Showing 99001 words to 102000 words out of 127530 words
kyau da yawa. Qasar ta canza ka, ta amshe ka. Yayi murmushi, a zuciyarsa yace, ina girman kan? Ya dubeta, nayi kyau? Khadija dama can ni mai kyau ne. Tadan ta6e bakinta tare da yin dana sanin fadar hakan a ranta, ta lumshe ido. Maza sunada kyaune? Kawai dai ka samu hutu. Yayi dariya, ko ma dai yaya ne kin yaba, kuma nagode. Taso kidan taka in gani, tafiyarki ta koma daidai? Yaya dake zaune bakin gado tana jinsu, sai ta tashi, "bari in kira abbansu saddam in fada masa ka iso, ta fice.
[20/09 8:59 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa
4⃣1⃣Mimi tace, in kayi haquri, ai zaka gani, ba sai kasa ni yin wata tafiya ba. Yace, amma kin daina dingishin? Harynxu tana tare da jin haushin maganarsa ta dazun, tace, "Qila." ya matso ya zauna a bakin gadon, ya rage muryarsa, "kinyi baqi, kin rame. Amma muryarki dinnan mai sauti can qasa da miskilancinki suna nan." Ta zuro qafafunta ta dayan gefen ta sauka. Sannan tace, bai kamata kaji mamakin ganin na canza ba, domin kafi kowa sanin komai. Ina Mahmud? Shi ma ya miqe, yana gida. Anjima ki shirya muje mu gaida malam. Ta girgiza kai, "ban fita kayi haquri." yayi dan murmushi, hakane, tam bari na dan yi wanka kafin a kira magriba. Ta nufi gurin madubinta tana fadin yanada kyau. Ummi ce tasa ruwan wanka takai masa. Ya bude jakarsa ya dauki kayan wankansa cikin wata jaka ta leda, wadda aka yita don saka kayan wanka. Sannan ya ciro jallabiyarsa, wata mai shegen kyau ruwan hanta, tana da zif daga qirjinta har wuya, sai kuma tsintsiyar hannu da ma6alli. Sai hula mai kalar zaren da akayi dinkin. Mimi tana kallonsa da gefen ido, ya dora kayan saman gadonta, sannan ya fita. Da kallo tabi bayansa. Kyawunsa yana bata mamaki. Bayan ya fito, sai daya shirya tsaf, Mimi tana ta satar kallonsa. In ta ga alamun zaya waiwayo saita sauke kanta. Ya feshe jikinsa da turarukan larabawa, qamshinsa ya gauraye ko'ina, sannan ya kalleta, nayi kyau? Cikin zolaya yayi tambayar. Ta ta6a baki, tare da cewa, ina wani kyau anan? Yace son ranki kk fada. Bari inje gidanmu. Daga can in wuce in gaida malam. Tace ka gaida su. Ya dauki qaramar jaka daga cikin jakunkunan da yazo dasu. Tabi bayansa da kallo har ya saki labulan. Ta jingina da sif dinta tana mamakin yadda ya rikita ta har haka. Yaya tana zaune zatayi alwalla, ya ajiye jakar a gabanta, tsarabar 'yan gidanmu ce, su yaya jallabiyu, matan kuma dabino ne da zam-zam. Inna kuma harda darduma da wata doguwar riga. Yaya tace, yayi, Allah ya bada lada. Yace Ameen. Ya dauka ya fita.4⃣2⃣Duk wanda suka gaisa da Ismail, sai yace, Masha Allahu kayi kyau. Yana shiga gidansu ana kiran magriba, ya Kalli dakinsa yayi murmushi, sannan ya shiga cikin gidan, babu zato suka ganshi. Don haka suka shiga kallon kallo. Sai kuma aka shiga yi masa sannu da zuwa. Yayi musu qwarjini sosai, don haka da 6are-6aren jiki sukayi ta amsa gaisuwarshi. Ya shiga dakin inna sai yaga ta qara masa tsufa. Ya gaida ta sannan ya kawo tsarabarsu ya bata tare da yi mata bayani a gurguje ita kanta duk sai yaga tayi sanyi. Ya nufi masallaci. Bayan sun idar da sallah nan sukayi ta gaisawa da mutane suna tayi masa sannu da zuwa. Yana tare da jama'a har zuwa bayan isha'i, sannan ya nufi Unguwar su Mahmud. Ya shiga cikin gidan suka gaisa da mutan gidan, sannan ya fito ya zauna gaban Malam inda suka gaisa tare da ci gaba da hira. Malam