Showing 87001 words to 90000 words out of 127530 words

Chapter 30 - CANJIN RAYUWA

16 Oct 2024

8164

dubu ciki gidan, ba Gidansa bane? Ko da kudinta yake bin mata? Ba Kuma sammata zunubin za'a yi ba. In bata iyawa ga hanya nan ta fita. Yarinyar da bakuyi mata tarbiyyar arziki ba sai rowar tsiya. Naje nida qawayena tayi mana rowa. Haka yara da suka je ko dan turare ta gagara basu. Sbd haka shi kansa bakusan abida take masa ba. Don haka ya kamata ya nema, lokacinsa ne. Ku fita a Gidana! Kuje kukai 'yarku asibiti, ko nawa aka caza zamu bada albarkacin danmu da take dauke dashi.
[17/09 1:18 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa

1⃣1⃣Momy Nafisa tace, kin bani mamaki, da sunan wasa ban zace ki ahaka ba. Hajiya Bilkisu tace, nafi nan, in dai akan yarana ne. Haka kema ban zaci 'yarki bata samu tarbiyya ba. Hajiya Nana tace, zo muje! Kuskure dai anyi shi tunda aka basu aure. Hajiya Bilkisu tace, Eh kuje, bazan takura ma dana ba, ya mori quruciyar sa da lafiyarsa. Haka dai aka rabu ana fadawa juna magana. Gidan Na'ima suka dire, inda suka dauke ta zuwa asibiti. Kai tsaye Gado aka bata sbd halin da take ciki. Momy Nafisa ta kira Alhaji bashir ta fada masa cewa, an kwantar da Na'ima a asibiti, kuma an tabbatar musu da cewa, tana dauke da juna biyu. Daganan bata fada masa komai ba. Lokacin data yo wayar, Alhaji suna zaune a babban falo, shi da saudar shi da kuma yara. Nan suka shiga murna kamar ance ta haihu. Yace, abata wayar. Momy tace, tana varci. Yace, ko inzo in duba jikinta? Tace, a'a kayi zamanka Alhaji. Jikinta da sauqi. Kasan dama shi ciki, in an dauka, sai an sauke kafin a samu lafiya gar-gar. Yace, haka ne. To, zamu kira in ta farka. Sauda tace, bani mu gaisa, suka gaisa. Tayi mata murna, tare da fatan samun sauqi. Bayan sunyi sallama ne, sauda tace, al'amarin Allah kenan, mai rayuwa cike da canji, da kuma launi kala-kala. Dama rabon a gurin Na'ima yake, shiyasa Mimi ta bijire. Yace, hakane. Allah ya nuna mana daidai ya bamu ikon bi.
Yace, Ameen. Ta danyi jim, ita kuma Mimi ko menene labarin ta? Oho. Alhaji yadan runtse ido, sannan yace, tana samun sauqi insha Allah. Allah yasa, inji Hajiya sauda. Kwanan Na'ima uku a asibiti sannan aka sallameta, suka wuce Gida. Abbas dai baizo ba, amma Hajiya Bilkisu tazo ta kuma biya kudin komai. Shi ko minister baisan komai ba, saida Alhaji bashir ya kira shi yace, kai zanyi wa murna ko juna za ayi wa murna? Minister yace, tame? Na'ima tana dauke da jikanmu. Ba ka samu labari bane? Cikin murna minister yace, bani da labari. Kasan yau kwana na uku bana qasa. Ynxun haka durowa ta kenan, ina filin jirgi. Kaine mutum na farko da na amsa wayarka. Nayi murna sosai, kuma naji dadi qwarai. Amsarka kuma ni za'a yiwa jika. Domin kai ka dauki dan Gidan Abba. Suka sa dariya, sannan sukayi sallama. Cikin murna minister ya isa Gida, sai dai baiji kowa yayi masa batun jikan da zai samu ba. Hajiya Bilkisu tana rawar jikin tarbar sa ta hanyar abinci da sauran kyautatawa.
