Showing 3001 words to 6000 words out of 127530 words

Chapter 2 - CANJIN RAYUWA

16 Oct 2024

8146

gaskiya ko dai bake ce ki ka haife ta ba?ya aje cokalin hannunshi,na rasa me take miki,ita dai ba ma a kasan nan take karatun ta ba.sai ta zo hutu irin haka,amma sam ba kya ko yin kewar ta. hajiya ta tsiyaya masa lemun abarba,wanda ta hada masa,a cikin kofi sannan ta tabe baki ta ce,halin ta kawai zata canza,in dai tana son soyayyata.yanzu baka kalli shigar da tayi ba? tun daga abuja ka sako ta gaba har katsina, kana mahaifinta ga shi kanta a waje,kayar jikinta duk sun dame ta,wai ita dole ta waye. ya kalli MIMI sannan ya kalli sauda, da dan murmushi,ina laifin kwalliyarta,ni ban ga aibun ta ba,haka 'yan mata matasa irin ta ke yi.ya kalli MIMI,ci kifin ki uwata kar ki damu kin ji?tsaki hajiya ta yi ta nufi dakinta.sai lokacin MIMI ta samu damar yin mita,kaga ko dad,sai da nace ka barni can in gama hutu na,ka ce aa sai na zo, ni daman na san hajiya ba za ta taba so na ba. Ta mike tsaye tare da kallon jikinta,shiga tafa, mene ne aibunta?ya kalle ta cikin sigar lallashi yace, ban ga laifi ba.ita hajiya wai sai tace,sai na saka hijabi da atamfa,ni kuma ba zan iya sa iri wannan kayan zafin ba.na yi karatu na waye ni ba irin su usaina ba ce kauyawa.yayi murmushi,shgwabarta tana burge shi.kallon ta ya ke yi tamkar 'yar shekara biyu. ya mike ya zagayo wajen ta ya dafa kafadarta,kar ki damu uwata.mamanki tana sonki,na san ta ga nafi damuwa da kene cikin 'ya'ya na,kin san don ita ce ta haife ki,shi ya sa fa.in da a ce kamar hajiya binta ce ko nafisa da tuni na sallame su,kin manta na taba kora hajiya binta saboda ke?ta ce na tuna Dad,
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (8)Ya ce to kar ki damu ina son mahaifiyarki ko da bata haifamin ke ba, bare ta haife ki. kina son a ce mahaifanki biyu ba su tare?ta ce ba zan so ba dad.amma ka yi mata magana ta daina matsa min,ya ce zan yi mata, amma ke ma ina son cikin kwana biyun nan ki canza kaya sawarki,ki rinka saka irin wadanda take so.ta ce zanyi in dai za ta bar ni in yi abinda na ke so,ya ce za ta barki mana kin ji,ki dai na kuka.ya yi ta lallashinta har ta daina kuka. suna cikin cin abinci hajiya ta sake fitowa daidai lokacin yara suka dawo daga lslamiyya da sallama suka shigo, ita ce ta amsa sallamar,husna da hasina ne a gaba,suka ce sannu da gida hajiya ta ce yawwa sannunku da dawowa yara na.ina sauran? kafin suba ta amsa sai ga su suna ta yin sallama,da hannu ta nuna masu gurin dining,ga dadin ku,suka nufi gurin suna gaida shi da daidaya.ya dafa kan husna da hasina, su ne kanana a gidan, yana ta amsa masu.MIMI ta hada rai ita ba ta son hayaniya. dady ya ce,ba ku gaida sista MIMI ba.suka kalle ta don suna tsoron ta,sannu yaya MIMI,cikin daure fuska ta ce,yawwa,na amsa duka ne ba sai kowanne ya gaishe ni daya bayan daya ba.hasana da