yayi murna da zuwansu, sannan ya saka musu albarka. Sun jima suna hira suna ta bashi labarin makarantar. Daga bisani suka nufi gidansu Rabi'a, shida Mahmud. Yaro ya samu ya tura cewa, ana kiran Rabi'a. Bayan tafiyar yaron ne yace, bari mu gani tana fita da bananan. Ismail yace, kar kayi zargi. Rabi'a ba zata yi maka haka ba. Dan aiken ne ya katse su da cewa, wai ance tayi aure. "Aure?!" Mahmud ya tambaya cikin faduwar gaba. Ismail yace, ba kunyi waya ba? Mahmud cikin tashin hankali yace, ko jiya munyi waya, bazata kawai naso inyi mata, shiyasa bance mata muna hanya ba. Ismail yace kai yaro je kace inji Mahmud. Tare da dan aiken suka fito tayi murna sosai da ganin masoyinta. Tace ina zuwa. Duk da cewa dare ne, saida ta qara hoda a fuskarta sannan ta fesa turare mai madaidaicin qamshi, sannan ta dauki tabarma ta fito. Shikam Ismail, suna gaisawa daya lura masoyan suna dokin juna, sai yaga ya dace ya basu guri. Don haka sai yace, to ni zan tafi. Suka yi musabaha da juna. Ismail yana cewa, sai na shigo da safe. Zan shigo in kawo ma Malam tsarabarsa. Mahmud yace, shikenan Allah ya kaimu. Gidan yaya Amina zaka kwana? Ismail yace, a'a Gidanmu zanje in gyara dakina ynxunnan. sukayi bankwana ya wuce.
4⃣3⃣Gidansu ya koma, inda ya bude dakinsa, duk qura da yanar gizo-gizo. Ya kai qarfe goma sha biyu Tsakanin share-share da kuma goge-goge, sannan ya shiga gida yayi wanka. Sai daya kwanta sannan ya tuna cewa yayi masu yaya alqawarin cewa, zai koma. Ya kalli agogon wayarsa, a fili yace dare yayi. Washegari tunda ya dawo daga masallaci ya sake kwanciya bai farka ba sai qarfe takwas. Ya shiga cikin gida suka gaisa da mutan gidan. Sai dai yayi Mamakin ganin yadda suka sakar masa fuska. Amma sai ya tuna cewa fa yayin dawafin sa a dakin ka'aba, yayi ta roqon Allah cewa, Allah yasa shida 'yan uwansa da suke uba daya sun fahimci juna. A fili yace, Allah ya amshi addu'ar sa. Bayan yayo wanka ne, sannan ya ciro jakar kayansa tada, ya cire ma abbansu saddam kala biyu, sannan ya dauki sauran zuwa cikin gida yaba yayyinsa, sannan ya nufi gidan yaya Amina. Mimi ce amsa sallamarsa lokacin da ya isa gidan. Tana zaune akan qaramar kujera, tana wanke-wanke a bakin rijiya. CiKin Mamaki ya kalleta, tare da tausayi, yace, Mimi kece kk wanke-wanke? Ina Ummin? Ta dago ta kalleshi, "sunana khadija ne, ba Mimi ba. Ummi sunje makaranta, yaya kuma taje ganin likita. Ko dama tana nan ka san tana buqatar taimako. Ya tsugunna kusa da ita, qamshinsa ya daki hancinta, gabanta kuma ya shiga wata irin faduwa. Maganarsa tamkar rada yace, in taimaka miki ko? Ta dago ta dubeshi, wata irin kunyarsa ce ta ji ta kamata, sbd cikin idonsa ta kalla, ta sunne kanta cikin cinyarta. Tace, ka barshi kawai, "yaya ma za'ayi kayi aikin mata? Cikin kwaikwayon muryarta yace, ai nima na matanne, kinga kenan babu laifi don nayi aikinsu ko? Yadda yayi din, sai taji ya birgeta sosai. Tace, nikam ka barshi kawai. Ya miqe tare da fadin shikenan tunda bakison taimako. Ya koma kan galan din ruwa ya zauna. "ki gama muyi magana dake. Tace, to. Kallonta kawai yakeyi cikin tausayi da birgewa. Ta gama ta kife, ta kai kwandon mazauninsa, Sannan tasa ruwa ta wanke gurin. Tana sanye ne da doguwar riga, tun irin kayanta ne data zo dasu. A ransa yace, kaya masu tsada sunada qwari, dubi yadda har ynxun kayanta suke da kyansu. Zasu jima basu lalace ba. Ta dubeshi, sannan ta nufi dakinta.
