Showing 63001 words to 66000 words out of 127530 words

Chapter 22 - CANJIN RAYUWA

16 Oct 2024

8149

kuma Ismail yana cewa Mahmud, ya
kamata kaima ka tafi. Shi kuma yana cewa, bari dai
in an dibi jininka din sai na wuce. Sallamar wasu
matan ne, yasa su yin shiru daga zancen da suke yi
don jin ko su waye.
Dai dai lokacin mimi ta dangana daga kukan da
takeyi har ma ta yanke hukuncin yadda zatayi. Nata
ganin, abin da zai fissheta, in sun samu sauqi ita da
khalil, zata bishi gidansut tunda shi hajiyarsa tana
sonsu tare, sai ta zauna a gidansu, in ya kammala
karatu sai ayi musu aure, Amma ta daukar ma kanta
alqawarin yadda daddy yace ya barta, ita ma har
abada ba zata sake nemansu ba.
Dama hajiya bata sonta, shikenan zata yi Rayuwar ta
da khalil, ta amince bata da kowa sai shi din.
Sallamar matan ne ta katse mata tunani. Ta daga ido
ta kalle su. Ko cikin mata dubu ba zata kasa sheda
fuskar mahaifiyar khalil ba. Ba wai don kamar da
sukayi dashi ba, domin tun kafin suje gidansu a
kwanan baya ita da khalil din, ta mallaki hotunan
mahaifiyar tasa masu dinbin yawan gske a wayar ta
wadanda khalil din ke turo mata. A ranta tace
shikenan ma tazo tafiya damu. Nasan khalil ya riga
ya fada mata komai. Sai taji wani farin ciki ya darsu
acikin zuciyar ta.

Kukan da mahaifiyar khalil din ta fashe dashi ne ya
katse tunaninta, tare da tattaro dukkan hankalinta
zuwa gurin ta. Ji tayi tana fadin. Alahu Akhbar!
Yarinyar nan babu rabon kuyi aure da khalil, ajalinsa
ya jawo miki wahala. Ni dama nayi tunanin wannan
zazzafar s soyayyar da khalil ya kamu da ita, da qyar
in zai rayu, yaron nan bai ta6a min sata ba tunda ya
taso, sai dalilin wannan soyayya. In da mahaifinsa ya
bada hadin kai, kila da ynxun khalil yana raye. Allah
ya baki lfy. Mimi ta zaro idanu tana kallonsu.
Qwaqwalwarta ta kasa saita zantukansu. Wai suna
nufin khalil ya mutu ne?
Ismail kuwa ya rikice, yana ta yi wa nurse din alama
da yatsansa a baki wai suyi shiru, amma sam basu
lura ba. Saima fadi da nurse din take yi, wai iyayen
wanda ya mutu dinne suka zo daukar gawarsa, shine
suka ce a rakosu su duba ta. Daya matar kuwa
wadda suka zo tare, fadi takeyi, kiyi haquri aunty
Amina, Addu’a kawai zaki yi masa, kinyi dauriya a
gida, baki masa kuka ba, sai anan? Cikin kuka mai
tsanani mahaifiyar take cewa, ban gaskata
mutuwarsa ba saida nazo naga gawar khalil. Ihun da
mimi keyi ne ya katse mahaifiyar khalil.
Wani yunquri da mimin tayi shine ya saka su nufar
gadonta. Sai dai Ismail ya rigasu isa. Duk da haka
kafin yakai ta riga ta kai qasa a sume. Ya dauke ta
yana fadin, inata alamta muku cewa kuyi shiru. Sbd
batasan komai game da mutuwarsa ba, amma sam
baku kula ba, gashi kunsa itama za’a rasa ta. Ya dora
ta akan gadon yana cewa, ku taimaka ku kiramin
likita! Mahaifiyar khalil fadi take, Inna lillahi wa inna
ilaihi raji’un! Ai ban san bata sani ba, nurse kuwa tuni
tayi qasa da gudu don kiran likita.
Qarfe sha daya da mintina momy Nafisa ta shiga
gidan ‘yarta Na’ima. Aljannar duniya. Ha ta furta
lokacin data iso cikin falon farko, Ta kalli ‘yar tata,
wadda tazo ta bude mata qofa. Na’ima kina cikin irin
wannan gdn kk daga hankalinki? Na’ima ta turo baki,
momy ni wannan gdn yayi mintg girma, abin haushi
kuma ni hadai ke yini a cikin sa. Momy tace, a’a ina
masu aikin da akace an kawo miki? Tace, suna
gefensu. To ai su ba abokan hirana bane momy. Suje
su raina ni? Momy tace, ba nufi na kenan ba, ba wai
kuyi hira ba, ina nufin a qalla kina jin motsin wasu a
cikin gdn. Na’ima ta turo baki, to momy shifa bashi
da lokaci na.
Momy tace, matsalarki dai mijinki ko? Na’ima tace
eh. Momy nafisa tace, kije kice masa inason ganinsa,
ko har ya fita? Na’ima tace, yananan banji fitar sa ba.
Ta miqe ta nufi sama cikin zumudi. Tana bude qofar
ta jiyo shi yana waya, yana zaune a kujerar
computer. Daidai abinda kunnenta ya jiyo yana

