shi lafiya.

Ranar a nan cikin d'akin ya kwana wanda sai da Haidar d'in ya gama hargitsa ko'ina kamin maganin da ya sha ya fara yi masa aiki lokacin shima Abban shi ya samu ya runtsa.


*****


Tafe nake ina nanata haddar karatuna wanda ya kasance shine abokin hirata a koda yaushe, ban damu da ruwan da yaima jikina sharkaf ba balle na damu da mutanen dake kallona musamman matasa, basu gabana haka zalika bawai ta tasu nake yiba Kawata dije na had'u da ita a dai-dai kwanar gidan mu tana cewa.


"Kai Rumana duk kin jike karfa mura ta sargafeki kin dai san batai miki da sauki ko?'' Dariya nayi kafin nace.


''Uuhum aini yanzu mun zama k'awaye da murar ma kina ganin yanzu wankan asuba inna kesawa inyi kullum duk safiyar duniya wai sai taji ina d'an tsami-tsaki.''

"Allah yagani inna bata kyautawa wallahi kenifa inda nice da tuni na koma garinmu wallahi, da gata da komai amma in like inda ba'a san daraja taba, kai ina wallahi bazan iya ba.'' Cewar dije. Kallonta nayi kamin nace.


''Lallaima Dije, kindai san bani da uwa bani da uba yanzu komawa nayi, kilama gara nan d'in da can tunda can d'inma da ai neman kai suka dinga yi dani, kedai kawai Allah ya kyauta amma wallahi kunji dad'i tunda kuna tare da iyayenku.'' Cikin tausayawa Dije tace.


"Haka ne Ruma to kema Allah ya saka miki ya kuma k'ara miki hakuri da juriya Insha Allah zakiga sakamako nan gaba.'' Da murmushi a fuskata nace.


''Amin dije na gode, wai ya maganar haddarki kingama kuwa?" Hab'a ta kama tana cewa.


''Tab inafa na tsaya wasa kedai na san kingama ai.''


Anan muka rabu kasancewar akwai gidaje hud'u tsakanin gidan mu da nasu. Wani mugun rankwashi ta bini dashi lokacin da na ajiye ruwan da alama shine sanun daya dace dani a wannan lokacin. Baba dake kwancewa kaza dabaibayi yace.


''Inalillahi mai tayi miki haka dan Allah?" Mtwsss taja dogon tsaki kafin tace.


''Yoo a ban zama zan sauke mata kenan? Ai kaima kasan bazai yiwu ba tunda na sauke mata ruwa dole na bata ladan ta.'' Kai ya girgiza kafin yace.


''Akwai Allah wallahi zaki mamakin ranar da zai kamaki akan zalintar yarinyar nan da kike yi.''


Nidai shigewa nayi d'akina ba tare da ko d'igon hawaye ya zabo min ba, duk da irin mugun zafin da naji kuwa, to yaushema zanyi kuka bayan inda sabo yaci ace na saba da duka da rankwashi....










*MAMAN KHADY*🙇🏻‍♀
[4/2, 11:15 AM] Re@l💍 K@usy🌹: 💞💞💞 *RUMANA* 💞💞💞


Na


*MAMAN KHADY*🙇🏻‍♀
(Mk)


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert and perfect writer's)




Page 5.






Domin duk a tunanin shi zaiga yana wani hauka na daban lokacin da ya kama masa, sai yaga inaa..dan tuni ya lafe a jikin Mudin idanunsa a lumshe bakinsa a bud'e har wani miyau yake fitarwa da alama yana jin dad'in abinda Mudin yake yi mishi har cikin ranshi.

Cike da tausayin Hydar Mudi ya taimaka mishi har sai da yaga ya koma wani baccin sannan shima ya samu ya kwanta, sai dai zuciyarshi cike da tsoron Allah akan abinda ya aikata yanzu duk da cewar taimako yayi kuma shi ba wani abin yaji a cikin zuciyarsa ba, ya fara tunanin. yanzu ya san inda lafiyar Haidar qalau ai ko wajan motarshi bai isa yaje ba balle ai maganar kwanciya kusa dashi harma ya tab'a mishi jikinsa. Lallai komai na Allah tsare yake sannan bawa baya tab'a wuce k'addararshi.

****


Washe gari cikin garin BAKORI: Da kyar na samu na yakice baccin dake damuna na mike lokacin iyayena suna d'akin inna har lokacin suna maida yanda akai akan yanayin hidimar data gudana ajiya.


