Showing 6001 words to 9000 words out of 127530 words

Chapter 3 - CANJIN RAYUWA

16 Oct 2024

8150

zaman hularsa,ya sa hannu ya shafi kumatun ta, ki ci gaba da yi min addua sauda,ke ce kurum ki ke fada min son ranki in ji ban ji haushi ba.ya cire takalminsa tana fesa masa turare ya ce,ban sani ba ko zamu gama tattaunawa da wuri ko ba zamu gama ba, amma ko yaya ne dai daga can zan wuce malumfashi. in duba su binta da yara sannan in kewayo gona ta, na jima ban leka ta ba.inda lokaci zan shiga masari can ma na jima ban je ba.kin ga sai na kwana kenan,gobe zan dawo in dauki uwata mu koma inda muka fi wayo.ta ce,allah ya tsare sai ka dawo din amma batun tafiya da MIMI ne nake tunani a kai.ya kalle ta, kamar yaya?ta ce,sai ka dawo dai allah ya tsare,ya dan tabe baki amin.suna fitowa falo yara suka nufo suna yi masu sannu da fitowa tare da gaishe shi,ya amsa da daidai,ya kalli usaina,MIMI fa?ta ce tana kwance dady,ya ce,shikenan zamu yi waya.hajiya ta raka shi har mota,ba sabon abu bane,haka ta saba tun suna da kuruciya.falo ya kacame,yaran suna ta karin kumallo,sai hayaniyarsu da karar kofuna.MIMI ta fito sanye ciki riga da wando masu dan kauri na barci. sauri ta ke yi,tare da fatan allah ya sa dad dinta bai fita ba,don ba za ta taba bari ya fita ya bar ta ba.ta iso gurin hajiya,fuskar ta babu annuri ta ce,ina kwana hajiya?ba tare da ta dube ta bata ce,lafiya lau.MIMI tayi tsaye shiru,tana son yin magana amma tana tsoro.hajiya ta dago ta dube ta,ga kayan shayi can a kan dining,na san ba kya shan kunu,ta ce tam!ehemm!da ma zan gaida dady ne,yana ciki ne? hajiya ta ce a'a.
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (16)Ya tafi malumfashi sai gobe zai dawo.MIMI ta zaro idanu yaya dady zai min haka ya tafi ya bar ni,ta kalli hajiya wanda ta soma watsa mata harara ta ce,hajiya don allah ina waya ta?hajiya ta ce,sai za ku tafi zan baki,don ni ba za kiyi mani chatin din naki ba a nan,ki karya ki je ki yi wanka,in malamin su hussai ya zo zaki bisu,ki je daukar karatu a gurinsa.ina sa ran ma alhaji ba zai tafi da ke ba,nan zai bar ki sai kin san addininki za ki tafi,ko da zaki cinye hutun ki a nan. cikin sauri MIMI ta koma daki cikin kuka sai da tayi me isarta ta shiga wanka,a fili kuwa fili kuwa fadi ta ke, allah ba zan zauna ba, shi ya sa na tsani zuwa katsinan nan.dolenta ta saka atamfa riga da siket,a cikin durowarta ta ciro don tana da kaya a nan gida, duk lokacin da aka yi wasu usaina sai an yi mata.ta shirya tsaf ta koma kan gado ta kwanta tana tunanin yadda za ta yi.amma ko ta halin kaka baza ta zauna cikin irin takurar ba.can ta hango wayar hasana kan durowar ta.cikin sauri ta tashi ta dauko,layin dad ta kira wanda ta san in ta kira zai dauka da sauri,cikin kuka ta soma magana,bayan ya daga dad kaga hajiya ta dauke min waya ta,kuma wai ba zan tafi ba,ni dai dad wallahi bazan zauna ba.ya ce,ya shiru uwata kar ki damu ba zan barki ba ni ma,yanzu me kike so?ta ce,phone di na,ya ce,shikenan zan ce ta ba ki,kin ci abinci?ta ce,aa ya ce,to kije ki ci zan sata baki wayarki kin ji? ta na zaune a kan dining ta hada shayi tana sha da cokali cikin hankali don ita sam bata da hanzari,tana kallo lokacin da hussaina ta kawo ma hajiya waya ta ce,dady ya kira,ta daga.ta na jin lokacin da hajiyar take cewa,tsaya kaji alhaji, sai kuma tayi shiru,da alama ya katse ta ne,ya hana ta magana,don taga hajiya tayi shiru,amma ranta a bace yake.sai kuma tace to alhaji naji zan bata, amma bana son chatin din nan data keyi.MIMI ta yi murna,a ranta tace dady na kenan,ta nufi daki da murna,alhaji ya ce,kar ki damu sauda,'yarki mai kamu kai ce.ita da kowa ya shaida ko saurayi ba.