cewa, “tsaya mana kiji Jennifer. Kar kisa ma kanki
damuwa, na fada miki ba wadda nakeso din na aura
ba, ko da ita dince ma kinsan cewa ke ta musamman
ce, kina tsammanin rayuwa ta zata tafi sak ne in
babu ke? Cikin turanci yake magana. Yayi jim,
alamun yana sauraron abinda take fada. Sannan yayi
‘yar dariya, tare da cewa, na san dai zaki iya bada
sheda ta kan fadar gsky komai dacinta. Ya sake yin
jim, sannan yace, to zan tabbatar miki da cewa kinfi
wadda aka kawomin a matsayin mata. Zan tabbatar
miki yadda ke da kanki zaki gamsu da batun, ya sake
saurawa. Sannan yace, fadamin me zan miki ki yarda
tunda naga kina tantama, kamar kin manta ni waye.
Dariya taji ya saki, tare da fadin, ai wannan mai sauqi
ne, in dai kwana da nine, ina me yi miki albishir
cewa, ni da ke yau a gida na zamu kwana. In nayi
miki haka, zaki gamsu cewa ni dake mutu-ka-raba?
Maganar ta maqale, bai qarasa ba, sakamakon jin
muryar Na’ima da yayi cikin kuka tana cewa, dama
mata kk nema? Ya saki murmushi, sannan ya maida
wayarsa kunnensa. Baby zan kira ki zuwa Anjima. Ya
kashe wayarsa, sannan ya juyo da kujerarsa gaba
daya, don irin mai jujjuyawarnan ce, cikin fara’a
yace, baki sani ba dama? Ta tsaya tana Numfashi,
tare da mamaki, gami da zaro idanu. Yayi murmushi
mai sauti, kina nufin dama bakuyi bincike ba? Ya
girgiza kai ayya.
Ni qasurgumin manemin mata ne. Sannan ina shan
wiwi da giya kadan, akwai wata matsala ne? Ta rasa
me zata ce, sai kuka. Cikin kuka take cewa, ba zan iya
zama dakai ba. Mutumin da baya iya 6oye laifinsa.
Yace, oho, dama kinzo kin la6e min ne? Kada ki
zauna dani din mana, dama ni na kawoki? Ko na riqe
ki ne? To kazo momy na tana jiran ka a falo, ya ta6e
baki, wacece kuma momy? Tace, don wulaqanci,
mahaifiyata dince baka sani ba? Ya kalli danqareren
agogon bangon falon, me kuma tazo yi da wannan
safiyar?
Ya kalli computer dake gabansa. Ta jirani, aiki nakeyi,
in zata iya, in kuma ba tada lokaci, taje ta dawo wani
lokacin, in abinda tazo dashi ya dame ta. Na’ima
tace, wadda ta haifeni ce fa? Yayi mata wani kallon
banza, cike da izgili yace, don ta haifeki, ni ta haifa?
Kuka ta fasa, sannan ta juya ta tafi ranta a 6ace,
hankalinta kuma a tashe. Cikin kuka ta sami momy
nafisa
zaune a falo, tana zaune tana jiranta. Momy kinji
abinda na sameshi yanayi? “me? ” inji momy. Na’ima
ta fada jikinta, tana kuka, na sameshi yana waya. Don
nayi masa magana, kai tsaye yace min waishi yana
neman mata. Kuma wai yana shan giya da wiwi.
Momy nafisa ta zaro idanu, cikin faduwar gaba tace,

