Showing 39001 words to 42000 words out of 127530 words

Chapter 14 - CANJIN RAYUWA

16 Oct 2024

8156

ta ja motar zuwa bankinta na karamin asusunta,inda ta kwashe kudinta kaf.ta nufi babban asusun da ke wani bankin daban,ta dibi dubu dari biyu.za ta kara sai kiran dad ya shigo.ta daga ya ce,MIMI kina ina ne?ta ce, ina banki ne.dad ya ce,yaya kika taba wannan account din MIMI?ta ce,dad ba ni da kudi ne,kuma zan yi gyaran jikina ne.ya kalli alhaji akilu,ya ce,shi ke nan ya isa,ki bari zan ba ki kudi. kar ki kuma cira daga wannan account din,ina son yi miki wani tsari ne da kudin.za ki yi kasuwanci kina daga gida,kuma na manyan kudi kin gane?MIMI ta ce,eh dad ba zan kara cirewa ba.ya ce,shi ke nan. alhaji bishir cikin dariya ya ce,ka ji 'yar kwal uba? wai tana fadin bata so,amma ta zo tana dibar kudi wai za ta yi gyaran jiki.suka sa dariya.alhaji akilu ya ce,me na fada maka?kiyayyar mata ba ta zuwa ko'ina.amma shi ma abbas din ai shi ya dace ya ba ta kudin gyaran jikin. alhaji bishir ya ce,ai ita da shi duk daya ne.ka rabu da shi,zan ba ta.alhaji akilu ya kira layin abbas.bayan ya dauka,ya ce abbas ya baka bai wa amaryarka kudin gyaran jiki ba?abbas ya ce,dad ta ki ba ni damar in san abin da take bukata ne.amma zan ba ta anjima. ya ce,shi ke nan ka je ka ba ta.ka lallabe ta,ka san yarinya ce.abbas ya ce, insha allah dad. MIMI gida ta wuce ta adana kudinta da duk abin da ya kamata ta tafi da su,amma banda kaya. lsma'il ya dangana har zuwa ranar ashirin da tara da alhaji bishir ya yi musu albashi.duk da kin karatun da MIMI ta yi,bai sa alhaji canzawa daga dubu darin da ya alkawarta zai ba shi ba.lsma'il yayi ta juya kudin a cikin dakinsa,yana farin ciki.sam bai taba rika su ba a hannunsa ko na wani ma bare nasa.lalle goben nan sai katsina,ya je ya biya kudin gaisuwa,ya hada kayan sa rana,ya sai ma zainabu waya,yayi alheri,yayi sabbin dinkuna,yana ta baje burinsa.nan ya kira mahmud ya sanar da shi cewa gobe yana tafe.
[01/10 9:45 pm] Abdul: (4)Tun dare yake ta shirin sa,washegari ya kira hajiya sauda ya fada mata cewa yau yana son zuwa gida ya ga 'yan uwa.ta ce ba laifi,sai ka iso.ln ka zo kuma don allah ina neman ka.ya ce babu matsala.sai dai ina son don allah ki sanar da alhaji sbd ban san lokacin da zai fito ba.ta ce,ya ba ka albashi dai ko?ya ce, wallahi ya ba ni.ki yi min godiya.ta ce,to zan sanar da shi yanzun nan. ba a yi minti talatin ba, sai ga hamisu direba ya ce lsma'il ya je in ji alhaji.a falo ya same shi.ya zauna,ya gai da alhajin cikin girmamawa.alhaji ya ce, sauda ta kira ni,ta sanar da ni cewa zaka je gida yau. haka ne?ya ce,eh alhaji.lna son in je in ga 'yan uwa ne. alhaji ya ce,da fatan ba mu takura maka ba ko?ina nufin ka ji dadin zama da mu?lsma'il ya ce,na ji dadi sosai.alhaji ya ce,to ina fatan za ka dawo.lsma'il ya ce,eh to,na ji ana cewa za a yi wa wadda na zo in koyar da ita aure,shi ne ban sani ba ko hakan yana nufin ni ma na gama aikina ke nan?alhaji yayi murmushi,ai in na lura ita din bata yin karatun,amma kannenta suna yin karatun. kana yi mana salla.ga yaran nan suna yin karatu sosai,suna yin salla a kan lokaci.wannan ya fi min komai.yanzun ma da ka ce zaka je gida din,na kira ka ne in ji ko kwana nawa za ka yi?lsma'il ya ce,to ina ganin dai zan yi kamar sati daya.alhaji ya ce,har sati daya?na zaci baza ka wuce kwana uku ko biyu ba.har me zaka yi haka?lsma'il ya ce,eh to ina so dai za a sa ranar aurena ne tukuna.alhaji yayi 'yar dariya,oho haka ne?to ba damuwa.allah yasa alheri.ya laluba aljihunsa,dubu biyar ya kara masa.ga wannan kayi kudin mota.ka amshi lambata gurin sauda.ln ya so in ka tashi kira na.sai ka kira ni kai tsaye,ba sai ka bita gurin hajiya sauda ba.lsma'il ya ce,to na gode sosai. bayanan fitarsa ne momy nafisa ta ce,na lura yaron nan yayi maka ko?alhaji ya ce yana da hankali sosai.lna son mutum haka.har gareji, hamisu direba ya kai lsma'il,bayan yayi sallama da dukkan maaikata gidan.
