Showing 6001 words to 9000 words out of 71894 words

Chapter 3 - YARIMA ASHMAN

19 Oct 2024

58442

Haka umma taitabin layi tafi awa2 har akayi sallar la'asar tukum layi yazo kanta.
"Nan tashiga tana addu ar samun nasara", har cikin office din aka shiga da ita sannan security din yafita yabarsu."
Shikuwa yarima hakimce yke kan kujera yana cikin suit bak'ake sunyi bala'in karbarsa kansa aduk'e yana yan rubuce rubuce . umma kuwa k'asa ta duka cikin muryar tausayi tace ranka yadad'e nazo gareka kataimakamun danALLAH kamar yadda ALLAH yataimakeka! da sauri yarima yadago yakalleta duk saiyaji tabasa tausayi yji bbu dadi kamar wannan dattijuwar ta duk'a gabansa aita haifi kamarsa,da sauri yace mamah tashi Ki xauna yanuna mata kujerar gefensa.
bbu musu ta tashi ta zauna"ahankali yace ina sauraronki fad'amun damuwarki nan umma ta fad'a mishi komai da komai harda zalincin da bala yyimusu da kashe megidanta da akayi ba'asan kowanene yyi kisanba.
Ajiyar zuciya yarima yyi yace sadda akakasheshi kunkaisa asibiti anduba meya kasheshi ,?tace ah ah Aida wuk'a ne akayi kisan.
Ok kawai yace yana tunanin alh jamilu bushasha dan gsky dole yasa ido akansa sbd mutane da yawa na zarginsa .
"Batare daya kalleta yacigaba da cewa to yanxun bakison ya aureta ?" da sauri tace eh yace to yanxun zan mik'a case d'in kotu ,nikumane lauyen dazai kareki kin fahimta ?umma tace eh yace sannan banison kiji tsoro ko shakkunsu ki fito kifad'i gsky hakan zaibamu samun nassara akansu insha ALLAHU .
Umma tace to insha ALLAH zanbada had'in kai."umma batabar gunba Saida yarima yatura case d'in kotu ,sannan yakarb'i Nokia dinta yasaka number ta awarsa yace duk abinda kenan zaikirata.
"godiya da saka masa albarka umma taitayi,hakan yak'arasa yarima jin kaunar matar dason taimaka mata sbd yanason talaka mai mutunci gaahikuma sai saka masa albarka take."
Haka umma ta fito tahau adedeta ta wuce gida murna fal aranta.

Tana xuwa gida ta dauki wayarta takira baba mlm wato yayan mahaifinta Wanda yaruk'eta ya auradda ita kasancewarta ta tashi iyayenta sun rasu shiya mayemata gurbinsu.

Bayan ta shiga yad'aga suka gaisa nan tazaiyana masa abinda ke faruwa had'e da cewa tamayi k'rarsu kuma yasmeen da Omar suna hanyar xuwa gunshi.

"" nan yace to gara da ta yi kararsa dan shima bala yakaisa bango nan sukayi sallama ta kashe kiran"

Yah Omar ta kira yace ai befi awa1 su ida isaba,wayar yasmeen ta karba had'e da tambayar umma ko Kawu balan yadawo?

"Umma tace ah ah."

Nan sukayi ta yar fira tukum sukayi sallama had'e da cewa insun isa zasu kirata.

___________________
6angaren yarima kuwa bebar office ba Saida aka tabbatar masa da cewa ankaima alh jamilu bushasha da Kawu bala takardai sammaci gobe da misalin karfe 12:pm za'a fara shariar.

"Sannan yadawo gida ,bayan yyi wanka yahuta bayan sallar isha'i yakira umma ta d'aga had'e da yin sallama nan yarima yagabatar da kansa had'e da yima ta bayanin lokacin da za'ayi shariar dakuma kwatanta mata kotun saidai yace taje kamar misalin karfe 11:am kawai dan xaimata wasu tambayoyi.