da gske? Kai inajin wasa yakeyi, zalayarki kawai yake.
Kin ta6a ganin mai aikata irin wadannan qazaman
laifukan sannan ya fada ma matarsa kai tsaye? Dole
zaiji shakka. Ki barshi bari yazo.
Na’ima tace, ai yace, ba zaizo ba, shi yana aiki. Momy
ta yi shiru tana ta kallon Na’ima cikin matuqar
mamaki, sannan ta miqe. Muje gurin nasa, mara
mutunci kawai. Na’ima ta kalleta. Da kin barshi kawai
momy, tace muje kawai, bazan dauki raini ba, gara
in taka masa birki.
Ta tasa Na’ima suka nufi saman. Yana latse latsensa a
computer, yaji shugowarsu, amma sai ya dauke kai,
yayi kamar baiji shugowarsu ba. Saida momy tace,
bakaji Sallamar mu bane? Sannan ya waiwayo,
fuskarsa babu annuri, yace, naji. Ina jinku, aiki
nikeyi, ina kwana? Duk da baice su zauna ba saida
momy Nafisa ta zauna, sannan tace “lfy” shine wato
Abbas nace kazo, amma kacemin kana aiki ko? Ya
nuna computer da hannuwansa guda biyu, ba gashi
ba kina gani? Ya juya yaci gaba da aikinsa. Tace, to
zaka iya bani ‘yan mintuna muyi magana? Ya hada
tafukan hannuwansa wuri daya ya murza tamkar
mai jin sanyi, sannan yace, kamar minti nawa? Ta
zaro ido cikin mamaki. Abbas ni kk tambaya? Ashe
baka da mutunci har haka? Da sauri ya juyar da
kansa gefe yana kuma dannar zuciyarsa, don kar ya
nuna mata ainihin kalarsa. Taci gaba da cewa, to
zuwa nayi inji laifin da Na’ima tayi maka da har zaka
soma wulaqanta ta daga kawo ta.
Har na qaryata ta, sai kuma gashi nima ka gwadamin.
Ya kalli Na’ima, me nayi miki harda zaki kai qara ta?
Tace, ko Yanxun dana shigo ba na sameka kanayin
magana da wata bane? Ya daga murya cikin zafin rai
yace, me ya dameki don kin sameni ina waya da
wata? Meye naki a ciki? Ya kalli momi, tunda taxo
gidannan ban ta6a shiga harkarta ba sbd banason
matsala. Tayi harkarta inyi tawa.
Momy tace wannan kuwa ba zai yiwu ba kana
mijinta. Sannan kace, kowa yayi harkarsa? Ko kuwa
dama baka amince da auren bane? Ya miqe tsaye
yana kallon momy tare da cewa, “au dama baku sani
ba? Ya girgiza kai, ni gsky mimi na gani nace inaso.
Momy tayi shiru tana kallon sa, gabanta ke faduwa,
damuwa ta bayyana qarara akan fuskar ta. Ta sauke
ajiyar zuciya, ta rasa me zata ce, sai ta kalleshi tare
da aje fushinta, to ynxun me kace? ko ince me kk
nufi? Ya kalleta, ban gane ba.
Momy tace, matsayinta. Yayi murmushi, sannan ya
koma ya zauna kan kujerar computer tare da yin
juyi. Ban sani ba gsky. Momy ta miqe tsaye ta sake
daga murya, to me ya hana ka cewa iyayenku baka
sonta tun kafin a daura auren? Yace, momy karki kiji