usaina sune 'yan matan da suke bi MIMI a haihuwa.dad ya kale su ku shirya da kannen ku, yau yazo ya kai ku super market ku sayo tsarabarku, don ban riko komai ba, kowa ya je ya zabo abinda ranshi ke so. Yara suka shiga murna hasana da hussaina suka ce dad,mu kam ba zamu je ba.ya ce,saboda me?suka ce,muna da karatun hadda gobe,malamin mu zai zo, bin abdulrahaman.hajiya ta ce,tabbas ba ku da halin fita, in ba haka ba zaku sha dukan tsiya gurin shi.duka kuma?in ji dad dinsu,hajiya tace sun wuce duka kenan?karatu sai da zare ido.abdulkarim ya yi sallam, ya shigo falo suka amsa,ya iso gurin dadin shima ya gaida alhajin.MIMI tana ta chatin dinta ba ta dago kai ba,shima bai ko kalle ta ba. ya dubi su hasana ya ce, kun dawo?suka ce eh! yaya sannu da zuwa, dazun hajiya ta fada mana zuwan ka. mun je dakin ku kana wanka,
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (9) Kuma lokacin lslamiyya ya yi dole muka tafi.ya ce,na ji shigowar ai, ya ya zauna,usaina na fadin,lslamiyya lafiya,munyi murajaa ne yanzun. ya ce, kun kusa fara jarabawa kenan suka ce eh! hasana ta ce,yawwa yaya don allah ka amsar mana hadda in anjima mun yi magariba, gobe da safe muna da malamin gida bin abdulrahaman.abdulkarim cikin sigar tsokana ya ce, bani da lokaci,ku ce gobe zanyi kallon duka. usaina ta ce agaji yaya abdul, bulalarshi akwai zafi,suka sa dariya tare.ya ce,bari mu yi sallah sai in karbar maku,suka ce,yawwa yayanmu mun gode. MIMI daga wurin da take zaune tana jin su tana kuma kallon su,sai ta soma mita,ni na san duk 'yan gidan nan ba sa so na,dole kawai suke gani na,kalli yaya abdul,ko kallo na bai yi ba.alhaji yace,kai! abdulkrim,ya ce naam,ya zo ga ni dad.ya ce baka ga MIMI ba ne?ran abdulkarim ya baci,nan a take fuskarsa ta nuna,cikin wata murya marar dadi ya ce,na ganta mana dadi.shine ba za ka yi mata magana ba? Kafin ya yi magana hajiya ta amsa da cewa, in duniya da gaskiya ita da shi wanene gaba?shine ya kamata ya gaida ta,ko ita ce ya da ce ta gaishe shi?. alhaji ya ce,amma ita bakuwa ce.bayan haka kuma yaushe rabonsa da ganinta?a kalla ya nu na kewarsa gare ta ko?kan abdul yana kasa tamkar ya sa kuka don haushi da takaici.hajiya ta ce,bai gaishe ta din ba.tafi abinka abdulkarim,cikin sauri ya wuce.su hasana ma suka yi dakinsu ita ma hajiya ta juya zuwa dakinta,MIMI ta kalli dad,kawai mu koma kalli fa duk yanda suka watse suka barmu,ya dafa ta karki damu ina zuwa. baki gado hajiya sauda ta zauna ta zabga tagumi,wannan abin ya ci mata rai,a ce mutum kamar alhaji ya dinga irin wannan abu sai ka ce yaro.kirikiri yana gani garkiya sai ya runtse ido saboda son zuciya,bai san cewa haka zai sa kan 'ya'yansa ya rabu ba ne?sallamar shi ce ta katse ta,ta dago ta dube shi,shima ya iso ya zauna bakin gadon.haba hajiya ki sakarwa 'yarki fuska mana?ke ba abin faharin ki bane a ce nafi son 'yarki,duk cikin 'ya'ya na?