" nan tace to had'e da yimasa godiya sukayi sallama. "


YOLA

Ban garensu yasmeen kuwa sai ana kiran magrib suka isa yola.
Kaitsaye gidan baba mlm suka wuce ,asoro suka samesa zaune shida wasu jama'a dan gidansa baka rabashi da mutane.
"Murmushi yyi irin nasu na tsofi yace yakalli yasmeen yace ga amaryata !ga amaryata!!yar dariya tayi tace ,amaryarka tsohuwadai Tana kuma cikin gidanka ba.duka sukayi dariya nan itada yah Omar suma gaisa ta shiga ciki ,shikuma yah Omar yatsaya sukayi mgrib tukum yashiga ciki yasamu har yasmeen tayi wanka abinta.
Nan shima yaje yyi sukayi isha I akaci abinci ,sannan baba mlm yashigo sukayi ta fira dasu yasmeen sai da dare yafara tukum yasmeen tacewa inna wato matar baba mlm ita bacci takeji ,yah Omar ma yace shima bacci n zaiyi.inna tayi murmushi tace raggaye dku kawai time k'asa zan barki ki kwana kaikuma zaure zaka kwana dariya akayi gaba d'aya.
Nan yasmeen tayiwa yah Omar sallama ta wuce dakin inna tahaye kan babban gadonta mai rumfa irin na daa."
Shima yah Omar yaje ya kwanta.

********
Alh jamilune keta safa da marwa a parlourn sa yana mamakin wai kamarshi wata banxar talaka marar y'anci zatayi kara.murmushin mugunta yyi afili yace zan dauki barrister saminu inkinsan wata aibaki San wataba tunda naga yarki na kwadaitu da ita dan haka kota yaya sai hak'a na yacimma ruwa ya bushe da dariya irinta bosawa.


Wayarsa yadauka ykira bala."

Yana d'agawa bala yace wai kaji wannan matsiyaciyar k'ararmu tayi Ashe?

"Wata dariya alh jamilu yakece da ita yace hmmm karabu da ita aimune akanta ai nadauki barrister ita inama sukaga kud'in daukar barrister tunda kace ai talakawane sosai.


Kawu bala yace eh gsky can ta matse mata ai gobene haka aka rubuta jikin takardar sammacin.

Ok kawai yace had'e da cewa to sai goben kazo sai mu wuce tare ko.

" bala yace to, nan sukayi sallama."

Da misalin karfe 11pm yarmane zaune akan katafaren bed dinsa ga lap top agabansa yana using da ita.

Kiran salma ne yashigo wayarsa ,tsaki yyi dayaga itace yashare dan bayason takura arayuwarsa musammun inyana abinda yashafi aikinsa bayason amatsamasa.


Sake kiran taitayi ,Saida ta masa5miss call akira6 yyi peaking call din,cikin shagwaba da kissa tace haba baby kanajin kirana shine kayi ignoring dina kamun adalci kenan?


Lumshe idanunsa yyi yace pls salma una wani aiki zankiraki latter,da sauri tace aikin yafini mahimmanci matsayina na wacce zaka aura?


"Atak'aice yace eh."

Cikin jin haushin kalamansa tace to nagode dan talura kwata kwata bata gabansa,katseta yyi da cewa wato fushi kikayi ko ?

"Eh nayi saina rarrasheni kabani hkuri."

Yar dariya yyi yace hakan baya cikin tsarina ni Prince ashman nafi karfin bawa mace hkuri ko rarrashinta saidai nitabani takuma rarrasheni,kuma bama kiranki kadai ba zanyi kinsan nanda 5weeks zanxo nan k'asar yin wani course na 3month kinga muna tare har kigaji da ganina.


Cikin xak'uwa tace to baby ina sauraronka, nan sukayi sallama yakashe wayar dan yakosa sugama ya ida aikinsa.


Washe gari tun 10:30 am yarima yanufi kotun daza ayi Shari ar.