haushi na. Ko na fada musu ba zasu fahimceni ba a
wannan lokacin tunda suna da burin kansu. Ya nuna
Na’ima, ke kuma ki bani lokaci, in burikan iyayen mu
sun cika, sai in sauwaqa miki. Da sauri momy ta
katse shi da cewa, ha Abbas, ai ko mutuwa tana
kunyar idon mahaifi, inji masu magana.
A gabana kk fadin bakason ‘yata? Yayi guntun
murmushi, momy kenan. Don dai ni ba danki bane,
saiki takura min? Ya kamata kusan cewa, shi so ba’a
masa dole. Ni mimi na gani nace inaso. A tsari na
farar mace nake so. Kinsan kowa da ra’ayinsa. Qila
da fara ce da nayi manage. Momy ta miqe, shikenan
na fahimce ka. Yace, Yauwa nagode da kk fahimceni,
kuma naji dadin haka, don ni mutum ne mara son
takura. Ta kalli Na’ima, tashi muje.
Na’ima wadda ke ta faman kukan takaici, ta miqe
tana cewa, nidai kawai momy ki tafi dani, bazan iya
zama ba. Yace, kin kawo shawara, ku tafi tare kawai
momy, ta dube shi a qufule.
Babu inda zanje da ita, zan kuma sanar da
mahaifiyar ka, daka-duka auren yau kwana biyu,
sannan ace tana gida? Yace, umm, yadda kuka za6a
haka zakuyi. Amma in da zakiji shawara ta, da sai
ince kar ki kai qara ta gurin momy na, sbd itama
irinki ce, tafi son ‘ya’yanta akan na kowa. Ni dai kunji
ra’ayina. Sannan don Allah a daina takura min, a
kuma guji shiga harkata. Basu sake cewa komai ba
suka fice. Shi kuma yaci gaba da aikinsa. Dakin
Na’ima suka koma sukayi jugum-jugum. Na’ima tana
ta faman kuka. Mommy ta kalleta cikin damuwa,
sannan tace, share Hawayenki. Badai farar mace
yakeso ba?
Na’ima tabi ta da kallo. zamu duba mayukan cikin
akwatinki, in babu wanda zaisa kiyi fari, saimu shiga
kanti. Kafin da wata guda, sai kin koma tamkar
baturiya. Daga nan sai ki dinga yin duk wani abu da
zaki ja ra’ayinsa. Na’ima ta dan ta6e baki tallafe kanta
sbd tsabar ciwon da yake yi, tace, hmm mu gwada
mu gani, haka suka sauke kafatanin kayan shafan
dake cikin lefen, amma basu fahimci komai ba,
ma’ana basu gane ko mayukan zasu iya yi mata
bilicin din ba.
Momy ta dafa Na’ima, cikin sigar lallashi, karki damu
Na’ima, zan nemi Shawarar Aminiyata hajiya nana,
domin na ta6a jin suna zancen qwayoyin da suke
saka fari. Na’ima tace, to kafin ta wuce saida ta
tabbatar hankalin ‘yar tata ya kwanta, ta nuna mata
cewa ta zauna tayi haquri, ta zauna kada ta sake
maganar tafiya. Ta kwantar da hankalinta, wata rana
sai abin da tace masa zaiyi.
Momy dai ta tafi cikin takaici, ta bar Na’ima cikin
damuwa. Ta jima sannan ta tashi ta shiga cikin kicin

