Showing 18001 words to 21000 words out of 127530 words
kallon 'yar mutane saboda me?kar dai ka ce min son wata kake yi daga cikinsu?bashir ya ce laifi ne yin hakan?lsa ya ce,aa ban ce ba,sai dai ka bani dariya kawai,duk 'yan matan da ke cikin garin katsina? ka rasa wanda za ka zaba sai wadanan 'yan ruga mitsi-mitsi da su?kabiru na'allah ya ce,in dai fulanin nan nema,ba su son baiwa bare 'ya'yaansu.bashir ya ce,ku yi min addua in rabo na ce za su bani,don gaskiya na ga wacce nake so.suka sa mishi dariya. Abin ya wuce da tunanin bashir,domin ranar da tunanin 'yar fulani ya kwana,ya kosa ya je su kai kudin shanu,don haka tun tara ya shirya ya nufi banki ya ciro kudi,daga nan suka nufi mashi. ko da suka isa burinsa ya ga yarinyar da ta hana rayuwarsa sakat, har suka bayar da kudin shanun suna kokarin zuba su a mota,amma bai ga giccin wani da ba.ya kama mota zai hau sai ya hango ta tana kada nono cikin dan kuttunsu da suke cire mai,da sauri ya fasa shiga motar ya nufi gurinta. sallama yayi mata ta dago a firgice ta ji abin kamar daga sama,ganin mutum sai ta amsa cikin dariya. ya ce,'yan mata ya ya sunanki? ta kalle shi ta ce, suna na?ta kau da kai,ta ci gaba da abinda ta keyi.lsa ya kwada masa kira daga nesa,bashir ka zo mu tafi mana,bashir gani ya ke idan fa ya tafi ya bar damarsa,ya ma rasa ta kenan,shi damuwa.don haka da ya ga abinda zai dame shi,nan da nan zai yi maganin abin,in har zai iya, musamman in na kudi ne, tunda yanzu ba laifi yana samu. sake komawa yayi ya sa aka yi masa sallama da ardo,wanda ya tafi don ya adana kudinsa.kabir yazo gurinsa,
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (45)Zo mu je in ya so mu sake dawo wa,bashir ya ce,ba a haka da ni,ka san ni in ina son abu,zan yi duk abinda zan iya in kuna sauri kuyi gaba zan zo.kabiru ya gane fusata ta sa bashir fadin haka,sai yayi dariya,ya yafito lsa mani da hannu, suka zosu ukun suna jiran fitowar ardo. ya ce,da muna daki daya da ku,duk ku kayi aure ku ka barni,dole ku yi min dariya.duk yadda suka dauki lamarin da zafi gurin ardo,maana ba sauki sai suka ga akasin haka.ardo yana da ilimin addini,ya fahimce su,kuma yayi masu bayanin cewa lallai sun yi dace,domin har an bayar da ita,sai wanda aka baiwa din ALLAH yayi masa rasuwa wata biyu kenan. ya kara da cewa,in yana son ta ta amince ya nemi soyayyarta,in ta amince gurin shi babu wata matsala.kwana biyu tsakani bashir ya sake yi wa rugar fulanin tsinke,cikin ado aljihu dam da kudi.lsa mani yasa shi yin tsarabar sarka da 'yan kunne,wai mutanan ruga suna son abin ado mai kyalkyali.bai samu ardo a gida ba sai babban dansa jabiru.sun gaisa inda yayi masa bayanin cewa,ardo ya je cikin gari maganar tafiyarsa aikin hajji.sai dai yayi wa jabiru alheri,ya ce, masa yana son ganin bengel,kamar yadda ya ji ardo ya ambata rannan. sai