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (10) Ya kama hannunta cikin sigar lallashi ya ce,haba sauda kin fa san ina tsananin sonki, sonki ne fa ya shafe ta ko baki lura ba?ta daga ido ta kalle shi,ban musa ba,na san kana so na,amma ni burin na shine ka yi adalci tsakanin yaranka alhaji, ko don gudu rarrabuwar kansu. ya ce,menene na yi mata wanda ban yi masu ba?ta kalli cikin idon shi,ai ba za su kirgu ba,banda nuna tsantsar kulawa a fili, duk cikin yaranka wanene ka kai kasa wajen karatu bayan ita?to indan wannan ne,karatun na su na gida ya fina ta cin kudi sauda. umm, haka dai za ka ce,tunda kana son kare kanka,ya ce, ni dai ina neman alfarma ki sakar mata fuska ki dan ja ta a jikin ki har mu tafi.ta kalle shi,ta rasa me zata ce masa,sai kurum ta ce to. don tana son kawo karshen zancan, ya shafi kumatun ta,na gode,ya matso da bakin shi saitin kunnuwanta,ina son a kyuatata shimfida ta anjima. don na iso da muradin hakan. Ta sake murmushi tare da kallon shi,wai alhaji yaushe zaa girma ne?ta yi tambayar cikin sigar wasa. ya janyo ta jikin shi,wa ya ce miki ana girma da lada? sai dai in mutuwa ce ta dauka.suka sa dariya tare, daidai lokacin aka yi kiran sallar.suka mike, ta ce lokacin sallah yayi bari in fita 'yan mazan nan sai nayi fama sannan su wuce masallaci.tare suka fita ya nufi dakin shi,har lokacin MIMI tana zaune a falo.sai dai lokacin ta koma kan kujerar zaman mutum biyu tana ta chatin. alhaji ya nufe ta yana cewa,mamana kina hutawa ne?ba tare data dago ba,ta ce eh dady.ya ce da kyau.ya wuce dakinsa. hajiya sauda ta dube ta,ki tashi kiyi sallah,ta dago ta kalli hajiyar ta ga fuskarta a daure,ta zabga mata harara na ce,ki tashi ki yi sallah.tsam ta mike ta nufi dakin su usaina inda nan ne take sauka in ta zo,kayan tama cikin suke.sai dai ita bata sm hakan saboda a abuja sasanta dabam, amma a nan hajiya ta hana a yi mata dakinta dabam.ta sami su hasana suna sallah, ta fadi kan gado ta ci gaba da chatin dinta.ga al'ada alhaji in ya fita sallah,
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (11) Yakan kai sha biyu bai shigo gida ba zai yi ta gaisawa da mutane, abokai zuwa 'yanuwa suka ji cewa ya shigo gari.don haka ita ma hajiya bata fito ba sai bayan sallah isha,ta shiga daki alhaji don sake kalailai ce shi,tare da kunna turarukan kamshim daki,ta fitar ma da alhaji kayan barci,ta dama masa fura,ta nufi dakin yaranta don ta tabbatar suna cikin koshin lafiya.daki maza ta fara shiga, umar da aminu suna ta yin home work, abdullahi yana kwance kan gado, sadik yana buga game a tv. ta ce,sarkin game kai ka yi home work dinka? ya ce, eh nayi hajiya ta kalli abdullahi,kai fa bawan allah yau da wuri zaka yi barci kenan? ya tashi zaune kaina ke ciwo hajiya shi yasa ki kaji na ce dad ya bari sai gobe mu je super maket din.don ba zan iya kula da su ba. ta ce,ba sai kun yi haka ba,ya ce,kin shiga daki lokacin ta ce,to ka sha magani?ya ce eh!ta ce to allah ya sawwake,ya ce ameen.ta ce,sadik tashi ka kulle muku kofar ku sai da safe,suka ce,to ta ce,kar