1⃣2⃣Ya Kalli abicin sannan ya kalleta, "Wai ni banji kunamin batun jikan da zan samu ba. Wani abinda kuka bani haushi, wanda ya kamata ace nina bashi labarin qaruwar, sai shine yake bani" Da sauri ta soma neman yadda zata wanke kanta, sbd tasan shi akwai maida qaramar magana babba. Tace "wai dama Alhaji ban fada maka ba?" kaina bisa wuya. Ya dauki cokali, "ta yaya kk zaton zan manta da wannan babban labarin in har kin fadamin? Ta dora hannunta akan nasa, kayi haquri nayi tsammanin cewa, na fada maka sbd hankalinmu yana tashe, ita Na'imar ce babu lfy. Yace, banji haushi ba Bilkisu. Na dai yi miki takaicin rasa goron albishir daga gareni. Yace, Abbas din fa? Shima bai fadamin ba, kodai wani abu ya faru ne, ko kuma yana shirin faruwa? Tace, babu wani abu, ina zaton dai bai wuce, jikin matarsa ba, kuma ga yanayin aiki. yace tana gida ne ko asibiti? Ta soma in-ina, "eh, a'a tana asibiti, amma munyi shawara in an sallameta su wuce gida, sbd ta dan qara samun qwarin jiki. ya aje cokalin dake hannunsa, "ban amince da wannan Shawarar taku ba! Wai keda wa kuka shawarta? Tace, da Abbas ne da kuma mahaifiyarta. Yace, to nan Gidan ya kamata ta dawo, sbd jikana ya saba da gidansu tun kafin ya iso Duniya. "A ranta tace tirqashi! Wannan wace irin qaunar jika ne haka? Amma a fili sai tace, ai sai a canza shawara, duk ba laifi bane. Yace, shi kuma Abbas yazo, shima jikana a bude masa account din, kamar yadda nake yiwa 'ya'ya na. Sannan jikana na fari, in ya kasance namiji, zanyi masa kyauta mai tsoka. Yayi 'yar dariya, meya kamata in ba jikana? Hajiya Bilkisu, wadda abubuwa uku suka tarun mata a lokaci daya, qaryar da tayi masa, takaicin dawowar Na'ima Gidansu, ga kuma kudin da ta lura za'a 6arnatar ma cikin. Cikin yaqe tace, sai mu jira mu gani me zamu samu? Yayi 'yar dariya, kuma fa Gskyrki ne, qila ma 'yan biyu ne. Ta lumshe ido sbd takaici, sannan ta bude, Allah yasa haka. Yace, Ameen. Yana shiga wanka, ta nufi dakinta. Cikin sauri ta kira Abbas a waya, ta karanto masa duk yadda sukayi. Tace, ynxun yaya kkga za'ayi? Domin dadynku ya zurfafa da qaunar abinda ke cikin matarka. Abbas yace, karki damu, zanje gidan kuma dole ta dawo.
[17/09 1:18 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa

1⃣3⃣Na'ima tana zaune a dakin momy tana cin tuwon semo, suhaila ta shigo, tana cewa "sis Na'ima ga Abbas nan yazo da abokansa. Na'ima ta ture tuwon dake gabanta gefe, tare da jan tsaki, tace, ni bazan fito ba harma naji na qoshi. Suhaila tace, suna tare da momy ai. Na'ima ta fito falonta, ta tsaya inda ba zasu ganta ba. Tana iya jiyo muryar Abbas yana cewa, "Ayyuka ne suka sa ni banzo asibitin ba, amma ai momy tazo. Tace, Momyn taka me tazo tayi in ba wulaqanci ba? Don haka inason in fada maka babu inda Na'ima zataje. A Gidanka ma bataji dadi ba bare a gidan iyayenka? Usman yace, ayi haquri dai momy. Nan da can duk daya ne. Momy tace, ba zataje ba. Abbas yace, shikenan zan kira daddyn nan gidan. In ba zata koma ba, saidai mu rabu. Momy tayi shiru, ta kasa magana. Domin tasan Alhaji baisan komai ba a kan matsalar. Da qyar tace, ka fada masa mana! Zai matsa mata dole ne? Abbas ya miqe, ku tashi muje su usman! Zan bada mamaki Gidannan. Suna fita Na'ima ta fito tana kuka tace, Momy ni bazan koma Gidansa ba, bare Gidan iyayensa. Ni tsoron mamansa ma nakeji. Momy tace, qyaleshi yayi ta fadama daddynku din. Ynxun ne suka san ki koma can? Da suna so ki koma da basu kaiki asibiti ba? Na'ima dai sai kuka, ita kuma momy tana lallashi.
Shi kuwa Abbas ya gama tsara ribar da zaici gurin mahaifinsa da wannan cikin. Ynxun burinsa a samu namiji kamar yadda mahaifinsa ke matuqar so. Haka kuma shi da mahaifiyar sa suna ruwan ido akan abinda ya kamata su za6a a matsayin kyautar da kakan zai bawa jikansa. Shi dai yana sha'awar gidan saida motocin Alhajin nasu, yayin da Hajiya Bilkisu ke sha'awar wani kamfanin Alhajin. Ranar asabar, Alhaji Bashir yana zaune a bayan mota tare da 'yan samarin sa guda hudu, malumfashi suka nufa gurin Hajiya Binta. In sun kwana biyu su wuce masari don ganawa da dangi, wato su ziyarce su. Wayarsa ta buga, Ameen ya miqo masa, yana kallo yaga lambar Abbas. Bai ta6a kiransa ba. A fili yace dan nemabbaka ta6a kirana ba, sai yau da aka samu qaruwa. Ya daga suka gaisa, sannan yace, daddy dama inason in fada maka ne an sallami Na'ima daga asibiti, amma momy tace, ba zata dawo gida ba saidai ta zauna Gida gurinta. To kuma daddyn mu daya dawo yace ta koma can gidanmu gurin Hajiyarmu. Da naje don mu taho, sai kuma momy ta hana. Ran Alhaji Bashir ya 6aci matuqa, cikin zafin rai yace, karka damu zansa akawo ta har gurin Hajiyar taku. Abbas yace, nagode daddy. Alhaji yace, babu komai. Suna yin sallama ya kira layin momy Nafisa, tana dagawa, ko amsa Sallamar ta baiyi ba ya soma ruwan bala'i. Nafisa kina hauka ne zaki rabo yarinya da Gidanta? Sbd me? Ba zan amince ki zubarmin da mutunci ba, in har ke baki damu da naki mutuncin ba.1⃣4⃣Tace, tsaya kaji Alhaji! Ba zanji komai ba. Ya katse ta. Zan kira Hamisu ynxun nan yaje ya kai yarinyarnan Gidan minister, kamar yadda suka buqata. Sannan zan gargadeki, kar ki bari inji wata matsala ta fito da sunanki a ciki, ko wani tseguminku na mata. Aure zaki kashe mata ko me? Tace, kasan da Yarin..."ya sake katseta, ba nace kiyimin shiru ba ne? Kinsan Allah kikayi sanadin kashewa yarinyarnan aurenta, ko kuma kika zama silar matsala tsakanina da Abokina, wlh saina baki mamaki, zan yi miki abinda baki zata ba bare tsammani. Ke baki da hankali ne? Baki ganin halin da nake ciki na rashin Mimi da kuma ciwon dake damunap. Shiyasa har in koma ga Allah ba zan daina son Sauda ba da ganin qimarta da girmanta. Kizo katsina ki ganni, kiga yadda na samu lfy da kwanciyr hankali, sbd ina tare da mace ta gari mai tattali. To na fada miki, ki fita idona in rufe. Ya kai qarshen maganar tare da kashe wayarsa
Momy Nafisa, tayi shiru da waya a hannunta, bata ta6a ganin ranar da Alhaji yayi dogon sababi ba kamar na yau. Bata da wani za6i face, yin abin da yace, amma dukda haka saida ta kira layin Hajiya Nana, ta fada mata cewa, Alhaji yace, lallai sai Na'ima ta koma Gidan surukanta. Hajiya Nana tace, ki barta ta koma zamu san yadda zamuyi mu samu mafita. Tana aje wayar, Hamisu yana shigowa. Ya gaida momy, ta amsa rai 6ace. Yace, maigida yace... Ta katseshi, karka cikani da surutunka! Jeka naji, zata zo inta shirya. Ta shiga dakinta inda Na'imar take kwance kan gado, ta zauna a bakin gadon. Na'ima taso kiji! Tace, menene? Bayan ta taso, momy tace, ki tashi ki koma can gidan su Hajiya Bilkisun. Na'ima ta soma kuka, ni ba zanje ba momy. Gsky, na haqura da auren Abbas. Baya sona ko kadan. Momy Nafisa ta riqe kai, cikin damuwa tace, kai ni dai wannan abu ya isheni dai, wannan abu ya isheni. Duk nice na jawoshi. Inda nasan ma haka halin Abbas din yake, wlh da nabar Mimin ta auri Abbas din. Na'ima tace, inda itan ce na tabbata ba zai mata haka ba, don yana mugun sonta. Momy tace, yi mata zaiyi dan bariki, dan bariki ne. Da an gama soyayyar, za'a shiga tsiyar. Ke dai ynxun ki tashi muje can din mu gani. Na'ima tana kuka, tana komai ta kwashi nata ya nata aka nufi Gidan minister da ita.
[17/09 1:18 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa

1⃣5⃣Mimi tana zaune a tsakiyar katifar dakin Ismail na zaure, da idanu take ta bin dakin da kallo tamkar bata ta6a shiga cikinsa ba. Ismail dake qoqarin kunna mata 'yar tsohuwar fankarsa, ya kalleta, "me kk kallo a dakin? Shine dai, ba'a qara komai ba, kuma ba'a rage komai ba. Mimi batasan ma yayi ba, tunaninta yana can gurin sashinta na Abuja, amma dubi inda take ayau. Gsky bata ta6a tsammanin ko a cikin mafarkinta abinda ya faru dinnan zai faru da ita ba. Kuma kowane lokaci tayi dogon tunani don ta gano menene laifinta a cikin duk wadannan abubuwan da suka faru, amma bata gano ba. Kowane lokaci tunaninta yana tsayawa ne akan laifin na mahaifanta ne. Tafi dogara akan cewa, basa sonta ne, ko kuma tace, daddy ya daina sonta, don dama can Hajiya ba wai tana sonta bane. Da wannan ta dogara, takeson nesanta kanta dasu iyayen nata yadda ba zasu sake jin labarinta ba.
Ismail dai tsaye yayi yana kallon yadda hawaye ke kwaranya daga idanunta. Dukda cewa ya saba da ganin kukan mimi, amma daga ganin wannan na musamman ne. Da haka ya nufi gurinta, ya zauna a gefen katifar, cikin sanyin murya ya kira sunanta, "khadija! Kina jina khadija? Kina jina? A firgice ta kalleshi, yace me kk yima kuka? Cikin shasshekar kuka tace, babu komai. Yace, khadija, Kalle ni! Ta dago ta kalli cikin manyan idanunsa. "zuwa ynxun na fahimci halayenki a dan zaman da mukayi, fahimta ta sosai. Inda ni marubuci ne, tsaf zan rubuta halayenki. Duk kalar kukan da zakiyi, ina iya fahimtarsa. Nasan kukanki na shagwa6a, nasan kukan ki na rigima, sannan nasan na takaici da kuma na zallar baqin ciki. Wannan kukan naki na tsantsan baqin ciki ne, hade da takaici. Don Allah ki fadamin menene silar wannan kukan naki?" Ta sunkuyar da kai. Yace, karki manta kin dauki alqawari a asibiti cewa, zaki riqeni tamkar dan uwanki. To, in baki fadamin damuwarki ba, wa zaki fada mawa? Kuma nima ynxun dole ne in inada wata damuwa kece zaki fara sani, kafin kowa tunda kece muke daki daya. Ki kalli cikar Gidanmu, amma babu wanda zan iya kaima kukana cikinsu. Daga yaya Amina, sai Mahmud, sune abokan shawarata. Fadamin abin da yasa ki kuka.
1⃣6⃣Tace (cikin shessheka) Na tuna yadda mahaifana suka watsar dani. Dubi inda na dawo. Ni ko cikin novels din da nake karantawa na turanci, labarai irin na turawa masu yin wata irin rayuwa da tasha bambam ta tamu, amma ban ta6a cin karo da labarin masu hali irin na iyaye na ba. Ismail yace, khadija inkin duba tsaf, zakiga cewa, kema fa baki kyauta musu ba. Yadda na samu labarin gatan da mahaifinki yayi miki, bai dace ki watsa musu qasa a ido ba. Amma shikenan duk abinda zai faru ya riga da ya faru. Bari in miki wani alqawari, na sani cewa arziki na Allah ne, amma inya bani, zan miki duk abinda kkso. In ya kai arzikina kamar na mahaifinki, zanyi miki fiye da abinda mahaifinki yayi miki. Inason ki rubuta wannan ki ajiye ko don sheda. Amma ynxun inason ki daina kukan nan, ki kuma yi haquri da yadda kk sameni. Ta runtse idanunta. Ina matuqar da na sanin dawowa ta hutu daga Dubai, na rantse da na san cewa duk wadannan abubuwa zasu faru dani, da na zauna can nayi hutuna. Daddy ya matsamin wai in dawo, ya kuma sake matsamin inje katsina. Ashe yamin hakane sbd ya daina sona.
Ismail ya sake yin qasa da murya, "ki daina fadin haka khadija. Ki sani bawa baya iya gujema qaddararsa. Sannan bana zaton akwai iyayen da zasu daina son dansu. Kuma na tabbata inda iyayenki suke, ynxun suna tare da takaicin rabuwa dake. Hankalinsu yana kanki. Tace a'a ban yarda da batunka ba. Hankalinsu yana kaina ne zasu watsar dani bayan sun samu labarin halin da nake ciki? A dan qaramin tunani na kome nayi musu bai dace su banzatar dani ba acikin halin ciwo. Shiyasa nima nakeso ka nesantani dasu kamar yadda kayi min alqawari. Ta soma wani irin kuka mai shiga rai. Baisan lokacin da ya rungume taba ajikinsa. Kiyi shiru. Zanyi miki duk yadda kk so khadija. Saidai ina sake neman hadin kanki. Yadda kk sameni talaka, ki qara haquri. Kinji khadija? Kimin alqawarin zama na har abada. Ko na tafi makaranta ki zauna da yaya kinji. Haka dai Ismail yayi ta lallashin Mimi da kalamai. Kasancewarsa mai hikimar magana, har tayi shiru, ta kuma amince, tare da alqawarin ko baya nan kar ya damu babu inda zataje.
[17/09 1:18 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa

1⃣7⃣Ismail ne ya girka musu abinci, taliya ce yayi dafa duka, ya zabga kifi. Kuma Mimi taci sosai. Matsalarsa ban daki, amma tunda ga 'FO' din daya siyo mata, sai yace, tayi amfani dashi, zai dinga zubarwa. Cikin kwana ukun da sukayi, Mimi har nauyin Ismail takeji, domin ko cikin dare ta farka fitsari ko ba haya zaisa ta a 'FO' in ta gama, ta wanke sai yazo ya zubar, kuma ta lura yanada matuqar tsafta sosai sbd yadda yake gyaran dakin, ya wanke komai na girki, sannan yayi musu wanki. Wanka ne dai matsalarta ynxun, don acikin kwanaki ukun nan batayi wanka ba, sannan yana sata su danyi tattaki a cikin layin ya sagale ta a kafadarsa don tadan taka qafarsa. Sai dai damuwarta yana matsa mata sai ta saka hijabi, ita kuma bata saba da yawo dashi ba. Da ma shi ya sai mata sbd sallah. Yakan lallasheta da cewa, kinga duk kayanki matsattsu ne, khadija ki saka, in mun dawo daki, sai ki cire. A ranar ne Ismail ya daga katifa yayi share-share, har ya ciro ma Mimi Jakarta. Daya gama share-sharensa, sai ya taimakawa Mimi, ta koma kan katifar dama cikin zaure ya zaunar da ita. Sannan ya dauko Jakarta ya ajiye a gabanta. Har ta dauki littafin daya bata na tarihin Annabi Muhammad (SAW) ta bude tana cewa, ina page na ashirin da uku. Sai yace ga jakarki. Tace jefa ta can kan akwatunan can. "yace da kudinki a ciki fa." Ta dago ta dubeshi, sannan ta kalli jakar, "kudi?" yace duba mana. Ta ajiye littafin, sannan ta dauki jakar, ta zazzago kudin. Cikin mamaki ta kalleshi, "dama ba dasu ka biyamin kudin asibiti ba? Yace a'a. Tayi shiru tana kallonsa, ta sake cewa kodai bakasan dasu bane? Yace na gansu. Sai taga ya qara qima a idonta. Sai tace, nagode sosai, amma ka amshi wannan kudin kayi duk abinda kkso dasu, na baka. Yace, kudin da yawa khadija, ki riqe abinki. Tace babu abinda zanyi dasu. Amfanin dana debo kudin don inyi dasu basu min ba. Komai ya zama

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login