jabiru ya ce,oh!sauda? ai saudatu sunanta,ardo kadai ke fada mata bengel, na gode bari in turo ta,domin yanzu zasu fita tallar nono.yana tsugune sauda ta isko shi,tana sanye da koriyar atamfa da kuma farin mayafi mai kyalli.duk da fuskarta babu walwala farin ciki gurin bashir ba ya misaltuwa.ta tsuguna can nesa da shi,ta gaishe shi,ba tare da wata kwana-kwana ba ya ce, saudatu kina so na?rufe fuska ta yi da gefen mayafinta ta ce,ardo ba za ya bada ni ga wanda ba bafulatani ba.ta yi magana cikin hausar da bata goge ba.ya ce,kar ki damu ardo ya san da zuwa na,ya amince in nemi soyayarki. saudatu yarinya ce ba za ta wuce sha uku-sha hudu ba,sai kyau tamkar balarabiya.ta ce,in na amince me zai faru?ya ce, aure ne zai faru,ya fada cikin kwaikwayon muryarta, ya lura akwai kuruciya,
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (46)Gurin yarinyar.ta ce,kamar ya ya?yanzu da na amince sai a kama aure? ya yi dariya,to me za a jira?zan turo iyaye na su gana da naki,zan bayar da sadaki da duk abinda kuke yi na al'ada,sai a daura mana aure.ta sake kallon shi,sai me daga nan?ya ce, a kai ki gida na,ta ce,ina?ya ce,cikin gari,ta ce daga nan sai me?kuma me zanyi a gidanka?ko kaima kana da shanun ne da zan dinga tatsar nono ina kaiwa kasuwarku.ya ce,aa abinci kawai za ki dafa min,sai in kin haifa min yara ki kula min da su.ta rufe fuska,zan tafi ya ce,haba da sauri haka muna hira mai dadi? ya ce,saada ce ke jira na za mu je talla.ya ce,wace ce saade?ta ce,'yar'uwa ta ce, kanmu daya,ya ce,tare zaayi maku aure?ta ce,ni kan zan tafi ta fada tare da rufe fuskarta.ya ce, ba na son tallar nan,ta ce,ni kan ina son zuwa talla,don naga kasuwa,kai kam,me ya sa baka so?ya ce,ina tsoron kar wani ya kwace min ke.ya ciro tsarabar sarka cikin gidanta ya ce,ga wannan,ta amsa da murna. tana godiya.ya sake fiddo da sabbin kudi 'yan naira goma-goma ta yi ta godiya ya ce,mata zai dawo jummaa ta ce,sai ka zo,cikin abinda bai fi wata daya ba ya mallaki zuciyar 'yar fullo.lyaye sun shiga, inda aka tsayar da rana,sai ardo ya dawo daga aikin hajji.su biyu aka hada bikinsu da saade,ita an kai ta wata rugar fulani da ke kusa da su.lta kuma saudatu can masari aka yi da ita,inda mahaifinsu ya ba su daki. satinsa guda ya koma katsina,a nan tudun wada ya nemi daki,ya koma ya dauko ta,ya saka ta lslamiyya saboda ya lura tana da karancin ilimin addini.ta kasa fahimtar cewa shi din fa mijinta ne,fa di take,yadikko,ta ce, ka da ta bari namiji ya taba ta,balle ma jikinta,ita kan ba 'yar iska ba ce. sai da ya lura ta saka hankalinta a karatu,kuma tana fahimta,sai ya samu malamin ya sanar da shi matsalarsu,nan malamin ya cire minti biyar kullum yana yin nasiha ga dukkan dalibansa don akwai me irin matsalar addini bai rufe komai ba,don haka bayani filla-filla ya dinga yi masu ya yin.