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (17)Shi yasa nike dubawa don in samo mata miji wanda zai kimanta min ita,ya bata kulawa fiye da wanda take samu a guri na.
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (18)Hajiya ta ce umm!allah ya taimaka,ai ni dana zaci ma baza ka iya auradda ita ba(cikin gatse tayi maganar)ya ce,kash kin ji ki da wata magana kuma sauda,in ban aurar da ita ba ai kuma na cuce ta.ina maki kaga an taba haka?ke dai kiyi mana addua,ta ce,allah ya taimaka,kun gama ganawar ne?ya ce,eh,yanzu haka muna hanyar malumfashi sai na dawo ta ce,allah ya tsare,ka dawo lafiya,ya ce, amin,ga dai uwata nan amana naba ki,katse wayar yayi ba tare da ya jira jin amsa daga bakinta ba.ga zaton MIMI tana aje wayar alhaji zata zo taba ta tata,amma sai taji shiru. ta sake fitowa falo nufin ta kila hajiya ta ganta ta tuna,idan ta manta ne, amma sai taga hajiya ta ci gaba da lamuranta.yaran duk suka yi wanka suka fito,husna da hasina suka shiga falo da gudu suna cewa,ga malam nan yazo.ga mamakin MIMI sai ta ga duk yara sun rude, wasu sun dauko alkur'anin su suna karantawa da sauran littafai da yake masu.a ranta ta ce ni ko bari in ga wanene malamin ,kai har naji na tsane shi tun kafin in ganshi.a zaton ta nan zai shigo sai ta ga abdullahi da umar da aminu da sadik sun soma fitowa bayan dawowansu sai zainab da hasana da hussaina suka fita. hasina da husna kuma sun dukufa suna ta karbarma juna hadda,kafin a zo kansu.MIMI ta tabe baki tare da cewa,wahalar da kai,basu dade ba suka dawo.su hasana sun mike kenan hajiya ta fito daga daki ta ce,ke ma tashi kije, ta nuna MIMI ta hada rai,sai dai bata da damar yin musu,don babu alhajin da zai tare mata.hasana ta ce. yaya MIMI sai kin sako hijabi fa,ta banka harara,ban dauko ba,ina wasa da ke ne?in ki ka kara yi min magana sai na mare ki. suka yi shiru suka wuce,ta warware dan kwalin kayanta ta yafa,tana biye da su har falo baki,kafin su shiga sai da suka kara gyara hijabansu suka yi sallama suka shiga,ta tsaya tana mamaki wai malami ne suke yi ma bare-baren, malamin ma wai na lslamiyya,ita malami ko na boko bata dauke shi wani abu ba,face bawan ta mai ci a karkashin su.bare da ba zata iya,
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (20)Saboda ba son karatun ta ke yi ba.ka soma mata daga fatiha don ba na zaton ta iya,don allah malam lsmail kar kayi mata da sauki.lsmail ya ce, ba komai hajiya.amma ta saka hijabi ta ce,to ba komai bari in sasu hasana su kawo mata,in ta ki yi ka dake ta ko ka kira ni. hajiya ta fita shi kuma ya kai duban shi gare ta, MIMI ta cika tayi tam.ya na zama hasana tana shigowa da sallama,shine ya amsa,ta ce,yaya ga shi, harara ta watso mata,ta ki amsa,hasana ta aje a hannun kujeraq da take zaune ta fita. ya kalle ta,malama ki saka hijabinki mana,cikin sauri ta dago kai ta dube shi duban tsana mai tsanani,domin ba a taba ci mata mutunci kamar yau ba a gaban kaskantacce irin wannan.ba a taba rena mata wayo ba kamar yadda shi din ya yi mata,ya ganta sarai,amma ya ce,bai ganta ba.abin yayi mata ciwo fiye da abinda hajiya tayi mata.ta harare shi sama da kasa sannan taja tsaki, malam baya daukar reni,sabi da haka sai ya hada rai tare da rufe alkuranin shi. ta ce kai waye suna da ake kiranka? ina son ka sani na wuce ka rena min wayo kuma kai baka isa ka koya min karatu ba.ya daga hannu tare da katse ta da cewa ke.ba ki da ladabi ne? gaskiya ba tarbiyyar nan gidan ba ce,domin yaran gidan nan mazansu da matansu nayi shedar su guri ladabi game da sanin darajar mutane,ke ma ina yi maki nasiha ki canza.kuma ina son ki sani karatun nan in kin yi kin ma kanki ne bani ba,don haka ka da allah yasa ki yi,ya mike ya fita abinsa. yana jiyo tsakinta gami da cewa, talakan banza kana ci a karkashin mahaifi na ka nuna ni da yatsa,to bari ka gani lokacin barin ka aiki yayi.har ya tafi ya dawo ke ma dukiyar daki ke takama ba taki ba ce,ta mahaifin ki ce,ina son ki sani ba keki ka dauke ni aiki ba bare ki sallame ni.ba kuma maula nake zuwa yi a gidanku ba,ina son ki san wannan.kafin ta sake yin wata magana ya wuce ya barta cikin takaici,lallai sai nayi maganin sa,shine mutum na farko a tun tasowar ta da ya taba fada mata abinda ya ke so,