[20/09 9:57 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa
4⃣4⃣Da kallo ya bita, yana tuno asalin Mimi 'yar gata, 'yar jin kai, yarinyar da batason talauci balle hulda da talaka. Matuqar tausayinta yakeyi ynxun. Sannan ya jinjina mata sosai, domin bai ta6a zaton zata sauko haka cikin sauri ba. Hakanan ya fahimci cewa halinta ne yin abinda tace zatayi. A fili yace, wannan ya zama dole in cika mata dukkan alqawuran dana daukar mata. Wata zuciyar tace, harda saki? Gabansa ya fadi, amma sai ya miqe ya nufi dakin. Tana kakka6e gado, ya shigo ciki. Yace, ina zan zauna? Ta nuna masa bakin gado, bayan ta gama gyarawa, ka zauna anan. Ya zauna, yana kallonta tare da ci gaba da tuno da gatan ta har ta gama. Aikin dai babu sauri, amma tsaf-tsaf. Ta kalleshi, in nace zanyi wanka zan 6ata maka lokaci ko? Yace, yi wankanki. Ta dauki hijabi ta saka sannan ta fita. Ta dauki ruwan wankanta da Ummi ta zuba mata, sbd bata iya jan ruwa a rijiya, tsoron rijiya gareta. Bayan fitarta ne yaga wani littafi akan Allon gadonta. Ya dauka ya Kalli bangon, INDA RAI, DA RABO. Haka yaga an rubuta ajikin littafin, sunan littafin shine yaja hankalinsa zuwa ga bude shafukan littafin yana dubawa jefi-jefi har ta fito. Lura da tayi baya kallonta, sai ta shafa manta a cikin hijabin, da tazo saka kaya ne ta kalleshi, a tunaninta hankalinsa yana kan littafin ne, sai ta faki idonsa ta saka kayan. Murmushi yayi, a ransa yace, khadija ke nan, domin tunda ta fito hankalinsa yana gurinta. Bayan ta gama tazo ta zauna a daya gefen gadon. Ya dubi littafin, menene ma'anar inda rai, da rabo? Ta danyi murmushi, bansan yaya zance maka ba, sbd ka san bansan kan hausa sosai ba. Kawai dai naji su yaya suna sauraron littafin ne a rediyo, shine nace, a siyomin. "wa ya siyo maki? Tace ban sani ba yaya ce tasa aka siyo. Yace, kin karanta? Ta daga kai, alamun eh. Kin qaru da wani abu? Tace, sosai ma, duk da cewa labarin soyayya ne. Yace, shikenan zaki bani labarin wani lokaci.
[21/09 3:17 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa
4⃣5⃣Ya aje littafin ya fuskance ta sosai, "ki bani hankalinki muyi magana mai muhimmanci. Ta sunkuyar da kai, "ina sauraronka" bata iya kallonshi, don sai taga yayi mata wani qwarjini, ya cika dakin, "zan fara da son sanin matsalarki, in kina da wata matsala. "tana wasa da hannunta, tace, ni banida wata matsala, domin duk abinda akaci, shi za'a babi daidai qarfinsu, kuma zuwa ynxun na iya cin komai. Kuma ba'a takura min, komai nakeso nayi, zanyi ba wulaqanci. In babu zan haqura kamar yadda kowa ya haqura, shine kawai. Yace, na fahimta, to kina son siyan wani abu, ko burin yin wani abu, ina nufin na kudi? Ta saci kallonsa, banison komai na kudi, don duk abinda nakeso na kudi, bakada qarfin saimin. Don haka kar ka damu, khadija ba mimin daka sani bace, Nayi haquri da iyayena ma bare wani abin duniya. Babu komai a raina. Babu abinda yake birgeni cikin duniya ynxun. Yace, har nayi zaton zaki koma makaranta, don ki kammala digiri dinki? Tace, baka zaton in na fita iyayena su samu labarina. Yace, har ynxun baki huce da fushi dasu ba? Tace, na huce tun bayan da bakanan yaya Amina tayi ta karantomin kurakuraina ta hanyar nasiha, har na fahimci irin sa6awar da nayiwa iyayena. Ynxun kam ina nesanta kaina dasu ne, sbd ganina kusa dasu zaita sakasu cikin 6acin rai, zasu dinga tuno abinda nayi musu. Shiyasa bana fita. Banida wani buri daya wuce cikawa da imani inje in tarar da khalil. Gaban Ismail yayi matuqar faduwa, domin bai zaci jin haka daga bakinta ba. Baisan lokacin daya ce, dama har ynxun baki manta da khalil ba? Da sauri ta kalleshi, ta yaya kk zaton zan manta da wanda yake matuqar sona? Wanda ke fadamin kalamai masu sani cikin farin ciki, da nishadi. Wanda ke kwadaita min wata irin rayuwa, amma kafin mukai gareta, sai mutuwa ta katse hakan. Ya barni cikin qunci da takaici! Kuka ya kufce mata.