fa ku manta da yin addua lokacin barci,suka ce to.ta nufi dakin su husna da hasana da kuma zainab yar gidan hajiya binta, wace ta ki komawa wajen uwarta,tun lokacin da alhaji ya saki hajiya binta,ya kwaso yaran ya kawo su nan.hajiya sauda tace sam ba zai yiwu ba,lallai ya mayar da ita,ta rike kayanta. domin ita kanta ba zata sa araba ta da 'ya'yanta ba.shine da ya dawo da ita ya mayar mata da yaran amma ban da zainab,don kuwa ta kekashe ba9a ta bi su ba. lta ta fi son zama a nan, hajiya sauda ta rike ta,ta hada da 'ya'yanta guda goma sha biyu da ta haifa suka zama sha uku.su kam sun fara barci.don haka ta shigo ta yi masu addua tare da kulle masu kofar dakinsu. hasana suna zaune suna kara ma juna haddar alkur'ani mai girma, ita kuwa 'yar gwal,wato MIMI tana kishigide kan gado.tana ta chatin,kai tsaye gurinta hajiya ta nufa ta fisge wayar da sauri MIMI ta dubi wayar cikin bacin rai.tana ganin hajiya sai ta yi kasa da kai kamar munafuka,kin yi sallar ne? cikin tsawa ta ji maganar MIMI,
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (12)MIMI ta yi shiru, ta ce,ba ki ji niba ne?ta girgiza kai tare da fadin banyi ba. hajiya ta rufe ta da fada bangane ba kiyi ba? Anya ma kina yin sallar na kuwa? ta kalli hajiya cikin sauri tare da fadin ina yi mana,hajiya tace,karya ne kalli agogonki karfe nawa ne yanzu?da har zuwa yanzu baki yi ko sallar magariba ba bare lsha.in na lura musulunci ba ya birge ki,lslamiyya kin daina,duk wani abu da lslam yazo da shi,komi na addini kin mayar da shi kauyanci,ke ga 'yar boko ko?MIMI dai bata dago kai ba,hajiya ta ce,na san ko zaa kashe ki yanzu da kyar in zaki iya kawo mini fatiha cikakkiya. kin zauna kina ta danne-dannen waya,in ba ki sani ba ne gara ki sani,kina cutar kanki ne.rayuwar daki ka daukar wa kanki ba mai dorewa ba ce,don haka ba ta dace da ke ba.ki ta shi ki yi sallar yanzun nan, sakarya marar hankali. simi-simi MIMI ta tashi ta nufi bandaki,hajiya ta ce,tunda abin naki ya soma nisa haka,wayewar taki har ta kai ki da gudu salla,to nan gida za ki kare hutunki.ki dau karatu gurin malamin yaran nan,ki koyi salla tun da bani da tabbacin kin na yi.bari baban naku ya shigo,ta juya ta fita da wayar a hannunta.MIMI daga cikin bandaki,kuka wiwi ta dinga yi,ita kam baza ta iya zam har ta gama hutu cikin takurar ba. a silent hajiya ta saka wayar MIMI ta ja durowa ta jefa.MIMI tana kuka ta yi sallar,su hussaina suna kallonta,ta idar ta fada kan gado ta ci gaba da kuka.don ita amshe mata wayar da hajiya ta yi,ya fi bata mata rai fiye da fadan,don jin ta take tamkar an raba ta da ranta, sam bata nisa da wayarta. misalin shabiyu saura alhaji ya shigo,tuntuni yake ta neman layin 'yar lelanshi,amma sai tayi ta ruri har ta yanke ba a daga ba. hajiya ta shiga ta same shi tana cikin shirin barci,ya kalle ta da wayansa a hannu,MIMI fa?ta kalle shi,in kira maka ita ne?ya lura cikin gatse ta yi masa maganar,don haka sai ya ce,aa dama in ji ko ta yi barci ne,saboda ina ta kiran wayarta bata dauka ba.cikin jin haushi hajiya ta ce oho..