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (47)Nasihar.sauda ta fahimci komai,kuma ta mika wuya ga mijinta game da neman gafarar sa,lokacin watannin su goma da aure, shi kam yayi ta ji da ita tare da kara son ta tamkar ya ba ta kamshi. sunyi shekara uku,kafin ta samu cikin farko,ta sauka lafiya danta namiji, ya ce,sunan mahaifinsa aliyu,suna kiran sa abba, kullum kara son saude ya ke yi,saboda biyayyanta da ladabi.a wannan lokacin mahaifinta ardo ajalinsa ya sauka,sun shiga tashin hankali,domin damuwarta ta tayar da hankalinsu sosai.tana nan a rugarsu har ta yi sati biyu da kyar ya lallabe ta suka dawo. Bayan iyayensu sun fita takaba,sai aka yi masu rabon gado,sauda ta samu shanu tara da raguna, saboda su biyu ne a gurin ardo,bashir ya ce,ta ba shi aronsu ya saida,zai fadada kasuwancinsa,in komai ya daidaita zai maido mata da shannunta ko kuma kudinsu. amma ta je ta yi shawara da yadikkonta,yadikko ta ce,ki ba shi,in kin san zai ba ki.sauda ta ce zai ba ni,ta ce,to ki ba shi,sauda ta tattara komai da ta mallaka ta damka ma mijinta. ALLAH ya sama abin albarka,inda kasuwanci ya bunkasa ya fadada ta hanyar bude manyan shagunan kayan masarufi, kayan abinci,shaddoji da zannuwa,ba a fi shekara ba ya soma fita irin su kwatano,togo da dai sauransu.kafin shekara biyu ya fara shiga china da dubai.ln ya sayo kaya sai ya raba ma 'yan kasuwa. daidai lokacin ne ta sake haihuwar danta na biyu,inda aka rada masa muktar.bayan ta yaye,shine suka je aikin hajji,shine ya biya masu ita da shi,da wata shekara ta zagayo kuma ya biya wa mahaifinsa. shekara daya ya bude kamfanin kansa da ake sarrafa robobi da katifu. shekarar ne ta sake haihuwar danta na uku,aka sa ma shi suna abdulkarim. lokacine ya soma nuna mata maitarsa ta son 'ya mace.ya ce,sauda ban taba fada miki ba tun cikin abba na ke son 'ya mace.ln kina da ciki koyaushe ina cikin addua,ta ce,mu ci gaba da adduar ALLAH ya bamu 'ya mace amin.sai in sa mata suna khadija,suna mahaifiya ta ce,
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (48)ALLAH ya bamu masu albarka.abdulkarim ya shiga shekaru uku,amma ba ta samu wani ciki ba,lokacin ne alhaji bashir ya hadu da hajiya binta a saudiyya, bazawara ce,mijinta ya mutu,ya bar mata dukiya, amma bata taba haihuwa ba.a girme zata girme sauda,a boye suka yi ta soyayya,don ya rasa yadda zai yi ya fada ma sauda,sam baya son bacin ranta.wani dare bayan sun gama muamalarsu ta ma'aurata,sai ya rike hannunta yana me sake jaddada mata cewa sonta daban yake a cikin zuciyarsa.matuka take jin dadi a duk lokacin da ya yi irin wadannan kalaman,ta ce,ai tuni ta san haka,kuma ta yarda da wannan.ta kuma fada masa cewa,ba fa sama da shi a rayuwarta,amma in an cire yadikkota.ya yi murmushi sannan ya ce,kin san aure mukaddari ne ga kowane bawa ko?ba tare data fahimta ba ta ce hakane. ya ce,zan kara aure,da farko ta dauka wasa ne, amma jin yadda ya kuke yana ta zayyana mata inda suka hadu,da inda maganar ta tsaya a halin yanzu,sai ta mike cikin fushi ta nufi dakinta.kishi kenan,kumallon mata,rigima sosai suka yi har ta bukaci kudinta.ba da bata lokaci ba ya maido mata,sannan ta dauki matakin kaurace masa,ya yi ta lallabarta amma ta ki.ta kai kudinta gidansu,inda za a sai mata filaye da shanu.wannan ne karo na farko da ya taba kai karanta gurin kannin mahaifinta.har gida baffa ya zo yayi mata fada da nasiha,ta ci kukanta ta hakura doke. An yi biki inda aka kawo amarya sabon gida daya gina masu a sabuwar unguwa.katon gida mai tsari,sai da zama ya soma yin nisa,a nan saudatu ta gane lallai mijinta ya fi son ta.don haka ta saki ranta ta zauna da su zuciya daya. cikin wannan zaman ne ta samu cikin MIMI,haihuwar MIMI ta zo masa cikin nasarori,randa aka haife ta, rannan ya bude kamfaninsa na fulawa a kano.da ya dawo ya ga 'ya mace kyakyawa,mai kama da abar son shi wato mahaifiyarta,yayi murna tamkar ya hadiye 'yar. Yayi walima gagaruma, inda aka rinka sanarwa a jarida,gidan rediyo da talabijin,sabon abu,saudatu ta ga sabon abu kamar na fari.