Cikin motarsa mai bak'in glass yazauna ina sauraron xuwan umma.

"Befi minti10 yahango mai adedeta ya ajiyeta ta nufo gun."

Nan yafito,umma na k'okarin gaidashi ,amamakinta taga duka yagaida ita ,cikin jin kunya ta amsa fuska sake, yarima ya zauna kan wata kujera umma ta biyosa nan yafara magana da ita dagaya mata koda sun dauki lauyer inya mata tambaya ga irin amsar dazata bashi,sannan yafadamata yaddac xatacewa alkali inya tambayi akan me take k'ara?

Synkai kusan 30 minit yarima nakarawa umma karfin guiwa yana nuna mata yadda zasuyi ,cikin ikon ALLAH su sami nassara .

Kamar daga sama umma ta hango Kawu bala yafito dg mota shida alh jamilu.

Wani fad'uwar gaba alhj jamilu yaji shida Kawu bala dasuka ga umma na magana da barrister Ashman isma'il khaleed ,sun tabbatar shine lauyen dazai kareta....


Share pls

YARIMA ASHMAN???`???`???`???`???`???`

Story & written by mmn fareesa

Wannan page din nakune, YARIMA ASHMAN FANS grp1,2&3 kuyi yadda kkso dashi inamugun ji daku???i???i

Mmn musaddeeq &mmn Bilkisu nasadaukar da wannan page gareku nagode sosae da kaunarku gareni da masoyana baki daya???j???_???j???_???j???_.

??T15&16

Wannan kotu ta zartar da hukunci kamar haka,
Bala dole yahakura dayiwa y'ar k'aninsa auren dole ,abarta tazabi Wanda takeso".Sannan kotu tabawa Mariya damar duk sadda bala yasake xuwa gidan ta batare da ixinintaba koda tashin hankali to ta sanar kotu."
Sannan alh jamilu dole yahakura da wannan auren ,inma yyima bala hidima ko kaimasa kudin auren to yakarb'i kayan sa.
Wannan hukunci dole kubisa sbd wannan kotu bata lamunci acanza wata sharia ba inhar tayi hukunci akanta".
Alk'ali yana kaiwa nan yabuga guduma kowa yatashi .
"Yarima yakalli umma yyi murmushin samun nassara yamike dan fita had'e da yiwa umma nuni ta biyosa.
gab da yarima zai fita yaga alhj jamilu ,Kawu bala brr saminu fuskarsu murtuk kamar an aiko musu da sakon mutuwa ,wani mugun kallo barrister saminu yyiwa yarima, murmushi yarima yyi Wanda yasan yak'ara batawa barrister saminu rai.
Ida fita yyi had'e da tsayawa gefen wasu kujeru yana jiran umma.
" hango su alh jamilu da Kawu bala yyi suna mgn sannan suka shiga mota sukabar gun .
Umma nafitowa ta isa gun yarima tanata fara'a ,tsayawa tayi had'e da cewa 'y'allab'ai ngd sosae da da wannan taimako da karamci dakamun bazan taba mantawaba ALLAH yyimaka albarka yasa kagama da duniya lfy, cikin jin dadin addu ar ta yace ameen mama ,kada kidamu .
"Ahankali yarima yace amma mama ina ganin maganar kisan mai gidanki dukda kince anjima amma gsky zansake binkice akanta harsai Nagano ko wanene yyi kisan insha ALLAH dan inad'an wani zargi daban.to amma zan yi tafiya wata k'asa zanyi wata3dana dawo insha ALLAH zankiraki inxo har gd sai musake binkice.
Cikin jin dadin maganganunsa umma ta ce to amma ngdsosai ALLAH yasaka da alkhairi, murmushi yyi yace ameen ,nan sukayi sallama ya wuce gd itakuma tahau adaidaita ta nufi gd cikin farin ciki.