Da sallama na shiga tare da makurewa a gefe ina gaida su. Inna da kanta ta kawo min abin karyawa ta tana fadin.


"Sannu Ruma ya gajiyar ciwon kan ya sauka ko?''


Kaina na d'aga mata kawai naja kofin shayi zuwa gabana da biredi, yau da kayan dadi zamu karya kenan. Zuciya ta tayi murnar hakan dan ba sabawa aka yi ba.


Baba rabi'u da baba ne suka shigo, suma gaida su nayi na cigaba da karyawa ta ina jin duk abinda suke fad'a.

"Ruma duba rigunan nan kigani duk cikin kyautukan da kika samu ne.'' Cewar gwaggo lami.

Wasu riguna ne dogaye masu masifar kyau dan ban tab'a ganin irin suba bakina har kunne nake cewa.


''Amman dai sunyi kyau sosai na gode Allah ya saka da alkhairi.''


Baya na tashi da sauri ina niyyar guduwa lokacin da baba ya zube min wasu kud'i masu tsananin yawan gaske dami-dami dasu a jikin kaure, ba sabun ba.


Innace ta rikeni tana dariyar itama tare da cewa.


"Kedai wallahi Ruma kin cika tsoron masifa, dallah gani zaki yi kud'in da kika samu ne dubu dari bakwai da hamsin ne, amma mun yanke shawarar za'a sai miki kadara na dubu d'ari biyar sauran kuma za'a rabawa dangi, d'ari da hamsin nida malam d'arin kuma sai a ajiye miki kisai sababbin kaya da sauran abin da kike buk'ata muna fatan hakan yai miki?''


Kaina a k'asa ina hawaye babu abinda ya fad'o min sai tunanin iyayena inama suna da rayuwa suma su dangwali albarkacin haihuwata. Duk sai jikinsu yai sanyi ganin ina kuka, da kyar na daure nace da ita.


''Inna duk yanda kuka yi hakan yayi amma dan Allah cikin wanda aka bani ina so acire rabi aje akai masallaci asai wani abin mai muhimmanci ko tabarmi ko butuci ko alkur'anai domin suma iyayena su sami ladan.''

''Allahu Akbar Allah yai miki albarka Ruma" Cewar baba.

Da yamma Baba yana zaune inda yake yin alwala yana yin asuwaki nikuma ina zaune cikin baranda ina had'a littatafan dana samu bakina har kunne tsabar farin ciki da jin dad'i, Inna na gefe tana ta gyaran kajin da ta siyo dama inna akwai son dad'i ita dai a rayuwarta ta sami jin dad'i ace yau itace hajiya Suwaiba, Shi yasa ko kujerar makkan dana samu tana cewa itace zataje ta yiwa iyayena addua' babu wanda ya musa domin ansan bama zata yarda ba.


Sallama aka yi har sau uku kafin baba ya mike da sauri yana nanata ana zuwa. Har ya fita sai kuma gashi da sauri yana fad'in.


''Suwaiba kawo tabarma alhaji Yahaya ne da kaninsa wanda ya yiwa Ruma kyautar kujerar makka.'' Da sauri kuwa ta mike har jikinta na rawa


''Laallah! Kace manyan baki ne damu to sannunsu.''


Kasa zama tayi sabida zullumin me kuma ya dawo dasu har wani lekawa take yi ko Allah zaisa taji wani abu. Niko ina gefe ina dariya domin lokuta da dama lamarinta kan bani dariya.

Gefena ta dawo tace. ''Ruma kaddafa malam ya gayama alhajinnan cewar ba kece me zuwa makkan nan ba dan nasan zai iya wallahi.''

"Kai haba inna ya za ai yace haka dama ai dole ke zaki ai babu wanda yafi cancanta da zuwa saike, nidai kin san tsarabata ta da bance ko inna?''

Cike dajin dad'i ta dafani tana cewa. "Ah kwarai ma kuwa, insha Allah d'iya ta shi yasa nake sonki wallahi.''


A can zaure kuwa, Alhaji Yahaya ne ya kalli malam Sule bayan sun gama gaisawa yace.


"Nasan kila zakai mamakin ganinmu anan, toh malam wannan dai sunansa Yusufa nasan ba sai nayi maka bayanin shi ba, kasan na gayyaceshi wajan walimar jiya kuma gashi ya samu ya halarta harda da gudummawarshi wacce ba'a zata ba, to kuma daga baya sai ya nuna sha'awar Rumana akan shigowa cikin iyalinshi ma'ana yana so ya nemawa yaronshi Haidar auranta idan ba ayi mata mijiba shi yasa yana gaya min nace ai duk gida ne bari kawai muzo da wuri, gashinan ayi komai agaban shi domin da tun safema zai tafi amma sabida wannan maganar sai ya dakata.