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (19)Face bawan ta mai ci a karkashin su.bare da baza ta iya bambamce shi da maigadi ko mai sharan gidansu,kosawa ma ta yi ta shiga ta gani wane gaja ne? ta jingina da kofar,sannan ta kai kallonta gurin shi,yana zaune kan kujeran zaman mutum daya sanye yake da jallabiya mai ruwan madara mai dogon hannu da maballi a hannu,tare da kwala a wuyarta.ga wani dan ado da zare mai ruwan kasa da aka yi a wuyar da hannun rigar,bata kai can kasa ba,irin dai shiga ta sunna,hular kanshi baka ce irin wanda ake kira minista. ya na rike da alkurani yana bude inda suke.su kuma su hussaina suna zaune a kasa kan kafet a gabanshi duk suna rike da alkuraninsu,MIMI ta tabe baki tare da harde hannuwanta a kirjinta,tana kare masu kallo.a ranta ta ce,tabdi,ai ba a yi mutumin da zai zo gidan ubanta ta zauna a kasa yana kan kujera ba.malam lsmail ya dago ya kalli bakin kofa da kyawawan idanunsa,duhun mutum ya gani,ya sa shi kallon gurin ya kalli MIMI da ke tsaye ta watso masa wani kallo da ba zai iya fassarashi ba.ya mayar da kanshi ga abinda yake yi.su hussaina suka ci gaba da kawo masa hadda yana yi masu 'yan gyare-gyare, suka kamalla,sannan suka soma sauran littafai. ta shiga ta zauna tare da daukan rimote ta kunna tv, ya dago ya dube ta, tamkar zai yi magana,amma sai ya fasa. ya san da gadara tazo, bayan su hussaina sun kamalla,sai hussaina tace, yaya kizo mun gama,ta kalle su cikin harara,ku fita mana, suka fita suka je suka sanar da hajiya ko mai.ita kam suna fita ta mike tana tafiyar nan tata, ta isa kan kujerar gefen shi ta zauna. ya dago ya dube ta,ya mike tare da tattara littafansa,ya nufi fita,a bakin kofa suka ci karo da hajiya zata shigo,ya dakata ta kara so suka gaisa,ta ce, har ka mata karatun?ya ce, wace kenan?ta ce, MIMI, bangan ta ba ai,hajiya ta ce aa ta shigo ciki falon, ta ce gata nan fa,ya dawo cikin falo,ok!wannan ce? na ganta amma ban zaci karatu za ayi mata ba.ita kuma bata fada min ba. hajiya ta ce,ai ba zata fada maka,
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (21)Kuma tana son ya zama na karshe, takaicinta ma talaka ne shi, ba wani isashshe ba. daf da zai fita daga cikin gidan,abdulkarim ya yi masa sallama,ya tsaya suka gaisa ta hanyar yin musabaha.ya ce,ai ina ta sallama baka ji ba,ya ce, na ga fuskar ka ba walwala ko yaran ne suka hada maka zafi?malam lsmail ya ce,ko kusa ai yaran gidan nan basu da matsala sam, sai dai wata bakuwa da hajiya ta ce a koya mata karatu,amma ba yar ta bace ko?abdulkarim ya sake matsowa kusa da shi,ya ce,ba dai MIMI ba? lsmil ya ce,kamar haka naji an kira ta,gaskiya saboda ita zan iya daina zuwa gidan nan in har zata dinga zuwa karatu.abdulkarim ya ce,kai mata nuna maka halinta kenan,don allah kayi hakuri zan fada ma hajiya, kuma ina zaton ma gobe zata tafi,lsmail ya ce, shikenan ba damuwa. suka yi sallama ya fita, abdulkarim ya nufi ciki kai tsaye zuwa falon hajiya, duk suna falon,MIMI kuma tana kujerar dining,ranta cinkushe,ya kalli hajiya,ke ki ka tura MIMI tayi karatu gurin lsmail,ta ce tayi masa rashin kunya ko? abdulkarim ya ce,ta yi masa kenan tunda ya ce, matsawar zata dinga zuwa gurinsa daukar karatu to kuwa zai daina koyar da yaran gidan nan. hajiya cikin fushi mai tsanani ta rufe MIMI da fada,ta ce,in kika sake na samu labarin kin yi sanadiyar koran malamin nan sai kin sha mamakin abinda zan yi miki,sai kin yi zaton ban sanki bama,sam bare ki tuna cewa nice na haife ki.don malamin nan ya fi min ke amfani,MIMI ta sa kuka,hajiya ta ci gaba,tunda na lura karatun ne baki so,to sai kin yishi,bari alhaji ya dawo nan zai barki sai nayi maganin abinda ke damun ki a cikin kanki. MIMI ta fada daki tana kuka. hajiya ta kira layin malam tana bashi hakuri a kan abinda MIMI tayi masa,yace babu komai ai yarinya ce. washegari misalin shadaya da rabi alhaji ya dawo.ya iso cike tam,ya ce,a ba MIMI wayanta, amma ba a bata ba.sai dai yadda ya samu hajiya rai bace kamar ma har kuka tayi,sai kuma ya juya da tambayar shi kanta yana son jin abinda ya same ta ciki,