*********
Bangaren Kawu bala da alh jamilu kuwa ,tafe suke cikin mota rai bbu dadi, alh jamilu cikin b'acin rai yace wlh saina nunama yaron nan kalata wlh yabi a hankali kada yaga d'an sarkin garin nan yanemi yatakani ,naga bayan wad'anda suka fisa taurin kai bare shi karamin kwaro wlh sai inyi ajalinsa.
" bala yyi tsaki yace bar mutsiyaci wlh kamar nashak'esa ",inyasan wata ai baisan wata kaga yanxun kawai mubari ayi sati2da yin shari'ar nan sai intura yan fashi suje har gdansu yasmeen d'in su satomun ita inrufe fuska ta nabiya buk'a da ita inaga hkan xai fi,alh jamilu yafad'a yana kallon bala.
Bala yyi dariyar bosawa yace hakan yyi nima dg nan sai a satomun uwar nahuta da ita dan tun bayan mijin yarasu naso aurenta tak'i"alh jamilu yace tabbas haka xamuyi nan suka cigaba da mugayen maganganunsu.
Shikuwa bala dadi fal aransa dan dama yana tunanin kada alh jamilu yace yabiyasa kudinsa dan yanagani d'aukewar numfashi kawai zai sa ya iya bada kudin nan.


___________________

Bangaren umma kuwa cikin jin dadi ta isa gd takira bb mlm ta sanar da shi komai yyi murna da hakan sannan yace to cikin satin nan zasu dawo dan duka yau kwanansu d'ayafa .

" umma tace to nan sukayi sallama. "

WASHE GARI

YOLA
da misalin karfe 10 nasafe ,bayan yasmeen ta karya tayi wanka ta fito soron gidan dan gaisawa da mlm da yah Omar.

"Tana shiga tasami mlm shida wani dattijo kamarsa saidai shi daga ganinsa yanada wadata sosai."

Cikin tsokana ta ce ina kwanan Ku tsaffi?

Murmushi sukayi suka gaisa,ana wasa da dariya ,nan yasmeen ke tambayar mlm ina yah Omar ,kafin yace wani abu yah Omar yashigo tare da wani yaran mlm .

Murmushi yah Omar yyi yace oh baby banisa nayiba taso muje ciki mu gaisa kinga tsaffin nan na kallanmu.

Yar dariya tayi tace eh gsky muje.

Mlm da amininsa sukace kulbabbi kawai."

Aminin mlm yace mlm wa,annan yaran wai suwane?
ne wlh yau nafara ganinsu sai naji duk sun kontamun arai.

Mlm yasanar da amininsa matsayinsu agunsa had'e da cewa ai yayan mariyane dan yasan shiya riketa,kuma yalabartamai dalilin zuwansu ,kuma yasanar dashi komai akan yadda Shari ar takasance.

Ajiyar zuciya tsohon yyi yace to inba damuwa ni ina nemawa jikana aurenta.

Mlm yace to! to!! to !!ngane amma kana ganinba matsala ?

"Hmm bbu wata matsala nayi iko da iyayansa balleshi ma."

Baba mlm yace to zankira mahaifiyarta indai ta amince to xanmaka mgn ammafa yarinyar nan karatu take.

Tsoho yace ba damuwa in anyi auren zata cigaba.

Mlm yace to shikenan nan yyi sallama da amininn nasa .

Wayarsa mlm yafito had'e da kiran Mariya ,bayan sun gaisa yazaiyana mata komai da komai akan yadda sukayi da alh tsoho amininsa.

Umma tayi shiru tana tunani ,can tace baba bakomai kabasa aurenta ,nasan bazaka yadda ta auri mutumin banxaba,amma kada kafad'a mata intazo zansanar da ita dan kartaji yanxun asami matsala .

",intaxo mun rarrasheta da Omar harta yarda ALLAH yasa hakanne yafi alkhairi."