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (49)Wani abinda ya fi bata al'ajabi,tuni ya amshi renon jaririyar tamkar ba zai fita ba.ya na burge ta har ta soma jin haushi, domin baya kula da ita yanzu kamar da koyaushe uwarsa MIMI,wai shi sam baya son jin kukanta,duk lokacin da yaji kukanta,ya dinga fada kenan,ita kuma ga shegen kuka.sannu-sannu MIMI ta soma girma, sai ta shiga yi ma kowa kuya sai dady,lokacin zama take yi.amma in dady yana gida ko hajiya sauda bata amincewa ta dauke ta.hakanan zai iya barin kowa da komai ya lallasheta,in har tana kukan rigima.haka ta taso cikin mugun gata da rigima ga shagwaba,abin da ta ce,shi zaayi,su abba har suka soma jin haushinta, yayyanta kenan.domin kirikiri zata yi laifin da ya kamata a zane ta,amma sai a ce ko kallon banza ba zaayi mata ba.da aka tashi sanya ta a makaranta,sai aka sanya ta a wadda tafi ta kowane yaro tsada a gidan,makarantar da duk wani mai ji da kansa a katsina nan yake kai 'ya'yansa.sai wani babban abin takaici a gurin hajiya sauda yadda kirkir MIMI ta ki lslamiyya. Da ta dage sai an sa MIMI,hakan ya hakura aka sa ta,in ta je bata komai sai kuka da birgima,rannan wani malami ya dan dake ta,saboda ta ki yin shiru kuma ta ki zama ta kage a tsaye,ai ko ya gane kurensa,domin 'yan sanda alhaji bashir ya kirawo wa malamin.lokacin da MIMI ta sanar da shi cewa malaminsu ya duke ta,'yan sanda suka rufe shi,ya ce a rama wa 'yarsa dukan da yayi mata,domin shine mutum na farko daya soma dukn ta.hajiya sauda ta yi bakin ciki matuka,haka nan ita ce taje ta yi belin malamin tare daba shi hakuri.tun daga lokacin ta kawo idanu ta zuba wa mijinta da 'yarsa,ya ce ta daina zuwa lslamiyya,wai sauda ta dinga koya mata a gida,ai ita da ilimi. sauda ta ce,ai ba zai yiwu ba,a ce baza tayi lslamiyya ba,yaushe za ta san kanta bare addinita.sai ya ce,ai ita mace ce,in ta iya na sallah tunda ba waazi za tayi ba,ba limanci zata yi ba ya ishe ta.sauda ta ce,ai kuwa a dai rayu cikin jahilci.