[01/10 9:45 pm] Abdul: (5)Kowa yayi kewarsa, damuwarsu kar ya dade ko ya ma ki dawowa. shida na yamma daidai ya isa gida.matasan da suke zama a gindin bishiyar da ke kofar gidansu suna nan zaune kamar yadda suka saba.hirar ta kwallo ce sai ta siyasa.dukkansu sun juyo suna yi wa lsma'il sannu da isowa,bayan dayansu ya sanar da su cewa ga lsma'il nan ya dawo.ya isa gurinsu ya babba su hannu suka gaisa.suna ta yi masa murna da samu aiki a abuja. wasunsu har suna cewa.ustaz ka ga yadda ka yi kyau kuwa?gaskiya abuja ta amshe ka! shi dai godiya yayi musu,ya shige gida.kai tsaye cikin gidan ya shige.matan gidan suna ta haramar sauke girki, sallamarsa suka ji.fatu ce ta soma ganin sa.cikin irin faraar da bata taba yi masa ba ta ce,ga yan abuja,ga yan abuja!nan dai aka yi ta masa sannu da zuwa.ya amsa cikin jin dadi da mamakin fatu.a wata zuciyar ya ce,kila don dai ta daina ganin sa ne. dakin lnna ya shiga ya gaishe ta,sanan ya mika mata tsarabarsu.ya tashi ya koma dakinsa ya bude,yayi kakkabe-kakkabe a gurguje,sbd lokacin salla ya kusa.ya shimfida katifarsa,ya dauki bokitin ruwa wankansa ya kulle kofar da makulli,ya nufi cikin don yin wanka.da ya dawo,yayi alwala ya zura jallabiyarsa ya sake kulle kofa ya nufi masallacin kusa da su. bayan idar da sallar ya dawo ya zauna ya kasafta kudinsa,ya adana sauran ya canza kaya tare da fesa turarurruka masu kamshi.ya yi kyau matuka cikin shadda mai ruwan toka,ya murza hula.ya kosa ya ga zainabu,ga shi tunda ya shigo garin katsina yake ta neman layin mahmud. cikin nishadi yake takawa,duk da lokaci bayan lokaci gabansa yana faduwa.sam ba ya ganin nisan gidan su zainabu daga nasu gidan.a kafarsa ya taka.har ya je kofar gidan,sai kuma ya tuna bai zo mata da tsaraba ba.don haka ya juya,ya tare dan acaba ya hau,sai wani shago ya je inda ya siyo mata waya ta naira dubu biyar.ya sake komawa kofar gidan.kamar an turo shi,sai ga kanin zainabu.kafin lsma'il yayi masa magana har ya juya da gudu ya koma ciki.a ran lsma'il ya ce,
[01/10 9:45 pm] Abdul: (6)Yawwa kira ta,kai ma ka zo ka dan ja wani abu.kwarai idanunsa suka kosa su ga fitowarta.cikin duhun zauren ya ga alamun fitowar mutum.a zatonsa zainabunsa ce,har da gyara tsayuwa. muryar mahaifiyarta ya ji daga sama tana cewa,sannu malam lsma'il da zuwa.cikin faraa ya ce,yawwa lnna. cikin girmamawa ya gai da ta.ta amsa.ta ci gaba da cewa,sai ka samu labarin zainabu ta yi aure ko?ledar wayar da ke hannunsa ta subuce,ta fadi a kasa.cikin in-ina ya ce,mene kika ce lnna?ta ce,zainabu ta yi aure.allah ya sa ba rabonka ba ce.kodayake laifinka ne. tunda baka kawo ko da sallama ba.lsma'il ya ce, inna don allah kar kiyi min haka.da shirina na zo.sai an sa bikinmu zan koma.ta ce assha!ai ka bar shiri tun rani yaro.tana gidan alhaji lawan.ba tare da jiran sake ji daga gare shi ba ta koma ciki. lsma'il ya tsuguna,ya dauki wayarsa jiki babu karfi,zuciyar na tafarfasa,ya nufi gidan yaya amina.da kyar ya kai. sai ganin mutum ta yi babu ko sallama.kan tabarmar da ya gani a