4⃣6⃣Shiru yayi tamkar ruwa ya cinyeshi, nazarin zantukanta yakeyi. ya dan qara matsowa kusa da ita, ya tausasa muryarsa qwarai. "Yi haquri khadija, inda zaki bani labarin soyayyarku da khalil, zanso ji. Ta dubeshi, fuska cike da hawaye, ba zan iya ba. Banason in tuna da komai game da labarin. Abinda kawai ba zan manta ba shine tsananin son da khalil yayi min. Haka kuma ba zan manta da yadda nayi ta wulaqantashi ba. Salon son da khalil yake nunamin ta hanyar chatting dina a facebook, wtsapp, da sauran irin wadannan kafofin, tun bana bashi amsa, har dadin kalamansa suka sa na soma bashi amsa, duk da ni ba amsa mai dadi nake bashi ba. Ranar dana soma son khalil, yawun bakina na watsa masa fa a cikin mutane. Amma kasan me yayi? Ismail yace, a'a tace,, ga mamakina sai naga kurum yasa harshensa ya lashe yawuna daya sauka kan kafadarsa, sannan yayi murmushi, "komai naki inason sa. In na bari yawunki ya sauka a qasa nan, nayi muguwar asara. Ta soma sabon kuka, wannan kadan ne daga irin son da khalil yayi min. Ismail yace, shikenan kiyi haquri. Allah ya yafe masa tace Ameen. Yayi shiru. Yasan ynxun yaya Amina ta rage mashi hanya da tayi wannan jihadin, na yiwa mimi nasiha harta fahimci cewa tayiwa iyayenta laifi, ba zai wahalar shawo kanta don zuwa basu haquri ba. Amman wannan ba ynxun ba. Ya dubeta, har ynxun tana share hawaye. Nace kiyi haquri. Kuma zaki iya samun wanda yafi khalil sonki, kema kuma ki soshi fiye da son da kk yiwa khalil din. Ya girgiza kai, Da wuya hakan ta kasance, nina kulle babin so, koda na samu mai sona, ni kam na tabbata ba zan soshi ba. Ismail yayi murmushin yaqe, to yaya batun islamiyya fa? Mimi tace ina daukan karatuna a gurin yaya Amina. yayi dariya, shikenan Allah ya biyata da aljannarsa.
[21/09 7:46 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa
4⃣7⃣Ya miqe ya dauko jakar tsarabarsu, ya dawo ya zauna bakin gado, "zo ki za6i abinda kk so cikin tsarabata. Ta matso. Ya dauko jakar ya dora ta saman Gadon. Ya soma ciro jallabiya, pink mai ratsin baqi, sai jarta, itama mai ratsin baqi, sai takalma da riga da wando kala biyu, duk ire-iren wadanda take sawa. Ta tsaya tana kallonshi, sbd ta san tsadar kayan. Kafin tace wani abu, sai kurum taga ya ciro wani gwangwani a can qarshen jakar, ya miqo mata. Da sauri ta kar6a sbd irin turarenta ne. Ta soma karanta rubutun jiki a fili tace, "tabbas shine" ta dago ta dubeshi, "siyan turarennan kayi? Yace eh, siya miki nayi. Tace ina ka samu kudi haka? Na ga kai din dalibi ne, kuma duk kayan nan suna da tsada, musamman wannan turaren? Yayi murmushi, "munyi aikin raba abinci ne ga mabuqata aka biyamu. Ta soma hawaye, ban ta6a tunanin zan qara amfani da wannan turaren ba. Nagode sosai. Ya tausasa murya don jin dadin sake burgeta. Karki damu khadija, nayi miki alqawarin in Allah ya buda min, zanyi miki gatan da yafi wanda kk ta6a shiga a fannin jin dadi. Ta sa idanunta cikin nasa, "nasan zaka iya, domin duk abinda kayimin alqawari, ka cika. Ina ganin kimar ka sosai, ynxun saura abu daya ya rage. Ya zaro mata manyan idanunsa, me? Tayi shiru, gabanta yana faduwa. Yace karki damu ki fadamin, qila na manta ne. Ta sunkuyar da kai, "maganar rabuwarmu." Gabansa yayi wani mugun faduwa. Dakin yayi tsit na wasu daqiqai kamar hudu. Maimakon yaci gaba da zancen, sai kawai yace, yau yau dale kuka karya ne a gidan nan? Yunwa nakeji. Tace, ruwan Lipton ne da biredi. In zaka ci ina zaton akwai a flask. Yace zansha shayin, kinsan mu shine ma abin shanmu kowane lokaci. Ta miqe ta nufi kicin ya bita da kallo, tafiyarta ta dawo tamkar da, cikin nutsuwa da kamewa. Ta dauko filas din ta hado da kofi da cokali da kuma suga. Sai ledar bread din. Zuciyarta kuwa tambayar kanta takeyi menene dalilinsa na share zancen rabuwarsu? Yace, ba zanci bread ba. Na saba dana can da mukeci bashi da suga.