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (50)Tun daga lokacin MIMI bata kara lslamiyya ba, hajiya sauda sai ta dauki matakin tsare ta da bulala tana koya mata,in ta kiya sai ta zane ta.a kan haka suka yi rikici,wai bata son MIMI,shi ko sai ya dauki matakin tafiya da ita duk inda za shi.ta zama tamkar jaka,shi ke kai ta boko ya kuma dauko ta,ko da yana ofishinsa ne,lokacin tashi yayi zai bar komai ya je ya dauko ta.ta na gurinsa,sai zai bar ofis sannan sun koma gida tare.ln ko za shi wata kasa ko wata jihar,to fa zai kashe mata makaranta,tan gefen damansa. hajiya binta tana matukar bakin cikin abinda MIMI ke yi,tamkar ta kashe yarinyar ta ke ji.cikin haka sauda ta haifi 'yan biyu duk mata,hasana da husaina,ta yi murna sosai,tana zaton tunda ga wasu yara mata 'yan biyu ma abin shaawa,to lallai mijin na ta zai rage son MIMI,za su ture mata gwamnati ko ta samu ta yi mata tarbiyyar da ta dace,amma me?sai yana cewa,MIMI fa dabam take,da duk wasu 'ya'ya da ya haifa baya da kuma wanda zai haifa nan gaba. haka hajiya sauda ta kawo ido ta zuba masu, wai sai data kai MIMI ba ta maimaita kayan sawa,sai in ta yi raayi,ci-banza-ci-wofi shine abincinta.amma ba wai abincin kirki ba,wanda aka dafa ba,haka hajiya sauda ta yi ta haihuwarta a kai-a-kai,ta yi abdullahi sai ameen,sannan umar da sadik,a jere ta yi ta haihuwarsu,amma har lokacin MIMI ita ce ta gaba goshi.lokacin da hajiya sauda ta samu cikin husna, lokacin ne ita ma hajiya binta ta samu nata rabon. sauda tayi mata murna sosai ita mata yi farin ciki matuka.kasan cewar wannan ne farko da zata ga kwanta aduniya,lokacin data haihu an samu mace aka sa mata zainab,kishin MIMI yasa suke yawan rigima da mijin,ita wai dole sai yaji da 'yarta kamar yadda ya keji da MIMI. A wannan lokacin ne ya gina wani katafaren gidan gona a malumfashi,kuma ya gina wani gida a cikin garin malumfashi don haka sai sauda ta bashi shawarar ya maida daya daga cikinsu can tsakanin ita da hajiya binta,don ita kan bata son rigima ta gaji da takalarta fada da binta ke yi kan,
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (51)MIM.ya yarda kuma ya dauki hajiya binta ya maida ta malumfashi, bayan husna,sai cikin hasina shima bata yaye husna bata same shi.wani sabon al'amari,wata jumaa sauda tana daki kwance guraren shadaya na rana,sai jummai mai yi mata aiki ta yi sallama ta ce, hajiya kin yi bakuwa.ta fito taga mace wayayya kuma gogaggiyar 'yar boko,daga ganinta kuma 'yar masu hali ce,ko kuma mijinta mai hali ne.sauda ta ba ta mazauni, ta sa aka kawo masu abin sha.suka gaisa,sauda ta ce, sai dai bangane ki ba fa? bakuwar ta ce,suna na nafisa kuma daga abuja na zo nan,na san cewa ba ki sanni ba.amma ni sai ta dan yi shiru,sauda dai ta ji gabanta yana ta faduwa. cikin zakuwa,ta ce,ina jinki?bakuwar ta ce,za kiyi mamaki idan na ce miki ni matar mijinki ce?gaban sauda ya fadi cikin daga murya ta ce,me ki ka ce? bakuwa ta ce,ni matar alhaji bashir ce maigidan nan.jikin sauda ya soma bari ta ce,karya ki ke yi, mijina ba zai yi aure ba tare dana sani ba wallahi. Nafisa ta daga mata hannu tare da cewa kar ki rantse,domin mun yi aure da shi shekaru bakwai kenan.ta nuna babba daga cikin yaranta ita ce na'ima kuma ita ce 'yarmu ta fari.sai wannan sunan ta suhaila,sai kuma wannan karamin ahmad.na'ima sa'ar abdullahi ce danki,kuma inda MIMI 'yarki tana nan zata shaida miki,domin ita kadai kawai ta sanni,ta san yara na a duk lokacin da alhaji ya je abuja MIMI tana zama a hannu na ne. Na dade ina son ya kawo ni in ganku iyalinshi,ku sanni amma yaki sai ya ce, zai kawo ni,sannan wai baya son ki tada hankalinki, ni kuma naga cewa akwai mutuwa.shi yasa tunda ya sanar dani zai tafi china ni kuma na dauri aniyar zuwa mu gana daku saboda halin rayuwa.hajiya sauda jinta kawai take yi tamkar a cikin mafarki.sai da ta lallashi zuciyarta sannan