Cikin farin ciki malam yake furta. "Alhamdulillah lallai abu yayi kya, Allah ya taimaka kuma ya shige mana gaba sannan ya zab'a mafi alkhairi. Toh amman wani hanzari ba gudu ba, nasan dai kasan cewa yarinyar nan marainiya ce ba uwa babu uba ita mai d'akin nawa itace yayar mahaifinta kaga kenan akwai yiwuwar dole sai anyi shawara da iyayenta nacan kadda suga kamar munayi musu karan tsaye akanta, kuma wallahi kaga ansami sab'ani domin sai d'azu suka wuce can gida maska.''

"Toh ai babu komai ni sai muje dakai har can garin domin neman izini amma yanzu dai ka kiramana ita innar tata taji daga bakina kasan halin mata.'' Cewar alhaji Yahaya.


Tare suka dawo da ita cikin zauran jikinta duk yai sanyi musamman data hangi wata dalleliyar mota daga k'ofar gidan, ga manyan mutane zaune a cikin zauren wanda ya gama bud'ewa da kamshin Alhaji Yusuf domin tasan sai dai shi d'in domin alhaji Yahaya anriga an saba dashi.

Bayani sukai mata dalla-dallah yanda zata gane kafin shi Alhaji Yusuf d'in ya d'ora da fad'in.


"Kamar dai yanda yaya na yai miki bayani yarona yana kasar waje karatu amma ya kusa gamawa abinda yasa nai mishi sha'awar Rumana gaskiya na yaba da tarbiyyarta sannan nasan kowa zaiso ace ya had'a iri da ita, ina fatan zaku amince domin Haidar shi kad'ai ne yarona ina so ya samu mace ta gari.''


Wata zufar farin ciki ne ta zubowa Inna ta ko'ina daga jikinta kafin ta d'an muskuta ta kuma gyara mayafinta tace.


"Toh shikenan insha Allahu komai ba zai gagaraba tunda ba ayi mata mijina ba, sannan ga malam komai nene sai kuji daga gareshi.''


Cike da farin ciki Alhaji Yusuf yabar garin BAKORI bayan yayan shi yai mishi alkawarin cewar a cikin satin nan zaija malam Sulen suje maska domin nemowa Haidar auran Rumana din. (To ruma da auran mahaukaci🤭)


Sai dare ya shiga cikin katsina hankalinshi kwance bakinshi cike da adduar Allah yasa abinda yake son shiryawa ya zama alkhairi garesu baki d'aya.

Mudi yayi murnar ganin shi duk da cewa har sun kwanta bacci lokacin, sai da ya gama duba jikin Haidar d'in yaga babu matsala sannan ya wuce d'akin shi wanda aka gama fesheshi da asirirrika kala-kala.

Da bismillah ya jefa kafarshi tare da bi da ayatul kursiyyu da falaki da nassi domin haka kawai ya farajin fad'uwar gaba lokacin da ya dumfaro d'akin nasa.

Kwance take saman gadon shi tayi dai-dai tana kwasar baccinta, wankanshi ya wuce yayo ya gyara jikinshi sannan ya rab'a gefenta ya kwanta bayan ya gama tofe jikinshi da addu'a.


*******


"Oh gaskiya rikonki ya zame min alkhairi Ruma, Allah ya jikan iyayenki, zanzufa makka zanje sannan ga wannan alhaji da yake so ki auri d'anshi kinga shikenan muda talauci munyi hannun riga ko?''

Turo bakina gaba nai ce. ''Kai inna nidai wallahi bana sonshi kin dai san duk yaran da ake kaiwa kasar waje karatu a iskanci suke dawowa, kuma shikenan saiki aura min wanda bazai tab'a sanin darajata ba?''

"Innalillahi na bani ni Suwaiba, Ruma kina da hankali kuwa? Toh wallahi ahir d'inki da yimana bakin ciki, gobe idan Allah ya kaimu zamuje maska gaba d'ayan mu, saura idan an tambayeki ki musa Allah saina yankaki aikin san zan iya ko?''


Kuka na saka mata nace. ''Inna duk ga masu sona nan a garin nan ga Mansur ga K'asim ga malam Umar kullum nacin tambaya suke yi zasu turo kinaki sai wannan daga zuwa wama yasani ko d'an fillan kai ne.''


Dariya tayi kamin tace.

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login