dinsu masu aikinta ssuna ciki. Dattijuwar tana zaune
tana firar dankali. Yarinyar kuwa tana wanke-wanke.
Daqyar ta amsa gaisuwar da suke mata, wai ita dole
ga matar gida, ta kalli tsohuwar, me za’ayi da wannan
dankalin? ‘Yalla6ai ne yace ayi masa cips da shayi.
Na’ima tayi sororo, cikin muzanta, domin itace ya
dace tayi masa, ko kuma tazo tasa ayi masa, amma
sai ta wayance da cewa, dama har ynxun baku kai
masa ba? Dattijuwar tace, hajiya zuwansa kenan
yazo yai magana. Na’ima tace, ni bance sai kinyi min
lissafi ba. Inason ki gasa min bread da kifi, Na’ima
kenan. Wannan kuma ai cimar mimi ce. Yinin ranar,
Na’ima ta kasa sukuni.
Domin ita gsky tana matuqar son Abbas. Tana jin
lokacin da zai fita wuraren daya saura na rana, ta fita
taje gurin window tana leqensa har ya dau motarsa
ya fice. Qarfe goma da mintuna na dare, taji
tsayuwar motarsa. Cikin sauri ta fito falonta wanda
tasan nan ce kadai hanyar binsa don hawa samansa.
Ta dau gayu cikin riga da wando matsattsu, kanta
babu dan kwali, tayi wankan turaruka har maqaqi
suke mata a wuya.
Sai dai kash! Tayi dana sanin fitowa daga dakinta,
don burge angonta, domin kuwa da wata budurwa
ya shigo, bayan ya buga alarm ta bude, sororo tayi
cikin tsananin kishi, ba tada wata power da zata iya
ce musu wani abu. Kuka ta saka sannan ta juya ta
nufi dakinta. Abbas ya kalli Jenifer, kin gani ko? Har
ynxun babu kamarki, tayi murmushi suka nufi
samansa bayan ta saqalo hannuwanta a qugunsa.
Tana fadin, na yarda honey.
Cikin matsanancin kuka, Na’ima ta kira layin momy,
wadda shugowarsu kenan daga asibiti, ita da daddy.
Jikinsa da dan sauqi, shine ya matsawa likitan ya
sallamesu, don ya tsani zaman asibitin. Momy Nafisa
bata son daddy yaji wannan matsalar, don haka taqi
dagawa, saida ta shiga dakinta. Tana dagawa ta fara
da cewa, meyasa bakida haquri ne? Na’ima ba nace
zanyi shawara bane? Zan kiraki da kaina. Tsaya kiji
momy, da karuwa fa ya shigomin gida. Karuwa??
Momy ta tambayi Na’ima. Ta rantse, sannan ta ci
gaba da cewa, ni bansan yaya zanyi ba ynxun, Momy
tace, ki barshi zuwa gobe zanje gurin uwarsa. Na’ima
ta shiga daki, ta zauna bakin gado cike da nadamar
auren Abbas.
Kuka take sosai, amma babu mai lallashi. Qarfe shida
na yamma, innar su Zainabu ta shigo tare da
Aminiyata, inna yalwa, suka sake dawowa gidan
Zainabu, ta danji dama, tana zaune kofar dakinta. Jin
muryar innar tata yasa gabanta faduwa. Rai a dagule
ta kallesu, sannan ta shiga dakin, suka bi ta ciki,
Aminiyar inna ta kalli Zainabu, meye kika dagule rai?

Zainabu ta sunkuyar da kai. Ni wallahi da baku dawo
ba, za’a ce iyaye na suna ta sintiri. Da ma aikowa
kawai kuka yi.
Ni bana son abin gorin nan gidan. Inna tace a daura
miki goruba, mu dai in burinmu ya cika ina ruwan
mu dasu? Inna yalwa tace, anqi a turo wani din,
basha zakiyi ba. Ta daga hijabinta, ta ciro wata gora
mai dauke da maganin da suka hado. Tace, zauna
kisha shi maza-maza. Zainabu ta soma kuka tana
shan maganin. Tasha kusan rabi suka ce, ki ajiye
Anjima sai ki shaki shanye sauran. Karki sake baki
shashi ba. Tun fitarmu daga gidannan, muna can
muna qoqarin hadoshi. Don haka ki maida hankali ki
shanye.
Alhaji lawal ya dawo gurin su Maman bushira yanata
zage-zage, wai shi za’a kawo wa raini da rashin
mutunci? To, shifa ba zai bada jininsa ba bare kuma
kudinsa. Duka-Duka yaushe ne akayi auren ma? Ko
wata daya ba’a yi ba za’a ce har tanada wani ciki?
Uwar gidan tace, haba Alhaji yaya kake irin wannan
maganar? Sbd Allah, dubi yadda mutane suke
kallonka. In jiya kuka yi aure, ai ba abin Mamaki
bane ku wayi gari da ciki. Kai dai kayi fatan samun
sauqinta, ka kuma bada duk abinda ake nema. Ya
kalleta a fusace, sisi na bazai ciwon kai ba. Zanje in
fadawa uwarta, wadda ta kawo mata maganin zubar
da ciki. Sai su zo suyi jinyar ta, da kuma kudin sun,
tace haba Alhaji don Allah ka duba wannan
al’amarin. Cikin tsawa yace, in zakije gida, kizo muje!
In ba zakije ba, in tafi.
Tace, abarta da wa? Tsaki yaja, sannan ya wuce
abinsa. Nurse tazo ta kira maman bushira zuwa
dakin da aka ajiye Zainabu. Sannan taba ta wata
takarda, ta nuna mata wata qofa, ki shiga zakiga
wasu nurses, anan ne zaku biya kudin gadon, sannan
zasu rubuta muku takardar shaidar biya. Likita zai
shigo ya rubuta magungunan daya kamata tasha.
Maman bushira dai, to, kurum tace, tana tsaye da
takarda bayan tafiyar nurse. Gashi ba tada ko sisi
tunda fitar bana shiri bane.
Shi kam Alhaji lawal, kamar yadda ya fada, gidan su
Zainabun kuwa ya zarce. Kafin ya kai saida ya kira
direbansa, dan korensa. Bayan ya daga, sannan yace,
iroro kana ina ne ynxun?
Yace, Alhaji naje gidan, ance kunje asibiti da amarya
ba lfy. Alhaji yace, mu hadu gidan iyayenta ynxun
nan. Ka hau aca6a. Yana isowa qofar gidan, ya hangi
iroro har ya iso, suna tsaye da dan acha6an, iroro ya
nufo Alhaji yana cewa, sannu da qarasowa Alhaji.
Alhaji yace, har ka rigani, to me kuma dan acha6a ke
jira? Iroro yace, banida ko kwabo Alhaji, daman kai
nake jira in sallameshi. Tsaki Alhaji yaja, sannan ya