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (13)Na zata ita ma nan zamu kwana tare don kar wani abu ya cinye ta. ya mike tare da kama hannunta,sauda kin canza sani na ba haka kike ba.yanzu kin zama mai saurin fushi.ta kalli fuskarsa,kai da 'yarka kuka canza ni.ya ja hannunta,to zo mu zauna in ji mai zan samu.ya basar da wancan zancen.ita ma sai ta biye masa da cewa,duk abinda kake so.ya tallabe fuskarta kin san mene ne sauda?ta girgiza kai kullum na kalli fuskarki.rana mai tarihi a guri na.hajiya sauda ta ce, ikon allah ni kan da a ce kalmar karatu ce,da sai in ce,tuni na haddace ta,tun muna da kananan shekaru. ya yi 'yar dariya ina jin dadin tuna baya,wani lokacin sai in ji tamkar in mai do lokaci.ta lumshe ido, ai alhaji kuruciya cike ta ke da shirme,in ta wuce sai ayi ta kewarta,
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (14)Ni kaina ina son tuna baya,rayuwa tana da sauri,duk da haka in muna tare,sai in rika jin kaina tamkar 'yar kasa da shekara ashirin.yayi dariya,a haka ni ke kallon ki sauda,kullum na kan ce, lokacin na sauri.ta kwantar da kanta a kafadarsa.allah ya kara mana tsaw rai da rayuwa mai amfani.a kunne ya rada mata amin.da ma an ce soyaya bata tsufa, sai dai masoya su tsufa, allah ka yi mana mai kyau. karfe bakwai alhaji bashir yana ta shiri cikin sauri,hajiya tana taimaka masa gurin saka kaya, rokonsa take yi ya dan sa wani abinci a bakinsa,ta ce don kai nasa a yi kunun gyada da kosai,saboda na san kana so.ya kalle ta,ta na saka masa liks a hannun riga ya ce,ki yi hakuri mata ta,ba komai,na yi alkawarin zan gana da wani mutum ne,wanda na fi wata guda ina neman damar ganinsa. ta ce,duk da haka ka karya zai fi.ya ce sai na dawo,domin in na samu damar da nike nema a gare shi,kasuwanci na zai ninka,in ko haka ta samu yaya kika gani?ta ce, umm! kai dai da ma kullum saurin ka bai wuce kasuwanci,a kasuwanci ina ne ba a sanka ba,duk fadin afirka ina ne sunanka bai kai ba! wane irin kudi ne baka mallaka ba kullum cikin samun riba ka ke. ta mika masa hularsa,me ya kamata ka nema kuma alhaji?yanzu baya ga aljanna? murmushi ya yi,ba tare da yaba ta amsar duk tambayoyin da ta jero masa ba.ta ci gaba, ni dai ba zan gaji da baka shawarar cewa,kamata yayi zuwa yanzu kayi murabus ka bar abba da mukhtar su jagoranci kasuwancinka.ya ce,ni kuma fa ta ce,ka zo mu zauna mu huta,mu karasa rayuwarmu,'yan kananan yaranmu su shaku da kai.ya saki dariya tare da cewa,sauda kenan.in ki ka fadi wata magana sai ki tuna mimi tadinmu na farko da ke.ta ce au!kana nufi maganar ma dana fada shirme ce?ya ce,kusan haka,kina cewa in bar ma su abba ragamar kasuwanci,ki na tsammanin za su yi jarumtar kasuwanci kamar ni? bai jira amsa ba,ya ci gaba da cewa,da ma MIMI ce babba,ko da tana mace na san za ta iya.amma su abba shirme kenan,shi yasa kika,
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (15)Ga ko shawara ce na fi son yi da ita koyaushe ta na bani shawara ta musamman yadda ake fadada kasuwanci a duniya ta cikin yanar gizo.su kuwa su abba bakin ku daya.kullum in takaita kasuwanci a iya gida nijeriya,ni kuma na wuce nan tuni. ta ce,ka fahimce ni ba muna cewa kar kayi kasuwanci da waje ba ne aa,ai bunkasar ka ta isa ka yi kasuwanci da waje.harkar shigo da magunguna ne muka ce ka daina,tunda ana yawan zargin kana shigo da haramtattun magunguna da kuma miyagun kwayoyi.ya gyara

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login