Mlm yace amin hade da sakamata albarka ,nan tace to gobe sudawo gd sbd makarantar yasmeen d'in, nan mlm yace yauwa aiko anyi auren to xata cigaba da karatunta.

"cikin jin dadi umma tace to nan sukayi sallama ."

Adaren ranar mlm yaje har gidan alh tsoho yasanar dashi sun amince ."

Atake yace jibi za'a zo da uban yaron yagaidakai yanema masa auren dan yanxun zan sanar dashi awaya.

Nan baba mlm yadawo yasanar dasu yah Omar gobe zasu tafi gida su shirya ,ji yasmeen tayi gabnta yafad'i tace miyasa zasu koma?

Mlm yace ai komai yadaidaita anfasa aurenta da alh jamilu.

Murna sukayi ta yi itada yah Omar.

Washe gari tun bayan sallar asuba yah Omar da yasmeen sukayi ban kwana da baba mlm da inna ,suka wuce tasha abinsu....


6angaren umma kuwa ,sai fargaba take dukda tasan yaranta akwai tarbiyya gashi suna mata biyayya tasanma dole yasmeen ta amince tunda sun gama mgn da Mlm bazata so mlm yyi k'arantaba ko mutuncin sa yazube.da wannan tunanin ta yini ,kuma kad'an kad'an takira su taji sun kusa isowa gd....

Bayan azahar suka dawo,umma tarbesu da abinsha Dana ci Saida suka huta sosai sannan umma tace yasmeen taje tayi wanka.

"Bbu musu ta ce to had'e da fita dg dakin."

Tana fita umma ta kalli yah Omar dke cewa nima bari naje gidan kwana nayi wankannan...

Umma ta katsesa dacewa zauna muyi mgn ,nan yazauna yamaida hnkalinsa gunta.

Nan tazaiyane masa komai akan baba mlm yabada auren yasmeen ga jikan amininsa.

Zaro ido yyi yanuna be yardaba,umma tanunasa illar hakan had'e da cewa inason Omar kucireni kunya katayani shawo kanta dan yanxun inta shirya zan mata maganar.

Hade da cewa harda kai nakeso katayini rarrashinta kaji ,dan inkanuna kayarda nasan xata amince kuma zata cigaba da karatynta bayan auren,nafiso ayi da yardarta banson tayi zaman kunci,kuma inason nunama bala cewa iko daku yana hannuna yaga ko bbu shi tsab yasmeen xata auru..

Yah Omar yace eh gsky Dan akazo Neman aure ta gun Kawu bala ai saiya kunyatamu karshema tak'i yin daraja gun mijin sbd Kawu akwai son abin duniya.

Umma tace yauwa Ashe kagane?gashi can ta fito yi shiru ,nan yah Omar yyi shiru had'e da latsar wayarsa ,adedenan yasmeen ta shigo dakin tana cewa yaya kaje kayi wanka ,kallonta yyi yace jeki shirya tukum zanyi mgn dke ,batakawo komaiba ta shiga k'uryar d'akin dan shiryawa itadai umma batace komaiba tana jira yasmeen ta shirya ayi mgn....