ciro naira dari biyu ya miqa masa, iroro ya amsa tare
da cewa, Yauwa. Ya biya dan acha6a, sannan ya zuba
sauran aljihunsa. Ya kalli. Alhaji, “lafiya dai kazo nan?
Alhaji yace, zuwa nayi in sanar da iyayen Yarinyar
nan Zainabu suje suyi hidimarta a asibiti.
Kaji ma wai har tanada ciki, Duka-Duka yaushe akayi
bikin? Iroro yace, tafdijam! Ba don ma baka mori
kudinka ba ai da sakinta kayi kawai, ka kawo wata.
To, jinyar cikin takeyi a asibitin? Alhaji yace, sun
dirka mata maganin zubar da ciki, jini ya 6alle mata.
Ai shiyasa nace, suzo suyi jigilar, iroro yace, kayi gsky
Alhaji. Kuma zan soma duba maka madadinta tun
daga ynxun.
Alhaji yace, shiyasa nake matuqar sonka iroro. Sau
da yawa in kayi magana, kamar ka shiga raina. Da
ace ta kwana biyu, zuwan nan da nayi, yadda take
asibitin nan, da takardar ta zanba iyayen ta. Amma
su gama jinyarsu, zan dawo da ita, ba zanyi asara ba,
kuma ba zamuyi dogon Zango da ita ba, don daga
gani ita irin masu jarabar haihuwarnan ce, sai kace
6era.
Cikin fada likitan ya shigo, ya kalli Ismail, “kai kanaso
ne sai zuciyar ta ta buga tukunna? Me zaisa ku fada
mata mutuwarsa? Don Allah ku fita waje, banason
ganin kowa anan sam. Bai saurari kowa ba, bare
yasan ba laifin Ismail bane. Gaba dayansu sukayi
waje,, Ismail yana cewa, kun gani ko? Nasan dama
laifina zai gani. Cikin kuka mai tsanani, mahaifiyar
khalil take cewa, kuyi haquri, nima ban sani bane,
Mahmud yace, karki damu hajiya, babu komai,
shidai Allah ya jiqansa. Tace Ameen, bari mu tafi,
Allah ya bata lfy.
Ameen ya rabbi, ina fata ‘yan sandan sun baku
jakarsa da wayarsa ko? Sai dai ban sani ba, tunda
tare da mahaifinsa muka zo, qila sun bashi, Mahmud
yace, ‘yan sandan sunzo lokacin da mukazo. Tace
bari zanyi musu magana in munje. Mahmoud yabi
su da kallo, suka tafi cikin damuwa. Ismail kam
tamkar zuciyar sa ta buga don damuwa. Ya qosa
likitan ya fito don yasan halin da ake ciki. Ya kusan
rabin sa’a tare da taimakon nurses, sannan ya fito, ya
kalli Ismail, fuskarsa a daure, ku biyoni office. Sun
sameshi a tsaye yana duba wani file. Suna shigowa
bai zauna ba, kuma bai musu izinin su zauna ba.
Sai ma fada da ya

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login