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (22)Damuwa mai tsanani irin wanda bai taba gani a fuskarta ba,ta ce,ko kaji bazaka magance mun abinda ke damuna baya tausasa murya haba sauda yaya zaki ce haka?daga lokacin da muka zama maaurata shekara talatin da bakwai zuwa yanzu kin taba samun kanki cikin matsala ban taimaka miki ba?ta dube shi,karon na san bazaka...ya daga mata hannu dole ta dakata ya ce.amsa min kawai. ta ce,ban ce baka taimakamin ba alhaji,amma karon na san zai yi wuya, ya kama hannunta. matsalar kudi ce?ta ce,aa ni da yar gwal dinka ce MIMI,ta kalli fuskarsa yayi dan murmushi,ki ce abun me sauki ne,me ya faru?ta ce,ina son dai ka bar ta a nan saboda sam bata san komai kan addininta na musulunci ba. sallah har da kuka tayi,saboda allah a ce kamar MIMI shekararta nawa?amma bata yin sallah,malamin yaran nan lsmalil don ance taje ya koya mata karatu kurum, ta je tayi masa rashin mutumci. sannan ta toge tana jiran ka dawo ta ce ka kore shi.to bazan yarda ba,ita kanta ma dole ta zauna ya koya mata karatu,don baza ta koma bata yi tazama cikin jahilci, yayi shiru yana nazari.ya san dai komai za a yi bazai bar MIMI a gidan nan ba. ta ce,ai dama na san zai yi wuya ka bar MIMI nan,to ina son tunatar da kai iyaye abin tambaya ne game da kiwon da aka ba suna 'ya'ya a ranar gobe kiyama, ta mike ta fita abinta. ya fito falo.hussaina tana yin home work ya ce,ke ce da MIMI ta same ni a daki na.itama cikin kuka wiwi ta cewa dady,don allah ka kori malamin nan wallahi na tsane shi.tunda nake ba a taba yi mini abinda yayi min ba.ina son in nuna mi shi talaka ba komai bane a guri na.alhaji ya ce,uwata yi shiru ki daina kuka.zauna,ta zauna a kan kujera shi kuma yana bakin gado ya ce,MIMI ina son kibar batun koran yaron nan,domin mahaifiyarki mata zo min da zancen.ta bukaci in barki a nan ki kare hutun ki,domin ta lura baki cika son ibada c,kuma nima tunda baki son yin sallah bazan amince ba, domin abin yayi yawa kenan MIMI.don gaskiya mahaifiyarki tana da hujjar cewa in barki,
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (23)MIMI ta rude,dad don allah kar ka bar ni,ka san fa ba sa so na. ya ce,suna sonki na sani MIMI,in kin dan zauna zaku shaku ni ma ba a son raina zan barki ba.ta soma kuka wiwi tana fadin dady kawai ka ce ka daina so na,please dady kar ka barni ba zan zauna ba.ya dafa ta,shikenan naji ki yi shiru zan tafi dake,amma kin san dole sai ta bata rai ko?ta ce,dad in mun tafi zata huce,ya ce aa dole mu sunkuyar da kai mu tafi da yardar ta.ta yi shiru tana tunani,ya katse tada cewa, dole mu samu wani malami wanda zai dinga koya miki karatu,don ni maba zan so a ce 'ya ta mai kyau kamarki,bata san komai a cikin addininta ba take wata dabara ta fado wa MIMI ta ce,dady me zai sa bazaka daukar min wannan malamin ba? ya kalle ta,ke kika ce kin tsane shi zaki ce a daukar miki shi?ta kirkiro murmushi,dady naga yanda hajiya ke son karatun shi ne.sai naga in shine zata fi saurin yarda in tafi.yayi 'yar dariya me wayo kawai,to zan shawarce ta,amma zaki yi karatun ko?don na sanki duk abinda kika ce kin tsana,tabbas kina nufin abinda kika fada,ta ce,zan yi dady.ya girgiza kafadarta cikin jinjinawa 'ya ta.kira min mahaifiyarkin in lallaba ta ta amince ina so ki bata hakuri a bisa laifukan da take tuhumarki,

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login