shimfide ya zube zaune tare da dora kansa a guiwowinsa.cikin fargaba ta ce,lsma'il lafiya?ta tambaye shi fiye da sau biyar,ya dago kai da kyar ya ce,lafiya lau.ta ce ina fa lafiya,dube ka fa?me ke maka ciwo?ya girgiza kai, babu. ya sake dosa kansa a kan hannuwansa wadanda suke sarkafe a guiwowinsa.ya ce,yaya ashe zainabu ta yi aure?ta ce,au da ma damuwar ke nan?ta sake tausasa murya,ka yi hakuri.allah ya rubuta cewa zainabu ba matarka ba ce.nan ta shaida masa abin da ta ji game da auren. ya ce,mahmud bai kyauta min ba.me zai sa muna waya,amma yaki sanar da ni?ni na san da a ce ina nan ba yadda za a yi a raba ni da ita.sam mahmud bai cika alkawari ba,kuma bai rike min amana ba.yaya amina ta ce kar ka ga laifinsa,domin a boye duk aka yi komai.sai daurin aure aka ji.lsma'il ya sauke ajiyar zuciya,wasu zafafan hawaye suka zubo kan kumatunsa.ta ce,haba don allah lsma'il,sai ka ce ba namiji ba?kamar baka da ilimi.ka fa san komai mukaddari ne.ka yi hakuri,zainabu ba rabonka ba ce.
[01/10 9:45 pm] Abdul: (7)Allah zai baka wadda ta fi ta komai.lsma'il ya ce,shi ke nan yaya na gode.ya ciro dubu uku daga aljihunsa, ga wannan yaya.ta amsa tana fadin, har da kudi haka.ya ce,ba yawa.lna ganin gobe ma zan juya kawai,da ma da kyar alhajin ya bari na taho. ta ce,haba dai ka dan kwana biyu mana?ya ce,aa ba zan iya zama a garin nan ba,ina tuna zainabu.lna bukatar cire ta daga raina. ya mike a kasalance,ya dauki ledar wayarsa ya ce,to ni sai na dawo.ta ce, ba zaka biyo ba gobe ke nan?ya ce sammako zan yi. da kyar ya isa gida.tunda ya bude kofarsa ya fada kan katifa,bayan rufe kofar ya soma kuka.shi kansa bai san yana tsananin son zainabu haka ba sai da ya rasa ta.ya yi kuka sosai,ya dangana,ya fita cikin dare yayi alwala.gurin allah ya yi ta kai kukansa.bukatarsa allah ya cire masa son zainabu,ya ba shi dangana ya sada shi da mafi alheri. daga bisani ya dauki alkurani,yana karantawa. Kafin wani lokaci,salama ta sauka a zuciyarsa.sai da yayi sallar asubahi,ya soma jin barci. yana dawowa daga masallaci ya kwanta.ba shi ya farka ba sai goma saura. shi ma kwankwasa kofarsa aka yi ya farka.ya tashi da kyar ya zare sakatar.mahmud ne,don haka ya dawo ya zauna. mahmud ya shigo,shi ma ya zauna. lsma'il ya ba shi hannu suka gaisa.ya ce,na yi ta kiran wayarka a kashe. mahmud ya gyara zama.ina sane na kashe,domin bana so ka rike ni a ranka.na san dai zuwa yanzu kaji komai.lsma'il ya tsura ma bakin kofa ido,kamar mai kallon wani abu a gurin. mahmud ya ce,ka yi hakuri allah ya kaddara ba matarka ba ce.lsma'il ya ce,duk da haka mahmud,kai ma na ga laifinka.me zai sa ba ka kira ni ka fada min ba?na tabbata zainabu dole aka yi mata,don tana so na.mahmud ya ce,fada maka ba zai kare ka da komai ba.a lokacin da na samu labarin kwana kadan suka rage a daura aure. amma ka yi min afuwa.lsma'il ya ce,ni yanzu zan shirya in koma abuja.malam yana nan kuwa?mahmud ya ce,yana nan.na dai bar shi a gida. haba dai ka ce yau za ka koma?ya ce.tun jiya katsina ta fita daga raina.