Share pls


YARIMA ASHMAN
???`???`???`???`???`???`

Story & written by mmn fareesa

??T17&18

Bata wani jimaba ta fito cikin doguwar Riga ta atamfa.
Xama tayi kusada yah Omar had'e da aza kanta gefen kafad'arsa tana cewa yah baya wanka yazama kazami,"yar dariya yyi yace keko ?"baby kin maidani kakanki ko? Murmushi tayi ,had'e da kallan umma tana cewa wai ummu wanne d'an arzikin yakareki akotu ?dan nidai mlm da yabamu lbr yace karar su kikayi ,kukayi shari'a
"Ahankali umma ta zaiyane musu irin taimakon da yarima yamata da jajircewarsa,har da inyadawo zai sake binkice akan mutuwar mahaifinsu.
Aidaga yah Omar har yasmeen sunyi mamaki dukda shi yah Omar yasan yarima yanada taimakon talakawa,kuma shi yadauki alkawarin duk runtsi sai yyi binkice yagane Wanda yakashe musu uba to gashi ALLAH yakawo masu yarima yataimakesu.
Cikin jin dadi had'e da k'aunar yarima yah Omar yace gsky mutumin nan yyi mana mutunci ALLAH yabiyashi yakareshi dg Sharrin abin halitta.
" umma tace ameen yah ALLAH."
Yasmeen kuwa mamakine fal aranta amma sai asan tabbas yarima besan matsayinta agun ummaba dakuma cewa itace za'ayiwa auren ,inda yasani bazai taimakesuba,wani iri taji azuciyarta intatuna rashin mutunci datayi masa amma indai tasake had'uwa dashi zata bashi hkuri ammafa bazata d'auki rainiba gsky Dan.. Ummace ta katseta da cewa Auta ina Neman wata alfarma agunki?
da sauri yasmeen tace alfarma umma?"aikinfi karfin hakan aguna saidai kibani umarni kawai.
Cikin jin dadin magnarta umma tace duk abinda nasakaki zakumun kinmun alk'awari?
Yasmeen tace eh,
Umma tace to baba mlm yabada aurenki ga jikan amininsa yyi hakane dan daga ni har Ku ya isa damu ,kuma yyi hakane sbd baki kula kowa bakya soyayya duk da bansan ko a skul kinayiba.
Azabure yasmeen ta d'ago kanta dg kafadar yah Omar idanunta cike da kwallah tace aure !umma karatunfa?umma tace xaki cigaba ai ,tace to wanene za 'a auramun ?umma tace nima bansanshiba amma ai kinsan bazai had'a ki da mutumin banxa ba ko?"
Yah Omar ne yadafa kafad'arta yace baby nah kiyi hkuri kinji kiyi biyayya ga umma da Mlm dkuma ni dan nima inason auren nan ALLAH yana tare dke kuma zai taimakeki.
Fuska cike da hawaye tace to yaya na amince tunda kaima ka amince!
Cikin tausayinta yace yauwa babyn yah Omar amma kidena kuka kinji?to tace ta share hawayen ta.
Umma taita sakamusu albarka,nan yah Omar yafita dan yaje yyi wanka.


*********
Mai martabane zaune shida ammi kan 2seeter yarima yana zaune gabansu kan carpet yana sauraren yaji kiran me ,memar taba yake masa.

"Ahankali mai martaba yace ASHMAN! "

da sauri yakalli abban sa dan yasan wannan kiran da yyi masa babu wasa afuskarsa da maganarsa.

"Sarki yace inaso inbaka umarni matsayina na mahaifinka dan nasan kaf a y'ayana bbu maimun biyayya kamarka "

To alh tsoho yazab'a maka matar dazaka aura sauran sati 1yau sannan yau zanje yola nagaida kakan yarinyar kuma gobe zaa sata a lalle.

Arazane yarima ke kallon sarki da amminsa yace Abba pls...da sauri sarki yace oh musu zakamun toko ni danake sarki inajin maganar alh tsoho Balle kai.

Cikin tausayi had'e da rarrashi ammi tace yi hkuri kaji my son kayi biyayya ni inajin ajikina akwai alkhairi awannan auren kaji?

"Wani irin yanayi na haushi ,takaici bakin ciki yarima duk yashigesu danshifa bayason raini gsky ,dalilinsa na yarda kenan ya auri salma dan yasan zata masa biyayya irin yadda ykeso shiya sa kuma baida ra'ayin mace2".

Sarkine yace kayi shiru ,indan yarinyar dakakesone aiba damuwa inta ida karatun saika aureta.

Jiki a sanyaye yarima yace ALLAH yasa hakan shi yafi alkhairi. Yana fad'a yabar dakin.

" sarki da ammi sun tausaya masa to bbu yadda zasu iya

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login