[9/21, 16:54] A~PROF: 4⃣8⃣Ya miqe ya janyo jakarsa, ya zuba wani ganyen tea, ya zauna yana sha. Duk sukayi shiru, kowa da kalar tunaninsa. Shi ba wai ba zai iya sakinta bane, amma tsoron sa kar ya saketa, ta sake guduwa. Ta katse masa tunani, "Wai meyasa ka share batun da kawo? Ya kalleta, "ba sharewa nayi ba. Khadija muna buqatar qarin lokaci ne. Kiyi haquri har in kammala karatu na." Tace, zuwa yaushe? Ya dubeta da sauri, "kin samu wanda kk so ne? Itama cikin sauri ta kalleshi, "Allah ya kiyaye min, ni kam banason kowa. Nauyin ne nikeson a sauke min. Yayi murmushi baice komaiba. Sati biyun da Ismail sukayi a Nigeria sunyisu ne a cikin hidimar bikin Mahmud. Babu yadda baiyi da Mimi ba akan taje gurin walimar bikin, amma taqi, dolensa ya haqura ya barta. Bayan kwana biyu da kammala bikin, suka soma shirin komawa madina. Ango da Amarya cikin dokin juna a ranar tafiyar, ko cikin jirgi tamkar su hadiye juna suna ta birge Ismail, wanda ya lumshe ido yana tuno hawayen Mimi da suke zuba lokacin da sukeyin sallama. Ya tuna tambayar da yayi mata. Khadija wannan kukan kuma na menene? Ta girgiza kai, "nila ban san ko na menene ba. Ya ciro kyakkyawan hankici daga aljihunsa, sai qamshi yakeyi. "share hawayenki da wannan, sai in munyi waya kenan ko? Ya sauke ajiyar zuciya, tare da furzar da wani huci mai zafi. Yana kewar rabuwa da yarinyar. Yayi ta tuna huldarsuda kuma irin CANJIN RAYUWAR da Allah ya saukar mata. Allah yasa ya zama sanadin shiriyarta kenan. Labarin data bashi na tsohon saurayinta, abinda ya fahimta da Mimi, ita mutum ce maison aso ta, aji da ita, a nuna mata tsantsan so a fili, sannan a fada mata kalaman tada hankali. A fili ya furta cewa ban iya wannan ba. Sai kuma Zainabu ta fado masa, ya tuna da zancan su da yaya Amina bisa ganin da yayi mata. Yaya tace, masa tana gidan mijinta, qila dai tazo duba su ne. Haka yayi ta tunane-tunane har Allah ya kaisu lfy.
[9/21, 17:35] A~PROF: Satin su Ismail daya da tafiya, yaya Amina ta haifi 'yarta mace, aka sa mata Aishatu. Yaya tasha mamakin ganin 'yan uwanta mata yadda suka zo mata barka harda suna, sa6anin da ba kowa ke zuwa mata barka ba bare suna. Inna kuwa zuwanta uku. Mimi kam ta takura sosai ranar suna, domin sam batason jama'a, kamar ta bar gidan amma ba yadda zatayi, dole ta haqura.
[22/09 11:26 am] Inna👬👫: Canjin rayuwa
4⃣9⃣Lokaci yana qhudewa kwanaki quna qarewa, yau gashi su Na'ima anyi arba'in. Ta