[01/10 9:45 pm] Abdul: (8)Mahmud ya ce,allah yasa hakan shine mafi alheri.amma ya kamata ka dan yi kwana biyu.lsma'il ya ce,in na zauna babu abin da zan yi.da a ce na san da wannan matsalar.lallai da ba zan zo ba.mahmud ya ce,shi ke nan allah ya kai ka lafiya.ko wanka lsmail bai yi ba,ya hada nasa-ya-nasa ya shiga cikin gida yin sallama.fatu ta ce, lsma'il sai ka ji batun auren zainabu.bai san lokacin da murmushi ya sauka a fuskarsa ba.ya ce,zainabu ta yi aure.fatana allah ya bata zaman lafiya.fatu ta yi 'yar dariya,ka dangana ke nan?bai tanka ta ba,ya wuce abinsa dakin lnna.ya shiga ya sanar mata cewa zai koma,ya kawo dubu biyu ya bata.ta amsa tana godiya.ta ce ko ka hadu da yan uwanka?ya ce mun gaisa da asuba a masallaci,amma ga wannan ki basu.ya mika mata dubu uku.ta ce,an gode.allah ya saka da alkhairan.sai kuma kaji wannan yarinyar da kake nema ta yi aure ko?ya ce eh na ji lnna.allah bai yi dani ba.ta ce,duk da haka ma sun so yaudararka ne.ka je ka amshi duk abin da ka san cewa naka ne,lna nufin wanda ka bata.ka kuma lssafa kudin da ka bata, tallar nan duk a amso su,ya ce,lnna a bar wannan maganar kawai.ban bata don in karba ba.ya mike,ya fito,ta ce,to shi kenan allah ya tsare hanya.nan su ma matan gidan ya basu dubu daya,ya dauki jakarsa. Bayan ya ba mahmud dubu biyu,mahmud ya ce, kudin mene ne?ya ce,kudin albashina mana.dana yi niyyar gabatar da abubuwan aurena har zuwa a sa rana.amma tunda babu zancen,gara in yi alheri in samu lada. mahmud ya ce,na gode sosai.gidan su mahmud suka je,inda ya ba malam dubu uku.ya goya shi a mashin dinsa.har za su wuce tasha,ya ce,kodayake ka kai ni gidan alhaji bishir in gaisa da hajiya sauda.sai da suka je kofar gidan,ya kira layin hajiyar ya ce mata ga shi a waje,ta turo abdullahi suka shiga tare.lsmail bai boye mata komai ba game da MIMI na kin karatu ba.ya sanar da ita halin da yake ciki.ta ce,ba komai kar ya damu da batun MIMI tunda aure za ta yi.yanzu ya koma ya ci gaba da abin da yake yi,a kan zainabu kuma tace kar ya damu,
[01/10 9:45 pm] Abdul: (9)Kila ita din ba alheri ba ce a gare shi.ta ce,in da zai yarda ma da ya koma makaranta don zurfafa iliminsa gaba daya a fannin bokon da kuma lslamiyyar ya ce,shi ma tunaninsa ke nan a yanzu suka yi bankwana,bayan ta ba shi wani turare mai kamshi.ya fito mahmud ya kai shi tasha.bai samu motar abuja kai tsaye ba,don haka sai ya hau ta kaduna. suka miki hanya,zuciyarsa da rauni,bai san lokacin da zai warke ba. hajiyar mardiyya,matar alhaji lsa mani,abokin alhaji bishir ita ce ke kwada sallama a falon hajiya sauda.hasina ce ta fito daga dakinsu ta ce,sannu da zuwa maman su nabila.ta ce,yawwa hasina,hajiya fa?ta ce,bari in duba ta.nan hajiyar mardiyya ta zauna kan kajera.hasina ta fito ta ce, tana wanka ne.hajiya mardiyya ta mike,bari in shiga cikin dakin.kawaye ne sosai,har yanzu ba su yada juna ba,don sun fi mazan nasu zumunci,har da matar alhaji kabiru,hajiya ramatu, abokansa na tun ana talakawa. kan gado ta zauna tana 'yan dube-dube. ke kullum aka zo dakinki kal,sai ka ce amarya.daidai lokacin ta fito tana cewa, me kika ce?hajiya mardiyya ta maimaita.sauda ta yi dariya,to ni ke gyra dakina da kaina.ku ko kun fi son na 'yan aiki.ta ce,to meye aikinsu in ba shara da wanke-wanke ba?sauda ta ce,ku dinga duba masu. kullum ina fada muku,suna yi kuna dubawa,kuma gyara musu. hajiya mardiyya ta ce,ke ni zuwa na yi in ji dalili ko kuma laifin da nai miki baki fada min biki ba,sai dai in ji a gurin alhaji.hajiya sauda ta yi tsaki,kin san allah,ban san komai a kan bikin nan ba.ke in takaice miki,yanzu alhaji fushi yake yi da ni.hajiya mardiyya ta ce,a kan me?ta ce,kin san bata son auren,shi ke so.ya kira ni wai in tursasa mata ta yi abin da yake so.sai na nuna masa cewa ba ruwana, yanzu ne aka san da ni?to ni shawara zan ba ta,tursasawa ba.kar ki dada,kar ki raga.daga wannan shine laifina.wai ni ce ke zuga ta.har yau bai sake ce min kala a kan bikin ba.na'ima take fada wa su hasana ta waya wai nafisa ta je dubai siyan kaya.an kawo lefe,an yi kaza,an yi kaza.
[01/10 9:45 pm] Abdul: (10)Hajiyar mardiyya ta ce, amma alhaji bai kyauta ba. ko da keke zuga ta.ai kamata yayi ya baki hakkinki na haihuwa.sauda ta ce,ni ma dai shi na gani. don haka nasa musu ido.ya maki zuwa garin nan sam. ko kira waya yayi.sai ya yi ta wani dake-dake yana magana a cije. hajiya mardiyya ta ce, amma da kin yi masa magana da kanki,ki yi masa bayanin nufinki don ki amshi ragamar auren 'yarki. sauda ta ce,kin san allah ba zan kula auren nan ba.kuma ba zan taba yi masa magana a kan wai ya fahimci ban zuga MIMI ba.mu je a na zuga tan.ita ma ba halin kirki gare ta ba.so nake su gane kurensu,dukkansu shi da ita.mardiyya ta ce,shi ke nan,allah ya kai mu.mu dai za muje biki.ln abuja din ne,in nan ne ma dai duk da mu za a yi,allah ya taimaka, in ji hajiya sauda. Ana saura sati daya bikin ne,alhaji bishir ya zo katsina.bai ko sanar da zuwansa ba.barcin rana take yi lokacin da ya iso. yaran suka yi masa sannu da zuwa.kai tsaye ya nufi dakinsa,ya bude ya shiga.ya zuba jakar hannunsa da hularsa zuwa wayarsa a kan kujera. shi kuma ya zauna a bakin gado.hasna ce ta shiga dakin hajiya sauda ta tashe ta,tana sanar mata zuwan dady.ta sha mamaki sosai, domin sai ya sanar kafin ya isa.ta kalli husna,shi ne ya ce ki kira ni?husna ta ce,aa ya shiga dakinsa ne kawai.sauda ta ce,to je ki ina zuwa.har ta mai da kanta ta kwanta,a zuciyarta ta ce tunda da abin da ya zo gidan ke nan ba za ta kula shi ba.amma sai wata zuciyar ta ce, mijinki ne kina kasansa ki je. ta same shi yana cire safar kafarsa.ta yi sallama, ta shiga.daga bakin kofa ta tsaya tana fadin,sannu da zuwa.alhaji a ciki ya amsa da cewa yawwa.ta zauna a hannun kujera,na ji mamaki,ba ka ce min kana zuwa ba,kamar yadda ka saba.ya dago ya dube

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login